Ring ring
Uzairu badamasi

BARKA DA ZUWA SHAFI MAI ALBARKA

Alhamdulillah muna muku albishir insha Allah zamu dawo aiki gadan gadan!


Shafin farko

Haidar Ali

Tsoron Allah Na Munafunci

Ali khamenei3

Manzon Allah (s.a.w.a) ya ce:
"إيّاكم وتخشّع النّفاق وهو أن يُرى الجسد خاشعاً والقلب ليس بخاشع"



"Ku kula kada ku zame masu nuna tsoron Allah domin munafunci, hakan shi ne a ga jiki a zahiri dauke da tsoron Allah amma zuciya kuma ba ta tsoronSa".

(Tuhaful-Ukul shafi na 60).

Abin nufi da nuna tsoron Allah a wannan hadisi shi ne nuna siffar tsoron Allah da kankan da kai a gabanSa Madaukaki a lokacin salla, addu'a da zikiri (ambaton Allah). Idan mutum ya kasance a lokacin da wani ya kalli zahirinsa zai yi zaton cewa lalle mai tsoron Allah ne, amma a badininsa holoko ne (wato babu tsoron Allah tattare da shi), wannan shi ne nuna tsoron Allah na munafunci.

Ya zo cikin addu'ar dake cikin littafin Sahifatus-Sajjadiyya da irin wannan ma'ana cewa: Ya Allah ka azurta ni da hankali cikakke... da zuciya mai rinjaye. A nan za a iya fahimtar cewa mutum ya zame mai zahiri da badini iri daya, amma idan zahirinmu ya zame mai rinjaye da tsoron Allah da ambatonSa, badininmu kuma ya zame cikin gafala kuma ya nutse cikin rayuwar duniya, wannan ba karamin abin zargi ba ne a kanmu. Ya Allah ka azurta mu da zuciya mai rinjaye.



.
Copyright © 2018~2022.
( Uzairu Badamasi Sufi )
Harkarmusulunci@yahoo.com
All rights reserved

Bamu Da Alhakin Tallar Da Ake Sawa Akan Wannan Website Din