Polly po-cket
Uzairu badamasi

BARKA DA ZUWA SHAFI MAI ALBARKA

Alhamdulillah muna muku albishir insha Allah zamu dawo aiki gadan gadan!


Shafin farko

Haidar Ali

AIKIN HAJJI A MAHANGAR JAGORAN JUYIN JUYA HALIN MUSULUNCI

Ali Khamenei5


KEBANTATTUN SIFFOFI NA AIKIN HAJJI


Masaniya Kyautar Farko Ta Hajj

Duk da cewa albarkar da ke cikin aikin hajji, lamari ne da ke shafan dukkanin bangarorin rayuwar dan’adam sannan kuma irin wannan ruwa na rahama da ba za a iya kawar da shi ba, da ya hada tun daga kebantuwa ta zuciya da tunanin dan’adam har zuwa fagen siyasa da zamantakewa da karfi na kasa na musulmi da kuma hadin gwuiwa da aiki kafada da kafada tsakanin al’ummomin musulmi, lamari ne da ke samar da ci gaba da kuma karfi da kumaji. To sai dai watakila ana iya cewa mabudin dukkanin wadannan abubuwa, shi ne ‘masaniyar Ubangiji’. Sannan kuma kyautar farko ta aikin hajji ga mutumin da yake son bude idanuwansa da gaskiya sannan kuma ya amfanu da karfi na Ubangiji ‘na fahimta’, ita ce dai wannan masaniya maras tamka wacce idan ba a aikin hajji ba da wuya da dama daga cikin musulmi suke samunta, sannan kuma babu wani aiki ko ibada ta addini da za ta iya kawo wa al'ummar musulmi irin wadannan ilimi da masanaiya da ake samu a lokacin aikin hajji a lokaci guda.

Aikin Hajji Alama Ta Al’ummar Musulmi

Isowar ranakun aikin hajj, a dukkanin shekaru, tana tare ne da irin wannan shauki da kauna ta zuciya da take cikin kishirwa a dukkanin duniyar musulmi wadanda suka taru a jikin dakin Abin bauta da ginin abin kauna da kuma damfaruwa da wannan fagen bauta da neman kusanci a kan kasar wannan wajen. Ku gudanar da sannanun ranaku karkashin inuwar zikiri da albarkoki sannan kuma ku kasance cikin kariya da rahama da gafarar Allah Madaukakin Sarki Mai rahama. ‘Yan’uwan da suka zo daga nesa za su ga dukkanin kusurwoyin duniya guda hudu sannan kuma su ji irin karfi da girman da al’ummar musulmi suke da shi cikin rayayyen misali wanda ake ganinsa a fili.
Aikin hajji, alama ce ta al’ummar musulmi sannan kuma mai karantar da nau'i na mu’amala ta rayuwa wanda wajibi ne wannan al’umma ta rike shi wajen tabbatar da sa’adarta. Ana iya takaita aikin hajji cikin yunkuri da ke cike da manufa wanda kuma a ka yi shi ido bude da kuma nau’oi daban-daban zuwa ga kusurwa guda. Igiyar wannan yunkuri ita ce ambaton Allah da kuma hadin kai da taimakekeniyan bayin Allah, sannan kuma manufar hakan ita ce samar da karfafaffiyar cibiya ta ababen da suke kusata mutum da Ubangiji wajen tabbatar da rayuwar da take cike da sa’ada ga mutum: “Allah Ya sanya Ka’aba, Daki Tsararre, ma’aunin addini ga mutane, kuma Ya sanya wata mai alfarma da hadaya da ratayoyin hadaya” (Suratul Ma’ida 5:97)

Kebantattun Siffofi Na Musamman

Duk da cewa sirri da alamun aikin hajji sun wuce abin da za a iya rubutawa cikin wani rahoto da za a shirya, to sai dai a cikin hakan, duk wani idanun da ke iya ganin sirri, to kuwa a ganin farko zai iya ganin irin wadannan kebantattun siffofi na musamman: na farko shi ne cewa aikin hajji wani farilla ce na gaba daya da Allah Madaukakin Sarki Ya kirayi dukkanin musulmi wadanda suke da iko daga cikinsu daga dukkanin fadin duniya na su zo su kasance a wajen wannan Daki da kuma wadannan wajajen ibada zuwa ga wani waje guda cikin wasu sannanun ranaku, sannan kuma ta hanyar kokari iri guda da motsawa da zama da tashi (iri daya), hakan yana hada su waje guda: “Sa’an nan kuma ku malalo daga inda mutane suke malalowa. Kuma nemi gafara ga Allah. Lalle Allah Mai gafara ne, Mai jin kai” (Suratul Bakara 2:199)

Aiki Tare Na Kasa Da Kuma Na Kasa Da Kasa

A lokacin da wani sashe na wata al'umma, ta nufi wani waje sannan kuma ta yi wata tafiya zuwa wani waje tattare da wata manufa tsararriya ta tafi ta dawo, to a dabi'ance irin aiki tare da kusacin juna da ke tsakaninsu za su karu sannan kuma yanayin ababen da suke karfafa ruhi da kyawawan halayensu na kasa zai karu da kuma samun daukaka. Sannan baya da wadannan abubuwa, lamari ne na kasa da kasa; don kuwa al'ummomi daban-daban, duk da irin ababen tarayyar da suke da su har ila yau kuma suna da wasu abubuwa da suke da bambanci cikin su a tsakaninsu wadanda suke rarraba su sannan kuma a wasu lokuta hakan ma ya kan haifar da rashin jituwa a tsakaninsu. To aikin hajji yana iya zama abin da zai rage irin kaifin wadannan bambance-bambance da ake da su da kuma tabbatar da wadannan bangarori da aka yi tarayya cikinsu tsakanin al'ummomi daban-daban. A saboda haka mu dai ba mu da wani aiki (ibada) na wajibi da yake da irin wadannan bangarori.

