XtGem Forum catalog
Uzairu badamasi

BARKA DA ZUWA SHAFI MAI ALBARKA

Alhamdulillah muna muku albishir insha Allah zamu dawo aiki gadan gadan!


Shafin farko

Haidar Ali

Hadin Kan Musulunci Da Cutarwar Rarrabuwa A Duniyar Musulmi

“Fatan da nake da shi, shi ne cewa rayuwata ta zamanto bisa tafarkin hadin kai tsakanin musulmi; haka nan mutuwa ta, ta kasance bisa tafarkin hadin kai tsakanin musulmi”

Ali Khamenei5

Matsayi Da Karfin Al’ummar Musulmi

Wadannan al’ummomi ‘yan’uwa masu kaunar juna da suka fito da launuka daban-daban na daga bakaken fata, fararen fata da shudi sannan kuma suke magana da daruruwan harsuna, dukkaninsu suna ganin kansu ne a matsayin wani sashi na al’ummar musulmi mai girma sannan kuma suna alfahari da hakan. A kowace rana kuwa suna kallon bangare guda ne da kuma harshe guda suna neman dauki daga wajen Allah, sannan kuma daga wajen saukakken littafi guda suke daukan darasi da samun ilhami.
Wadannan mutane da ake kiransu da sunan al’ummar musulmi suna da wata wadatacciyar al’ada da kuma abin gado mai girman gaske wadda kuma take tare da gagarumin ci gaba maras tamka da ke cike da abubuwa daban-daban. Suna amfanuwa da irin hadin kai da fahimtar juna da aiki kafada da kafada (da ke tsakaninsu) wanda ya samo asali daga tasiri na Musulunci da tauhidi cikin dukkanin bangarori da rukunansu.
Al’ummar musulmi suna da kayan aiki masu yawa da za su iya amfani da su wajen kare hakkokinsu da kuma samuwarsu. Al’ummar musulmi wata al’umma ce mai girman gaske; tana da gagarumar dukiya; tana da mutane da suka yi fice a bangarori daban-daban sannan kuma ga jari irin na ruhi da kusaci da Allah wanda hakan ya ke ba wa mutanenta karfin tsayin daka wajen fuskantar masu son amfani da karfi; musulmi suna da wayewa da ci gaba na tsawon lokaci wanda a duniya ba shi da na biyu; suna da abubuwa da albarkatu da yawan gaske. A saboda haka musulmi suna iya kare kansu. A yau wajibi ne duniyar musulmi su yi duk abin da za su iya wajen kare girma da daukakarsu; wajen tabbatar da ‘yancinsu; wajen tabbatar da ci gabansu na ilimi da karfi na ruhi; wato riko da addini da kuma dogaro da Allah da kuma samun yakini da tabbaci na taimakon Allah Madaukakin Sarki.
“Alkawarinka ga bayinKa abin cikawa ne ”[1]wannan alkawarin Allah ne; alkawari ne na Ubangiji da za a cika shi cewa “Lalle Allah zai taimaki wanda ya taimake shi ”[2] Ta hanyar dogaro da wannan alkawari ne, za su shiga cikin fagen motsi da yunkurawa. Wannan aikin, ba wai kawai daukan bingida ba ne; wannan aiki, aiki ne na tunani, aiki ne na hankali, aiki ne na ilimi, aiki ne na zamantakewa, aiki ne na siyasa; dukkanin hakan saboda Allah da kuma tafarkin hadin kai na Musulunci ne. Al'ummomi suna amfanuwa da hakan, hakan nan gwamnatocin kasashen musulmi.

Ma’anar Hadin Kai Da Zumunci Na Musulunci

Ma’anar hadin kai wani lamari ne mai saukin gaske (wajen fahimta) wanda kuma yake a fili, hakan kuwa shi ne samun fahimtar juna da aiki kafada da kafada tsakanin kungiyoyi da mazhabobin musulmi da junansu ba tare da fuskantar juna da kuma fada a tsakaninsu ba. Abin nufi da hadin kai tsakanin musulmi shi ne cewa kada (musulmi) su dinga kore junansu, kada su ba dama ga makiya su sami dama da iko da mulki a kan juna, sannan kuma kada wani bangare ya zalunci daya bangaren.
Ma’anar hadin kai tsakanin al’ummomin musulmi, ita ce cewa a yi tafiya tare cikin batutuwan da suka shafi duniyar musulmi, su taimaki juna sannan kuma kada su yi amfani da abin da suke da shi da kuma karfin da suke da shi wajen cutar da junansu.
Hadin kai tsakanin musulmi ba yana nufin musulmi su yi watsi da mazhabobin da akidun da suke da su ba ne; face dai hadin kai tsakanin musulmi yana da ma’ana biyu ne, wadanda wajibi ne a samar da wadannan abubuwa biyun: na farko shi ne cewa kungiyoyi da mazhabobi daban-daban da ake da su – wanda kowane guda daga cikin su yana da akidar da kuma hukumce-hukumce irin na fikihun da ya kebanta da su – su hada kansu waje guda da aiki kafada da kafada wajen fada da makiya Musulunci. Na biyu shi ne cewa kungiyoyi da mazhabobi daban-daban na Musulunci su yi dukkanin iyakacin kokarinsu wajen ganin su kusaci junansu, a samar da fahimtar juna a tsakaninsu sannan kuma su hada da kwatanta dukkanin mazhabobi na fikihun da suke da su da junansu. Akwai da dama daga cikin fatawoyin malaman fikihu wadanda idan aka gudanar da bahasi na fikihu da kyau cikin ilimi da kwatanta su da junansu, mai yiyuwa ne ta hanyar ‘yar karamar gyara, a iya kusata fatawoyi mazhabobi guda biyu da junansu.



Ababen da Suke Tabbatar Da Hadin Kai Da Zumunci Na Musulunci

Tauhidi

Cikin al’ummar da ta yi imani da tauhidi, a duk lokacin da ya zamana tushe da kuma Ma'abocin halitta kuma mai iko da duniya, rayayye kuma tsayayye, wanda dukkanin rayuwa da duk wani abin da ya ke duniya suka ta’allaka da karfi da iradarsa ne, ya zama shi kadai ne, to mutane – shin bakaken fata ne ko fararen fata ko kuma masu wani launi na daban da kabilu daban-daban da kuma yanayi na zamantakewa mabambanta – za su zamanto tare da junansu; don kuwa suna da alaka da wancan Ubangijin ne, suna da alaka da wani waje guda ne sannan kuma suna samun taimako da dauki ne daga waje guda. Wannan wani sakamako ne na tilas na imani da kuma tauhidi. A bisa wannan mahangar, ba wai kawai mutane suna da alaka da junansu ba ne, face dai a mahanga ta tauhidi, dukkanin komai da bangarori na duniya da dabbobi da ababe marasa rai da kassai da sammai da dukkanin komai, suna da alaka da junansu sannan kuma suna tafiya tare da dan’adam. A saboda haka, dukkanin abin da mutum ya ke gani sannan kuma ya ke ji da kuma fahimtarsa, wani fage da kuma wata duniya da kuma wasu gungun abubuwa ne da suke cikin wata duniya lafiyayyiya da kuma wani fage dake cike da tsaro da zaman lafiya.

Siffa Ta Musulunci

A yau dukkanin musulman duniya, a duk inda suke a fadin duniyan nan – shin a kasashen musulmi ne, ko kuma a sauran bangarorin da su ne ‘yan tsiraru – za a ga cewa suna jin kishin addini da riko da Musulunci da kuma neman mutumci da kuma matsayinsu na Musulunci. A yau masanan duniyar musulmi, wadanda suka kosa daga tsarin gurguzu da koyarwar kasashen yammaci, sun kama hanyar kaunar Musulunci suna neman maganin matsalolin da bil’adama suke fama da su cikin Musulunci, suna kuma neman karin bayani. A yau zukatan al’ummar musulmi sun kama hanyar riko da addinin Musulunci da kuma kishinsa wanda ba a taba ganin irin sa ba cikin karnonin da suka gabata. Bayan shekara da shekaru na iko da mulkin mallaka na siyasa da al’adu da kasashen yammaci da gabashi suka yi wa kasashen musulmi, a yau dukkanin idanuwan matasan duniyar musulmi sun koma ne ga Musulunci; wannan wata hakika ce; su kansu mutanen yammaci da sauran ma’abota girman kan duniya sun tabbatar da hakan. Abin da ma’abota girman kan duniya suke tsoro, shi ne irin wannan jin riko da Musulunci da kuma alfahari da kasantuwansu musulmi. Hakan shi ne abin da ya ke tabbatar wa musulmi da hadin kai da tafiya tare da juna.

Addinin Musulunci

Addinin Musulunci abu ne wanda yake sanya al’ummar musulmi su dinga jin cewa akwai wata alaka a tsakaninsu da kuma hadin kai sannan kuma hakan ne zai sanya wannan adadi na mutane biliyan guda da wasu daruruwan miliyoyin musulmi su zamanto masu tsoma baki cikin batutuwa daban-daban da suka shafi duniyar musulmi.
A addinin Musulunci mai tsarki, hadin kai wani asali ne na asasi. Kama daga Allah Madaukakin Sarki – wanda shi ne asali da tushen hadin kai da tauhidi – har zuwa ga tasirin wannan hadin kai wanda ya hada da dukkanin halitta zuwa ga wannan cibiya mai girma ta koli
“Dukkan kowannensu masu komawa zuwa gare Ni ne ”[3] dukkanin komai zai koma ne zuwa ga zati mai tsarki na Allah Madaukakin Sarki; “Zuwa ga Allah ne makoma take ”.[4] Wajibi ne hadin kai ya zamanto bisa asasin Musulunci da kuma riko da igiyar Allah, ba wai bisa asasin wasu tunani marasa tushe da kuma kabila ba. Da hakan ne ake samun girma na Musulunci. Wajibi ne hadin kai ya zamanto wajen tabbatar da iko na musulmi; idan kuwa ba haka ba to zai zamanto maras ma’ana.

