Uzairu badamasi

BARKA DA ZUWA SHAFI MAI ALBARKA

Alhamdulillah muna muku albishir insha Allah zamu dawo aiki gadan gadan!


Shafin farko

Haidar Ali

Kyawawan Halaye 2 (Kyawawan Halayen Manzon Allah (s)

Ali Khamenei5

Don tabbatar da cewa kyawawan halaye na Musulunci sun sami gindin zama a cikin al'umma sosai sannan kuma su sami damar cakuduwa da ruhi da akidu da kuma rayuwar mutane, Manzon Allah (s.a.w.a.) ya kasance yana ban ruwa wa yanayin rayuwar mutane da ababe masu tsarki na Musulunci.

Sassauci Da Kuma Fushin Ma'aiki (s.a.w.a.)

Alkur'ani mai girma ya kasance yana jinjina wa Ma'aikin Allah (s.a.w.a.) saboda irin sassauci da taushin halinsa wajen mu'amala da mutane yana mai cewa masa lalle kai ba ka kasance mai kaushin hali ba "Saboda wata rahama ce daga Allah ka yi sanyin hali a gare su. Kuma da ka kasance mai hushi, mai kaurin zuciya da sun watse daga gefenka" (Suratu Al Imrana 3:159). Haka nan shi wannan Alkur'anin a wani wajen yana gaya wa Manzon Allah (s.a.w.a.) cewa: "Ya kai Annabi! Ka yaki kafirai da munafukai kuma ka tsaurara a kansu"(Suratut Tauba 9:73), wato ka yi kakkausar mu'amala da kafirai da munafukai. Ita kanta wannan kalma ta kaushi da ta zo cikin aya ta farko a nan ma tana nan; sai dai a wancan guri da muminai ne, a cikin mu'amala ne, cikin mu'amala ta daidaiku ne; to amma a nan kan a wajen gudanar da doka da gudanar da al'umma da kuma samar da tsari ne. A wancan wajen (wato wajen mu’amala da mutane) kaushin hali abu ne mai muni; a nan kuma (wato a wajen tabbatar da doka da tsari) kaushin halin abu ne mai kyau. A wancan wajen amfani da karfi abu ne mai muni, a nan kuma abu ne mai kyau.

Rikon Amanar Manzon Allah (s.a.w.a.)

Amanar (Manzon Allah) da kuma riko da amanarsa ta kasance ne hatta a lokacin jahiliya ana kiransa da suna 'al-Amin' sannan kuma a duk lokacin da mutane suke da wani abu mai muhimmanci, su kan kai masa don ya ajiye musu sannan kuma hankalinsu yana kwance suna jin cewa lalle wannan amana ta su za ta dawo hannunsu a duk lokacin da suka bukata. Hatta bayan bayyanar Musulunci da kunna wutar kiyayya da shi da Kuraishawa suka yi, a irin wannan yanayin ma dai makiyan idan har suna son a ajiye musu wani abu mai muhimmanci su kan zo wajen Manzon Allah (s.a.w.a.) su ba shi wannan abin. A saboda haka lokacin da Manzon Allah (s.a.w.a.) ya yi hijira zuwa Madina, sai ya bar Amirul Muminin (a.s) a Makka don ya mayar wa mutane da amanar da suka ba shi. A fili yake cewa a wancan lokacin akwai wadansu amanonin a wajen Manzon Allah (s.a.w.a.); ba wai amanar ta musulmi ba ce, face dai amana ce ta kafirai da wadannan mutane da suke kiyayya da shi.

Hakurin Manzon Allah (s.a.w.a.)

