Kyawawan Halaye 1 (Gina Kai)
Babbar GwagwarmayaBayan dawowarsa daga fagen yaki mai wahalar gaske, Manzon Allah (s.a.w.a.) ya ce: "Wannan karamin jihadi ne, bayan hakan kuma sai jihadi mafi girma". Jihadi mafi girma yana nufin jihadi (fada) da (son) zuciya. Bai kamata a takaita jihadi da zuciya kawai cikin ayyukan daidakun mutane ba. Tabbas fada da sha'awa da neman jin dadi da rayuwa cikin sauki da wuce gona da iri da munanan dabi'u da suke tattare da mu fada ne da zuciya sannan kuma lamari ne mai muhimmancin gaske. Wato wajibi ne mutum a ko da yaushe ya zamanto mai fada da shaidanin da ke tattare da shi, kada ya bar shi haka kawai ballantana ya ya sami damar tilasta wa mutum aikata munanan ayyuka ba.Ma’anar Gina KaiMa'anar gina ba a ko da yaushe ba ita ce cewa akwai wani aibi (a tattare da mutum) da wajibi ne a kawar da shi ba – a'a, a wani lokaci babu wani aibi na a zo a gani – face dai da wannan ma'anar ce ta cewa wajibi ne mu sanya ido wajen hana damar kutsawar abubuwan da suke haifar da aibin; kwayoyin cuta daban-daban da suke tare da mu, sannan kuma su bata mu, mu din nan da muke da koshin lafiya.Wajibcin Gina KaiGina kai, share fage ne sannan kuma wani sharadi ne na asasi wajen gina sauran mutane da gina duniya da kuma samar da sauyi da harhada hanyoyi masu wahala. A samuwar mutum, akwai dukkanin hanyoyin tabbatar da sharri, wanda ita ce ita kanta zuciyar mutum din – wacce ta fi dukkanin gumaka hatsari, ita ce gunkin zuciyar mutum da kuma son zuciyarsa – sannan kuma akwai mabubbugar dukkanin alherori da ababe masu kyau da kamala. Idan har mutum ya hobbasa da kuma yin himma zai iya ceto kansa daga fadawa tarkon zuciya mai umurni da munanan abubuwa da kuma sha'awace-sha'awacen zuciya, sannan kuma za a shimfida masa mabubbugar alherori.
Muhimmancin Gina Kyawawan Halayen MatasaGina kyawawan halayen samaruka da matasa da kuma kananan yara lamari ne mai muhimmancin gaske ga dukkanin kasashe da kuma dukkanin al'ummomi ta bangaren cewa al'ummar musulmi – wato al'ummar da take son rayuwa karkashin inuwar tunani da hukumce-hukumcen Musulunci – tuni ta tilasta wa kanta yin gwargwarmaya sama da irin gwagwarmayar da aka saba da ita. Don kuwa dukkanin al'ummomi suna da irin ta su gwagwarmayar sannan kuma babu wata al'ummar da za ta iya samun hanyar da ta dace ba tare da gwagwarmaya ba. Ba za a iya samun gyara wata al'umma ba tare da gwagwarmaya ba; wato ba tare da kokari da mujahida wajen fuskantar masu adawa ba. Saboda a dukkanin wajaje, akwai wadansu abubuwa da suke koyar da yara aikata sata, fasadi, ragwantaka da kama hanyar da ta ba ta dace ba – gwargwadon al'adu daban-daban na mutanen - da kuma kwadaitar da yara zuwa ga aikata wadannan munanan halaye.Gina Kai A Lokacin SamartakaIdan har aka tambaye ni cewa me kake fatan gani daga wajen wani matashi? To lalle zan ce: neman ilimi, tsarkake zuciya da kuma motsa jiki. Lalle ni dai ina ganin wajibi ne matasa su zamanto suna da wadannan siffofi guda uku.