Alkur’ani

Alkur’ani mai girma ya kasance yana kiran musulmi zuwa ga hadin kai. Alkur’ani mai girma ya ja kunnen musulmi da cewa matukar kuka yi watsi da hadin kai da fahimtar junan da ke tsakaninku, to kuwa za a kawar da irin karfi da matsayi da mutumcin da kuke da shi. Abin bakin cikin shi ne cewa a yau ana iya ganin wannan bala’in cikin al’ummar musulmi. A yau irin makirce-makircen da ake kulla wa al’ummar musulmi makirci ne mai girma da nauyin gaske. Idan har a yau kuna ganin yadda (makiya) suka kara kaimi wajen kulla makirci wa Musulunci ba kyakkyaftawa, to saboda wayewar da al’ummar musulmi suka samu ne ya sanya makiya din cikin damuwa. Ma’abota girman kan duniya, masu kwadayin (albarkatun) kasashen musulmi da kuma masu tsoma baki cikin gwamnatoci da kasashen musulmi suna tsananin damuwa da jin tsoron hadin kai tsakanin musulmi ne.
Musulunci yana magana ne da “Ya ku wadanda kuka yi imani” ba wai “Ya ku wadanda kuka zama ‘yan Shi’a” ba ko kuma “Ya ku wadanda kuka zama ‘yan Sunna” ba, ana magana ne da muminai. Muminan da suka yi imani da me? Wadanda suka yi imani da Alkur’ani, wadanda suka yi imani da Musulunci, wadanda suka yi imani da Annabi. Kowane guda yana da akidar da ya rika wadanda suke da bambanci da na dan’uwansa. A lokacin da aka ce:
“Kuma ku yi riko da igiyar Allah gaba daya, kuma kada ku rarraba ”[5]ana magana ne da muminai; ba wai magana ne da wata jama’a ta muminai ba. A lokacin da aka ce: “Kuma idan jama’a biyu ta muminai suka yi yaki (fada), to ku yi sulhu a tsakaninsu ” [6] ana magana ne da wadannan muminan; ba wai ana magana ne da wata jam’a ta muminai ba ne. Ta hanyar wannan tushe da ginshiki ne Musulunci zai iya kawo karshen irin wannan tushe na rikici na mazhaba da ya mamaye dukkanin bil’adama.
Alkur’ani mai girma yana cewa:
“Kuma ku yi riko da igiyar Allah gaba daya, kuma kada ku rarraba ”[7]riko da igiyar Allah ga dukkanin musulmi wani nauyi ne da ke wuyansu; to sai dai Alkur’ani mai girma bai takaita da kiran musulmin da cewa su yi riko da igiyar Allah kawai ba, face dai yana cewa ne musulmi su yi riko da igiyar Allah a yanayi na gaba dayansu; wato “gaba dayansu”, wato kowa da kowa, gaba dayansu. Wannan gaba dayan da wannan hadin kan, shi ma wani wajibi ne na daban. A saboda haka, musulmi ba ya ga cewa wajibi ne su yi riko da igiyar Allah, haka nan kuma wajibi ne wannan riko da igiyar Allah ya zamanto na gaba daya ne tsakanin musulmi dukkaninsu. Wajibi ne a fahimci wannan riko da igiyar Allah sannan kuma a aikata hakan. Ayar Alkur’ani mai girma tana cewa: “A saboda haka wanda ya kafirta da Dagutu kuma ya yi imani da Allah, to, hakika, ya yi riko da igiya amintacciya ” [8]hakan yana ba wa riko da igiyar Allah ma’ana. Riko da igiyar Allah yana tafiya ne tare da kafirta daga dagutu.

Manzon Allah (s.a.w.a)

Annabi mai girma kuma Manzon Allah (tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi da alayensa) shi ne mafi muhimmancin abin tabbatar da hadin kai (tsakanin musulmi). A baya ma na fadi hakan cewa al’ummar musulmi suna iya haduwa kan wannan ginshikin; don kuwa waje ne da dukkanin so da kaunar musulmi suka taru; shi ne tushen kauna da soyayya ta duniyar musulmi. A halin yanzu kuna ganin yadda wasu alkalumma da suka karbi kudade daga wajen yahudawan sahyoniya suke ta kai hari kan wannan ginshikin da kuma ci masa mutumci; don a sannu a hankali su sami damar kawar da irin muhimmancin da cin mutumcin al’ummar musulmi da kaskantar da duniyar musulmi yake da shi (cikin zukatan al'umma, wato irin yadda suke nuna damuwarsu kan hakan). Wannan shi ne batu na asali; zai yi kyau idan ‘yan siyasar mu, masananmu na ilimi da al’adu, marubutanmu, mawaka da masu ayyukan adabinmu su ba wa hakan muhimmanci sannan kuma dukkanin musulmi su sami kusaci da junansu da kuma wannan take. Kada su damu da bangarorin da ake da sabani a cikinsu, kada su dinga tuhumar junansu, kada su dinga kafirta junansu sannan kuma kada su dinga fitar da junansu daga da’irar Musulunci. Zukatan al’ummar musulmi a duk fadin duniyar musulmi suna samun nishadi da farin ciki cikin tunawa da Annabi da kuma nuna kauna ga Manzon Allah (s.a.w.a). Dukkanin mu masu so da kaunar wannan mai girma ne.

Ahlulbaitin Annabi (amincin Allah ya tabbata a gare su)

Daga cikin abubuwan da za su iya zama ginshiki da kuma abin da za a iya zama karkashin inuwarsa wajen tabbatar da wannan hadin kan sannan kuma dukkanin musulmi su zamanto suna da ra’ayi guda kansa, shi ne koyi da Ahlulbaitin Annabi (s.a.w.a.). Don kuwa dukkanin al’ummar musulmi sun yi imani da Ahlulbatin Annabi.
Duniyar musulmi za ta iya samun hadin kai da hadin baki cikin abubuwa guda biyu da suka shafi Ahlulbaiti: daya daga ciki shi ne so da kauna wanda wani lamari ne na zuci da kuma akida saboda an umurci musulmi da su so Ahlulbaiti (tsira da amincin Allah su tabbata a gare su) sannan kuma dukkaninsu sun yi imani da hakan. Hakan yana iya zama abin da dukkanin zukatan musulmi za su koma gare shi. Abu na biyu, koyarwa ta addini da kuma hukumce-hukumcen Ubangiji wanda ya ke a matsayin adalci na Alkur’ani da kuma Hadithul Thakalain, wanda Shi’a da Sunna da sauran kungiyoyi na Musulunci duk sun ruwaito shi.


Gwarzon Namijin Tarihin Bil’adama

Kaunar Amirul Muminin (tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi) da son wannan babban mutum na cikin tarihin bil’adama da kuma tarihin Musulunci, ba lamari ne da ya kebanci ‘yan Shi’a kawai ba, hatta ma ba abu ne da ya kebanci musulmi ba; face dai wannan wani lamari ne da ma’abota ‘yanci na duniya suka yi tarayya da musulmi a cikinsa. Mutanen da ba ma musulmi ba ne, sun kasance masu nuna so da kauna ga wannan mutum mai haske da haskaka, sun rubuta littafa da kuma rera masa wakoki. Babban kuskure ne idan aka dauki Amirul Muminin Aliyu bn Abi Talib a matsayin wata hanya ta haifar da rarrabuwa tsakanin musulmi. Wannan ma’abocin girma wata halitta ce wacce dukkanin musulmi da kuma dukkan mazhabobin Musulunci sun kasance masu so da kaunarsa. Irin wannan alaka da kuma kauna suna daga cikin siffofin na asali wadanda dukkanin wani mutum mai adalci zai mika musu wuya; wannan shi ne abin da dukkanin al’umma suka yi tarayya kansa.


Sunna Da Tarihin Rayuwar Ma’asumai (a.s.)

Hadin Kai Cikin Magana Da Tsarkakar Zukata

Abu na uku da (Amirul Muminin, amincin Allah ya tabbata a gare shi) ya yi ishara da shi cikin wasiyyar da ya yi da ‘ya’yansa biyu wato Hasan da Husaini shi ne ‘kyautata tsakanin mutane biyu’. Wato mutane su kasance masu kyakkyawar alaka a tsakaninsu. Zukata su kasance tare da juna. Su zamanto suna da magana guda sannan kuma kada a sami sabani da kaurace wa juna. Yayin da ya kawo wannan jumla, sai ya hada ta da wata shaida da hujja daga wajen Ma’aikin Allah (s.a.w.a.). Ya kasance mai jaddada hakan sannan da kuma nuna damuwarsa. Ba wai cewa kyautata tsakanin mutane biyu muhimmancinta ya fi muhimmancin umurni da tsara lamurra ba ne; sai dai saboda rashin kyautata tsakanin ya fi cutarwa. A saboda haka ne ya ke nakalto wannan jumla daga wajen Annabi (s.a.w.a.) yana cewa: na ji kakanku yana cewa: “Kyautata tsakani ta fi (kowace) salla da azumi ”[9]kyautata tsakanin mutane da kyautata alaka tsakanin mutane ta fi kowace irin salla da azumi. “ta fi kowace salla da azumi”. Idan kuna so ku je ku yi salla da azuminku. To amma akwai wani aiki wanda falalarsa ta fi dukkanin wadannan biyun. Mene ne wannan abin? Shi ne “kyautata tsakani”. Idan kuka ga a wani waje cikin al’ummar musulmi an sami sabani da rikici, to ku tafi wajen ku kawo karshen wannan rikicin. Falalar hakan ta fi ta salla da azumi.

Dan’uwa na Addini Da Abokin Tarayya Cikin ‘Yan’adamtaka

Sakon Musulunci, sako ne na hadin kai da tsaro da kuma ‘yan’uwantaka. Amirul Muminin (amincin Allah ya tabbata a gare shi) yana da wata jumla ta har abada dangane da dukkanin mutane. Yana cewa: wannan mutumin da ya ke gabanka, imma dai dan’uwanka ne na addini, ko kuma dan’uwantaka ne da kuka yi tarayya da shi cikin halitta, ta kowace fuska shi mutum ne. Wajibi ne dukkanin mutane su kasance masu hadin kai a tsakaninsu da kuma nuna rahama da jin kai wa juna; hakan kuwa ba lamari ne da ya shafi wata jama’a ko kuma wata kungiya ba. A saboda haka ne a Musulunci, aka umurci musulmi cewa hatta mutanen da kuke da sabani da su cikin addini da akida, ku kyautata alaka da su. Allah Madaukakin Sarki yana cewa: “Allah ba Ya hana ku, daga wadanda ba su yake ku ba saboda addini kuma ba su fitar da ku ba daga gidajenku ba, ga ku kyautata musu kuma ku yi musu adalci. Lalle Allah Yana son masu adalci ”[10] Wannan shi ne ra’ayin Musulunci. Wato mutumin da ma kuke da sabani na tunani da akida da shi, wanda yake da wata akida ta daban, to nan ba shi ne wajen muzguna masa ba, ba kai ne abin koyinsa ba. “Allah ne mai hukumci, sannan kuma wajen komawarsa ita ce kiyama ”.[11] Wannan ma maganar Amirul Muminin (a.s) ce. Kai din nan kana fuskantar wani mutum ne wanda ko dai wanda kuka yi tarayya cikin akida da ‘yan’uwantaka ne, ko kuma bai kasance wanda kuka yi tarayya cikin akida da shi ba to amma kun yi tarayya cikin halitta da shi.