Irin hakurinsa ya kai matsayin da abubuwan da wasu ba za su iya hakurin jinsu ba, to a wajensa ba sa damunsa (wato zai tsaya ya saurara). A wasu lokuta makiyansa a Makka su kan yi masa wata mu'amala wadda a wani lokaci yayin da mai girma Abu Talib ya ji hakan ya yi tsananin fushi ta yadda har sai da ya ciro takobinsa ya nufi wajen ya fuskanci wadannan mutane ya ce musu duk wani wanda ya sake irin wannan cin mutumci ga Ma'aiki to kuwa zan sare kansa. To amma Manzon Allah (s.a.w.a.) duk da irin wannan yanayi na cin mutumci da aka yi masa ya iya hakuri. A wani wajen ma kace nace ya taba shiga tsakaninsa da Abu Jahl ta yadda Abu Jahl ya fadi wasu kalmomi na batanci a gare shi; to amma wannan mai girman sai ya yi shiru da nuna hakuri da juriyarsa. Ganin haka sai wani mutum ya tafi wajen (Sayyidina) Hamza ya gaya masa cewa ga abin da Abu Jahl ya aikata ga dan'uwansa (wato Manzon Allah); nan take Hamza ya nuna damuwarsa ya kama hanya ya tafi wajen Abu Jahl ya buge shi har sai da ya fasa masa kai. Daga baya kuma cikin irin wannan yanayi na fushi ya zo wajen Manzon Allah (s.a.w.a.) ya karbi Musulunci. A wani lokaci wasu su kan zo masallaci su mike kafafunsu su ce wa Manzon Allah (s.a.w.a.) ka yanke mana faratunmu – kamar yadda ya zo cewa yanke faratu ne – haka Manzon Allah (s.a.w.a.) cikin hakuri da juriya yake jure wa irin wannan rashin da'a.

Kira Zuwa Ga Kyawawan Halaye

A ko da yaushe ku kasance masu kiran mutane zuwa ga kyawawan halaye – wato irin su yafuwa, rufe ido, rahama, kaunar juna, hakuri da tsayin daka cikin ayyuka, hakuri, kame fushi, rashin ha'inci, nesantar sata, nesantar fadin munanan maganganu a kan wasu, bakar zuciya da sauransu. A ko da yaushe mutane suna bukatar wadannan abubuwa. Ba za a iya ayyana wani lokacin da zai zamana mutane ba su da bukatar wadannan abubuwa ba. A ko da yaushe suna bukatar wadannan abubuwa. Matukar dai aka rasa wadannan ababe masu kima a cikin al'umma, to daga lokacin da ta kai kolin ci gaba, to kuwa al'umma za ta zamanto mummuna wacce ba za a iya jure mata ba.

Jaruntakar Manzon Allah (s.a.w.a.)

A lokacin jahiliyya akwai wata yarjejeniyar hadin gwuiwa da aka cimma mai suna 'Hilf al-Fudhul' – yarjejeniyoyi da yawa ban da yarjejeniyoyin da mutanen Makka suka kulla a tsakaninsu – wanda Manzon Allah (s.a.w.a.) ya kasance a cikinta. Wata rana wani bako ya shigo cikin garin Makka ya sayar da kayansa. Wanda ya sayi wannan kaya nasa kuwa shi ne Aas bn Wa'il wanda ya kasance daga cikin manya masu fadi a ji na garin Makka. A lokacin da ya sayi kayan sai bai ba da kudin ba. Dukkanin kokarin da wannan bakon ya yi wajen samun wanda zai taimaka masa karbo masa wannan hakki na sa ya ci don kuwa ya rasa ma wanda zai taimaka masan. Don haka sai ya tafi kan dutsen Abu Kubais ya daga muryarsa yana cewa: Lalle an zalunce ni. A yayin da Annabi da baffansa Zubair bn Abdul Mutallib suka ji haka; sai suka taru suka dauki matsayar cewa lalle za su kare wa wannan mutumi hakkinsa. Sai suka tashi suka tafi wajen Aas bn Wa'il suka bukace shi da ya ba wa wannan mutumin kudinsa, nan take ya tsorata ya ba shi kudinsa. Wannan yarjejeniya da hadin gwuiwa ta ci gaba da wanzuwa a tsakankaninsu sannan kuma suka kuduri aniyar cewa duk wani bakon da ya zo garin Makka sannan kuma mutanen Makka suka zalunce shi – saboda a mafi yawan lokuta baki da wadanda ba mutanen Makka ba ne suke zalunta – lalle za su kare shi. Bayan bayyanar Musulunci, har bayan shekaru Manzon Allah (s.a.w.a.) ya kasance yana cewa ni dai har ya zuwa yanzu ina jin cewa ina cikin wannan yarjejeniya. A lokuta da dama ya sha yin mu'amala da makiyansa wadanda aka yi nasara a kansu da suka gagara fahimtar lamarin. A shekara ta takwas bayan hijira, a lokacin da ya sami nasara a kan garin Makka duk da irin wannan karfi da daukaka da take da ita, cewa ya yi: 'Yau din nan rana ce ta rahama', wato yau rana ce ta yafuwa, a saboda haka bai dau fansa a kansu ba. Wannan shi ne irin jaruntakar wannan mutum mai girma.