Magance Matsalolin Al'ummar Musulmi

Allah Mai hikima da daukaka wanda Ya cancanci godiya daga wajen bayinSa, Ya kiraye su zuwa ga taruwa a Dakinsa sannan kuma ya dora wa ManzonSa nauyin kira zuwa ga aikin hajj; ya sanya aminci a fagen Daki (Ka'aba) da kuma kawar da gumakan jahiliyya sannan kuma ya sanya shi ya zamanto wajen dawafin muminai da wadanda suke nesa, sannan kuma wata alama ta jama’a, daukaka da kuma taruwa ta al’umma. Dakin Allah, wanda masu kula da Ka’aba da masu dawafi da sa’ayi a lokacin jahiliyyar farko suka mayar da shi wata kasuwa ta tijara da mulkinsu, da amfani da shi kayan amfaninsu daga wajen mutane; (Allah) ya daidaita shi tsakanin wadanda suka zo daga nesa da wadanda suke wajen; ya sanya aikin hajji ya zamanto wata alama ta hadin kai da daukakar musulmi da kuma hadin gwuiwa da aiki kafada da kafada a tsakaninsu sannan kuma ya lalata da dama daga cikin bala'oi da matsalolin daidaiku da kuma al'ummar musulmi suke fuskanta sakamakon nesantar tushe da asalinsu da suka yi; irin su akidar jin cewa ‘yan kasashen waje wani abu ne da mantawa da irin kwarewar da ake da ita da yarda da tarkon da aka dana da gafala daga Allah da zama fursunoni a hannun ma'abota duniya da mummunan kallo ga 'yan'uwa da sauraren maganganun makiya dangane da su da kuma rashin nuna damuwa da makomar al'ummar musulmi, kai da ma rashin sanin wani abu mai suna al'ummar musulmi, da nuna halin ko in kula da abin da ke gudana a sauran garuruwa da kasashe na musulmi da nuna rashin kula da halin ko in kula da irin makircin makiya Musulunci da musulmi, da kuma irin manya cututtuka masu halakarwa wadanda tsawon tarihin Musulunci suke barazana ga al'ummar musulmi sakamakon samun ikon wadanda ba su dace ba da kuma rashin masaniyar Ubangiji cikin rayuwa ta siyasa da kuma makomar al'ummar musulmi. Sannan kuma a karnoni na karshe-karshen nan sakamakon kasantuwar karfi na 'yan mulkin mallaka na 'yan kasashen waje a wannan yankin da kuma 'yan amshin shatansu lalatattu masu bauta wa duniya, wadanda suka zamanto babbar annoba ga al'umma.

Kasantuwa Mai Ma'ana

A hakikanin gaskiya wajibi ne kasantuwar musulmi a lokacin aikin hajji ta zamanto wata kasantuwa ce mai ma'ana, idan kuwa ba haka, to idan dai har lamarin ya zamanto ya takaita ne kawai da bangare na addini da ambaton Allah to ai mutum yana iya zama a gidansa ma ya yi ta ambaton Allah. Dalilin da ya sa aka ce (musulmi) su taru a wani waje guda saboda wannan dalili ne. Saboda amfanin da musulmi za su gani a lokacin aiki hajj. Na'am aikin hajji zai iya samar da sauyi na cikin zuciya tsakanin daidaikun musulmi sannan kuma ya samar da ruhin kadaita Ubangiji da kyautata alaka da Ubangiji da kuma dogaro da shi haka nan kuma zai iya hado jikkunan al'ummar musulmi da suka rarrabu waje guda da kuma samar da wani karfi mai iya aiwatar da wani abu. Zai iya sanya su su san junansu sannan kuma su saurari maganganun juna da irin ci gaban da suke da shi da kuma bukatun da suke da shi sannan kuma su yi musayen irin kwarewar da suke da ita. A fili ana iya cewa matukar dai aka yi kokarin amfanuwa da wannan takalifi na Musulunci yadda ya dace, to kuwa bayan wani lokaci wanda ba mai tsawo ba, al'ummar musulmi za ta iya isa ga daukaka da kuma karfin da take da shi.
Aikin hajji a zatinsa yana da wasu abubuwa na asali guda biyu, su ne: kusaci da Allah cikin tunani da aiki, da kuma nesantar dagutai da shaidan da jiki da rai. Dukkanin ayyuka da abubuwan da aka hana a yayin aikin hajji, saboda cimma wadannan abubuwa guda biyu ne da kuma wajen tabbatar da su, wanda hakan yana a matsayin takaitaccen abin da Musulunci da dukkanin sakonnin Ubangiji suka kumsa ne.


BANGARORIN KYAUTATA RUHIN MUTUM NA HAJJI

Ladubban Hajji

Wadanne irin gafalallun mutane ne mutanen da suke rage kimar aikin hajji, da ranakun hajji da ayyukan aikin hajji ta hanyar mai da hankali akan abin duniya. Dole ne aikin hajji ya zamana an yi shi cikin sanin abin da ake yi da kuma nutsuwa da ladabi. Bayan ayyukan ibada na hajji da wadanda su ne suka hadu suka yi aikin haji, kuma shi aiki ne da yake da ladabi wanda kuma shi ne ruhin hajji. Wasu suna yin wadannan ayyukan, amma suna gafala daga barin ruhi da hakikaninsa. Ladubban hajji su ne kaskantar da kai a gaban Ubangiji da kuma ambatonsa. Ladubban hajji su ne jin cewa a gaban Ubangiji ake. Ladubban hajji su ne samun mafakar da muminai masu riko da yin tawassuli da hallarar Ubangiji suke yi. Dole ne a fahimci wannan Aljannar a kuma shige ta; dole ne a yi wa aikin hajji irin wannan fahimta. Ladabin hajji shi ne zaman lafiya da sauki. A lokacin aikin hajji an hana yin rikici da muminai da fada da ‘yan'uwa da yin fasikanci da jayayya. Ladabin aikin haji shi ne nutsewa a cikin hakikar ma'anar hajji da kuma amfanuwa da shi a tsawon rayuwa baki daya. Labadin aikin hajji shi ne ‘yan'uwantaka da samar da kauna da hadin kai. A lokacin aikin hajji ne kadai ake samun damar tabbatar da hadin kai a tsakanin dukkan al'ummar musulmi. Wadannan al'ummun da suke zuwa daga kowace kusurwa ta duniya saboda kaunar Ka'aba da kaunar hubbaren Annabi da kaunar ambaton Ubangiji da yin dawafi da sa'ayi; wannan dama ce da za a yi amfani da ita domin kulla ‘yan'uwantaka.