Jamhuriyar Musulunci ta Iran

Makiya dai sun gwada hanyoyi daban-daban wajen haifar da rikici tsakanin al’ummar musulmi. A yau suna fuskantar wani sabon lamari ne wanda shi ne cibiyar hadin kan dukkanin musulmi, hakan kuwa shi ne ‘Jamhuriyar Musulunci’. Wannan dagaggiyar tuta da kuma karfafafiyar murya, wani sabon lamari ne wanda kundin tsarin mulkinsa da kuma taken da yake rerawa suna cikin koyarwar Musulunci ne don haka a dabi’ance zai janyo hankulan zukatan musulmi a duk fadin fadin duniya. A yau, babu wani waje da yake neman aiwatar da hukumce-hukumcen Musulunci da dukkan wannan karfi. Abin nufi ba shi ne al’ummomi ba; don kuwa su al’ummar musulmi a duk inda suke zukatansu suna son Musulunci sannan kuma a shirye suke su yi aiki da Musulunci. Abin nufin shi ne siyasun da ake gudanarwa da tsarurruka da gwamnatoci wadanda idan har ma sun faro ne da sunan Musulunci, amma a duk lokacin da suka fuskanci tsananin takurawa da barazana ta duniya, sai su ja da baya.
A saboda haka bayan nasarar juyin juya halin Musulunci a Iran da kuma yaduwar tunani da koyarwar hakan a duk fadin duniyar musulmi, daya daga cikin hanyar da ma’abota girman kan duniya suka dauka wajen fada da irin wannan yaduwar Musulunci a ko ina da juyin juya halin Musulunci na Iran ya samar shi ne su bayyana juyin juya halin Musulunci na Iran din a matsayin wani yunkuri na ‘yan Shi’a da ma’anarsa ta kungiyanci – ba wai da ma’ana ta gaba daya ta Musulunci ba – sannan a wani bangaren kuma sun yi ta kokarinsu wajen haifar da kiyayya da munafunci tsakanin ‘yan Shi’a da ‘yan Sunna. Mu dai tun farko, saboda la’akari da wannan makirci da shaidanci, mun kasance a ko da yaushe muna jaddadawa kan hadin kai tsakanin musulmi kuma mun yi dukkanin kokarinmu wajen ganin mun kashe wutar wannan fitina kuma da yardar Allah da falalarsa mun samu nasarori daban-daban (a wannan fagen), wanda daya daga cikin hakan shi ne kafa majalisar kasa da kasa ta kusato da mazhabobin Musulunci. Tun farkon juyin juya halin Musulunci har ya zuwa yanzu Jamhuriyar Musulunci ta Iran ta kasance tana kiran kasashen musulmi zuwa ga hadin kai a tsakaninsu. Idan har a ko da yaushe Iran ta kasance tana kokarin kiyaye ‘yan’uwantaka da abokatakanta da gwamnatocin kasashen musulmi, ba wai saboda gwamnati ko kuma al’ummar Iran suna da wata gagarumar bukata da wannan alakar ba ce; sai dai saboda dukkanin duniyar musulmi za su amfana ne daga irin wannan alaka.



Amfanonin Hadin Kai Da Zumunci Na Musulunci

Nasara Da Daukakar Musulmi

Wajibi ne musulmi su fahimci irin karfin da suke da shi – wanda shi ne irin wannan karfi na imani da hadin kai da aiki kafada da kafada tsakanin kasashen musulmi – sannan kuma su dogara da hakan. Matukar dai kasashen musulmi suka hada hannunsu waje guda, za su zamo tsintsiya madaurinki guda (za su zamanto wani karfi), to a irin wannan lokacin makiya ba za su sami jaruntakar tsayawa a gabansu ba da kuma tilasta wa wadannan kasashe abin da suke so ba. Matukar musulmi suka kama hannayen juna suka kasance masu kaunar junansu, ko da kuwa akidojinsu sun saba wa juna, amma ba su zamanto wani kayan aiki a hannun makiya ba, to kuwa duniyar musulmi za ta sami daukaka.
A duk inda al’umma suka kasance a wajen, suka ci gaba da kiyaye wannan kasantuwa ta su sannan kuma suka yi hakuri da wahalhalun da ke tattare da hakan, ba abu ne mai yiyuwa ba masu karfi na duniya – Amurka da makamantanta – su sami damar aiwatar da abin da suke son aiwatarwa a kan su. Al’ummomi dai su ne masu yin nasara. Wannan wata hakika ce. Matukar dai al’ummar musulmi tana son ta ciyar da irin wannan yunkuri na ta gaba da kuma ci gaba da samun nasara, wajibi ne su yarda da wasu abubuwa, wanda na farkonsa shi ne hadin kai.


Nasara Kan Matsaloli

Matukar musulmi suka hada kansu waje, matukar suka farka, matukar suka fahimci irin karfin da suke da shi, matukar suka amince da cewa ana iya sauya irin yanayin da ake ciki a halin yanzu sannan kuma suna iya samun iko kan makomarsu, haka nan kuma idan har suka fahimci yadda wasu al'ummomin irin su al'ummar Iran masu girma suka sami nasarar samun iko kan makomarsu sannan kuma ba su zamanto karkashin ikon manyan kasashen duniya ba, to su san da cewa ko shakka babu matsalolin da duniyar musulmi take fuskanta za su kawo karshe. A yau wannan shi ne ginshikin dukkan komai.
Ba godo ba, ba mika kai ba, ba tattaunawar sulhu ba, ba kuma kowane guda daga cikin hanyoyin da wadansu masu saukin tunani suke gabatar wa musulmi ba, dukkanin wadannan ba hanyoyi ne da za su tseratar da musulmi ba. Abu guda ne kawai maganin, hakan shi ne hadin kai, riko da Musulunci da kuma koyarwarsa, tsayin da ka wajen fuskantar matsin lamba da toshe hanyoyi ga makiya.
A yau maganin da duniyar musulmi take bukata yana cikin komawa ne ga Musulunci, da ababen da suke kusata mutum da Ubangiji da hukumce-hukumcen Musulunci sannan kuma musulmi su tabbatar da hadin kai a tsakaninsu wanda hakan ya samo asali ne daga hukumce-hukumcen Musuluncin. Wato wannan jaddadawa da Musulunci ya dinga yi kan hadin kai tsakanin musulmi da kuma kawar da kiyayya da gaba da kulla makirce-makirce a tsakaninsu.


Karfafa Tattalin Arziki Da Karfi Na Siyasa

Kasashen musulmi dai ba su da wani fada da karo da juna cikin manufofi. A samu wata jama'a ta musulmi, wani gungun na musulmi (waje guda) lamari ne mai kyau da zai amfani kowa, ba wai kawai ga wata jama'a ta musamman ba. Manyan kasashen musulmi ma za su amfana daga samun kasashen musulmi a dunkule; kasashe masu rauni da kanana wadanda kuma suke fama da talauci ma za su amfana. Hakan abu ne da zai amfani kowa. Ko shakka babu idan da kasashen musulmi ba su goyi bayan musulman kasar Bosniya ba, to da a halin yanzu babu wani labarin mutanen Bosniya a kasashen Turai, da tuni aka kawar da su.
Tun daga waje mafi nisa na yammacin duniyar musulmi a halin yanzu – wato yammacin nahiyar Afirka – har zuwa ga karshen gabashin duniya – wato zuwa gabashin asiya, duniyar musulmi ne inda musulmi suke zaune. Mafi muhimmancin yankunan duniya, suna hannun musulmi ne. Daya daga cikin irin wadannan yankuna shi ne wannan yanki na Tekun Fasha wanda dukkanin duniya suka kasance cikin sahun kokarin cika jakkunansu daga albarkatun kasar da wannan yanki yake da shi sannan kuma su koma inda suka fito. Dukkanin duniya tana bukatar man fetur din wannan yankin. Matukar al'ummar musulmi suka hada kansu waje guda, to kuwa duniyar musulmi za ta amfana sosai.


Mulki Da Iko

A halin da ake ciki, (makiya) suna ta kokari ba kama hannun yaro wajen ganin al'ummar musulmi ba su hada kansu waje guda da kuma aiki tare da junansu ba. Bukatar da musulmi suke da ita zuwa ga hadin kai ta kan karu sama da kowane lokaci ne a lokacin da wadannan kokari suka karu ne. A bisa tunanin da ya yi kusa da hakika, shi ne cewa manufar dukkanin wannan kokari ita ce su hana fatan da ake da shi na iko da kuma mulki na Musulunci – wanda a halin yanzu ya kusa cimma gaci. A dabi'ance ya ke cewa matukar Musulunci yana son samun iko sannan kuma musulmi suna so su yi riko da Musulunci, to hakan ba abu ne mai yiyuwa ba cikin irin wadannan sabani. Mafi munin cikas din da ke bisa kan hanyar samun iko da mulkin Musulunci shi ne cewa musulmi a lokacin mulkin Musulunci – shin a wata kasa ce guda ko kuma a wasu kasashe daban-daban na musulmi; babu wani bambanci cikin hakan – su fada wa junansu.


Abubuwan Da Suke Haifar Da Rarrabuwa

Shirka

Irin tunanin da suke cike da shirka, su kan rarraba kan mutane. Al'ummar da aka gina ta bisa asasin shirka, za ta raba al'ummar bil'adama da mai she su baki dangane da junansu. A lokacin da ya kasance a wata al'umma wacce ta gurbata da shirka, a duk lokacin da aka gabatar da batun tushen Ubangiji da karfin da ke juya duniya, to a dabi'ance mutane za su kasance a rarrabe a tsakaninsu; wani yana bauta wannan Ubangijin, wani kuma ga wani Ubangijin, na uku kuwa da wani Ubangijin. Al'ummar da ta ginu bisa shirka, tsakanin al'ummomi da kabilu, akwai wata katanga wacce ba za a iya kutsa ta ba, sannan kuma akwai wata hanya wacce ba za a iya hada ta ‘yar’uwarta ba.