A lokacin samartaka, cikin mutum sauki zai iya nesantar zunubai. Cikin sauki zai iya kusatar da kansa zuwa ga Ubangiji. Bayan gushewar lokacin samartaka ma ana iya yin dukkanin wadannan abubuwa; to sai dai akwai wahalar gaske. Wasu suna zaton cewa lokacin samartaka lokaci ne na sabon Allah (wato mutum zai iya yin sabon Allah a wancan lokacin) sannan tsufa kuma lokacin tuba (wato lokacin da ya tsufa kuma sai ya koma ga Allah)! Wannan kuskure ne. Samarkaka ita ce lokacin tuba. Haka nan kuma lokacin addu'a ma shi ne lokacin samartaka. Samartaka ita ce lokacin dukkanin komai.
Tarbiyya Ta Kyawawan Halaye Da Kuma Tilasci Na Kyawawan HalayeWasu suna zaton cewa bai kamata a dinga tsoma baki da kokarin shiryarwa cikin kyawawan halaye da addini na matasa ba, wajibi ne a bar su haka nan kawai; alhali kuwa shi kansa hakan nuna rashin kula da nuna halin ko in kula ne ga makomar matasa masu tasowa. Ko da yake a fili yake cewa tarbiyya ta kyawawan halaye ta bambanta da tilascin dabi'u (wato a tilasta wa wani aikata wani abu). Tilasta kyawawan halaye ba lamari ne abin so ba; Musulunci kuma bai umurce da hakan ba. Tarbiyyar mutane karkashin inuwar tilasci da kuma matsin lamba riya ce ko kuma son nuna kai da munafunci ne. Ba abu ne abin so ba; amma tarbiyya, lamari ne mai matukar muhimmancin gaske. Ta hanyar kyawawar tarbiyya ce za a iya tarbiyyantar da matashi da mai she shi mai riko da addini. Wajibi ne manufa ta asasi ta zamanto ita ce matashi ya zamanto mai riko da addini, mai kyawawan halaye irin na Musulunci sannan kuma ma'abocin siffofin da Musulunci ya yarda da su.
Hanyar Gina KaiAmirul Muminin (a.s) yana cewa: "Duk wanda ya nada kansa a kan mutane a matsayin shugaba, to ya fara da koyar da kansa kafin koyar da waninsa" a fili wannan magana tana nuni ne da cewa wajibi ne mu fara da gina kanmu tukun (kafin mu je ga wadansu). Wajibi ne mu kula. Matakin farko sannan kuma mafi muhimmanci a fagen gina kai shi ne mutum ya kalli halaye da dabi'unsa kallo irin na suka; ya kalli irin aibin da yake da su da kyau sannan kuma ya yi iyakacin kokarinsa wajen ganin ya kawar da su. Hakan wani nauyi ne da ke wuyanmu, wajibi ne mu kiyaye kanmu sannan kuma mu rage irin karkarwar da muke da ita a kan wannan tafarki, sannan kuma mu nemi taimako daga wajen Allah Madaukakin Sarki.
Mu gano irin munanan halayen da suke tattare da mu, wanda hakan daya ne daga cikin bangarori masu wahalar gaske. Kada mu zamanto masu biyayya ga son zuciyar mu. Mu kalli irin aibobin da muke da su, mu yi jadawalinsu da sanya a gabanmu. Mu yi kokarin wajen ganin mun shafe wasu daga cikinsu. Idan har muna da hassada ne, to mu kawar da wannan hassadar. Idan muna da taurin kai ne, sai mu yi watsi da shi. Idan har a fagen rayuwa muna da kasala da rashin kumaji ne, sai mu yi watsi da hakan. Idan har mun kasance masu fatan sharri ne ga wadansu, sai mu yi watsi da wannan dabi'a ta fatan sharrin. Idan har mun kasance masu karya alkawari ne, sai mu yi watsi da karya alkawarin. Idan mun kasance masu karya yarjejeniyar da muka kulla ne, ko kuma masu nuna halin ko in kula, to shi ma dai sai mu yi kokarin rabuwa da wannan dabi’ar. Lalle Allah Madaukakin Sarki zai taimaki wadanda suka yi kokari a wannan tafarkin. Lalle Allah Madaukakin Sarki ba zai bar mutanen da suke kokari a fagen isa ga kamala haka nan kawai ba, sannan kuma shi ne wanda zai fara samun duk wata ribar farko da za a samu. Baya ga haka, amfanin da ke cikin fada da son rai, gyara kai da kuma gwagwarmaya a tafarkin Allah – wanda hakan shi ne jihadi mafi girma – ba wai lamari ne da ya shafi shi mutum kadai ba; face hakan ya shafi al'umma, kasa, yanayi na siyasa da daukaka ta kasa da kasa da kuma fagen tattalin arziki da yanayi na rayuwa ta duniya da lahira na mutane ne.