Kwarewa Ta Addini

Ga shi kansa mutum, damar hajji, wata dama ce ta shiga fage na addini da abubuwan da suke kusata mutum da Ubangiji; ya kan fitar da kansa ne daga cikin irin rayuwarsa da ya saba da ita wacce take cike da irin wadannan ababe masu gurbatawa da kuma dukkanin wadannan matsaloli da kuma kai shi zuwa ga wani yanayi na tsarki da ababen da suke kusata mutum zuwa ga Allah da zabin kansa. Daga lokacin da kuka shiga cikin wadannan ayyuka na hajji, abubuwan da suke halal ne a sauran lokuta na rayuwa, to a wajenku haramun ne; daura harami yana nufin haramta wasu abubuwa ne a kanku wadanda a sauran lokuta na rayuwa da aka saba da ita halal ne; sannan da dama daga cikin wadannan abubuwa ma dai suna sanya gafala ne, wasu kuma suna haifar da faduwa da lalacewar mutum ne.
'Yantar da kai daga dukkanin kazamta ta abin duniya a dukkanin wajaje da kuma cikin dukkanin ayyuka shi ne ganin Ubangiji, ko da kuwa a cikin 'yan wasu ranaku ne, hakan kuwa babban guzuri ne ga dan'adam. Dukkanin ladubba da ayyukan hajji an samar da su ne saboda alhaji ya samu damar samun wannan kwarewa ta ruhi sannan kuma ya samu jin wannan dadi. Ababen da ke karfafa ruhi da suke cikin aikin hajji, shi ne dai wannan zikiri da ambaton Allah saboda an tara ruhi ne a wani waje cikin ayyukan hajji. Wajibi ne wannan mabubbuga mai albarka ta ci gaba da wanzuwa hatta bayan gama aikin hajji sannan kuma a ci gaba da wannan nasara da aka samu.

Nesantar Alamun Alfahari

Ana karbe dukkanin ababen da suke sanya alfahari na zahiri na abin duniya daga gare mu; na farkonsu shi ne tufafi. Mukamai da darajoji da tufafi da tufafin alfahari da dukkanin wadannan abubuwa za su koma gefe, kowa da kowa zai kasance ne cikin tufafi iri guda. Kada ku kulli madubi wanda wani bangare ne na son kai da girma kai. Kada ku yi amfani da ababe masu kamshi (turare) wanda abu ne na shiga tsakani. Kada ku gudu daga rana ko kuma ruwan sama, kada ku yi tafiya karkashin wani rufi – a lokacin da kuke tafiya – wanda hakan wani abu ne da ke nuni da son sauki da son jin dadi; haka nan sauran ayyukan haramai suke, haramta wa kai abubuwa da suke samar da jin dadi da sha’awace-sha’awace na rai, an haramta jin dadi na jima'i a wannan lokacin; dukkanin abubuwan yin alfahari, dukkanin abubuwan da suke nuna bambanci. Za a kawar da dukkan wadannan abubuwan.


Damar Gina Kai

Matakin farko ga alhazai shi ne gina kansu. Sanya ihrami da dawafi da salla, mash’ar da Arafa da Mina, hadaya da jifa da aski, dukkanin wadannan ayyuka, wata alama ce ta kankan da kai da tawali’u na mutum a gaban Allah Madaukakin Sarki sannan kuma wadansu wajaje ne na zikiri da kankan da kai da neman kusaci da shi. Bai kamata ku gudanar da wadannan ayyuka masu cike da ma’ana cikin gafala ba. Wajibi ne matafiyi zuwa kasar aikin hajji, tsawon dukkanin wannan lokaci na gudanar da ayyukan hajjin, ya ji cewa lalle yana gaban Allah Madaukakin Sarki ne, cikin wadannan miliyoyin mutane wajibi ne ya ji cewa shi kadai ne a gaban Abin kauna (Allah) ya gabatar masa da bukatunsa, ya bukata daga wajensa sannan kuma ya mika masa zuciyarsa, ya fitar da Shaidan da soyace-soyacen zuciyarsa daga cikin zuciyarsa, kamar yadda yadda kuma ya fitar da tsatsar handama da hassada da tsoro da sha’awa daga cikinsa. Ya gode wa Allah Madaukakin Sarki saboda shiriya da ni’imarsa, ya sanya zuciyarsa a bisa tafarkin jihadi saboda Allah, ya kasance mai tausayawa ga muminai da kuma rashin sassauci ga makiya da masu fada da gaskiya. Ya karfafa azamar da yake da ita wajen tabbatar da maslaharsa da kuma maslahar duniyar musulmi, sannan kuma ya kulla alkawari da Ubangijinsa wajen kyautata duniya da lahira.
Aikin hajji wata babbar dama ce ta gabatar da wadannan gaskiya da makamantanta masu yawan gaske – wanda mu al’ummar musulmi na Iran muka same su albarkacin masaniyar Musulunci da shiriya ta Musulunci – ga sauran al’ummomin duniya sannan kuma a farkar da su. Da dama daga cikin zukatan al’ummar musulmi na duniya a farke suke; wajibi ne su ji cewa suna da magoya baya a dukkanin fadin duniyar musulmi don su sami damar samun jaruntaka da karfin gwuiwan da ake bukata. Dukkanin wadannan abubuwa suna karkashin inuwar aikin hajji ne, don haka kada ku gafala daga ma’anawiyya ta hajji da kuma amfanuwa da ma’anoni masu girma kuma na koli da suke cikin addu’oi da ziyarori da ayoyin Alkur’ani mai girma.


