Hijabi wani lamari ne mai kima ne wanda ya yi daidai da dabi’ar mutum. Duk yanda tsiraici da yunkuri zuwa ga haduwa tsakanin namiji da mace, ya dada karuwa sannan kuma wadannan jinsuna biyu suka ci gaba da bayyanar da jikinsu ga ‘yan’uwansu, to hakan wani yunkuri ne da ya saba wa dabi’a da kuma bukatar dan’adam.
Allah Madaukakin Sarki, bisa asasin maslaha sannan kuma saboda kyautata rayuwar mace da namiji, Ya samar da wata dabi’a ta yanayi a gare su don su sami damar gudanar da rayuwar duniya kafada da kafada. Ya sanya wasu ayyuka da nauyi a wuyan mace, sannan kuma ya sanya wasu ayyuka da nauyin a wuyan namiji; ya sanya wasu hakkoki ga mace sannan kuma ya sanya wasu hakkokin ga namiji. A matsayin misali hijabin mace ya fi tsanani da wahala a kan hijabin namiji. Ko da yake namiji a wasu wajajen ma wajibi ne ya kiyaye hijabi (wadannan iyakoki da aka tsara), wajibi ne ya rufe wasu sassa na jikinsa; to amma dangane da mace kan wannan lamarin ya fi tsanani. Saboda me? Saboda dabi’a da irin siffofi masu taushi na mace, mazhari ne na kyau da halitta, ta yadda matukar muna son kada al’umma ta zamanto ta fada cikin rikici da lalata da gurbata sannan kuma kada ta fada cikin fasadi, wajibi ne a kiyaye wannan jinsin cikin sutura. A irin wannan yanayin ne, namiji bai zamanto kamar mace ba, a nan namiji yana da ‘yanci sosai sama da mace. Hakan ya samo asali ne daga yanayi na dabi’ar su ne da kuma abubuwan da yake cikin mahangar Ubangiji wajen gudanar da duniya.
Muhimmancin Ado A Musulunci
A Musulunci, an ba wa batun ado da kyau muhimmancin gaske. Asalin akidar so da kaunar ado da abubuwa masu kyau, wani lamari ne na fidira. Ko da yake watakila hakan yana da bambanci da akidar son sabunta lamurra. Son sabon abu wani lamari ne da ya fi zama na kowa da kowa. Wadannan lamurra na ado da tufafi da abubuwa da kika ambata, wasu abubuwa ne na musamman da mutum – musamman ma dai matasa – ya ke tsananin son ado da kawa sannan kuma zukatansu suna so su zamanto su kansu suna da kyau. Mun sha jin cewa: "Hakika Allah mai kyau ne kuma yana son abu mai kyau". Dangane da batun kula da kai (gashi) da yanayin mutum, akwai hadisai masu yawa cikin littafan hadisanmu. A cikin littafin 'Nikah' an yi fadadden bahasi dangane da wajibcin mace da namiji su kula da kansu. Wasu suna zaton cewa wajibi ne a matsayin misali maza su aske gashin kansu gaba daya; a'a. Cikin shari'a, an bayyana cewar mustahabi ne matashi ya bar gashin kansa. Ya zo cikin wata ruwaya cewa: "Gashi mai kyau na daga cikin karamomin Allah, don haka ku girmama shi"; ko kuma a matsayin misali akwai wata ruwaya da take cewa Manzon Allah (s.a.w.a) a duk lokacin da yake son fitowa wajen sahabbansa, ya kan je ya tsaya wa gaban wani kwano na ruwa don ya gyara kansa da kuma gashinsa. A wancan lokacin babu irin wannan madubin da muke da shi a halin yanzu wanda kuma ya ke da yawa. Al'ummar garin Madina kuwa talakawa ne. Manzon Allah (s.a.w.a) ya kasance yana da wani kwano na ruwa, wanda a duk lokacin da yake son fitowa wajen sahabbansa, ya kan yi amfani da shi maimakon madubi. Wannan alama ce da take nuni da cewa gyara kai da gashi, sanya tufafi mai tsafta da kuma kula da kyau da ado, wani lamari ne abin so cikin shari'ar Musulunci. To sai dai abin da yake mai muni da kuma cutarwa shi ne a mai da hakan ya zamanto wata hanya ce ta haifar da fitina da fasadi da kuma tsiraici.
