pacman, rainbows, and roller s
Uzairu badamasi

BARKA DA ZUWA SHAFI MAI ALBARKA

Alhamdulillah muna muku albishir insha Allah zamu dawo aiki gadan gadan!


Shafin farko

Haidar Ali

Ghadir Cikin Jawaban Ayatullah Khamene’i

Ali Khamenei5

Hakikanin Tarihin Ghadir Khum [1]

Dangane da asalin waki’ar Ghadir, yana da kyau dukkanin mutanen da suke da wata alaka da tarihin Musulunci su san cewa, lamarin Ghadir, wani lamari ne da aka sallama masa; wato lamari ne da babu shakka cikinsa; ba wai ‘yan Shi’a ne kawai suka ruwaito shi ba; face dai hatta malaman hadisan Sunna – shin na lokutan farko ne ko kuma na tsaka-tsaki da wadanda suka biyo bayansu – sun nakalto wannan lamari, wato wannan abin da ya faru a wannan waje na Ghadir Khum a lokacin hajjin ban kwanan [2]da Manzon Allah (s.a.w.a) ya yi. A wancan lokacin daga cikin tawagar musulmi da suke tare da Manzon Allah (s.a.w.a) a wannan tafiya ta aikin hajji, wasu daga cikinsu har sun wuce gaba (wato sun tafi). Don haka sai Manzon Allah (s.a.w.a) ya aike musu da sako cewa su dawo da baya, sannan kuma ya tsaya har wadanda suke baya su ma suka iso. An tara gagarumin taro a wannan wajen. Wasu sun ce mutanen da suka taru din sun kai dubu casa’in, wasu kuma sun ce dubu dari wasu ma cewa suka yi mutane dubu dari da ashirin ne suka taru a wannan wajen. A cikin irin wannan yanayi mai zafin gaske, ta yadda hatta mutanen da suke zaune a Jazirar larabawa – wadanda mafi yawansu suna rayuwa ne a sahara da kauyuka wadanda tun da man sun saba da zafi – amma sun gagara jure wa tsayuwa a wannan zafi na (wannan waje na Ghadir Khum kuma a daidai wancan lokacin). Don haka suka shimfida abayoyinsu a kasa suka sanya kafafunsu a kai ko za su iya jure wa wannan tsananin zafi. Wannan lamari ne da ruwayoyin Ahlussunna sun tabbatar da shi. A irin wannan yanayin ne Manzon Allah (s.a.w.a) ya mike ya kuma daga hannun Amirul Muminin (amincin Allah ya tabbata a gare shi) sannan a gaban dukkanin halittu ya ce: “Duk wanda na zamanto majibincin lamurransa, to wannan Aliyun ma majibincin lamurransa ne. Ya Allah Ka jibinci wanda ya jibince shi sannan kuma Ka yi adawa da wanda ya yi adawa da shi”. Ko da yake wannan jumla tana da wata jumla a bayanta da kuma a gabanta; to sai dai bangare mafi muhimmancin shi ne cewa Manzon Allah (s.a.w.a) a wannan wajen ya sanar da batun wilaya – wato iko na Musulunci – ne a hukumance sannan kuma a bayyana sannan kuma ya bayyanar da Amirul Muminin (a.s) a matsayin mutumin da ya ayyana (a matsayin halifan musulmi a bayansa). Wannan wani batu ne da ‘yan’uwanmu Ahlussunna ma cikin karbabbun littattafansu – ba wai guda ba, ba kuma biyu, cikin gomomin karbabbun littafansu – sun ruwaito shi. Marigayi Allamah Amini ya tattaro wadannan abubuwa cikin littafinsa na Al-Ghadir, sannan baya ga shi din ma akwai littattafa da yawa da aka rubuta kan wannan batu.