Shaidan

A duk inda aka sami sabani tsakanin muminai da kuma tsakanin bayin Allah na gari, to kuwa ko shakka babu shaidan da makiya Allah suna wajen. A duk inda kuka ga akwai sabani, to ku duba ku gani, ba tare da wata matsala ba za ku ga shaidan a wajen ko kuma (za ku ga) shaidanin da ke cikin zukatan su kansu mutane wanda ake kira da ruhi mai umurni da mummunan aiki, wanda hakan shi ne mafi muni da hatsarin shaidan. A saboda haka, a gafen duk wani sabani ko dai son zuciya ne a wajen ko son matsayinmu ne ko kuma shaidani na waje, wato hannayen makiya da ma'abota girman kai da azzalumai masu karfi na duniya.

Jahilci Da Gurguwar Fahimta

Idan har kuka ga al'ummar musulmi tana fuskantar matsalar rarrabuwa, hakan tana faruwa ne saboda musumi sun gagara fahimtar cewa hadin kai daga cikin addini ya ke. A yau rana ce wacce wajibi ne al'ummar musulmi, shin fitattu na siyasa da al'adu da addini ne ko kuma sauran mutanen gari, su kara yin taka tsantsan sama da na shekarun baya, su fahimci irin yaudarar makiya sannan kuma su yi fada da hakan. Daya daga cikin yaudarar da suka fi ci da kuma haifar da wutar fitinar rarrabuwa ita ce wajen amfani da kudade da kuma kokari ba kama hannun yaro wajen ganin musulmi sun shagaltu da sabani a tsakaninsu. Sannan kuma a wannan karon ma su yi amfani da gafalarmu da kuma gurguwar fahimta da tsaurin ra'ayi wajen haifar da rikici da sabani a tsakaninmu.
Cikin wadansu mazhabobin na yau, akwai karancin fahimta. Idan dai ba su ba, to dukkanin duniyar musulmi kafirai ne; duk wani wanda yake nuna kauna ga Manzon Allah (s.a.w.a.) kafiri ne?! Duk wani mutumin da ya nuna farin cikinsa a ranar maulidin Annabi, ya raba alawa tsakanin mutane (don murna), kafiri ne?! Mene ne dalilin irin wannan kuncin fahimta? Mu dai mun yi tsananin farin ciki cewa alhamdu lillahi, cikin irin wannan rarrabuwa, mun sami nasarar mika hannuwanmu da kuma kama hannun sauran musulmi.


Tsauri Ra'ayi Na Kabilanci

Akwai wani lokaci a baya da ake karfafa da kuma yada kabilanci, 'yan kasanci (mai muni), (fifita) harshe, jini da makamantan hakan a tsakanin al'ummar musulmi. A fili yake cewa irin wannan yanayin wani mafari ne na rarraba bangarorin al'ummar musulmi daga junansu. Mun ga dai yadda batun farisanci da Iraniyanci na wuce gona da iri da kuma komawa ga irin tsaurin ra'ayi da tunanin da ke cike da kura-kurai da suke da alaka da kabila da jini ya dinga yaduwa a lokacin tsohuwar gwamnatin da ta shude a wannan kasar. Saboda me? Wata fa'ida hakan take da ita ga al'ummar Iran? In ba cutarwa ba, ba ta da wani tasiri na daban. Mafi muhimmanci da girman cutarwar da hakan ta haifar ita ce raba al'ummar Iran da sauran al'umomi na musulmi sannan da kuma haifar da yanayin kiyayya da kyama tsakanin wannan al'umma da sauran al'ummomi. Irin hakan ne suka yi wa al'ummar larabawa. Irin hakan suka yi da wasu kabilu da al'ummun wannan yanki sannan kuma suna ci gaba da yi.

Masu Iko

Sabani da karo da juna da fada da yake-yake da gaba da kiyayya wasu lamurra ne da tun karnoni aru-arun da suka gabata kuma har zuwa yau din sun kasance a tsakanin kabilu da kungiyoyi daban-daban na Musulunci sannan kuma a ko da yaushe hakan lamari ne da ya ke cutar da musulmi. Cikin tarihin Musulunci, dukkanin ko kuma wani bangare mai girman gaske na irin wadannan sabani da karo da juna da fadace-fadace sun samo asali ne daga wajen cibiyoyin masu karfi na duniya. Tun daga sabani na farko-farko – wato batun halittar Alkur'ani da makamantan hakan – har zuwa ga sauran sabanin da suka kasance tsawon tarihi tsakanin kungiyoyin musulmi – musamman a lokuta masu yawa tsakanin Shi'a da Sunna – da suka faru, a mafi yawan lokuta masu karfi na duniya su ne suke haifar da irin wadannan sabani. Ko da yake jahilci na gaba daya da tsaurin ra'ayi wanda bai dogara da wani mandiki da kuma irin tunzura juna da ake yi suna da tasiri, amma wadannan abubuwa share fage ne kawai kuma babu guda daga cikinsu da ya haifar da irin wannan lamari na zubar da jini da ya faru cikin tarihi. Wadannan lamurra masu girman gaske suna komawa ne ga wadannan masu karfi wadanda suke neman samu amfani cikin irin wadannan sabani. A lokacin da mulkin mallaka ya shigo cikin kasashen musulmi – a wasu kasashen kai tsaye, a wasu kasashen kuma ba kai tsaye ba – ya bayyana cewar wannan lamari shi ne abin da suke son cimmawa.

YunkureYunkuren Haifar Da Rarrabuwa Cikin Duniyar Musulmi

A yau a duniya saboda gina masallaci mai cutarwa[12] , ana kashe makudan kudade. Sannan don gina cibiyoyi da share fagen cutar da hadin kai na Musulunci da kuma haifar da rikici da yake-yake tsakanin kungiyoyin Musulunci, ana kashe makudan kudade. Akwai wadansu mutane wadanda suka kasance tamkar shaidan kamar yadda ya gaya wa Allah Madaukakin Sarki cewa:"Kuma hakika ina batar da su gaba daya "[13]ya sanya samuwarsa ta kasance wajen batar da bayin Allah, su din nan ma sun sanya kansu wajen haifar da rarrabuwa tsakanin mutane.
Babbar alamar wannan farkawa ta Musulunci ba wai su ne wadannan mutane wadanda a yau suke nan suna ta aikata ayyukan ta'addanci a duniyar musulmi ba. Mutanen da suke aikata irin wannan danyen aiki a kasar Iraki; mutanen da a duniyar musulmi da sunan Musulunci suke aikata mummunan aiki a kan musulmi; mutanen da mafi muhimmancin ayyukansu shi ne haifar da sabani da rikici tsakanin musulmi – karkashin inuwar Shi'a da Sunna, ta hanyar fakewa da batun kabilanci – wadannan mutane ne da babu yadda za su iya zama wata alama ta farkawar Musulunci. Wannan lamari ne da su kansu ma'abota girman kan sun san da shi. Su kansu wadannan mutane da suke kokarin bayyanar da Musulunci ta fuskar wadannan mutane da suka ci baya ga kasashen yamamci, sun san cewa wannan ba shi ne hakikanin Musulunci ba. A yau masu haifar da sabani a duniyar musulmi suna ta kokari wajen gani sun bakanta fuskar mazhabar Ahlulbaiti, ta yadda za a kyamace ta. A yau da dama daga cikin malaman fada wadanda suke da alaka da ma'abota girman kan duniya a kasashe daban-daban hatta kafirta 'yan Shi'a ma suke yi. A yau haifar da sabani tsakanin 'yan Shi'a da 'yan Sunna manufa ce ta Amurka; manufa ce ta 'yan mulkin mallaka na duniya sannan kuma manufa ce ta gwamnatoci 'yan amshin shatansu.


Wasu Gwamnatocin Kasashen Musulmi

Dukkanin irin wadannan albarkatun kasa, dukkanin irin wannan dukiya, dukkanin wadannan makami da ke hannun kasashen musulmi da kuma al’ummar musulmi. Da wani dalili ne ba za mu iya kare kanmu ba? Saboda kan mu ba a hade ya ke ba ne. Me ya sa kan mu ba a hade ya ke ba? Saboda gwamnatocin da ya zama wajibi su hada kawunansu waje guda suna da manufofi daban-daban ne: manufofi na kishin kasa, manufofi na kafirta juna, da manufofi da suka saba wa Musulunci. To amma al’ummominsu kan zukatansu a hade suke. Wasu al’ummomi guda biyu ne suke da gaba da kiyayya da junansu?
Al’ummomin Iran da Iraki, bayan shekaru takwas na yaki, amma haka suke rungumar junansu. Yaki dai ba shi da alaka da al’ummomi; sabani ba lamari ne da ya shafi al’ummomi ba; face dai abu ne da ya shafi gwamnatoci wadanda suke da manufofi wadanda ba na Musulunci ba. Wajibi ne a magance hakan.


Halin Ko In Kulan Malaman Musulunci Ga Ababen Amfanin Musulmi

Gaskiyar lamarin dai shi ne cewa shekara dubu kenan ‘yan Shi’a da ‘yan Sunna suke fuskantar junansu, sun rubuta litattafa a kan junansu, sun ci mutumcin ababe masu tsarkin juna, sannan kuma akwai fagen haifar da sabani da rikici tsakanin Sunna da Shi’a, to makiya za su yi amfani da wannan fage na tunani wajen haifar da rikici da rarrabuwa tsakanin wadannan manyan kungiyoyi da mazhabobi na Musulunci. Kamar yadda a wasu daga cikin kasashen musulmi, a wasu lokuta akan sanya wani daga cikin malaman Shi’a ya fadi wani wanda zai motsa ran ‘yan Ahlussunna ko kuma wani daga cikin malaman Ahlusunna su sanya shi fadin wata magana wacce za ta motsa rayukan ‘yan Shi’a, abin bakin cikin shi ne cewa ana samun irin wannan yanayin a wasu kasashen musulmin. Idan har malamai suka jin irin nauyin da ke wuyansu kan wannan lamari sannan kuma ba su takaita da cewa su din nan sun fahimci gaskiya ba sannan kuma ba su takaita da cewa suna da alaka ta ‘yan’uwantaka da malaman Shi’a ba, face dai suka yi kokarin haifar da ‘yan’uwantaka ta Musulunci tsakanin dukkanin musulmi, su sanar da su irin makirce-makircen makiya, matukar dai suka yi hakan, to kuwa wannan fage na gudanar da makircin makiya da haifar da rarrabuwa tsakanin musulmi zai kawu.