Hijabi Wani Batu Ne Na Ababe Masu Kima
Batun hurumi na jinsi a wajen musulmi wani batu ne na asali. A hakikanin gaskiya wannan wani asali ne. Musulmi sun yi imani da wannan asali da wannan ma'anar, duk kuwa da cewa hakan daya ne daga cikin rassa na addini. Kiyaye mu'amala ta jima'in da aka haramta, daya ne daga cikin rassa na addini. To amma shi kansa batun hurumin jima'i, wato tsakanin jinsi biyu akwai wani hurumi cikin hakan, shi kan wani ginshiki ne. Batun ba shi ne batun chador (chador shi ne irin bakin hijabin nan da matan Iran suke sanyawa); ba batu ne na rufe jiki ba; batun ba shi ne yadda iyakan za ta kasance ba ne. Mai yiyuwa ne hakan, a lokuta mabambanta da kuma bukukuwa daban-daban da kuma wajaje mabambanta ya zamanto ya samu wani irin yanayi. To amma shi kansa wannan iyakan, daya ne daga cikin asasi na tunanin Musuluncinmu. Batun hijabi, wani batu ne mai kima. Batun hijabi, wani batu ne wanda duk da cewa share fage ne ga wasu abubuwa masu girma, to amma shi kansa wani lamari ne mai kima. Mu dai an kayyade mu dangane da hijabi saboda kiyaye hijabi yana taimaka wa mace don ta samu damar isa ga wannan yanayi na koli na ababben da suke kusata mutum da Allah sannan kuma kada mu fuskanci ababen da suke sanya kaucewa hanya da suke kan tafarkinta.
Alakar Mace Da Namiji
An sanya wani hijabi tsakanin mace da namiji: za su yi magana da junansu, za su yi mu'amala a tsakaninsu, za su yi fada a tsakaninsu, za su yi abokantaka a tsakaninsu, amma cikin wani hijabi da kuma katanga. Wannan yana cikin Musulunci wanda kuma wajibi ne a kula da shi. To amma an hana tsallake haddi da keta hurumi da mutumci na bil'adama na mace da kuma mai da ita zuwa ga wani kayan aiki na jin dadi sannan kuma wata na'ura ta nuna kai.
A hakikanin gaskiya, Musulunci, yana son ganin mace ce wacce take da irin wannan daukaka da rike kai, wacce ba ta damu da cewa shin maza suna kallonta ko kuma a'a ba. Kun fahimta ko? Wato wajibi ne mace ta zamanto tana da irin girma da kuma rike kai ta yadda ba ma za ta ji cewa wai shin maza suna kallonta ko kuma ba sa kallonta ba. Ina hakan yake, ina kuma yadda macen da take sanya tunani da yin ado da gyaran gashi da kuma irin maganarta da yadda take tafiya don maza su kalle ta shi ma yake? Ko duba ku ga irin tazara da bambancin da ke tsakaninsu.
Nuna Kan Da Aka Haramta
A Musulunci, fitar da tsiraici (tabarruji) haramun ne. Tabarruji yana nufin nuna kan mata a gaban mazaje, don janyo hankulansu da kuma yada fitina. Hakan, wani nau'i ne na fitina kuma yana da matsaloli masu yawa. Matsalarsa ba wai kawai shi ne cewa wannan budurwar matashiya ko kuma wannan saurayi matashi zai fada cikin zunubi ne kawai ba - wannan ababe ne na farko-farko; mai yiyuwa ne ma muna iya cewa shi ne mafi karancinsa – amma sakamakon hakan ya kan koma ne ga iyali. Alal hakika irin wadannan alakoki wadanda babu wani kaidi da sharadi cikinsu lamari ne mai halakarwa cikin iyali; saboda kuwa iyali ya ginu ne cikin soyayya. Tun asali ma tushen iyali ya ginu ne bisa asasin so. Matukar aka lamunce wannan so da kauna – wato kaunar ado, kaunar jinsi na daban – ta daruruwan hanyoyi, to shi kenan wannan asasi mai karfi na iyali wanda wajibi ne iyali ya same shi, za a rasa shi sannan kuma (ginin) iyali zai zamanto ya girgiza, zai kasance kamar yadda a halin yanzu abin bakin ciki ya ke faruwa a kasashen yammaci; musamman a kasashen arewacin Turai da Amurka. Iyalai su kan gushe, hakan ya zamanto babbar musiba. Cutarwar hakan a matakin farko yana komawa ne ga su kansu mata. Ko da yake su ma mazaje din su kan shiga cikin yanayi na wahala sosai; to amma cutarwarsa ya fi fuskantar mata; daga nan kuma sai zuwa ga zuriya masu zuwa. Shin kuna ganin irin wannan zuriya marasa albarka da suke duniya da kuma kasar Amurka? Dukkan hakan sukan faro ne daga wannan wajen, wato mafari da mabudin sharrin wanda sakamakonsa shi ne shigowar sharri daya bayan daya.