Muhimmancin Ranar Idin Ghadir

Ko shakka babu ranar ‘Idin Ghadir’ tana da muhimmanci. A cikin ruwayoyi na Musulunci ya zo cewa irin girman da wannan rana take da shi ta wuce hatta na ranar ‘karamar salla’ da ‘babbar salla’. Hakan ba wai cewa an rage wani abu daga cikin irin muhimmancin da wadannan idoji na Musulunci guda biyu suke da shi ba ne, sai dai saboda wannan idin (na Ghadir) yana dauke ne da wani lamari mai girman gaske. Muhimmancin wannan idin da a cikin wadansu ruwayoyin Musulunci aka bayyana shi da mafi daukakan idin Musulunci shi ne cewa yana dauke ne da batun wilaya. Mai yiyuwa ne ana iya cewa manufar dukkanin wadannan wahalhalu da Manzon Allah (s.a.w.a) manyan (mutane) Musulunci da annabawan Allah, amincin Allah ya tabbata a gare su, suka sha, sun yi hakan ne don tabbatar da wilaya ta Ubangiji ne. A wani waje cikin maganganun da aka nakalto daga wajen Imam Sadik (a.s) a yayin da yake magana kan manufar jihadi a tafarkin Allah da irin kokarin da ake yi saboda addini yana cewa: “Don a fitar da mutane daga bautan bayi zuwa ga bautan Allah sannan kuma daga wilayar bayi zuwa ga wilayar Allah”. Wato manufar ita ce a fitar da mutane daga wilayar bayi da kuma bauta da fadaddiyar ma’anarta da ta zo cikin wadannan kalmomi zuwa ga wilayar Ubangiji. To sai dai dangane da batun idin Ghadir, akwai wannan batu ma na cewa a babin wilaya akwai wadansu kan iyakoki guda biyu masu muhimmanci: na farko shi ne kan iyaka na zuciya ta dan’adam ta yadda mutum zai iya sanya irada ta Ubangiji a kan kanta da kuma ba ta wilaya sannan kuma ya sanya kansa cikin wilaya ta Ubangiji. Wannan shi ne matakin farko kuma na asasi da matukar ba a samu hakan ba, to kuwa ba za a kai ga mataki na biyu ba. Bangare na biyu shi ne cewa a sanya fage na rayuwa cikin wilayar Allah. Wato al’umma ta dinga motsawa cikin wilaya ta Ubangiji. Babu wata wilaya, wilaya ta kudi ne ko wilaya ta kabila ko wilaya ta amfani da karfi ko wiyala ta ala’adun da aka saba da su na kuskure da za su iya hana tabbatar da wilaya ta Ubangiji sannan kuma su tsaya a gaban wilaya ta Ubangiji.
Mutumin da aka gabatar da shi da kuma ayyana shi a wannan rana; wato Amirul Muminin kuma shugaban masu tsoron Allah, amincin Allah ya tabbata a gare shi, ya kasance babban abin koyi cikin dukkanin wadannan fagage guda biyu na wilaya sannan kuma wani mutum na koli. Wato cikin wilaya a kan kai da kuma watsi da soyace-soyacen zuciya wanda shi ne bangare na asasi sannan da kuma bangaren kasantuwar hukumar Musulunci da kuma wilaya ta Ubangiji a matsayin abin koyi kamar yadda ya tabbatar da hakan (cikin ayyukansa) ta yadda duk wani wanda ya ke son sanin wilaya ta Ubangiji cikin tarihi to kuwa misalin hakan yana nan a wajensa.

