Kyawawan Halaye 3 (Musulunci Da Kyawawan Halaye)
Kyawawan Halaye Na Bautan UbangijiIdan har mutum yana son samun albarkokin Ubangiji, wajibi ne ya kiyaye kyawawan halaye na Musulunci da kuma hukumce-hukumcen Ubangiji. Alakar daidaikun mutane da Allah tana cikin cewa ne mutum ya yi kokarin wajen ganin aiki da zuciyarsa da halayensa su zamanto sun yi daidai da abubuwan Allah Yake so, su nesanci bin son zuciya da karya da tuhumce-tuhumce da dora soyace-soyacen zuciya a kan rayuwarsu, sannan kuma ya karfafa ambaton Allah da kokarin karfafa alaka da Allah da fada da son zuciya da kuma ibada ta hakika a kowace rana cikin ayyuka na daidaiku.
Tushen Kyawawan Halaye Na MusulunciBayan gabatar da mahangar da take cike da hikima dangane da duniya, shi kansa mutum, tauhidi, kyawawan halaye da tsari na siyasa da zamantakewa masu karfi da kuma ayyuka na ibadu na daidaku, addinin Musulunci ya kirayi dukkanin bil'adama zuwa ga: kawar da munanan abubuwa da rauni da ababe masu lalata rayuwa daga gefensu sannan kuma su karfafa zuciyarsu da imani da tsarki da gaskiya, da kauna da fata da kuma nishadi, sannan kuma su tseratar da duniyar su daga talauci da jahilci da zalunci da nuna wariya da koma baya da amfani da karfi da kaskanci da kuma wulakanci.
Kyakkyawar Rayuwa Ta Ubangiji Da Kuma MusulunciAllah da ManzonSa suna kiran dan'adam zuwa ga rayuwa mai kyau wacce take cike da tsarki. Rayuwa mai tsarki, ba wai kawai ci da sha da kuma jin dadi ba ne; wannan dai ba shi ne abin da kiran Allah da Manzonsa suka kumsa ba. Zuciyar kowane mutum tana kiransa zuwa ga rayuwa irin ta dabbobi. Abin da dukkanin dabbobi suka a gabansu shi ne neman abinci da biyan bukatunsu na sha'awa. Sun kasance masu gwagwarmaya wajen cika cikinsu da kuma ci gaba da rayuwa ne. Rayuwa mai kyau tana nufin rayuwa a bisa tafarkin Allah da kuma tafarkin isa ga manufa ta koli. Manufa ta koli ta mutum ba wai kawai tana cikin ya cika cikinsa ta kowace hanya ba ce; wannan shi ne mafi karancin manufar da kowace dabba za ta iya dauka a matsayin manufarta. A wajen mutum kan, manufa ta asali ita ce isa ga gaskiya, samun kusaci da Allah Madaukakin Sarki da kuma misaltuwa da kyawawan halaye na Ubangiji. Misaltuwa da kyawawan halaye na Ubangiji ba wai wani share fage don aikata wani aiki ba ne; wasu ayyukan ne suka zamanto share fagen isa ga kyawawan halaye na Ubangiji. (A matsayin misali) Adalci share fage ne na isa ga kyawawan halaye na Ubangiji da kuma samun haske cikin rayuwar mutum. Hukumar Musulunci da kuma iko na annabawa sun zo ne saboda tabbatar da hakan; Manzon Allah (s.a.w.a.) yana fadin cewa: "Hakika an aiko ni ne don in cika kyawawan halaye".