Hijabi Da Ci Gaba Na Zamantakewa Na Mata
Musulunci yana son ganin ci gaban tunani, ilimi, zamantakewa da siyasa – a dukkan bangarori – da falala da ma’anawiyya ta mata sun kai mataki na koli sannan kuma samuwarsu ta kasance mai amfani na koli ga al’umma da kuma bil’adama – a matsayinta na memba na wannan iyali - . Dukkanin koyarwar Musulunci ciki kuwa har da batun hijabi, sun ginu ne bisa wannan asasin. Batun hijabi, ba yana nufin mai da mace saniyar ware ba ne. Idan har wani yana da irin wannan tunani kan hijabi, to kuwa tunani ne na kuskure da ya kauce wa hanya. Lamarin hijabi, lamari ne na hana haduwa da cakuduwar maza da mata maras sharadi da kaidi cikin al’umma. Irin wannan cakuduwar, lamari ne mai cutarwa ga al’umma da kuma mace da namiji – musamman ma macen-.
FASALI NA BIYU: HIJABI A AL’ADUN KASASHEN YAMMACI
Kalubalen Hijabi Cikin Al'adun Musulunci Da Na Yammaci
Ni dai a lokuta da dama na sha fadin cewa: Ba mu ne za mu tsaya muna kare mahangar da muke da ita ba (dangane da mace), face dai wadannan karkatattun al'adu na yammaci ne za su kare da ba da amsa dangane wannan akida ta su. Abin da muke gabatarwa dangane da lamarin mace, wani lamari ne da babu wani mutum masani mai adalci da zai yi inkarinsa cewa wannan lamari mai amfani ne ga mace. Mu dai muna kiran mace ne zuwa ga kame kanta, zuwa ga nesantar sabo, zuwa ga sanya hijabi da kuma zuwa ga rashin haduwa tsakanin maza da mata da jima'i maras kaidi da iyaka sannan kuma zuwa ga kiyaye karama ta dan’adam da kuma rashin yin ado a gaban namijin da ba muharrami ba – don idanuwansa su ji dadi - . Shin hakan abu ne mai muni? Wannan shi ne mutumcin mace musulma. Wannan shi ne mutumci da karamar mace. Wadanda suke kwadaitar da mace wajen ta yi irin ado kaza don mazajen da suke kan tituna da kasuwanni su dinga kallonta don su biya bukatarsu ta sha'awa, wajibi ne su kare kansu dangane da hakan kan cewa da wani dalili ne ya sanya suka kaskantar da mace irin wannan kaskantarwar? Wajibi ne su amsa wannan tambayar? Al'adarmu, wata ala'ada ce wacce hatta manyan masanan kasashen yammaci sun amince da ita sannan kuma halayensu haka suke. A can ma suna da mataye masu yawa wadanda suke ganin girman irin mutumci na mace da suke da shi, wadanda ba a shirye suke su mai da kansu zuwa ga wata haja ta biyan bukatar sha'auce-sha'auce na mazaje da kuma idanuwa ba. Akwai irin wadannan mutane da yawa cikin kasashen yammaci.