Muhimmancin Jagorancin Da Ake Nema

Batun Ghadir da kuma ayyana Amirul Muminin (a.s) a matsayin majibincin lamurran al’ummar musulmi da Manzon Allah (s.a.w.a) ya yi wani lamari ne mai girman gaske wanda kuma yake cike da ma’anoni; a hakikanin gaskiya hakan yana nufin shigowar Annabi (s.a.w.a) cikin lamurran gudanarwa ta al’umma ne. Ma’anar wannan yunkuri da ya faru a ranar sha takwas ta watan Zil Hajjin shekara ta goma bayan hijira (wato lamarin Ghadir), shi ne cewa Musulunci yana kallon batun gudanar da al’umma ne kallon da ke cike da muhimmanci. Lamarin ba shi ne cewa lamarin gudanar da al’ummar musulmi wani lamari ne da aka yi watsi da shi cikin tsarin Musulunci ba da kuma masa rikon sakainar kashi ba. Don kuwa gudanar da lamurran wata al’umma yana daga cikin lamurra masu tasirin gaske da kuma muhimmanci cikin batutuwan da suka shafi al’umma. (Ko shakka babu) ayyana Amirul Muminin (a.s) da aka yi (a matsayin halifan annabi a bayansa) – wanda ya kasance alama ce ta tsoron Allah da ilimi da jaruntaka da sadaukarwa da adalci tsakankanin sahabban Ma’aikin Allah – lamari ne da ke bayyanar da bangaren irin wannan lamarin gudanarwa da jagoranci. A fili yake cewa wannan lamari shi ne abin da ke da muhimmancin gaske cikin babin gudanar da wata al’umma a cikin Musulunci. Mutanen da ba su yi imani da kasantuwar Amirul Muminin (a.s) a matsayin halifan annabi (s.a.w.a) kai tsaye bayan wafatinsa ba, to amma ba su da shakku cikin ilimi da gudun duniya da tsoron Allah da jaruntaka da sadaukarwar wannan ma’abocin girma wajen tabbatar da adalci; wannan wani lamari ne da dukkanin al’ummar musulmi suka yi imani da shi kuma suka tafi a kansa da kuma dukkanin mutanen da suka san Amirul Muminin (a.s). Hakan yana nuni da cewa, a mahangar Musulunci da kuma annabi (s.a.w.a), ga irin shugabanci da jagoranci da hukumar da ya zama wajibi al’ummar musulmi su nema ne.

Bayyananniya Da Kuma Boyayyiyar Hakikar Da Take Cikin Lamarin Ghadir

Akwai ababe da dama da ba su fito fili ba cikin lamarin Ghadir. Yadda lamarin ya ke dai shi ne cewa Annabin Musulunci mai girma (s.a.w.a) ya magance matsalar hukuma da imamanci – da wannan fadaddiyar ma’ana ta su – ne ga sabuwar al’ummar musulmi wacce aka kafa ta a wancan lokacin wato kimanin shekaru goma da nasarar da Musulunci ya samu da kuma kafa al’umma, inda a lokacin da ya ke dawowa daga aikin a Ghadir Khum ya nada Amirul Muminin (a.s) a matsayin halifansa kuma magajinsa. Shi kansa zahirin wannan lamarin (na nada Amirul Muminin da magance matsalar hukuma), tabbas yana da matukar muhimmanci ga mutane da suka kasance cikin wata al’umma ma’abociyar juyi da masu bincike da kuma tunani, wani lamari da riga kafi ne na Ubangiji. To sai dai abin da ke bayan fagen wannan lamarin akwai wadansu abubuwa masu girman gaske ta yadda idan har al’ummar musulmi suka dubi wannan lamarin da idon basira to kuwa tafarkin rayuwa za ta kasance musu a fili. Alal hakika idan da a ce al’ummar musulmi – shin ‘yan Shi’a ne wadanda suke daukan wannan lamari a matsayin lamari na imamanci da wilaya ko kuma wadanda ba ‘yan Shi’a ba wadanda sun yi imani da asalin lamari, sai dai su ba sa ganinsa a matsayin lamari na imanci da wilaya ne – sun dubi wannan lamari sosai da kuma idon basira, to da kuwa hakan zai haifar wa maslahar musulmi da abubuwan amfani masu yawan gaske.
Daya daga cikin wadannan batutuwa masu muhimmanci shi ne cewa ta hanyar gabatar da batun ayyana Amirul Muminin (a.s) da kuma nada shi a matsayin shugaba, an tabbatar da ababen lura da su cikin hukumci da kuma hukuma. Cikin lamarin Ghadir Manzon Allah (s.a.w.a) ya gabatar wa musulmi da kuma tarihi wani muutm ne wanda yake da dukkanin abin da Musulunci ya ke bukata. Wani mutum ne mumini; wanda ya ke da haddi na koli na tsoron Allah da nesantar abubuwan da Allah ya haramta; mai sadaukarwa a tafarkin addini; wanda abubuwan duniya ba su dame shi ba; wanda yake da kwarewa sannan kuma aka jarraba shi a dukkanin fagage na Musulunci: fagage masu hatsari; fagage na ilimi da masaniya; fagen yin hukumci da sauransu. Ta hanyar gabatar da Amirul Muminin (a.s) a matsayin shugaba kuma imami mai gudanar da lamurran musulmi hakan yana tabbatar wa dukkanin musulmi ne a tsawon tarihi cewa shugaban musulmi wajibi ne ya zamanto yana da dukkanin wadannan siffofi kuma abin koyi. A saboda haka, a cikin al’ummar musulmi, duk wani mutumin da ba shi da irin wadannan siffofi; wanda ya kasance ba shi da fahimta ta Musulunci, ba shi irin ayyukan na Musulunci, ba shi da irin wannan matsayi na jihadi na Musulunci, bai kasance mai ciyarwa da afuwa ba, ba shi da irin wannan kankan da kai da tawali’u a gaban bayin Allah da sauran irin wadannan siffofi da Amirul Muminin (a.s) yake da su, to kuwa bai cancanci shugabanci ba. Manzon Allah (s.a.w.a) ya gabatar da irin wadannan siffofi da abubuwan lura ga musulmi. Hakan kuwa wani darasi ne da ba za a taba mancewa da shi ba.
Wani lamarin kuma da za a iya fahimtarsa cikin lamarin Ghadir shi ne cewa Amirul Muminin (a.s) cikin ‘yan wadannan shekaru da ya sami isa ga halifanci da hukuma, ya tabbatar da cewa abin da ya fi ba shi muhimmanci shi ne tabbatar da adalci na Ubangiji da Musulunci. Wato adalci, wato tabbatar da manufar da Alkur’ani ya bayyana a matsayin dalilin aiko annabawa da saukar da littafa da shari’oi na Ubangiji, inda yake cewa: “Don su tabbata da adalci a tsakanin mutane”, wato tsayar da adalci na Ubangiji. Bisa koyarwar Musulunci adalci shi ne babban abin da ke lamunce daidaito a cikin al’umma. Hakan a wajen Amirul Muminin (a.s) shi ne lamari mai daraja ta farko.