Ana iya tabbatar da tsarkake zuciya ta wadannan hanyoyi: wato komawa ga Allah, debe kewa da Allah, tunani kan duk wata matsaya da za a dauka, kaunar dukkanin mutanen kirki na duniya da kuma dukkanin bayin Allah wadanda ba su da wata cuta da kuma mummunan manufa sannan kuma masu neman fatan alheri ga kowa.
Gina Kai Maras IyakaMusulunci da kuma mahanga ta duniya ta Ubangiji ta koyar da mutum cewa a tafarkin isa ga kamala bai kamata ya dakata a ko ina ba, sannan kuma bai kamata ya wadatu da wani haddi da ya kai ba. Wannan wata siffa ce ta bil'adama sannan kuma haka Allah Madaukakin Sarki Ya tsara. Wajibi ne a kowace rana a samu girma da daukaka. Wajibi ne mutum cikin batutuwan da suka shafe shi – lamurran da suka shafi mutum da Ubangijinsa – a kowace rana ya zamanto mai tausasawa, madaukaki, mai karin nesantar munanan abubuwa, mai siffantuwa da kyawawan dabi'u sannan kuma ya dada nesantar zunubai da kauce wa hanya da yake da su.
Mutum dai tamkar wani sinadari ne wanda idan har aka gudanar da wani aiki a kansa, za a iya juya shi zuwa ga yanayi daban-daban da kuma gudanar da ayyukan da suka zamanto wajibi cikin rayuwa. Wannan ita ce manufar rayuwa. Kaicon mutumin da ya gagara aikata wani abu wa kansa a fagen ilimi da aiki, sannan kuma ya bar wannan duniya tamkar yadda ya shigo ta, ba tare da ya sami wani sauyi ba in banda irin lalacewar jiki da rubewa da lalacewa da ya fuskanta wanda daman lamari ne da yake faruwa tsawon rayuwar mutum. Wajibi ne mumini a ko da yaushe ya zamanto mai sanya ido da kokarin ciyar da kansa gaba; a koda yaushe. Matukar mutum ya kula da kansa; ya sanya ido sosai, ya nesanci aikata duk wani abin da aka hana da wasu ayyukan da suka saba wa doka sannan kuma ya kama hanyar Allah da dukkan karfinsa, lalle zai yi nasara. Wannan shi ne dai wannan batun gina kai na ko da yaushe wanda kuma ya dace da irin tsare-tsare na Musulunci a wannan fage na gina kai. Wadannan salloli guda biyar na rana, yin zikiri; nanata fadin "Kai mu ke bauta sannan kuma daga wajenka muke neman taimako", yin sujada da yin tasbihi ga Allah da tsarkake Shi, dukkanin wadannan abubuwa saboda me ake yinsu? Saboda mutum ya zamanto a ko da yaushe mai gina kansa.
Tsarkake ZuciyaAyar nan ta
"Lalle ne wanda ya tsarkaka, ya samu babban rabo" (Suratul A'ala 87:14) tana nufin mutumin da ya tsarkake kansa, sannan kuma ya tseratar da ruhi da zuciyarsa daga dauda da munanan abubuwa, lalle ya samu babban rabo. Babban rabo yana nufin samun rabo cikin fagen rayuwa da kuma isa ga manufar da aka halitta mutum domin ita.
Abin da yake tseratar da mutum, shi ne dai wannan tsarkin. Abin da yake sanya mutum cikin damuwa, shi ne gurbata; gurbata ta kyawawan halaye, gurbata wacce ta samo asali daga sha'awa da kwace; gurbata da ta samo asali daga handama da rowa da sauran munanan dabi'u. Sakamakon irin wadannan munanan hali da wasu mutane suke da su hakan shi ne ya sanya su bakanta duniya, suka gurbata bayan kasa sannan kuma suka kafirce wa ni'imar Allah.