Kore Kimar Hijabi A Kasashen Turai
Lalle mu muna bukatar karin bayani daga wajen kasashen yammaci wadanda suka zo suka wulakanta mace tsananin wulakantawa a zamunnan da suka gabata har zuwa yau din nan. Ku duba ku gani a kasashen Turai da kuma kasahen yammaci, har zuwa cikin 'yan shekarun da suka gabata, mata ba su da wani hakki na mallakan dukiya mai cin gashin kanta. Har zuwa farkon karni na ashirin, duk kuwa da irin wadannan ikirari da suke yi, da kuma irin yaye hijabi mai tsananin ban mamaki da yake ta faruwa a kasashen yammaci a kusan kullum, da kuma irin wannan haduwa tsakanin maza da mata wanda ba shi da karshe – wanda suke tunanin cewa hakan girmama mace ce da kuma kara mata kima – amma ala kulli hal macen yammaci ba ta da hakkin ta yi amfani cikin 'yanci kan dukiyar da mallakanta. A gaban mijinta, ba ta kasance tana da ikon mallaka cikin dukiyarta ba. Wato macen da ta yi aure, to dukkanin dukiyarta da abin da ta mallaka, mallakar mijinta ne; ita kanta ba ta da hakkin ta yi amfani da ita; har daga baya a hankali a hankali har zuwa farko-farkon karni na ashirin inda aka fara ba wa mata hakkin mallaka da kuma aiki. Wato wannan batu wanda yana daga cikin hakkokin bil'adama na farko-farko, an kwace shi daga wajen mace; amma suna ta magana da kara matsin lamba a kan batutuwa masu kimar gaske wanda Musulunci ya ba shi muhimmanci. To dalilin da ya sanya muke ta magana kan batun hijabi, saboda wannan dalili ne.
Tsiraici da Shan Giya, Wata Karbabbiyar Al'adar Kasashen Yammaci
A yau a duniya, ana ta nuna damuwa sosai dangane da tufafin da mace za ta sa! Idan har aka samu wani mutum, wani jami'i, wani masanin falsafa, wani soja, wani dan siyasa ya nuna rashin amincewarsa dangane da tsiraicin mace, to wannan kan zai zamanto abin daga murya a duniya. Ba sa nuna damuwa ga mafi yawa daga cikin fasadi da munanan halayen da suke yawo. Idan har wata kasa ta nuna rashin amincewarta da shan giya da kuma daukan hakan a matsayin siyasarta, to wannan kan zai haifar da tada jijiyoyin wuya a duniya. Za su dinga yi maka dariyar cin mutumci, za su baka sunan wanda ya ci baya. Wannan, al'adar ina ce? Wannan al'ada ce a kasashen Turai wacce ta samo asali daga tsohuwar al'adun da suke da ita. To a halin yanzu irin wadannan halaye da dabi'u sun sami gindin zama a duniya, ta yadda idan wani ya nuna rashin amincewarsa da hakan, tamkar ya aikata wani gagarumin zunubi ne.
Wajibai Masu Karo Da Juna Na Kasashen Yammaci
A kasashen Turai da suke ganin kansu a matsayin wadanda suka ci gaba, sannan kuma cikin farfagandar da suke yadawa suke nuna cewa suna ba wa batutuwa irin su hakkokin bil’adama da ra’ayin mutane muhimmanci, amma ba sa bari wasu ‘yan tsiraru daga cikin mata da ‘yan mata musulmi (da suke rayuwa a wadannan kasashe) su gudanar da rayuwarsu cikin hijabi na Musulunci da kuma tafiya makaranta ba. A nan kan tilasci da tursasawa sun halalta, babu wata matsala cikin hakan, to amma Jamhuriyar Musulunci ta Iran kan saboda sun wajabta sanya hijabi cikin al’ummarta, sai ya zamanto suna ta sukanta a duk inda suka taru. Idan har wajabta wa mata sanya wani irin tufafu yana da matsala cikinsa, to kuwa matsalarsa ya fi muni kan wajabta sanya shi; don kuwa hakan (wato sanya hijabin) ya fi kusa da zaman lafiya da kwanciyar hankalin (al’umma). Alal akalla a dinga kallon wadannan abubuwa biyu da mahanga guda; to sai dai kasashen yammaci ba sa yin hakan.
Kaskantar Da Mace Cikin Al'adun Yammaci
Dangane da batun mace, kamata ya yi mahangarku ta zamanto na kai hari ne ba wai ta neman kariya ba. Korafin da kasashen yammaci suke yi dangane da mu shi ne cewa me ya sa matayenku suke sanya hijabi; da wani dalili ne ya sanya aka tilasta sanya hijabi. To ai su kansu ma sun tilasta (wa mata) rashin sanya hijabi; to amma lamarinsu dangane da mace ya fi wannan abubuwan da suke fadi. A al'adu na kasashen yammaci an kai mace zuwa ga lalata, an kaskantar da ita da kuma cin mutumcinta. Mace da namiji su zauna kan teburin diplomasiyya kafada da kafada, ko da wasa hakan ba zai cike gurbin cutarwar da suka yi wa mace ba. Sun mai da mace a matsayin wani kayan aiki na jin dadi da sha'awa, wannan babban cin mutumci ne ga mace.