Ibada Don Kawar Da Gafala

Damar da ke cikin aikin hajj, wata dama ce maras tamka. Dukkanin ibadu, wata dama ce ta dubi cikin ran shi kansa mutum. Mutane sakamakon gafala da Allah Madaukakin Sarki – wanda shi ne samuwa da ruhi na hakika – su kan gafala daga kansu, daga zuciyarsu da kuma hakikaninsu; “suka manta Allah, sai ya mantar da su kawukansu” A yau babbar matsalar bil’adama ita ce wannan. Mutane sakamakon gafala da Allah Madaukakin Sarki da suka yi sai suka gafala da kansu. Bukatun mutum, hakikani na mutum da kuma manufar halittan mutum cikin juye-juye na rayuwa ake mantawa da su. Abin da yake tunatar da mutum Ubangiji da kuma karkashin kulawa ta Ubangiji da kuma irin bukata da hakika da kuma bukatun da yake da su, su ne addu’a da ibada da kankan da kai a gaban Allah Madaukakin Sarki. A saboda haka aikin hajji ya zamanto mafi girma da daukakan ibadu a wannan bangaren; saboda a la’akari na lokaci da kuma la’akari na wuri da kuma la’akari na irin abubuwan da aka ba wa alhaji da kuma mai gudanar da ayyukan hajji, to wata ibada ce maras tamka. A saboda haka garin Makka da aikin hajj suka zamanto wasu abubuwa na tabbatar da tsaro ga dan’adam. Mutum, ta hanyar kankan da kai, tuna Allah da tawali’u da kuma nitsewa cikin tuna Allah, a cikin wannan buki mai girma da kuma ban mamaki, lalle a cikin zuciyarsa yana jin wani irin lamuni da kuma tsaro; wannan shi ne mafi girman bukatar mutum. Bala’in da manyan kasashen duniya masu karfi da kuma manufa ta duniya suka samar a kan mutum. Mutum ta hanyar fakewa da aikin hajji da kuma Musulunci yana iya samar wa kansa da aljanna da jin dadi a wannan wajen da kuma a wannan lokacin.
Na’am, aikin hajj ibada ce da zikiri da addu’a da istigfari; to amma ibada da zikiri da istigfari wajen samar da rayuwa mai dadi ga al’ummar musulmi da tseratar da su daga sarkoki da wahalhalu na bauta da mulkin kama karya da sanya musu ruhin daukaka da girma da kuma kawar da kasala da rashin kuzari. Wannan shi ne alhajin da ya tafi bisa asasi na addini da Amirul Muminin Ali (amincin Allah ya tabbata a gare shi) cikin Nahjul Balaga ya bayyana hakan a matsayin tutar Musulunci da jihadi sannan kuma abu mai kawar da talauci da rashi sannan kuma abin da ke kusatar da ma’abota addini da junansu.

Hajjin Annabi Ibrahim

Hajji irin na Annabi Ibrahim, shi ne cewa a wannan (irin hajjin) musulmi maimakon rarrabuwa za su yi tafiya ne cikin hadin kai, sannan kuma Dakin Ka’aba wanda gini ne da ke tabbatar da tauhidi sannan kuma alama ce ta bara’a da nesantar shirka da bautan gumaka, da irin wannan masaniya da kuma wannan ma’ana ce za su yi dawafi a zagayensa sannan kuma daga zahiri su isa zuwa ga badini da ruhin wannan aiki….sannan kuma su yi amfani da hakan wajen yin guzuri ga rayuwarsu da kuma rayuwar al’ummar musulmi.
Hajjin annabi Ibrahim shi ne dai wannan hajji na (annabi) Muhammadu, wanda a cikinsa akwai yunkuri zuwa ga tafarkin tauhidi da hadin kai, ruhi da kuma mafarin dukkanin bukukuwa da alamu (na addini), aikin hajji wata mabubbuga ce ta albarka da shiriya da tushe na asali cikin rayuwa da yunkurin al'umma guda, aikin hajji cike ya ke da amfani da kuma ambaton Allah, aikin hajjin da a cikinsa al'ummomin musulmi, za su ji samuwar al'ummar Annabi Muhammadu (tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi da Alayensa) da kuma kasantuwarsu, sannan kuma ta hanyar jin shu'urin 'yan'uwantaka da kusancin al'ummomi, za su yi watsi da shu'urin jin rauni da gajiyawa da kuma jin shan kashi. Hajjin annabi Ibrahim shi ne hajjin da a cikinsa musulmi suke watsi da rarrabuwa da kuma yunkurawa gaba daya.

Tafiya Tare Da Jiki Da Rayi

Aikin hajji ba wata tafiya ba ce ta jin dadi, aikin hajji wata tafiya ce ta neman kusaci da Allah. Tafiya zuwa ga Allah ce da jiki da rai; dukkaninsu biyu. Tafiya zuwa ga Allah ga ma'abota neman kusaci da Allah, ba tafiya ce ta jiki ba, tafiya ce ta zuciya da ruhi. A nan ga dukkaninmu mutane wannan tafiya zuwa ga Allah ta jiki da rai ne dukkaninsu biyu. To mu dauki jiki zuwa wancan wajen; hakan dai bai yiyu ba. Ko kuma abin Allah ya kiyaye a samu wasu mutane sakamakon jaddada wannan ni'imar – wato a lokuta daban-daban sun sami nasarar tafiya aikin hajj, don su ziyarci Allah – a sannu a hankali hajji ya zamanto musu wani lamari maras muhimmanci sannan kuma ya zamanto bai samu damar samun irin wannan haske ba. Wannan ba abu ne mai kyau ba.
Aikin hajj cikin zatinsa da yanayinsa yana da wasu tushe guda biyu na asasi: kusaci da Allah cikin tunani da aiki, da kuma nesantar dagutu da shaidan da jiki da rai. Dukkanin ayyukan hajji da abubuwan da aka haramta aikata su, an yi hakan ne saboda wadannan abubuwa guda biyu ne da kuma kama hanya wajen lamunce abubuwan da suke tabbatar da su. A hakikanin gaskiya hakan wani takaitaccen bayani na Musulunci da kuma dukkanin kiraye-kiraye na Ubangiji ne.