‘Yan Amshin Shata

Abin bakin cikin shi ne cewa a kasashen musulmi akwai wadansu mutane wadanda don neman samun kusaci da Amurka da sauran cibiyoyin karfi na girman kan duniya a shirye suke su aikata duk wani abin da ya saba da kuma haifar da rarrabuwa tsakanin ‘yan Shi’a da ‘yan Sunna. Ni dai a yau din nan ina ganin wasu hannaye a wasu daga cikin kasashen da suke makwabtaka da Iran wadanda da gangan kuma cikin tsarin da aka tsara suna ta kokarin haifar da rarrabuwa tsakanin Shi’a da Sunna da kuma rarraba al’ummomi da kabilu da mazhabobi daga junansu da kuma haifar da sabani tsakanin kungiyoyi na siyasa don su sami damar cimma haramtattun manufofinsu a kasashen musulmi. Wajibi ne mu yi taka tsantsan da kuma farkawa. Al’ummomi, gwamnatoci, dukkanin musulmi, kungiyoyi na siyasa, masana da masu fadi a ji, wajibi ne dukkaninsu su zamanto a farke wajen fuskantar wannan makirci na makiya sannan kuma kada su bari makiya su yi nasara cikin wannan manufa ta su.

Kirkirarrun Mazhabobi Na Jabu

Wajibi ne malaman Musulunci su yi taka tsantsan. Su yi taka tsantsan dangane da irin wadannan kirkirarrun mazhabobi – wadanda suke kafar ungulu ga hadin kai tsakanin musulmi. Su yi taka tsantsan dangane da wadannan daloli na man fetur da aka ware su don haifar da rarrabuwa tsakanin musulmi. Su yi taka tsantsan da wadannan hannaye da wadannan ‘yan amshin shata da suke kokari wajen ganin sun tsinke wannan“igiya amintacciya ”[14]da kuma lalata wannan hadin kai tsakanin musulmi. Ku yi fada da su. Wannan shi ne lazimin riko da hadin kai da kuma riko da tafarkin hadin kai na Musulunci. Idan kuwa ba a samu hakan ba, to hadin kai ba abu ne mai yiyuwa ba.
Hanyoyin haifar da sabani da rarrabuwa na lokaci mai tsawo wanda ya dauki shekaru dari ko dari biyu ko dari biyar, shi ne a haifar da yanayi na mulkin mallaka don su sami haifar da cuta da cutarwa cikin jikin duniyar musulmi wanda maganin hakan ba abu ne da za a same shi cikin sauki ba; irin su (akidar) wahabiyanci da sauran mazbobi da addinan da aka kirkiro su da nufin haifar da rikici da fadace-fadace cikin duniyuar musulmi.
Tun farko dai an samar da wahabiyanci ne da nufin cutar da hadin kai na Musulunci da kuma samar da wata cibiya – irin su haramtacciyar kasar Isra'ila – cikin al’ummar musulmi. Kamar yadda an samar da haramtacciyar kasar Isra'ila ne a kokarin da ('yan mulkin mallaka) suke yi na samar da wata cibiya da nufin fada da Musulunci, don haka suka samar da wahabiyanci da kuma wadannan sarakuna na Najad don su sami wata cibiya ta tsaro a gare su da za ta tabbatar musu da abin da suke so.


Cin Mutumcin Ababe Masu Tsarki

Jan layin da ba za a iya tsallake shi ba a mahangar tsarin Musulunci (na Iran) shi ne cin mutumcin ababe masu tsarki na juna. Mutanen da cikin rashin sani da kuma gafala, a wasu lokuta kuma saboda makauniyar tsaurin ra’ayi da babu bukatarta, shin a cikin ‘yan Sunna ne ko kuma a cikin ‘yan Shi’a ne, suna cin mutumcin ababe masu tsarki na juna, ba su san me ya kamata su yi ba. Babbar dama ga makiya su ne wadannan mutanen.
‘Yan Sunna da ‘yan Shi’a kowanne guda daga cikinsu ya gudanar da bukukuwa na mazhabarsa, ya gudanar da ladubba irin nasa, ya gudanar da al’adunsa da kuma gudanar da ayyuka na mazhabarsa, kuma ma wajibi ne ya yi hakan; to sai dai jan layin da ba za a iya tsallake shi ba shi ne cewa bai kamata a dinga yayata maganganu da tada jijiyoyin wuya (da fada) saboda cin mutumcin ababe masu tsarki – shin wanda wasu daga cikin ‘yan Shi’a saboda gafala da rashin sanin ya kamata suke yi ne, ko kuma wanda wasu ‘yan Sunna irin su ‘yan Salafiya da makamantansu suke yi da kore juna – da wasu suka yi ba. Wadannan su ne abubuwan da makiya suke so. Wajibi ne mu yi taka tsantsan cikin hakan.


Kokarin Haifar Da Sabani Na Kabilanci

Masana masu dogaro da ‘yan kasashen waje su ne suke haifar da mafi yawa daga cikin irin sabani na kabilanci da ‘yan kasanci da suka samo asali daga irin kishin kasan nan na wuce gona da iri da suke faruwa. A dabi’ance akwai wadansu abubuwa da suke cutar da hadin kai – sabani na kabilanci, sabani na mazhaba da kuma sabani na siyasa – wanda wajibi ne a yi fada da hakan. Cikin irin wadannan sabani na kabilanci da mazhaba ne makiya Musulunci kamar yadda suka saba suke haifar da sabani tsakanin musulmi. A fili ana iya ganin hannayen makiya da makirce-makircen makiya da kuma kulle-kullensu cikin irin sabanin da ake samu; wajibi ne a magance hakan. Bai kamata masu hankali na cikin dukkanin kungiyoyi da mazhabobi na Musulunci su bari irin wannan guguwa ta fitina da rarrabuwa – wadanda makiya suke tayar da ita – ta watsu cikin al’ummar musulmi ba da kuma sanya kwanciyar hankali da so da kauna da fahimtar juna cikin hatsari ba.


Hatsurran Rarrabuwa Cikin Al’ummar Musulmi

Kwadayin Makiya Musulunci

A duniyar musulmi a yau, mafi muhimmanci da girman hatsarin da ke yi mana barazana, shi ne rarrabuwa. A duk lokacin da muka kasance a rarrabe, to kuwa makiya za su ci gaba da samun fata da kuma kwadayi a kanmu. Shawararmu ga dukkanin gwamnatoci da hukumomin kasashen musulmi da kuma dukkanin al’ummomin musulmi, ita ce su samar da hadin kai da kusatan juna a tsakaninsu. Wajibi ne a yi watsi da sabani. Wasu daga cikin sabanin da ake da su din ana iya magance su; don haka mu magance su. Mai yiyuwa ne wasu daga cikin sabanin ba lamurra ne da za a iya magance su cikin sauki kuma cikin dan karamin lokaci ba; wajibi ne mu yi kokarin tsallake su. Wadannan su ne abubuwan da yahudawan sahyoniya da kuma Amurka suke ganin akwai cutarwa a gare su cikinsu, don haka suke ta kokarinsu wajen ganin sun hana faruwarsa.

Zalunci A Kan Al’ummar Musulmi

Idan har a yau al’ummar Palastinu tana fuskantar irin wannan makoma mai sosa rai; idan har a yau al’ummar Palastinu tana fuskantar irin wannan zalunci da cutarwa, dalilin hakan shi ne saboda rarrabuwar da take tsakanin musulmi ne. Idan har akwai hadin kai, to kuwa da ba a samu hakan ba. Idan har a yau kasar Musulunci ta Iraki tana karkashin mamaya, sakamakon sabani da rarrabuwar da take tsakanin musulmi ne; idan har a yau kasashen yankin gabas ta tsakiya suna fuskantar barazana ta kai tsaye daga wajen Amurka, hakan ya biyo bayan irin sabanin da ake da shi ne a tsakanin musulmi.

Zamiyya Da Kuma Ha’inci Ga Musulunci Da Musulmi

Duk wani mutumin da ya ke cikin tsoron manyan kasashen masu karfi da juya duniya, hakan saboda jin da ya ke yi ne na cewa shi kadai ne kuma ba shi da wata kariya. Idan har gwamnatoci da al’ummomi suna cikin fargaba, dalilin hakan shi ne wannan; idan har mutane suna cikin fargaba, wannan shi ne dalilin. Matukar al’ummomi da gwamnatocin Musulunci suna jin fahimtar juna da kauna a tsakaninsu; gwamnatoci suka ji cewa lalle al’ummominsu suna tare da su; al’ummomi suka ga gwamnatocinsu sun tsaya wajen tabbatar musu da hakkokinsu; al’ummomi suka ga al’ummomi suna cikin ‘yan’uwantaka da kuma kaunar junansu; to a irin wannan lokacin irin tsoro da fargaban da ma’abota girman kai suka sanya cikin zukatan wasu daga cikin al’ummomi da kuma shugabannin gwamnatoci ba za su sake samun gindin zama ba. Tasiri na farko na hadin kai shi ne cewa mutum zai dinga jin karfi a tattare da shi. Tasiri na farko na rarrabuwa kuma shi ne cewa tana yashe cikin mutum ne; “kuma iskarku ta tafi ” [15]sai su kawar da farin ciki da nishadi da kumajin wani mutum da wata al’umma.