Hijabi, Mabudi Ne Na Al'adun Musulunci
Don tabbatar da wani mulki na dindindin a kan wata kasa, to wajibi ne a sauya al'adun wannan kasar; wato wajibi ne wannan kasar ta tafi kafada da kafada da wadannan al'adu na kasashe masu iko din don su mika musu wuya gaba daya. A shekarun baya 'yan kasashen yammaci sun aikata haka a gabashi ko da yake ba su cimma wata nasara ta azo a gani ba. A yau ma abin da suke son aikatawa kenan a kasar Afghanistan kuma ko shakka babu daya daga cikin manufofinsu shi ne kawar da tushen mutumcin bil'adama. Da farko dai sun fara ne da Musulunci. Suna adawa da hijabi sannan kuma suna adawa da duk wani abin da zahirinsa na addini ne. Wajibi ne a kiyaye wadannan ababe masu kima da kuma karfafa su.
Kasashen yammaci suna inkarin Jamhuriyar Musulunci da cewa tana da wani tufafi na musamman ga matan kasar da wajibi ne su sanya shi; to amma wadannan gwamnatoci da suke tilasta wa mata fita tsirara da hana mata da maza sanya hijabi, ba sa nuna rashin amincewa ga irin wadannan gwamnatoci! Hakan saboda mene ne? Saboda hakan ya saba wa al'adun da aka amince da su a kasashen yammaci ne. Lalle suna nuna damuwarsu dangane da hakan.
Haramcin Sanya Hijabi A Kasashen Turai
Cikin ‘yan shekarun da suka gabata din nan, a kasashen Turai – wato a kasar Faransa da sauran kasashe ciki kuwa har da Jamus – sun kasance suna fada da hijabi. A wani bangaren kuma kuna ganin yadda suke ta magana kan tsari irin wanda ya dace da duniya. A matsayin misali a duk lokacin da suke son fadin cewa wajibi ne Jamhuriyar Musulunci ta aikata kaza to su kan yi amfani da kalmar cewa “wajibi ne kasar Iran ta aikata irin abubuwan da aka amince da shi a duniya”, wato abin da aka amince da shi a duniya shi ne dai irin wadannan abubuwa, wato abubuwan da suka dace da al’adun kasashen yammaci. To a saboda haka a ko da yaushe irin wannan matsin lamba da tsanantawa ta kasashen yammaci tana nan. A duk lokacin da wata al’ada wacce ba ta yammaci ba ta kunno kai, musamman al’adar Musulunci wanda wata al’ada ce da take kokari da kuma samar wa kanta wani matsayi sannan kuma ba ta san wani yanayi na rauni da gazawa ba, to a duk lokacin da take son ta tabbatar da irin matsayin da take da shi, to za su ci gaba da matsa mata lamba da kokarin kaskantar da ita.
FASALI NA UKU: HIJABI A TSARIN JAMHURIYAR MUSULUNCI NA Iran
Kutsawar Al’adar Sanya Hijabi
Mata da musulmi a kasashe daban-daban – shin kasashen musulmin da babu wani labarin hijabi ne wadanda suka kutsa cikin al'adu na yammaci ko kuma hatta ma kasashen Turai – suna komawa zuwa ga batun hijabi. Sannan mu kuma bayan nasarar juyin juya halin Musulunci mun ga yadda kasashen da ma suke da nesa wadanda suke karkashin tasirin da jan hankulan al'adun yammaci da Turai, suna koyon sanya hijabi da irin hijabinku matan Iran sannan kuma sun rungume shi. A tafiyar da na yi zuwa yankunan da musulmi suke na arewacin Afirka, a wata kasa na ga cewa mata da budurwaye suna dinka hijabinsu irin hijabin da matan Iran suke sawa. A yau kuma kasashen Turai ne a hankali a hankali suke kama hanyar riko da hijabi na Musulunci.