MANUFA TA GABA DAYA TA AIKIN HAJJI

Dubi Cikin Batutuwa Masu Muhimmanci Na Duniyar Musulmi

Batu mai muhimmanci da alhazan Dakin Allah ya kamata su dauke shi a matsayin wani bangare na manufar aikin hajj sannan kuma su aikata hakan, shi ne batutuwa masu muhimmanci da ke gudana a duniyar musulmi. Idan har aikin hajji ya zamanto wani taro ne mai girma na shekara-shekara na musulmi a duk fadin duniya, to kuwa ko shakka babu abin da ya fi dacewa ya zamanto abin kula a yayin wannan taron su ne muhimman abubuwan da suka shafi musulmi a halin da ake ciki a dukkanin yankuna na duniya. A cikin farfagandar ma'abota girman kan duniya a kan gabatar da wadannan abubuwa ne ta yadda babu wani darasi ko kwarewa ko fata ga musulmin duniya da za samu a duk inda suke, ko kuma idan a cikin wadannan abubuwa aka yi kokarin mummunan amfani da shi cikin ayyukan ma'abota girman kai, ba za a iya tona musu asirinsu ba, ko kuma gaba daya ma ba za a gabatar da hakan ba. Aikin hajji wani waje ne da ya zama wajibi a tona asirin irin wannan ha'inci na farfaganda, sannan kuma hakika ta fito fili kuma a samar da fagen da al'ummar musulmi za su sami farkawa da kuma fadaka.
Wani mutum ne da ke cikin kishirwa amma zai sha daga wannan idanuwar ruwa ta alkautharar (annabi) Muhammadu (tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi da alayensa) da kuma irin kumaji na Husaini, sannan kuma har ya zuwa yanzu ya zamanto yana da shakku da rashin fahimta cikin bangaren siyasa da ke cikin aikin hajji? Hajjin da babu bara'a a cikinsa, hajjin da babu hadin kai a cikinsa, hajjin da babu motsi da yunkurawa a cikinsa, hajjin da ba shi da barazana ga kafirci da shirka a cikinsa, to wannan ba aikin hajji ba ne sannan kuma ya rasa ruhi da ma'anar aikin hajji.

Hadin Kan Musulmi Da Tsoron Ma'abota Girman Kai

Daya daga cikin mafiya girma manufofin aikin hajji zuwa dakin Allah shi ne cewa al'ummar musulmi su kusaci junansu. Dalilin da ya sanya Allah Madaukakin Sarki ya ke fadin cewa: "Kuma ka yi yekuwa ga mutane da wajibcin Hajji za su je maka suna masu tafiya da kafafunsu da kuma a kan rakuma suna masu zuwa daga ko wane lungu mai zurfi." dukkanin al'ummar musulmi a wadansu ranaku ayyanannu sannan kuma a wani waje na musamman irin su Arafa da Mash'ar da Minna da Masjid al-Haram suke taruwa; da wani dalili ne ya sanya wadannan mutane (makiya) suke tsananin tsoron taruwar al'ummar musulmi waje guda? Batun shi ne cewa hadin kan al'ummar musulmi da kuma kalma guda da kuma tunani iri guda a wajen ma'abota girman kai musamman Amurka azzaluma da kayayyakin aikinta da cibiyoyin masu mulki na duniya, abu ne mai hatsarin gaske. Wannan wata hakika ne wacce a lokuta da dama marigayi Imam Khumaini (r.a) ya yi bayaninta.

Sakon Tauhidi Da Hadin Kai

Aikin hajji ya zo ne saboda tabbatar da kusanci da juna da kuma kalma guda ta al’ummar musulmi a duk fadin duniya. Tushen da ke hada dukkanin wadannan zukata waje guda shi ne dai wannan sako wanda a karon farko ya fito daga wannan wajen sannan kuma ya yadu zuwa dukkanin fadin duniya tsawon tarihi: wato wannan sako na tauhidi da hadin kai; kadaita Allah da hadin kai tsakanin al'ummar musulmi. Tauhidi yana nufin kore allantakan dawagitai da ma'abota girman kai da tursasawar masu son amfani da karfi, sannan kuma hadin kai mazhari ne na daukaka da tsayin dakan al'ummar musulmi. Aikin hajji, sama da dukkanin wani rubutu da kuma wata magana, ya fi gabatar da wannan sako madawwami a kowace shekara cikin al'ummomi sannan da kuma isar da shi zuwa ga dukkanin duniya. Duk wani musulmi a duk inda ya ke a duniyar musulmi, a lokacin aikin hajji, wajibi ne a wannan karon ma su fahimci wannan hakika (ta cewa) a karkashin inuwar wadannan abubuwa biyu ne za a iya tabbatar da ci gaba da kuma daukaka ta dukkan bangarori na kasashen musulmi, wato: tauhidi da dukkanin bangarorinsa na daidaiku da jama'a da kuma siyasa, sai kuma hadin kai da ma'anarsa ta hakika wanda kuma za a iya tabbatar da ita a duniyarmu ta yau.

Manufofi Na Gaba Daya Na Aikin Hajj

Kama daga zikiri da kasantuwa ta ma'anawiyya da kuma fahimtar kai da wani mutum musulmi zai yi a lokacin kadaitaka da Allah da kuma wanke zuciya daga tsatsan zunubi da gafala, har zuwa ga jin kasantuwa ta mutum a cikin al'umma da kuma hadin kan dukkanin musulmi da sauran al'ummar musulmi da kuma jin shu'urin tsayin daka na kasa da ya samo asali daga girma da daukakar al'ummar musulmi da kuma kokari kowane mutum wajen samun maganin cututtuka na ruhi wato zunubai, har zuwa ga kokari da himma wajen fahimta da kuma maganin cututtukan da al'ummar musulmi suke fama da su, da kuma tausayawa al'ummar musulmi, wato matsalolin da wannan al'umma mai girma take da su, dukkanin wadannan abubuwa suna cikin aikin hajji da kuma ayyukan da ake yi a lokacin wannan bukin ne.

Nesantar Manufa

Wajibi ne cikin bakin ciki a yarda da cewa lalle akwai tazara mai yawan gaske tsakanin irin yadda ake gudanar da wannan farilla ta Ubangiji da kuma yadda ya kamata a gudanar da ita din. Marigayi Imam Khumaini (r.a) ya gudanar da gagarumin kokari mai tasirin gaske a wannan bangaren sannan kuma ya gabatar wa al'umma irin yanayin yadda hajjin annabi Ibrahim, hajji da ke kawo daukaka da girma da kuma gina mutum ya ke a gaban dukkanin al'ummar musulmi, wanda gwargwadon wannan din ma da aka gabatar ya zamanto mai albarka a duniyar musulmi. To sai dai duk da irin wannan yaduwa, irin wannan tunani da irin wannan yanayin aiki cikin dukkanin al'ummar musulmi yana bukatar kokari tsakani da Allah na malaman addini da mahanga mai kyau da taimakon 'yan siyasan dukkanin kasashen duniyar musulmi, sannan kuma fatan da ake da shi shi ne cewa wannan gagarumin nauyi na asasi ya zamanto abin lura da ba da kulawarsu.