Gafala Daga Makiyi Na Hakika

Yau rana ce ta hadin kan duniyar musulmi. Don cutar da wannan dan hadin kai mai rauni da ake da shi a halin yanzu, wani irin kokari da kashe kudade ne ba su yi ba. Yanayin kasar Iraki da sauran yankuna na kasashen musulmi suna fuskantar irin wadannan makirce-makirce don su sami damar haifar da rikici da rarrabuwa tsakanin kabilu da kungiyoyi na Musulunci da al’ummomin musulmi, suna masu fakewa da abubuwa daban-daban: wadannan su kashe wadancan, wadancan su kashe wadannan; wadannan su kyamaci wadancan, wadancan su kyamaci wadannan; wadancan su yi gaba da wadannan, wadannan su yi gaba da wadancan, sakamakon hakan shi ne cewa za a mance da makiyi na asali na duniyar musulmi sannan kuma masu kokari wajen ganin sun sami iko da mallake wannan yanki.
Matukar dai masu goyon bayan Alkur’ani da kuma Musulunci – daga dukkanin kungiyoyi da mazhabobi – da gaske suke yi sannan kuma da gaske suke yi zukatansu suna son Alkur’ani ya zamanto mai daukaka da kuma girma, to wajibi ne su san cewa irin wadannan ayyuka da kuma wadannan kazaman kudade da aka ware su a wasu kasashe don haifar da rarraba tsakanin musulmi lamari ne da ke hana ci gaban Musulunci, hakan kuwa aiki ne na makiya.



Hanyoyin Samar Da Hadin Kai Da Kuma Karfafa Shi

Hanyoyin Samar Da Hadin Kai Da Kuma Karfafa Shi

Hadin kai yana da marhaloli guda biyu: daya marhalar, ita ce marhala ta harshe da bayani. Wannan marhala ce mai sauki ba ta da wata matsala ta azo a gani. Duk kuwa da cewa wadansu mutane dai ba a shirye suke su aikata wannan aiki mai saukin ba ma; akwai wadansu mutane da suke kafirta kungoyiyin musulmi a fili, akwai kuma wadansu mutane wadanda ba ma a shirye suke ko da kalma guda su fadi ba dangane da hadin kan musulmi da samar da fahimtar juna tsakanin kungiyoyin musulmi ba. Ala kulli hal, duk kuwa da cewa marhala ta magana, ba ta irin wannan yanayi na gaba daya; to amma dai ba marhala ce mai tsananin wahala ba. Marhala ta biyu, marhala ce ta aiki wacce a hakikanin gaskiya tana bukatar kokari da zage damtse. Aiki ne mai wahala; to amma wajibi ne a yi shi. Akwai wadansu mutane masu yawa da suke son cutar da hadin kai wanda wajibi ne da dukkanin bakin ciki a fadi cewa akwai kudade masu yawan gaske da ake amfani da su wajen karfafa hakan sannan kuma akwai daloli masu yawan gaske na man fetur da ake amfani da su wajen karfafa hakan. Ala kulli hal, da yake hakan wani wajibi da lalura ce ta wannan zamani, don haka wajibi ne a yi hakuri da wahalhalun da ke cikinta.



Ayyuka Na Al’adu

Bayyanar Da Bangarori Daban-Daban Na Manzon Allah (s.a.w.a)

Musulman duniya, cikin sauki sama da komai za su iya samun hadin kai a tsakaninsu karkashin inuwar sunan Manzon Allah (tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi da alayensa). Wannan wata siffa ce da wannan mai girman ya kebanta da ita. Mu dai a lokuta da dama mun sha fadin cewa: “wannan mai girma, ya kasance matattarar so da kaunar dukkanin musulmi. Musulmi suna kaunar annabinsu”. Ya Ubangiji Allah! Ka dai shaida cewa zukatanmu cike suke da so da kaunar Annabi. Wajibi ne a yi kokarin amfanuwa da wannan kauna, wajen bude wannan kofa da kuma kunce wannan kulli.
Malaman Musulunci, masanan musulmi, marubuta, mawaka da masana adabi na duniyar musulmi, a yau suna da wani aiki a kansu har zuwa inda za su iya wajen bayyanar da bangarori daban-daban na wannan babban bawan Allah ga musulmi da wadanda ba musulmi ba. Wannan al’amari zai taimaka nesa ba kusa ba ga hadin kan al’ummar musulmi da kuma irin so da kaunar da a yau ake gani tattare da matasan al’ummar musulmi zuwa ga Musulunci.
Matukar dai malaman Musulunci suka yarda da cewa Alkur’ani mai girma yana fadin cewa:
“Kuma ba Mu aiki wani Manzo ba face domin a yi masa da’a ”[16]Annabi ba ya zo ne don ya yi nasiha, ya fadi magana shi kenan mutane su ci gaba da ayyukansu ba tare da sun girmama shi ba; ya zo ne don a yi masa da’a da biyayya, ya shirya da al’umma da kuma rayuwar (mutane), ya kafa hukuma sannan kuma ya shiryar da mutane zuwa ga rayuwar da ta dace kuma ingantacciya.

Taka Tsantsan Wajen Fuskantar Makiya

Alkur’ani mai girma yana fadin cewa: “Ya ku musulmi ku bude zukatanku; kada ku taba mancewa da wadannan makiyan. Kada ku mance cewa lalle kuna da makiya; kada ku mance cewa makiyi yana nan ya dana makaminsa; kada ku mance idan har kuka yi kasa a gwuiwa, matukar kuka nuna gazawa, to kuwa makiyi zai kawo hari da cutarwa”. Makiyi yana son shigowa ta kowace hanyar da ta sauwaka masa don cutarwa: ta hanyar tattalin arziki, ta hanyar al’adu, ta hanyar siyasa sannan kuma ta hanyar tsaro. Wajibi ne al’ummar musulmi su farka:“Ashe, ban yi muku umurni na alkawari ba, ya ku diyan Adamu? Cewa kada ku bauta wa Shaidan, lalle shi, makiyi ne a gare ku bayyananne? ”,[17]kada mu mika wuya ga Shaidan; kada mu mance da makiyi, ku dinga tuna cewa makiyi yana nan. To amma dangane da wannan Shaidan din, cikin dukkanin jaddadawa Allah Madaukakin Sarki ya ke fadin cewa:“Lalle ne kaidin Shaidan ya kasance mai rauni ”;[18]wannan Shaidan din da wajibi ne a kula da shi, matukar ba a kula da shi ba, to kuwa za a fuskanci cutarwarsa. Matukar kuka farka, kuka kasance cikin sanin ya kamata, kuka hada kanku waje guda, sannan kuma kuka yi aiki da nauyin da ke kanku, to kuwa kaidinsa mai tsananin rauni ne babu wani abin da zai iya aikatawa.“Abin sani kawai, karfinsa yana a kan wadanda suke jibintar sa, kuma wadanda suke su, game da shi, masu shirka ne ”,[19]karfin Shaidan yana ga mutanen da suke jin tsoronsa ne, wadanda suke ganinsa a bakin komai. Sannan kuma suka amince da shi. Mutumin da ya dogara da Allah, sannan kuma ya zamanto bawan Allah, to wajibi ne Shaidan ya ji tsoronsa.

Tunani Guda Na Malamai

A cikin lamarin fikihu ma musayen ra’ayi tsakanin mazhabobi daban-daban yana iya kusata da dama daga cikin fatawoyi da kuma batutuwa na fikihu kusa da juna ko kuma ma ya sanya su su zama guda. Wasu daga cikin mazhabobin Musulunci sun gudanar da bincike masu kyaun gaske cikin wasu daga cikin babuka na fikihu; wasu za su iya amfanuwa da su. Mai yiyuwa ne wasu daga cikin hukumce-hukumcen na Musulunci da aka ciro su daga cikin Alkur’ani mai girma da kuma Sunna su zamanto sun samar da wasu sabbin abubuwa ga wasu daga cikin kungiyoyi na Musulunci; saura ma za su iya amfanuwa da su sannan kuma su kusato da wadannan fatawoyi kusa ko kuma ma su yi tarayya da junansu. Mu a wasu lokuta mu kan ga wadansu fatawoyi na wata mazhaba, alhali kuwa wadannan fatawoyi hatta a mazhabar ta su fatawa ce bakuwa mai ban mamaki. Mai yiyuwa ne ma’abota wannan mazhabar, su zamanto sun nuna halin ko in kula da wannan fatawar, ko kuma ba su damu da ita ba. Me ya sa ba za mu gudanar da bincike don mu gano fatawar da muka yi tarayya cikinta ba?

Fahimtar Malamai

Malaman Musulunci su zo su aiwatar da hadin kai na Musulunci a aikace, su fitar da wata takarda wacce dukkanin malamai masu tunani na duniyar musulmi da dukkanin masana da dukkanin ‘yan siyasa masu tsarkin zuciya na duniyar musulmi za su amince da ita wajen aiwatar da ita a aikace, sannan kuma su yi iayakacin kokarinsu, su shirya, don kada sauran musulmi su sami jaruntakar kafirta ma’abota tauhidi na sauran mazhabobi da sauran kungiyoyi.
‘Yan’uwa musulmi, shin wadanda suke Iran ne, ko wadanda suke Iraki, ko Pakistan, ko Labanon, ko Palastinu ko kuma wadanda suke sauran yankuna na duniya daga kowace mazhaba suke, su san cewa ra’ayin malaman Musulunci na hakika shi ne cewa: “zubar da jinin dan’uwa musulmi, tana daga cikin manyan laifuffukan da ba za a taba yafe su ba”. Mutanen da suke zubar da jinin ‘yan’uwansu musulmi a matsayin suna koyi da Musulunci! Da sunan riko da Musulunci! Wannan fita ce daga Musulunci. Wajibi ne kowa da kowa ya san cewa: ‘yan’uwantakar al’ummar Iran da sauran al’ummar musulmi na daban, wani ‘yan’uwantaka ne na hakika; sabani na mazhaba yana nan a wajensa, dan Shi’a dan Shi’a ne, dan Sunna, dan Sunna ne – a tsakanin ‘yan Sunna, a tsakanin ‘yan Shi’a akwai sabani na tunani da mazhaba; to amma wajibi ne dukkaninsu su zmanato karkashin tutar “La ilaha illallah Muhammadur rasulullah’ a matsayin ‘yan’uwa sannan kuma su ci gaba da tsayin daka a gaban makiyan al’ummar musulmi.