Idan har duniya ta zamanto cike da zalunci da babakere, idan har ma'abota girman kan duniya suna amfani da karfi a kan al'umma da kuma yi musu jafa'i, idan har wasu daga cikin al'ummomin sun sayi kaskanci da hannayensu sakamakon shirun da suka yi, idan har mafi yawa daga cikin gwamnatoci suna zaluntar al'ummominsu, idan har talauci da jahilci da rashin al'adu masu kyau sun yi katutu wa al'umma, idan har akwai yakukuwa da zubar da jini a duniya, idan har bama-bamai masu guba suna nan, idan har zalunci da wuce gona da iri da karya da yaudara suka zamanto akwai su, dukkanin wadannan abubuwa sun samo asali ne daga rashin tsarkin zuciya da mutane suke da shi; wato mutane su kansu ba su damu da aiwatar da ayyukan tsarkin zuciya ba sannan kuma ba su fahimci hakan ba.
Abin Nufi Da Tsarkin ZuciyaAbin nufi da tsarkake zuciya shi ne tsarkakewa da goge dauda daga zukatan mutane; tamkar likitan da ba kawai ya kan takaita ne da gaya wa mara lafiyar da ya ke kula da shi cewa ka aikata haka sannan kuma kada ka aikata wancan ba, face dai ya kan sanya kansa a wani waje na musamman ne yana ba shi maganin da ya dace sannan kuma ya hana shi amfani da duk wani abin da zai cutar da shi. Wannan ita ce hanyar da Ma'aikin (s.a.w.a.) ya dauka tsawon shekaru ashirin da uku na annabcinsa; musamman ma a shekaru goman da ya yi a Madina a lokacin da aka kafa hukumar Musulunci.
Motsa Jikin Tsarkake ZuciyaDukkanin ibadu da ayyukan wajibi na shari'a da aka umurce ni da ku din da mu aikata su, a hakikanin gaskiya su ne dai wannan tsarkakewa da kuma tarbiyya; an wajabta mana su ne don mu sami kamala; sannan kuma motsa jiki ne. Kamar yadda idan har ba ka yi wasannin motsa jiki ba, to jikinka zai gaza, zai zama ba shi da karfi sannan kuma cikin sauki za a iya cutar da shi. Amma idan har kana so jikinka ya sami karfi, ya yi kyau sannan kuma ya kai ga dukkanin bangarori na kwarewa da iyawa, to wajibi ne ka dinga motsa jiki. Salla, azumi, ciyarwa, nesantar zunubai, nesantar fadin karya da kuma fatan alheri ga bil'adama, dukkanin wadannan wasannin motsa jiki. Ta hanyar wadannan wasanni motsa jiki, ruhi da jiki ya kan sami karfi da kuma samun kamala. Matukar dai ba a aikata irin wadannan wasannin motsa jiki ba, mai yiyuwa ne a zahiri jikin ya nuna alamun kyau, to amma badininsa wani badini ne nakasasshe, kaskantacce wanda cikin sauki za a iya kutsawa cikinsa.
Gyaran Kyawawan HalayeA cikin wani hadisi daga Imam Sajjad, amincin Allah ya tabbata a gare shi, an nakalto cewa: "Dan'adam zai ci gaba da zama cikin yanayi mai kyau ne har zuwa lokacin da ya zamanto yana da mai yi masa wa'azi daga kanka", wato Ya ku 'ya'yan Adamu, yanayinku zai ci gaba da zama da kyau ne, har zuwa lokacin da ya zamanto kuna da wani mai yi muku wa'azi daga cikinku. Abin da yake tattare da ku wanda yake yi muku wa'azi da nasiha; ita ce zuciyarku, hankalinku, samuwarku, imaninku, dukkanin wadannan abubuwa ne da suke yi muku nasiha da wa'azi. Wa'azin sauran mutane yana da amfani; to amma wanda ya fi amfani shi ne shi kansa mutum ya dinga yi wa kansa wa'azi. “Idan har ya zamana kana da mai yi maka wa'azi a tattare da kai sannan da kuma mai yi maka hisabi daga cikinka”, wato har zuwa lokacin da mutum yake da mai yi masa wa’azi daga cikinsa sannan kuma ya ba da himma wajen yin hisabi wa