AIKIN HAJJI ABU NE DAKE TABBATAR DA HADIN KAI

Girman Jin Shu'urin Hadin Kai

Aikin hajji wani lamari ne da ke tabbatar da hadin kai da aiki kafada da kafada tsakanin al'ummar musulmi. Dalilin da ya sanya Allah Madaukakin Sarki Ya kirayi dukkanin musulmi da dukkanin wanda zai iya (gudanar da wannan aiki na hajj), zuwa ga wani waje na musamman sannan kuma a lokaci na musamman, sannan kuma cikin wani irin motsi da yunkurawa da ke nuni da tafiya tare da rayuwa tare a dare da rana da junansu. Tasirin farko na irin wannan lamari shi ne sanya jin shu’urin hadin kai da aiki na jama’a cikin kowanne guda daga cikinsu da kuma nuna irin shaukin zama waje guda da musulmi suke da shi da kuma haifar da daukaka da girma cikin zukatansu. Da irin jin wannan girma ne zai sanya hatta musulmin da ya ke rayuwa a kan koluluwar dutse, ba zai ci cewa shi kadai yake rayuwa ba. Ta hanyar jin irin wannan shu’uri na wannan hakika ne musulmi a duk inda suke cikin kasar musulmi, ba za a iya kwace musu irin wannan jaruntaka na fada da sansanin masu adawa da Musulunci, wato wadannan masu mulki na siyasa, tattalin arziki na duniya da ‘yan jari hujja masu haifar da irin wadannan fitina da suke faruwa da kuma wulakantarwa – wanda shi ne makamin farko na ‘yan mulkin mallakan yammaci wajen fuskantar al’ummomin da suka kai musu -. Ta hanyar jin irin wannan shu’uri na girma da daukaka ne gwamnatocin musulmi, ta hanyar dogaro da al’ummominsu, za su ji cewa ba sa da wata bukata ta neman taimako da fakewa da ma’abota karfi na kasashen waje, sannan kuma ba za a sami irin wannan gagarumar tazara da ke cike da musiba tsakanin al’ummomin musulmi da mahukunta ba. Ta hanyar jin wannan shu’uri na hadin kai da aiki na jama’a ne irin wannan tarko na mulkin mallakan jiya da yau – wato rayar da irin ra’ayin nan na ‘yan kasanci na wuce haddi – zai zamanto ba zai iya haifar da irin wannan tazara mai girman gaske tsakanin musulmi ba, sannan kuma kabilanci na larabci da farisanci da turkanci da na nahiyar Afirka da Asiya maimakon su zamanto masu gasa da adawa da hadin kai na Musulunci, za su zamanto wani bangare ne nasa sannan kuma mai kokari wajen tabbatar da shi (hadin kan), sannan kuma maimakon kowace kabila ta zamanto abin fakewa wajen korewa da kuma kaskantar da wata kabilar ta daban, hakan ya zamanto hanya ce ta isar da ababe da siffofi masu kyau na tarihi da jinsi da yankin kowace kabila da sauran kabilu na musulmi.

Ma’anar Wannan Taro Mai Girma

Duk da cewa a Musulunci akwai ibadu na jama’a, irin su sallar jam'i da sallar juma’a da sallar idi; to amma wannan gagrumin taro (hajji) da kuma irin wannan haduwa waje guda cikin zikiri da kadaita Allah da kuma tara dukkanin al’ummar musulmi daga dukkanin fadin duniyar musulmi zuwa ga wata cibiya guda, hakan yana da ma’ana. Dalilin da ya sanya dukkanin al’ummar musulmi duk kuwa da sabani na harshe da kabila da dabi’u da zauki da sabani na mazhaba da suke da su to amma an kiraye su da su taru a wani waje guda sannan kuma su dinga gudanar da wani aiki iri guda, irin wadannan ayyuka kuwa ayyuka ne na ibada da kankantar da kai da zikiri da ambato, hakan yana da cikakkiyar ma’ana. Bisa mahanga da koyarwar Musulunci a fili ya ke cewa haduwar zukata da rayuka ba wai kawai a fagen siyasa da jihadi ba ne, hatta tafiya zuwa ga dakin Allah da kuma tattaro zukata waje guda da kuma haduwa rayuka waje guda lamari ne mai muhimmancin gaske. A saboda haka ne a cikin Alkur’ani mai girma (Allah Madaukakin Sarki) yake fadin cewa“Kuma ku yi riko da igiyar Allah gaba dayanku”.
Riko da igiyar kawai shi kansa ba shi da wata fa’ida; “gaba dayanku” shi ne yake da muhimmanci. Ku riki igiyar Allah gaba dayanku; ku rungumi wannan waje da ake da tabbas a cikinsa na koyarwa da tarbiyya da shiriya ta Ubangiji. Kasantuwa tare shi ne yake da muhimmanci; zukata su zamanto tare, rayuka su zamanto tare, tunani su zamanto tare, rayuka su zamanto a waje guda. Dawafin da kuke yi – wato wannan tafiya da kuke yi wajen kewaye wata cibiya guda – wata alama ce da take nuni da yunkurin musulmi a kewayen tushen tauhidi. Wajibi ne dukkanin ayyukanmu da himmarmu su zamanto sun ginu ne bisa tabbatar da kadaitaka ta Ubangiji da kuma kula da Zati mai tsarki na Ubangiji. Wannan darasi ne da ya shafi dukkanin rayuwa.