Rashin Ingancin Dogaro Da Sabani

Taken Musulunci na hakika da Musuluncin da tsarin Musulunci ya ginu da kuma samuwa a bisa tushensa, shi ne cewa musulmai duk da irin sabanin da ke tsakaninsu na akida da kuma tushe na mazhaba, amma wajibi ne su zamanto suna da hadin kai a tsakaninsu; su dogara da abubuwan da suka hadu a kansu sannan kuma su nesanci abubuwan da za su sosa ran junansu. Irin wannan al’ada ta addini da irin wannan ma’ana da irin wannan mahanga wadda a cikinta akwai ‘yanci da adalci da tsarin demokradiyya da kuma yada hadin kai a duniyar musulmi a tsakanin al’ummar musulmi, wajibi ne hakan ya zamanto daya daga cikin fagagen da za mu ba su muhimmanci, sannan kuma wajibi ne mu yi kokari wajen cimma hakan.
‘Yan’uwa ‘yan Shi’a da ‘yan’uwa ‘yan Sunna su yi watsi da wajajen da suke da sabani a tsakaninsu; kada su dinga bayyanar da wajajen da suke da sabani a cikinsu a gaban jama’a. Su dinga bayyanar da hadin kan da ke tsakaninsu sannan kuma su dinga bayyanar da hadin kai na Musulunci. Mutanen da suke gudanar da ayyukan isar da sako, wajibi ne su dinga gudanar da hakan da dukkan kyautatawa da kuma amfani da hankali da ilimi don su juyar da zukata zuwa ga gaskiya da kuma hakika.
A duk inda kuke, idan har kuka ga wani mai magana, wani mai wa’azi, ko kuma wani marubuci cikin jarida, cikin maganganunsa yana son ya sanya mutane cikin damuwa da kuma cutar da hadin kan da ke tsakanin mutane, to ku san cewa lalle kusukure ya ke yi. Sannan kuma ku san hakan kawai ya wadatar, babu bukatar sai kun aikata wani abu. Ku san cewa mutanen da suke aikata irin wannan aikin, kuskure suke yi sannan kuma sun kama hanyar kuskure ne.



Hanyoyin Aiki Na Siyasa

Hadin Kai Wajen Fuskantar Makiyi Guda

Hadin kan al’ummar musulmi wani fata ne mai girma kuma mai tsarki sannan kuma ko shakka babu dukkanin zukata a duniyar musulmi suna kaunar ganin hakan. Sai dai wannan manufa tana da abin share fage a tattare da ita; saboda kuwa aiki ne mai girman gaske, sannan kuma baya ga hakan kuma akwai cikas da dama a kan hanya. A wannan rana sannan kuma a cikin wadannan ranaku, akwai wadansu cibiyoyi a duniya wadanda a ko da yaushe suna kokari ne wajen raba musulmi da junansu. Idan har za su iya, za su haifar da yaki tsakanin kasashe biyu na musulmi idan kuwa ba za su iya ba, za su yi kokarin haifar da yaki na siyasa da akida da mazhaba ko kuma kiyayya ta kabilanci. Ko da yake mutanen da suke aikata hakan ba wai mutane ne na kan tituna da lunguna ba, face dai cibiyoyi ne na masu karfi na duniya wadanda suke da kudade da kuma karfi na siyasa da tsaro na kasa da kasa. A bisa hakan ne, kokari wajen tabbatar da hadin kai tsakanin musulmi, ko shakka babu ba zai kasance ya rabu da fada da wannan kumaji ba.
Taron shugabannin kasashen musulmi, abu ne da ke nuni da hadin kai, karfaffen shugabanci da kuma aiki kafada da kafada tsakanin jami’an kasashe da kuma al’umma sannan kuma (shugabannin Amurka) sun ga karfi da iyawar gudanar da ayyuka masu girma da wahala. To sai dai a wajen ma’abota girman kai Musulunci da kuma wayewar Musulunci da ake samu hatsari ne a wajensu. A duk inda suka ga wannan hatsari kuwa, to kuwa za su kai hari kansa; za su ci gaba da kai masa hari; shin dan Sunna ne ko kuma dan Shia’a. Ma’abota girman kai da irin wannan mahanga suke kallon kungiyar Hamas da kuma mu’amala da ita, haka nan kuma da hakan suke mu’amala da kungiyar Hizbullah ta kasar Labanon. Wadannan ‘yan Sunna ne, wadancan kuma ‘yan Shi’a ne. Irin kallon da ma’abota girman kan duniya suke yi wa musulmai masu bauta da riko da addininsu kallo guda ne; shin dan Shi’a ne ko kuma dan Sunna.


Hanyoyin Aiki Na Tattalin Arziki

Duk wani aikin da aka gudanar da shi a yau wajen tabbatar da karfi na Musulunci sannan da kuma tsara al’ummar musulmi cikin dukkanin matakan da za su dauka, hidima ce ga Musulunci da kasashen musulmi da kuma bil’adama baki daya. Ayyukan bankin da shugabannin bankunan kasashen musulmi da kuma bankuna ci gaban Musulunci da sauran cibiyoyin kudi suka gudanar duk suna kan wannan turba da kuma tafarki ne.
Matukar dai kasashen musulmi suka kasance tare da junansu kasantuwa ta hakika; ba wai ina cewa ne su sami hadin kai a tsakaninsu hadin kai da ma’ana ta siyasa da take yawo ba, face dai su sami alaka mai kyau a tsakaninsu; a matsayin misali su ba da muhimmanci wajen samar da kasuwa ta bai daya wanda shi ne maganar da mu ke yi, sannan kuma su dau aniyar gabatar da matsalolin da suke fuskanta sannan kuma su yi kokari wajen magance su, to kuwa da dama daga cikin matsalolin da duniyar musulmi suke fuskanta za a magance su. A wata ma’anar, ba za su fuskanci da dama daga cikin matsalolin da suke fuskanta ba.



Ja Gaban Hadin Kai

Ayatullah Uzma Burujerdi da Sheikh Mahmud Shaltut

1-brojerdi

Wasu fitattun mutane guda biyu, wanda dayansu babban malamin fikihu na lokacinsa kuma babban marja'i na dukkanin ‘yan Shi’an duniya a zamaninsa sannan kuma malami maras tamka a shekarun baya-bayan nan ne wato mai girma Ayatullah al-Uzma Burujerdi sannan dayan kuma malamin fikihu ne kuma babban mufti na Ahlussunna sannan kuma jarumin shugaban jami’ar Azhar mai girma Allamah Sheikh Mahmud Shaltut. Marigayi Ayatullah Burujerdi daya ne daga cikin wadanda suka assasa cibiyar nan ta Darul Takrib ta kasar Masar. Marigayi Sheikh Shaltut shi ma haka yake, shi ya kasance daga cikin wadanda suka assasa cibiyar Darul Takrib. Wannan kusaci, wani nauyi da aiki ne da ke wuyan dukkanin malaman Shi’a da Sunna.
1-shaltout
Shekara da shekaru kenan – tun daga zamanin marigayi Ayatullah Burujerdi (yardar Allah ta tabbata a gare shi) da wasu daga cikin manyan malaman Ahlusunna a kasar Masar – aka samu wannan tunani na cewa ku zo mu ajiye sabanin da muke da shi gefe; dan Ahlusunna ya ci gaba da zama Ahlussunnansa; dan Shi’a ya ci gaba da zama dan Shi’ansa; ku kasance tare da akidun da kuke da su, to amma dukkaninmu mu hada hannayenmu waje guda. A wancan lokacin gagarumar himma da azamar babban marja’in Shi’a da kuma jaruntakar babban muftin Masar, ya haifar da gagarumin abin da ake bukata a wancan lokacin. A yau ma manyan cikin al’umma, masana, malaman addini, mufti da ‘yan siyasa, kowane guda daga cikinsu yana da wannan nauyi a wuyansa.
Wadannan manyan mutane guda biyu kimanin rabin karni kenan suka fahimci wannan hakikar da take a fili sannan kuma suka yi kokari wajen tabbatar da hakan. Sannan kuma matukar masana da ‘yan siyasa, suka kasance suna neman tabbatar da hakan, to watakila da a yau a duniyar musulmi da ba a fuskanci irin wannan sabani ba. Watakila da matsalar Palastinu da sauran yanayi mai tada hankali na duniyar musulmi ba su yi irin wannan lalacewa da sosa rai ba.


Sayyid Jamaluddeen Asad Abadi

Sayyid Jamaluddeen Asad Abadi shi ne mafi girman mutumin da a cikin tarihinmu ya kirayi musulmi zuwa ga hadin kai. Akidar Sayyid Jamaluddeen ita ce cewa matukar dai al'ummar musulmi tana son ta sabunta rayuwarta ta ruhi da siyasa, to ba ta da wata hanya face ta hada kanta waje guda. Dukkanin tafiye-tafiye da maganganu da tattaunawar da Sayyid Jamaluddeen ya yi duk saboda haka ne. 'Yan Ahlussunna suna cewa Sayyid Jamaluddeen dan Sunna ne, 'yan Shi'a ma suna cewa shi dan Shi'a ne. A saboda haka dukkanin bangarorin biyu sun yarda da shi. Sayyid Jamaluddeen wani sayyidi ne dan Shi'a dan kasar Iran ya kasance tare da Sheikh Muhammad Abdu, wani malami mai ba da fatawa dan Sunna mai bin mazhabar Shafi'iyya sun hada karfinsu waje guda inda suka cika duniya da sautinsu. Sayyid Jamal mutum ne wanda ya daga tutar rayar da Musulunci, don haka tutar sake rayar da Musulunci ba ruwanta da Shi'a ko Sunna.

Imam Khumaini (yardar Allah ta tabbata a gare shi)

1-khomeini

Koyarwa mai girma da marigayi Imam Khumaini ya ke bayaninta, ta kumshi: fada da ma'abota girman kan duniya, kiyaye daidaito, rashin sassauci cikin tafarkin 'ba gabashi ba, ba kuma yammaci ba', jaddadawa dangane da 'yanci na hakika da kuma dukkan bangarori na al'umma – wato dogaro da kai da dukkanin ma'anar kalmar – tsayawa kyam wajen kiyaye ginshikai na addini da shari'a da fikihun Musulunci, samar da hadin kai da aiki kafada da kafada, nuna damuwa dangane da al'ummomin musulmi da wadanda ake zalunta na duniya, daukakar Musulunci da al'ummomin musulmi da kuma rashin razana da ma'abota karfi na duniya, samar da adalci da daidaito cikin al'ummar musulmi, goyon baya ba ja da baya ga wadanda aka raunana da marasa galihu da kuma marasa shi da kuma wajibcin kula da su. Dukkaninmu mun ga yadda marigayi Imam ya kasance yana ci gaba da tafiya a kan wannan tafarki ba tare da komai kashin ja da baya ba. Wajibi ne mu ci gaba da bin wannan tafarki da ayyukansa dawwamammu.