Ma’anar Wilaya Cikin Waki’ar Ghadir

Dangane da lamarin Ghadir, Manzon Allah (s.a.w.a) bisa umurnin Ubangiji da kuma aiki da ayar Alku’rani ya sauke daya daga cikin mafiya girman wajiban da suke kansa ne: “Idan ba ka aikata hakan ba, to ba ka isar da sakonsa ba” Batun ayyana Amirul Muminin (a.s) zuwa ga matsayin wilaya da halifanci, yana da irin wannan muhimmanci ta yadda idan har ba a aikata hakan ba to kuwa ba ka isar da sakon da aka aiko ka da shi ba! Ko kuma abin nufin shi ne cewa ba ka isar da sakon da aka aiko ka da shi ba cikin wannan lamari na (halifanci da imamanci). Don kuwa Allah Madaukakin Sarki Ya ba da umurnin cewa ‘ka aikata wannan aikin’. Ko kuma sama da hakan, shi ne cewa asalin sakon Manzon Allah (s.a.w.a) ma zai iya fuskantar matsala saboda rashin aiwatar da wannan lamari sannan kuma tushen (Musulunci) zai iya fuskantar zamiya. Akwai yiyuwa hakan. Tamkar dai ba a isar da asalin sakon ba ne. Akwai yiyuwar hakan, ma’anar hakan ta zamanto cewa ta wannan bangaren lamarin zai iya samun gagarumin muhimmanci. Wato lamarin kafa hukuma, lamarin wilaya da gudanar da kasa, suna daga cikin bangare na asali na addini sannan kuma Manzon Allah (s.a.w.a) ya ba wa wannan lamari muhimmanci ya kuma gabatar da sakonsa ga idanuwan dukkanin mutane ta yadda watakila babu wani wajibi da ya yi masa haka! Ba salla ba, ba kuma zakka ba, ba kuma azumi ba, ba kuma jihadi ba. Wato ya tara mutane daga dukkanin bangarori da kabilu da suka fito daga yankuna daban-daban, ya tara su a wata mararraba guda dake tsakanin garuruwan Makka da Madina saboda isar da wani sako da wani umurni mai matukar muhimmancin gaske. Inda ya isar da wannan sako.