Mummunan Amfani Da Batun Hadin Kai

Wani irin jafa'i ne a sami wani mutum ya yi amfani da wannan hanya ta hadin kan al’ummar musulmi wajen haifar da rarrabuwa da fitina a tsakaninsu. Wannan magana ce da ta shafi kowa da kowa. Wannan ba wai magana ce da ta shafi wannan mutumin dan salafiyya mai tsaurin ra’ayi da kafirta mutane ba wanda ya ke tsayuwa a Madina yana cin mutumcin ababe masu tsarki na ‘yan Shi’a ba; magana ce da ta shafi kowa da kowa. Wajibi ne jami’an aikin hajj – masu kula da tawaga ta hajj da malaman da suke cikin tawagar hajji –su kula sosai kada su yi amfani da wannan kayan aiki na hadin kai wajen rarraba kan al’umma da haifar da fitina sannan kuma su cika zukata da kiyayya da gaba da juna ba. Wani abu ne wanda ya ke sanya zukatan ‘yan Shi’a sosuwa sannan kuma su yi gaba da ‘yan’uwansu musulmi wadanda ba ‘yan Shi’a ba; sannan kuma ya ke sosa zukatan ‘yan Sunna su yi kiyayya da ‘yan’uwansu musulmi ‘yan Shi’a; ku duba ku ga wadannan abubuwa mene ne su, wajibi ne a fahimci da kuma gano wadannan abubuwan sannan kuma ku yi watsi da su. Sannan kuma bai kamata aikin hajji wanda hanya ce ta magani, hanya ce ta hadin kai, hanya ce ta hada zukata, niyoyi da azama waje guda a duniyar musulmi, a mai she shi wata hanya ta rarraba kai, hanyar haifar da gaba da kiyayya. Fahimtar wadannan abubuwa lamari ne da yake bukatar gagarumar taka tsantsan da kula sosai.

Kafar Ungulu A Tafarkin Hadin Kai

Mutanen da a lokacin aikin hajji suke neman haifar da rarrabuwa, haifar da fitina da kuma kwadaitar da tunani marasa tushe da camfe-camfe, to ko sun sani ko ba su sani ba su ‘yan amshin shatan ma’abota girman kai wadanda suke son lalata irin wannan ajiya da rumbu da kuma kawar da shi gaba daya ne. Mutanen da ba sa son su bari al’ummar musulmi su ga irin wannan girma da daukakar da ke cikin wannan hadin kai sannan kuma ya samu irin wannan tasiri da ake bukata suna daga cikin mutanen da suka lalata wannan ajiya da rusa ta. Mutanen da ba sa barin hadin kai da gagarumin ci gaban al’ummar musulmi, hakan kuma a bisa tafarkin Allah – ba wai girma a matsayin abin alfahari ba, ko girma a matsayin mulkin mallaka da kaskantar da al’ummomi ba, ba wai girma a matsayin kaddamar da yaki a kan raunana na duniya ba; face dai girma ce wajen tabbatar da ababe masu kima na Ubangiji a tafarkin tauhidi – ya tabbata a duniyar musulmi, to lalle sun zalunci bil’adama. A yau duniyar musulmi tana cutuwa sakamakon yin watsi da nuna halin ko in kula da wannan gagarumin ajiya ta Ubangiji ne da suka yi.

Haifar Da Rarrabuwa Na Mulkin Mallaka

A yau daya daga cikin muhimman manufofin girman kan duniya da kuma Amurka a duniyar musulmi, shi ne samar da sabani; hanya mafi dacewa a wurinsu ita ce samar da sabani a tsakanin Shi'a da Sunna. Kuna ganin irin maganganun da ‘yan koren ‘yan mulkin mallaka suke yi dangane da batun Iraki, suna haifar da sabani da kuma shuka munafunci. Shekaru masu tsawo kenan da ‘yan mulkin mallaka da masu takama da karfi da shisshigi na yammacin Turai suke yin wannan. A lokacin aikin hajji dama ce da ta dace wajen su yi amfani da ita domin cusawa ‘yan Shi'a kiyayya da ‘yan Sunna da kuma cusawa ‘yan Sunna kiyayya da ‘yan Shi'a; sannan kuma su ci zarafin abubuwa masu tsarki a wurin wadannan da kuma cin zarafin abubuwa masu tsarki a wurin wadancan. Dole ne a zama cikin lura; wannan kuwa bai kebanta a cikin aikin hajji ba kadai; a kowane lokaci na shekara da kuma kowane fage dole ne a zama cikin lura. Abin da Amurka ta ke farin ciki kuma take murna da ganinsa, shi ne yaki tsakanin Shi'a da Sunna. Bayan gushewar karnoni su zauna suna kallon juna - kamar wadanda a lokacin yaki suke fuskantar juna - zukatansu suna cike da kiyayya da gaba suna zagin juna. Babu wata manufa musamman a cikin wannan lokacin mai muhimmanci kamar lokacin aikin hajji, ya zamanto an tilasta wasu mutane wajen haifar da sabani; dole ne mutane su zama masu lura; malamai masu girma da suke cikin tawagar aikin hajji da dukkan jin nauyi su lura da wannan lamarin, su lura sosai; su fahimci abin da makiya suke son cimmawa. Babbar rafkana tana tattare da cewa mutum ya zama mai aiwatar da shirin makiya da kuma yi wa makiya aiki amma kuma yana zaton cewa yana kare gaskiya ne. Wasu suna karbar kudi su zama ‘ya kore da kuma yin wannan aikin; wasu mutanen kan titi masu saukin kai da kuma makauniyar gaba za su iya tsokanarku akan abubuwan da suka shafi akidarku da abubuwan da ku ke tsarkakewa. Idan ku ka mai da musu martani to shakka babu sun cimma abin da suke nema; wannan shi ne abin da suke bukata; suna son su shagaltar da mu saboda su sami kwanciyar hankali.


BARA’A DAGA MUSHIRIKAI

Rukuni Na Asali Cikin Aikin Hajj

A cikin wannan gagarumin fage (na aikin hajj), a daidai lokacin da ambaton Allah na: “Sai ku ambaci Allah kamar ambatarku ga ubanninku, ko kuwa mafi tsanani ga ambato”, sannan da kuma sanar da bara’a daga mushirikai: “Kuma da yekuwa daga Allah da ManzonSa zuwa ga mutane, a Ranar Hajji babba cewa lalle ne Allah Barrantacce ne daga masu shirka, kuma ManzonSa ma (haka)” ana kirga hakan a matsayin rukunin hajji, (wato hakan yana nuni ne da) da nuna damuwa cikin duk wani yunkuri da motsi da ke faruwa tsakanin ‘yan’uwa – wato sassan wannan al’umma guda – da zai haifar da rarrabuwa da kiyayya, hakan ma a yanayi na koli; kai hatta ma dai kace-nace tsakanin ‘yan’uwa musulmi biyu wanda a sauran lokuta na rayuwa ba wani lamari ne mai muhimmanci ba; to a yayin aikin hajji an hana yin hakan “to babu jima'i, kuma babu fasikanci, kuma babu jayayya a cikin hajji”. Na’am, wannan wajen da yin barranta daga mushirikai – wato masu kiyayya da hadin kan al’ummar musulmi – ya zama wajibi, to jidali da dan’uwa musulmi – wato wannan bangare na al’umma guda ma’abociyar tauhidi – an hana kuma haramun ne, ta haka ne irin wannan sako na hadin kai da na jama’ance a lokacin hajji ya ke kara fitowa fili sosai. A hakikanin gaskiya aikin hajj daya ne daga cikin mafi kyawun tunani da mataki na Musulunci wajen kawar da gafala. Kasantuwar wannan buki na kasa da kasa ne ya ke isar da wannan sako na cewa al’ummar musulmi a cikin irin yanayinta na jama’ance tana nuna damuwa da yin watsi da gafala daga gare ta.