Alamun Hadin Kai Da Zumunci Na Musulunci

Daukakar Al'ummar Musulmi

Aikin hajji alama ce ta hadin kai tsakanin musulmi. Kiran da Allah Madaukakin Sarki ya yi wa dukkanin musulmi da kuma dukkanin wanda yake da dama zuwa ga wani waje na musamman a wani lokaci na musamman da kuma aikata wasu ayyuka wadanda suke nuni da rayuwa iri guda cikin tsari, sannan kuma suka kasance tare da juna dare da rana, to tasiri na farko na hakan shi ne sanya shu'urin hadin kai da aiki kafada da kafada cikin zukatansu da kuma sanya musu tunani da jin cewa su din nan abu guda ne sakamakon wannan taro na musulmi.
Aikin hajji alama ce ta hadin kai da kuma daidaito na al'ummar musulmi, kawar da katanga da hijabobi da kuma cike gurbin da ko dai makiya suka samar da shi ko kuma aka samar da shi saboda tsaurin ra'ayi na kabilanci da sauransu, da kuma samar da wani yanayin kama hanyar tabbatar da al'umma guda ta Musulunci, sannan a bangare guda kuma wata alama ce ta barranta daga makiya Allah, barranta daga mushrikai da hannayen shirka da kafirta.


Makon Hadin Kai

Jamhuriyar Musulunci ta Iran ta kirayi al'ummar musulmi duniya da cewa, ku zo daga ranar sha biyu zuwa ga ranar sha bakwai ga watan Rabi'ul Awwal mu tabbatar da hadin kai a tsakaninmu. A wata ruwayar – wanda a mafi yawan lokuta 'yan Ahlussunna ne suka fi jaddada wannan ruwayar, wadansu daga cikin 'yan Shi'a ma sun amince da ita – ranar sha biyu ga watan Rabi'ul Awwal rana ce da aka haifi Manzon Allah (tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi da Alayensa). Wata ruwayar kuma wacce mafi yawan Shi'a ne suka yi imani da ita da kuma wasu daga cikin 'yan Ahlussunna suna cewa ranar Sha bakwai ga watan Rabi'ul Awwal din ne. Ala kulli hal, tsakanin ranakun sha biyu zuwa ranar sha bakwai ga watan Rabi'ul Awwal din ranaku ne na haihuwar Annabi mafi girma (tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi da alayensa), wajibi ne a ba da himma da kokari dangane da hadin kan musulmi; wannan garkuwa mai karfin gaske wacce idan har aka tabbatar da ita, babu wani mai karfi da ya isa ya wuce gona da iri kan hurumin kasashe da al'ummomin musulmi.
Mu dai ba wai muna cewa ne 'yan Sunnan duniya su zo su zama 'yan Shi'a ba ne, ko kuma 'yan Shi'an duniya su yi watsi da akidunsu ba ne. Ko da yake idan har wani dan Sunna ko kuma kowane mutum ma ya gudanar da bincike, to wajibi ne ya yi aiki daidai da akida da kuma binciken da ya gudanar kowane irin abu ne kuwa. Taklifinsa yana wajen Ubangijinsa. Abin da muke fadi a makon hadin kai sannan kuma a matsayin sakon hadin kai shi ne cewa musulmi su zo su hada kansu waje guda sannan kuma kada su yi gaba da junansu. Abin lurarsu shi ne Littafin Allah da Sunnar Annabi (tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi da alayensa) da kuma shari'ar Musulunci. Wannan magana, ba magana ce mummuna ba. Wannan magana, magana ce wacce duk wani mai hankali wanda kuma ba shi da wata manufa ta daban zai yarda da ita.


Ranar Kudus

Ranar Kudus daya ne daga cikin abubuwan da suka yi fice wajen nuni da hadin kai da sada zumunci na hakika na Musulunci. Rana ce ta zumunci ta al'ummar musulmi karkashin tutar 'yanto masallacin Kudus mai alfarma wanda a duk inda aka ba wa al'umma dama kama daga gabashin duniyar musulmi, wato daga kasar Indonusiya har zuwa yammacin duniyar musulmi wato nahiyar Afirka da kasar Nijeriya za su fito don nuna goyon bayansu a wannan ranar. A yau duniyar musulmi suna nuna tsananin damuwarsu dangane da batun Palastinu. Dalilin hakan kuwa shi ne cewa duniyar musulmi ta farka. A saboda haka suke girmama wannan rana da kuma isar da muryarsu ga al'ummomin duniya wajen kare al'ummar da ake zalunta ta Palastinu; da kuma kara karfafa zukatansu ta hanyar amfanuwa da irin falalolin da suke cikin watan Ramalana da kuma kara karfafa imaninsu da alkawarin Allah Madaukakin Sarki.


Ranakun Idi Na Musulunci

Ranakun idi na Musulunci sun zo ne don rayar da ruhi da shu'urin hadin kai tsakanin musulmi. Ranakun idi na Musulunci suna nufin ranar da ake gudanar da bukukuwa ne a dukkanin fadin duniyar musulmi.
Idi na Musulunci, yana da bangarori biyu; wanda daya bangarensa shi ne komawa ga Allah da ababen da suke kyautata ruhi, daya bangarensa kuma shi ne taruwar dukkanin musulmi kan wani abu guda. Wajibi ne dukkanin idina da kuma tarurrukan bukukuwa na Musulunci su zamanto suna da wadannan siffofi a gare mu wanda zai kusato zukatanmu mu musulmi waje guda. A yau musulmi sama da shekarun da suka gabata suna bukatar zukatansu su kusaci junansu.


Darut Takrib (Majalisar Kusatar Juna)

Ni dai ina ganin kusato da mazhabobin Musulunci kusa da junansu wani lamari ne da ya zama wajibi wajen cimma manufofin tsarin Musulunci sannan kuma na yi imani da cewa cutar da hadin kai gagarumar cutarwa ce ga dukkanin al'ummar musulmi. Wannan Darut Takrib din da muka ba da shawarar (kafa ta) saboda wannan manufar ce. Darut Takrib din kasar Masar, a ra'ayinmu tana da girma kuma abar girmamawa ce; a yanzu ma haka take. Sai dai abin bakin cikin shi ne cewa ba su bar ta ta gudanar da ayyukanta ba. Kawai a wani lokaci ne ake buga mujallar 'Risalatul Islam' a lokacin da marigayi (Sheikh) Shaltut da Sheikh Salim da shugabannin jami'ar Al-Azhar masu girma suke raye ne take gudanar da ayyukanta da kyau. Marigayi Ayatullah Burujerdi wanda ya kasance marja'inmu ne, ya kasance mai ba da goyon baya ga Darut Takrib din kasar Masar din. Shugaban jami'ar Azhar, Sheikh Salim shi ne wanda ya sanya tubali da kuma share fagen kafa Darut Takrib din daga baya kuma marigayi Sheikh Shaltut ya zamanto shugaban Azhar wanda kuma ya kasance muftin fadan Masar ne. Shi kansa ya kasance shugaban wannan Darut Takirib din. Wadannan su ne suka kasance garkuwa ga Darut Takrib din. A yau duniyar musulmi tana bukatar wannan kusatan junan. Abin da ake cewa a cikin wannan kusatan junan shi ne cewa kungiyoyin Musulunci, a bangaren tunani da akida su kusaci junansu. Da dama daga cikin irin tunani na kungiyanci da ake jingina su ga juna an magance su ta hanyar bahasi da tattaunawa. Watakila an magance wasu daga cikin irin muggan fahimta, wasu akidu kuma an sauya su, sannan kuma wasu daga cikin tunanin an kusata su da junansu a yanayi na hakika. Ko da yake idan har hakan ta faru, hakan zai fi kowane yanayi kyau; alal akalla dai a ba da muhimmanci ga abubuwan da aka yi tarayya a kansu. Wannan shi ne mafi karancin amfani irin wadannan tattaunawa. A saboda haka, wajibi ne a nesanci gabatar da batutuwan da za su haifar da rarrabuwa.

==================
[1] Wasa’il al-Shi’a, juzu'i na 14, shafi na 395 Babin mustahabbancin ziyarar Amirul Muminin.
[2] Suratul Hajj 40.
[3] “Kuma suka kakkatse al’amarinsu a tsakaninsu. Dukkan kowanensu masu komawa zuwa gare Ni ne” (Suratul Anbiya’ 21:93)
[4] Suratun Nur 24:42
[5] Suratu Al Imrana 3:103
[6] Suratul Hujurat 49:9.
[7] Suratu Al Imrana 3:103
[8] Suratul Bakara 2:256.
[9] Al-Kafi, juzu'i na 7, shafi na 51 (babin Sadakat al-Nabiy sallallahu alaihi wa alihi)
[10] Suratul Mumtahana 60:8.
[11] Bihar al-Anwar, juzu'i na 29, shafi na 485.
[12] An yi wahayi wa Manzon Allah (s.a.w.a) dab a shi labarin makircin da munafukai suke kullawa wajen gina wani masallaci da nufin haifar da rarrabuwa tsakanin musulmi. A saboda haka ne Annabi (s.a.w.a.) ya ba da umurnin a ruguza wannan masallacin.
[13] Suratul Hijr 15:39.
[14] “A saboda haka wanda ya kafirta da Dagutu kuma ya yi imani da Allah, to, hakika, ya yi riko da igiya amintacciya, babu yankewa a gare ta. Kuma Allah Mai ji ne, Masani” (Suratul Bakara 2:256). [15] “Kuma ku yi da’a ga Allah da ManzonSa, kuma kada ku yi jayayya har ku raunana kuma iskarku ta tafi…” (Suratul Anfal 8:46).
[16] Suratun Nisa'i, 4:64.
[17] Suratu Yasin, 36:60.
[18] Suratun Nisa'i, 4:76.
[19] Suratun Nahl 16:100.


.
Copyright © 2018~2022.
( Uzairu Badamasi Sufi )
Harkarmusulunci@yahoo.com
All rights reserved

Bamu Da Alhakin Tallar Da Ake Sawa Akan Wannan Website Din