Gaskiyar Manzon Allah (s.a.w.a.)

Shi din nan ya kasance mutum ne mai gaskiya. A lokacin jahiliyya – kamar yadda muka fadi – ya kasance yana tijara; ya kasance ya kan tafi Sham da Yeman; ya kan kasance cikin ayari na ‘yan kasuwa. Daya daga cikin abokan kasuwancinsa a lokacin jahiliyya ya kasance yana cewa (Manzon Allah) ya kasance mafi kyawun abokin kasuwanci. Bai kasance mai taurin kai ba, bai kasance mai musu da tada jijiyoyin wuya ba, bai kasance mai sanya nauyinsa a kan wani daga cikin abokan kasuwancin na sa ba, haka nan bai kasance mai mummunan mu'amala da masu sayan kayayyakinsa ba, haka nan kuma bai kasance mai sayar musu da kaya da tsada ba, haka nan ba ya fadin karya, mutum ne mai gaskiya. Wannan gaskiya tasa ce ta sanya Nana Khadija ta ji cewa tana sonsa. Ita kanta Nana Khadijah ta kasance macen farko na garin Makka, mace ce mai dukiya sannan kuma daga cikin fitattun garin Makkan.

Tsarkin Zuciyar Manzon Allah (s.a.w.a.)

Tun daga lokacin yarinta, Manzon Allah (s.a.w.a.) ya kasance mutum ne mai tsarkin zuciya. Sabanin sauran yaran garin Makka da sauran yaran larabawa, ya kasance mutum mai tsarki da tsafta. A lokacin samartaka, ya kasance mai tace gashinsa, haka nan a lokacin da ya zama matashi ya kasance mutum mai kyautata yanayinsa. Bayan bayyanar Musulunci a lokacin da shekaru suka fara yi masa – wato kimanin shekaru hamsin, zuwa sittin – ya kasance mutum mai tsafta. Gashinsa ya sauko har kasa da kunnuwansa, amma a ko da yaushe yana cikin tsafta; sannan kuma mai gyara jikinsa da kuma sanya turare. Na ga wata ruwaya da take cewa a cikin gidansa ya kasance yana da wani wajen da ya ke tara ruwa don ya dinga kallon fuskarsa mai albarka a cikin – saboda a wancan lokacin babu madubi sosai – ya kasance ya kan gyara rawaninsa da kuma gemunsa a duk lokacin da yake son fita zuwa wajen sahabbansa. A ko da yaushe ya kasance cikin kamshin turare. A lokacin tafiya duk kuwa da irin rayuwa ta gudun duniya da yake da ita – wanda a nan gaba zan yi magana kan irin rayuwarsa wacce ta kasance cikin zuhudu – ya kasance ya kan dauki matsefi da turare a tare da shi. Ya kasance ya kan dauki kwalli don ya dinga shafawa a idonsa, don kuwa a wancan lokacin ya zama al'ada maza su kan shafa kwalli. A kowace rana ya kasance yana goge bakinsa sau da dama. Haka nan kuma ya kasance mai kiran mutane zuwa ga irin wannan amfani da miswaki da kuma irin wannan tsafta. Tufafin Manzon Allah (s.a.w.a.) sun kasance tsoffi, to amma duk da haka sun kasance cikin tsafta. Dukkanin wadannan abubuwa sun kasance masu tasiri a fagen mu'amala da halaye da kuma yanayi na waje. Wadannan wasu abubuwa ne wadanda a zahiri kanana ne, to amma a badini suna da gagarumin tasiri.

Son Jama'ar Manzon Allah (s.a.w.a.)