Ma’anar imamanci Cikin Ghadir

Imamanci dai shi ne irin wannan tsari da ake bukata na jagorantar al’umma sabanin sauran tsari na jagorantar al’umma da ke cike da rauni, sha’auce-sha’auce da son zuciyar dan’Adam. Hakika Musulunci ya fitar wa dan’Adam da wani tsarin shugabanci (imamanci) ne; wanda shi ne kuwa samun wani mutum da zuciyarsa take cike da hasken shiriya, wanda ya san koyarwa ta Musulunci da kuma fahimtarta – wato ya iya fayyace tafarki (madaidaici) – kamar yadda kuma ya kasance mai karfin aiki, - wanda shi ne (kamar fadin Allah Madaukakin Sarki cewa) Ya Yahya! Ka kama littafi da karfi (Suratu Maryam 19:12) - kamar yadda kuma son zuciya da son kai da rayuwar daidaiku ba su kasance masu muhimmanci ba a gare shi, to amma a daidai lokaci guda kuma rai da rayuwar sauran al’umma sun kasance abin girmamawa da ba da muhimmanci a gare shi, kamar yadda Amirul Muminina cikin shekaru biyar na halifancinsa ya nuna hakan a fili. Ku duba ku gani cikin kasa da shekaru biyar na mulkin Amirul Muminina an haifar wa dan’Adam da abin da ba zai taba mancewa da shi ba, kuma ya ci gaba da wanzuwa duk tsawon tarihi. Wannan dai sakamakon darasi da fassarar waki’ar Ghadir.

Ghadir Da Hadin Kan Al’ummar Musulmi

Batun Ghadir yana iya zama wani lamari na hadin kai tsakanin al’ummar musulmi; mai yiyuwa ne hakan ya zamanto abin mamaki, to amma hakikanin lamarin haka yake. Shi kansa lamarin Ghadir, baya ga bangaren da ‘yan Shi’a suka yi imani da shi a matsayin bangaren akidarsu – wato nada Amirul Muminin (a.s) da Manzon Allah (s.a.w.a) ya yi a matsayin halifansa wanda ake iya ganinsa a fili cikin hadisin Ghadir – an gabatar da asalin batun wilaya a cikinsa. To wannan kan babu wani batun Shi’a da sunna a cikinsa. Idan har a yau al’ummar musulmi a duk duniya da kuma al’ummomin kasashen musulmi suka rera taken wilaya ta Musulunci, to kuwa da dama daga cikin hanyoyi da suke cike da matsaloli da kuma kulle-kullen da aka kulla za a iya kunce su, sannan kuma za a kai ga magance mafi yawa daga cikin matsalolin da kasashen musulmi suke fuskanta.

Masdari

[1] Ghadir Khum sunan wani waje ne da ke tsakanin Makka da Madina wanda ya ke bisa hanyar da alhazai suke bi. Saboda kasantuwar wani ziri a wajen da ruwan sama yake taruwa don haka ake kiran wajen da sunan ‘Ghadir Khum’.

Annabi Muhammadu (tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi da Alayensa) a lokacin da ya ke dawowa daga hajjinsa na karshe sai ya tsaya a wannan waje na Ghadir Khum inda ya tara dukkan musulman da suke tare da shi a wannan wajen inda ya sanar da Aliyu bn Abi Talib a matsayin wasiyinsa kuma dan’uwansa sannan kuma halifansa a bayansa yana mai cewa hakan wani umurni ne daga wajen Allah. Sananniyar maganar nan tasa ta ‘Duk wanda na zamanto majibincinsa, to Aliyu ma majibincinsa ne’ wani bangare ne na wannan huduba mai girma da ya yi a Ghadir Khum wanda Shi’a da Ahlussunna duk sun tabbatar da ingancinta.

[2] Tun daga farkon watan Zil Ka’ada shekara ta goma hijiriyya wanda ya yi daidai da shekarar karshe ta rayuwar Ma’aikin Allah (s.a.w.a), ya sanar da dukkanin musulmi a duk inda suke a yankuna daban-daban da kuma kabilu daban-daban na musulmi cewa a wannan watan zai tafi Makka inda zai gudanar da Umra da Hajjin Tamattu'i a saboda haka za a gudanar da gagarumin taro na musulmi wanda daga baya ake kiransa da hajjin ban kwana.

.
Copyright © 2018~2022.
( Uzairu Badamasi Sufi )
Harkarmusulunci@yahoo.com
All rights reserved

Bamu Da Alhakin Tallar Da Ake Sawa Akan Wannan Website Din