Abin da kuke gani na cewa a wasu kasashen yammaci, a wasu daga cikin kasashen musulmi wadanda ba su da hukuma ta Musulunci, irin yadda suke adawa da hijabin Musulunci, hakan yana nuni ne da irin yadda mata suke komawa ga akidar sanya hijabi ne. A kasashen da suke makwabtaka da mu, a wajajen da ba a damu da hijabi ba, a kasashen musulmin da ni da kaina ma a kurkusa na gani inda ko da wasa ma ba a ma kawo sunan hijabi; tsawon shekaru ashirin bayan nasarar juyin juya halin Musulunci, mata musamman mata masana da ‘yan mata ‘yan jami’a sun sami alaka da sanya hijabi; suna kaunar sanya hijabi, sun kasance masu kiyaye sanya hijabi; misalin hakan baya ga su din nan hatta a kasashen yammaci ma ana iya ganin hakan. Lalle ku din nan kun zamanto abin koyi ne.
Tilasta Al’adun Kasashen Yammaci
Mutumin da ya fi gudanar da ayyukansa wajen amfanar da al’adun kasashen yammaci – wato alal hakika ya yi aiki ne don amfanin mulkin mallakan kasashen yammaci a kan Iran – sannan kuma ya yi aiki don amfanin mulkin mallaka ta hanyar Ingila sannan kuma a wancan lokacin ya aiwatar da gagarumin aiki, shi ne Ridha Khan. A yanayi irin na yanzu wani irin cin mutumci ne irin wadannan ayyuka ba su haifar ba. Wato wani sarki ya zo haka kawai ya sauya tufafin na kasa na wata al’umma da wata kasa! A kasar Indiya ko kuma wasu bangarori masu nisa na duniyar nan, al’ummomi suna da irin tufafinsu na kasa, suna ma alfahari da hakan; ba sa jin kaskanci da kunyan hakan. Amma wadannan mutane sai kawai suka zo, lokaci guda suka ce: wannan tufafi an hana sanya shi! me ya sa? Don kuwa ba za a iya zama malami masani da wannan tufafin ba! Abin ban mamaki! Babban masani Ba’iraniye wanda har ya zuwa yanzu ana karantar da ilmummukansa a kasashen Turai ya taso ne cikin irin wannan al’ada da kuma irin wannan yanayi. Shin wani tasiri ne tufafi ya ke da shi? Wannan wani irin magana ce?! Sun gabatar da irin wannan tunani abin dariya. Sun sauya tufafin wata al’umma. Sun kawar da chador din mata. Suna cewa: “Da chador wata mace ba za ta iya zama malama kuma masana ba sannan kuma ta kasance cikin ayyuka na zamantakewa ba”.
To ni dai ina tambaya: wani irin gudummawa ce mata suka bayar a fagen ayyukan zamantakewa a kasar Iran bayan da aka hana musu sanya chador din? Shin an ba da dama ga matan Iran a lokacin Ridha Khan da dan Ridha Khan wajen su kasance cikin ayyuka na zamantakewa? Ga maza ma ba a ba su wannan damar ba; haka nan ga mata ma ba a ba su wannan damar ba. A wancan ranar da matan Iran suka shigo cikin ayyukan zamantakewa sannan kuma suka daga wannan kasar da karfafan hannayensu sannan kuma suka janyo mazaje cikin fagen gwagwarmaya, da wannan chador din ne dai suka shigo fagen. Wani irin mummunan tasiri ne chador ya ke da shi? Wani irin tasiri ne tufafi ya ke da shi wajen hana mace ko kuma wani namiji gudanar da ayyukansa? Wannan wawan mutumin jahili mai son amfani da karfi – wato Ridha Khan – ya zo ya mika kai ga makiya. Kwatsam kawai sai ya sauya tufafin wannan kasar. Saboda mata a kasashen yammaci ba sa rufe kawunansu. Ya zo da wannan al’adar ce daga yammaci. Bai zo da abin da wannan al’umma take bukata ba. Bai zo da ilimi ba, bai zo da kwarewa ba, bai zo da kokari da aiki ba kama hannun yaro ba, bai zo da yin taka tsantsan kan ababen da suke da hatsari ba – don kuwa ko wace al’umma tana da irin nata siffofi masu kyaun din ta – bai zo mana da wadannan abubuwa ba. Abubuwan da ya zo da su din ma, cikin tursasawa aka amince da su. Ya zo da tunani, to sai dai ba tare da yin sharhi ba haka kawai a amince da abin da aka fadi; yana cewa tun da dai daga wajen mutanen kasashen yammaci ya zo to wajibi ne a yarda da shi. Yanayin yadda ake sanya tufafi da cin abinci da yadda ake magana da kuma tafiya, tun da dai daga kasashen yammaci suka zo, to wajibi ne a yarda da su; babu wata dama ta nuna rashin amincewa! Wannan wani bangare ne mai tsananin halakarwa ga wata kasa, hakan ba daidai ba ne.