Mu'amalarsa da mutane, mu'amala ce mai kyau. A ko da yaushe ya kasance mai murmushi da sakin fuska a lokacin da yake cikin jama'a. Sai dai idan har ya kasance shi kadai ne to a lokacin ne zai nuna fushinsa kan abin da ke damunsa. Ba ya nuna irin fushi da damuwar da yake ciki a gaban mutane. Ya kasance mai yawan murmushi. Ya kasance mai yin sallama ga dukkanin mutane. Idan har wani mutum ya cutar da shi, to kuwa a kan ga alamar wannan cutarwar a fuskarsa; amma dai ba ya bude bakinsa ya yi magana, ba ya taba bari a la'anci wani a gabansa ko kuma a fadi wani mummunar magana kan wani a gabansa. Shi kansa ba ya la'antar wani sannan kuma ba ya fadan mummunan magana kan wani. Ya kasance mai kaunar kananan yara; ya kan yi musu magana da harshe na rahama; ya kasance mai kyakkyawar mu'amala da raunanan mutane; ya kasance mai wasa da sahabbansa, ya kan sanya musu gasar hawa doki.

Abinci Da Tufafin Manzon Allah (s.a.w.a.)

Yana zama ne a kan tabarma; matashin kansa kuwa na fata ne da aka cika shi da ganyen dabino; mafi yawan abincinsa biredin sha'iri da dabino ne. An rubuta cewa har abada bai taba yin kwanaki uku a jere yana cin biredin da aka yi shi da alkama ba. Uwar muminai Ai'sha ta kasance tana fadin cewa: a wani lokaci a kan yi wata guda cur hayaki bai tashi daga madafin gidanmu ba. Ya kan hau abin hawa ba tare da sirdi ba. A wancan lokacin da akan yi ado wa dawaki da sanya musu sirdi masu tsada. Ya kasance mutum mai tawali'u. Ya kasance ya kan dinke takalmansa da hannunsa.

Ibadar Manzon Allah (s.a.w.a.)

Ibadarsa ta kasance wata irin ibada ce wacce sakamakon tsayawa a wajen sallarsa har kafafunsa su kan kumbura. Ya kasance ya kan gudanar da wani bangare na darensa a farke yana ibada da kaskantar da kai (ga Allah) da kuka da neman gafara da kuma yin addu'oi. Ya kasance mai neman taimako da kuma gafarar Ubangiji. Banda watan Ramalana, a cikin watan Sha'aban da Rajab da sauran ranaku na shekara duk da irin zafin yanayi a can amma ya kan yi azumi yau ya sha ruwa gobe. Sahabbansa sukan ce masa: Ya Rasulallah! Kai din nan da ba ka aikata zunubi; "Allah Ya gafarta maka abin da ya gabata na zunubanka da abin da ya jinkirta" – wanda ya zo ma cikin Suratul Fath cewa:"Domin Allah Ya shafe abin da ya gabata na laifinka da abin da ya jinkirta" (Suratul Fath 48:2) amma duk da haka kana irin wadannan addu'oi da ibadu da neman gafara, don me? Sai ya ce: "Shin ba zan zamanto bawa mai godiya ba", wato ba zan zamanto bawa mai godiya ga Allah ba saboda irin wadannan ni'imomi da ya yi min?!

Kyawawan Halayen Hukumar Manzon Allah (s.a.w.a.)