Damar Wayar Da Kai

Bai kamata a yi wasa da kuma watsi da wannan dama ta wayar da kai ciikin wannan farilla ta aikin hajj da kuma sanar da barranta da ma’abota girman kai da Amurka ba. Wajibi ne duniyar musulmi ta san cewa wasu irin lamurra ne take fuskanta kuma suke gabanta. Wajibi ne wadannan abubuwa su zamanto ababen da suke sanya nishadi da yunkurawa cikin duniyar musulmi. A cikin farfagandar da suke yi suna kokarin nuna cewa hakan ba shi da wata fa’ida; (da cewa) ma’abota girman kai dai sun riga da sun sami iko kuma babu wani abin da za a iya yi. Wannan ba shi ne hakikanin lamarin ba. Hakikanin lamarin shi ne cewa al’ummar musulmi wata rayayyiyar halitta ce wacce kuma take da kwarewa da kuma iyawa. A duk inda take so sannan kuma ta yi amfani da irada da karfinta, to kuwa babu wani karfi, Amurka ce ko kuma wanda yake gaban Amurka da zai iya mata wani abu.
Al’ummomi ta dukkan hanyar da za su iya nuna damuwarsu ga manufofi da ababen amfani na duniyar musulmi sannan kuma a daidai lokacin da suke tabbatar da hadin kan da ke tsakaninsu, za su iya bayyanar da barrantansu daga makiya duniyar musulmi. Wannan shi ne mafi karancin aiki da za a iya yi a lokacin aikin hajjin da Musulunci ya tsara shi sannan kuma a yi fatan ganin hakan daga wajenta.

Ruhin Da Ke Iko Cikin Aikin Hajj

Mu dai ba mun shigo da barranta daga mushirikai cikin aiki hajji daga waje ba ne. Wani bangare ne na aikin hajji, yana daga cikin ruhi na aikin hajj da kuma ma’ana ta hakika ta wannan gagarumin taro na aikin hajji ne. Wadansu mutane suna son cikin jaridu da maganganunsu a cikin duniya a ko da yaushe su dinga fadin cewa: ‘Ku din nan dai kun siyasartar da aikin hajji’ ‘ku sanya siyasa cikin aikin hajji’, me hakan yake nufi? Idan har abin da suke nufi shi ne mu din nan mun shigo da wata ma’ana ta siyasa cikin aikin hajji, to wajibi ne a fadi cewa: to ai babu wani wajen da aikin hajji ya kasance ba shi da wata ma’ana ta siyasa.
Barranta daga mushirikai da kiyayya da gumaka da masu bautan gumaka wani ruhi ne da ke cikin hajjin muminai. Matsayin aikin hajj, wani lamari ne da ke nuni da mika zuciya ga Allah da kuma kokari da himma a bisa tafarkinsa, sannan kuma barranta daga Shaidan da kuma jifa da koransa da kuma tsayawa a gabansa. Sannan kuma matsayin aikin hajji, lamari ne da ke tabbatar da hadin kai da haduwar ma’abota alkibla da kuma kawar da bambanci na dabi’a na mutane da tabbatar da hadin kai da ‘yan’uwantaka na hakika da imani a tsakaninsu. Aikin hajji, lamari ne da ke nuni da irin wadannan darussa masu girman gaske.


Musanta Bara’a (Daga Mushirikai)

Ni dai a wajena ba abin amincewa ba ne cewa wata gwamnati da take da nauyin kula da yin hidima wa masu ziyarar Dakin Allah, sannan kuma ta hana a gudanar da wani abin da zai tabbatar da hadin kai tsakanin musulmi da kuma tabbatar da daukakar al’ummar musulmi da kuma nuna kiyayya da rashin amincewa da ma’abota girman da makiya al’ummar musulmi ba. Wannan aiki wa zai amfana kuma wata kungiya ce cikin kungiyoyin da ake da su a duniya za ta amfana daga hakan? Shin nuna goyon baya ga al’ummomin musulmin da ake zalunta laifi ne? Shin tona asirin irin makirce-makircen Amurka da sauran ma’abota girman kai da suke yi a kan Musulunci da musulmi wani aiki ne da ya saba wa nauyin da ke kai? Shin kiran musulmi zuwa ga hadin kai da kuma yin Allah wadai da masu kokarin haifar da rarrabuwa ba umurni na Alkur’ani da yake a fili ba ne? Wadanda za su amfana daga dakatar da wannan nauyi mai matukar muhimmanci su ne Amurka da yahudawan sahyoniya.
Taken bara’a da al’ummar musulmi a yau suke rerawa a lokacin aikin hajji, taken barranta ne daga ma’abota girman kai da ‘yan amshin shatansu wadanda abin bakin ciki suna ta samun kutsawa cikin duniyar musulmi da dukkan karfinsu sannan kuma ta hanyar sanya al’adu da siyasa da tsari na rayuwar da ya gurbata da shirka a kan al’ummar musulmi, sannan kuma suna ta kokari wajen ganin sun rusa tushe da ginshikin tauhidi a aikace cikin rayuwar musulmi, suka sanya su suna bautan wani wanda ba Allah ba, tauhidinsu kuwa ya zamanto maganganu ne kawai na harshen baki da ke da suna na tauhidi amma kuma babu wata alama ta tauhidi da ta saura cikin rayuwarsu.


.
Copyright © 2018~2022.
( Uzairu Badamasi Sufi )
Harkarmusulunci@yahoo.com
All rights reserved

Bamu Da Alhakin Tallar Da Ake Sawa Akan Wannan Website Din