Zaluntar Mata Musulmi
Mace, cikin al'ummar tsarin da ya sha kashi na sarauta, a hakikanin gaskiya ta kasance wadda aka zalunta ta dukkan bngarori. Idan har mace tana son shiga cikin fagen ilimi, wajibi ne ta yi watsi da kaidi na addini da tsoron Allah da tsarkin da take da shi. Shin wata mace musulma tana iya kiyaye wannan hijabi na ta da kuma irin wannan tsarki da mutumci da take da shi a cikin jami'oi da fagagen ilimi da sauran cibiyoyi na ilimi da ala'adu? Shin abu ne mai yiyuwa wata mace musulma, a kan titunan birnin Tehran da sauran garuruwa na daban, ta ci gaba da tafiya cikin mutumci da kariya ta Musulunci ko ma da da rabin hijabi cikin sauki ba tare da cutarwa ta magana da ta muganen da zukatansu suke cike da son fasadi? Sun yi aiki ta yadda neman ilimi a mafi yawan lokuta zai yi wahala ga mace a wannan kasar. Ko da yake akwai wasu yanayi na musamman, amma a mafi yawan lokaci kasantuwar mata a fagen ilimi lamari ne da ba a samar da shi ba; sai dai ta hanyar cire hijabi da kuma nesantar tsoron Allah da kuma mutumci na Musulunci.
Hijabi Da Ci Gaba Na Zamantakewa Na Matan Iran
Musulunci da juyin juya halin Musulunci da kuma marigayi Imam sun zo cikin wannan kasar nan sannan suka mayar da mace ta zamanto wata cibiya da helkwatar ayyukan siyasa da kuma mika tutar juyin juya halin Musulunci ga hannun mace; alhali kuwa mace a irin wannan yanayin ma ta samu damar kiyaye hijabi da mutumci na Musulunci da tsarki da addini da tsoron Allah da take da shi. Babu wani da yake da wani hakki sama da haka a wuyan matan Iran musulmi.
Ku duba ku gani a lokacin da mace musulma ta dawo zuwa ga fidira da asalinta, wace irin mu'ujiza mai girma ce za ta iya aiwatarwa! Kamar yadda alhamdu lillahi aka gani cikin juyin juya halinmu da kuma tsarinmu na Musulunci, a halin yanzu ma ana ganin hakan. A yau, alhamdu lillahi, wasu irin masana mata a bangartori daban-daban na ilimi ne ba mu da su: daliban jami'a masu kokari da kwarewa, daliban jami'an da suka gama karatunsu da darajar karatu mai girma; likitoci kwararru! A yau a Jamhuriyar Musulunci ta Iran bangarori daban-daban na ilimi suna hannun mata ne; matan da suka kiyaye mutumci da tsarkinsu, haka nan kuma sun kiyaye hijabinsu – a yanayi na gaba daya -, sannan kuma suna kula da tarbiyyar 'ya'yansu yadda Musulunci ya tanadar haka nan kuma suna gudanar da ayyukansu na gida (a matsayinsu na matan aure) kamar yadda Musulunci ya tanadar, sannan kuma a bangare guda suna gudanar da ayyukansu na ilimi da siyasa. A cikin yanayi na Musulunci da kuma ruhi na Musulunci, mace tana iya isa ga hakikaninta; nesa da irin wannan almubazzaranci, nesa da irin akidar son ado da kuma nesa da kaskantar da kai a gaban amfani da abubuwa.
Sakon Mata Musulmi Na Iran
Matan Iran, musamman ma dai wadanda suka sami damar gudanar da ayyukansu a dukkanin bangarori na ilimi karkashin inuwar Musulunci da dokoki da hukumce-hukumce na Musulunci ciki kuwa har da lamarin hijabi, wajibi ne a sanar da ‘yan mata na duniya da daliban jami’a mata na duniya a aikace cewa ilimi ba yana nufin iskanci ba ne, sannan wajibin ilimi shi ne iskanci da munanan halaye cikin mu’amalar mace da namiji ba; face dai ana iya samun ilimi sannan kuma a kai ga matsayi na koli tattare da kula da dukkanin wadannan abubuwa. Sannan kuma samuwarku yana iya zama wani misali na wannan sako na Musulunci ga duniya.