Wannan mai girma ya kasance adali sannan kuma mai tunani. Duk wanda ya karanta tarihin shigowar Manzon Allah (s.a.w.a.) garin Madina – duk da irin wadannan yakukuwa na kabilanci, irin wadannan hare-hare, irin yadda ya janyo makiya zuwa ga tsakiyar wannan Hamada, irin wadannan bugu, irin wannan mu'amala da makiyi mai tsanani – mutum zai ga irin wannan tunani da ke cike da hikima cikin wannan tarihi wanda zai ba kowa mamaki. Ya kasance mai kiyaye doka da tsari, ba ya taba barin wani – ko shi kansa ko kuma ta hannun wani na daban – a karya doka. Shi kansa ya kasance mai bin dokoki. Ayoyin Alkur'ani mai girma ma sun yi ishara da hakan. Daidai da wadannan dokoki wadanda wajibi ne mutane su bi su, shi kansa ya kasance mai aiki da su sannan kuma ba ya taba bari a saba musu.
Hakan nan kuma daga cikin irin kyawawan halayensa na hukuma ya kasance mai girmama yarjejeniyar da aka cimma. Bai taba karya wata yarjejeniyar da aka cimma da shi ba. Kuraishawa su kan karya yarjejeniyar da aka cimma da su, to amma duk da haka shi ba ya karyawa. A lokuta da dama yahudawa sun karya alkawarin da aka yi da su, amma shi kan ina.
Ya kasance mutum ne amini. A lokacin da ya kama hanya zuwa Makka, babu wanda ya fahimci inda annabi ya nufa. Ya tara sojoji ya ce musu ku zo mu tafi. Suka ce ina, ya ce musu daga baya dai za ku fahimta. Bai bar wani ya fahimci cewa zai tafi Makka ba ne. Ya yi abin da har ya kusato garin Makka Kuraishawa ba su sami labarin cewa Annabi ya nufo Makkan ba. A lokacin da ya zauna cikin mutane, babu wanda zai iya fahimtar cewa shi din annabi ne kuma babban kwamandan su. Irin shugabancin al'umma da kuma sojinsa ya kai wani haddi na koli ta yadda ya kan sanya dukkanin mutane su gagara fahimtar me ake ciki. Duk da cewa al'umma ce 'yar karama, garin Madina da wasu garuruwan da suke gefen Madinan, daga baya kuma garin Makka da 'yan wasu garuruwa daya zuwa biyu; to amma ya kasance mai ba da himma ga ayyukan jama'a da kuma tsara su. A cikin wannan al'umma ta kauye, amma ya tsara ofisoshi da ma'ajiya da cibiyoyi na kididdiga a cikin al'umma.

Yadda Manzon Allah (s.a.w.a.) Ya Fuskanci Makiyan Musulunci

Manzon Allah (s.a.w.a.) ba ya kallon makiya da kallo iri guda. Hakan yana daga cikin bangarori masu muhimmanci na rayuwar Annabi (s.a.w.a.). Wasu daga cikin makiyan sun kasance makiya ne wadanda kiyayyarsu ta girmama; amma idan har Annabi ya ga cewa hatsarin da suke da shi bai girmama ba, bai damu da su ba, bai kasance mai tsananta musu ba. Akwai wadansu makiyan wadanda suke da hatsari, amma Manzon Allah (s.a.w.a.) ya kasance yana sanya ido a kansu da kula da su; tamkar Abdullah bn Ubay. Abdullah bn Ubay – wanda ya kasance munafuki ne na koli – ya kasance yana kulla makirci wa annabi; to amma annabi ya kasance yana sa masa ido ne kawai, bai damu da ayyukan da yake gudanarwa ba, haka lamarin ya kasance har karshen rayuwar Ma'aiki. Abdullah bn Ubay ya mutu ne jim kadan kafin rasuwar annabi; amma Manzon Allah (s.a.w.a.) ya ci gaba da hakuri da shi. Wadannan makiya ne wadanda ba su kasance masu hatsarin gaske ga hukuma da tsarin Musulunci da kuma al'ummar musulmi ba. To amma makiyan da suka kasance suna da hatsarin gaske kan Manzon Allah (s.a.w.a.) ya kasance mai tsanani a gare su. Shi dai wannan mutum mai tausayi, mai rahama, wannan mutumi mai kau da kai, amma ya ba da umurnin a kashe ha'inan Bani Kuraiza – wadanda sun kai wasu 'yan darurruka – sannan kuma a kori Banu Nazir da Banu Kainuka. Ya ci Khaibar da yaki; saboda sun kasance makiya ne masu hatsarin gaske. A farkon shigarsa garin Makka, Annabi (s.a.w.a.) ya nuna musu dukkanin rahama; amma su kuwa sun yi ha'inci da kulla makirci. Annabi ya kasance ya yi hakuri da Abdullah bn Ubay; ya yi hakuri da yahudawan da suke garin Madina. A lokacin da ya yi nasara a kan garin Makka, saboda babu wani hatsarin da za a iya fuskanta daga bangarensu, hatta mutane irin su Abu Sufyan da sauran manyan garin ya yafe musu; to amma wadannan makiya masu tsanani wadanda ba za a iya tafiya da su ba kan ya kalubalance su da dukkan karfinsa.

.
Copyright © 2018~2022.
( Uzairu Badamasi Sufi )
Harkarmusulunci@yahoo.com
All rights reserved

Bamu Da Alhakin Tallar Da Ake Sawa Akan Wannan Website Din


Old school Swatch Watches