kansa da kansa. Don kuwa lalle hisabin da mutum zai yi wa kansa zai fi zama ingantacce sosai a kan wanda wani zai yi masa; don kuwa babu yadda za a yi mutum ya boye wa kansa wani abin da ya aikata. Har zuwa lokacin da tsoron Allah ya zamanto takenka sannan kuma taka tsantsan daga azabar Allah ta zamanto mayafinka, to kuwa za ka ci gaba da zama cikin aminci da yanayi mai kyau. Wato ka zamanto mai tsoron Allah Madaukakin Sarki; ka sanya azabar Allah da kuma hisabinsa a cikin zuciyarka da kuma yin taka tsantsan wajen ganin ba ka girgiza ba don kada ka fada wajen da Allah zai yi fushi da kai. Matukar dai ka kiyaye wadannan abubuwa; wato ku kiyaye kanku sannan kuma ku yi hisabi wa kanku, ku tsoraci azabar Ubangiji da kuma fushinsa, to lalle za ku zamanto cikin alheri. Duniyarku ma za ta yi kyau, haka nan lahirarku ma za ta yi kyau, kyawawan halayenku ma za su yi kyau, haka nan rayuwarku ma za ta yi kyau; ba za a sami rashin tsaro a cikinku ba sannan kuma za ku sami rayuwa mai kyau.
Gabatar Da Tsarkake Zuciya A Kan KoyarwaKoyarwa da tsarkake zuciya sun bambanta. Duk kuwa da cewa matukar aka gudanar da koyarwa ta hanyar da ta dace, to tana tare da tsarkake zuciya, to amma tsarkake zuciya wani yunkuri ne mai cin gashin kansa.
Wannan tunani na cewa duk wanda ya shiga fagen ilimi, shi kenan a dabi'ance zai zamanto ya samu kyawawan halaye, lalle tunani ne da ke cike da kuskure wanda aka shigo da shi daga waje wanda kuma ya ginu bisa abin da kiristoci suka zo da shi a kasashen yammaci, sannan kuma ko da wasa bai yi daidai da fahimta da kuma koyarwa ta Musulunci ba. Don kuwa idan har wani masani ya zamanto mai kyawawan halaye, zai zamanto wani tushe da za a iya amfani da shi wajen sanya fata da kuma daukaka bil'adama da kuma kasarsa; wannan masanin zai iya mayar da manufa ta zamanto mai kyau sannan kuma yunkurinsa ya zamanto mai amfani ga bil'adama da kuma adalci da amfanar kyawawan halaye sannan da kuma wajen fada da bala'oin da suka yi wa duniya tabaibayi a yau.
Saukin GiniGina ruhi aiki ne mai sauki sannan kuma mai wahala – a wani bangaren lamari ne mai sauki, a wani bangaren kuma mai wahala – lamari ne mai sauki; don kuwa tamkar wani tafki ne mai girma wanda za a iya shigansa ta kowane bangare sannan kuma za a iya kai wa ga sakamako. Lamari ne mai wahala; don kuwa a kowane mataki akwai shaidanu wadanda su ke sanya waswasi cikin zukatan mutane; a saboda haka wajibi ne a yi tsayin daka.
Tsaro Na Kyawawan HalayeTsaro da tsari na zamantakewa, ba wai kawai shi ne ya zamana wani bai saci jakar wani ba ko kuma bai balle shagon wani ba ko kuma bai shiga gidan wani da kwashe masa kayan da ke ciki ba. Baya ga wadannan abubuwan, tsaro na kyawawan halaye daya ne daga cikin mafi muhimmancin lamurran da mutane suke bukatar sa. Rashin tsaro na kyawawan halaye shi ne mutane su gagara tafiya cikin kwanciyar hankali cikin unguwanni da lungunansu daidai da koyarwa ta addininsu da kuma abubuwan da suka yi imani da su, su dinga fuskantar wasu abubuwa da suke cutar da addininsu. Mutane suna son a lokacin da matasansu za su fita waje daga gidajensu ya zamana suna fuskantar wani yanayi na zamantakewa da ba zai yi mummunan tasiri cikin kwakwalansu ba.
.
Copyright © 2018~2022.
( Uzairu Badamasi Sufi )
Harkarmusulunci@yahoo.com
All rights reserved