Kyawawan Halaye A Nazarin MusulunciMahangar Musulunci dangane da batun akida da kyawawan halaye na mutane ba wai wata mahanga ce wacce ba ruwanta da wani nauyi da ke wuyan mutane ba. Addinin Musulunci ya sanya wani bangare na yada adalci ga batun kyawawan halaye; wato idan har ba a taimaka wa mutumin da za a iya hana shi kauce wa hanya ba, to kuwa ba a yi masa adalci ba. Idan har za a iya taimaka wa wani mutum a fagen kyawawan halaye da kuma shiryar da shi amma sai ya zamana ba a yi hakan ba, to lalle an zalunce shi. A karkashin ayar nan ta
"Daga sababin wannan Muka rubuta a kan Bani Isra'ila cewa lalle ne wanda ya kashe rai ba da wani rai ba, ko barna a cikin kasa, to kamar ya kashe mutane duka ne, kuma wanda ya raya rai, to, kamar ya rayar da mutane ne gaba daya" (Suratul Ma'ida 5:32) Manzon Allah (s.a.w.a.) yana cewa: (shi ne) wanda ya tseratar da wani mutum daga konewa ko kisa. A wata ruwayar kuma shi kansa Manzon Allah (s.a.w.a.) ya fadi cewa ko kuma aka shiryar da wani mutum guda. Daga nan sai ya ce: "wannan shi ne tawilinta mai girma", wato mafi girma da kyawun tawilin wannan aya da ma'anarta shi ne cewa idan har wani mutum ya kashe wani mutum na daban; wato ya samar da hanyar batarsa; ko kuma ya rayar da wani mutum, wato ya zamanto musabbabin shiriyarsa; to a nan kan
"kamar ya rayar da mutane ne gaba daya". Shiryar da wani mutum guda tana da girma da kimar shiryar da dukkanin bil'adama gaba daya; don kuwa kima ta bil'adama da take cikin wannan mutum da kuma sauran dukkanin bil'adama kima ce guda. A lokacin da ka taimaka wa dabi'a ta mutum sannan kuma ka shiryar da shi – shin a fagen akida ne, ko kuma a fagen kyawawan halaye – to ka taimaka wa dabi'ar bil'adama. A saboda haka, za su sami irin wannan kima. Hakan lamari ne da ke nuni da cewa batun shiriya da taimako wajen ceto mutane, nauyi ne da ke wuyan kowane mutumin da zai iya aikata hakan. Ko kuma abin da ya zo karkashin ayar nan mai girma da take cewa
"To mutum ya duba zuwa ga abincinsa" (Suratu Abasa 80:24) yana cewa wannan abinci na ruhi ne; wannan abinci ne na addini; kyawawan halaye ne. Dubi cikin abinci, ma'anar hakan ita ce cewa ka lura da abin da kake amfani da shi ko kuma abin da sauran mutane suke amfanuwa da shi daga hannunka. Hakan lamari ne da ke nuni da irin muhimmancin abinci na ruhi.
Tasirin Salla Cikin Kyawawan Halaye Na MutumSalla ita ce mafi kyawun abubuwan da za su iya kai al’ummar musulmi zuwa ga kyawawan halaye da daukaka ta ruhi. Salla tana sanya wa zuciyar mai salla kwanciyar hankali wanda sharadi ne na asali na samun nasara cikin dukkanin fagage na rayuwa, sannan kuma ta kan kawar da girgiza da rashin kwanciyar hankali wacce ita ce babbar abin da ke kafar ungulu ga tafarkin samun tarbiyya da karfafa kyawawan halaye.
Kyawawan Halaye Da Juyin Musulunci Na IranDalilin Juyi Cikin Al'ummar Bil'adamaA lokacin da aka sami faruwar wani juyi a wata kasa, an san cewa dalilin hakan shi ne sauya yanayi na zamantakewa a kasar; su kawar da hukuma; da kuma sauya tsari na zamantakewa da tattalin arziki. Wannan ita ce manufar wani juyin juya hali. To amma mece ce manufar sauya yanayi na zamantakewa na wata al'umma? Saboda a sauya halayen mutane ne. Saboda a lalataccen tsari na ja’irci haka nan kuma a tsari irin na dagutu ana tarbiyantar da mutane ne mummunar tarbiyya. Saboda a kan samar da mutane ne da suke da akidar abin duniya da rashin ababe masu karfafa ruhi tare da su. A kan samar da mutanen da suka kasance marasa cika alkawari, marasa tsarkin zuciya da kuma marasa gaskiya ne. Haka nan kuma ana nesantar da mutane daga rahama da mutumci da kauna da aiki tare. Wadannan abubuwa ne da wata lalatacciyar rayuwa wacce take cike da kura-kurai take samarwa. Ana yin juyin juya hali ne don a sauya al'umma sannan sauya wata al'umma kuma tana samuwa ne saboda a sauya halayen al'umma. Saboda ya zamana an tarbiyyantar da mutane da kyau. Adalci na zamantakewa wani tushe ne. Sannan kuma wata manufa ta asali kuma mai girma ce. To amma za a iya tabbatar da adalci na zamantakewa ne a lokacin da aka tarbiyyantar da al'umma; kada su yi zalunci sannan kuma kada su amince da zalunci.
Babbar Manufar Juyin juya halin MusulunciA karkashin hukuma ta Ubangiji da kuma hukuma ta gaskiya da tsarin siyasa na Ubangiji ne za a iya tabbatar da tsarkin zuciya da kyawawan halaye, sannan kuma Allah Madaukakin Sarki bai taba barin wani addini ba tare da siyasa ba. Abin da ya zamanto manufa ta asali kuma ta koli a juyin juya halin Musulunci na Iran shi ne tsarkake zukatan mutane. Dukkanin komai share fage ne na tsarkkake zuciya. Duk da cewa ana kirga tabbatar da adalci cikin al'umma da kuma kafa hukumar Musulunci cikin al'umma a matsayin babbar manufa, to amma shi kansa hakan wani share fage ne domin samun daukaka da kuma shiryar da mutum wanda ake iya samunsu cikin tsarkake zuciyar bil'adama. Rayuwa cikin wannan duniya – matukar dai ana son samun sa'ada – tana bukatar tsarkake zuciya, haka nan ma wajen samun matsayi na lahira, shi ma ya dogara ne bisa tabbatar da tsarkin zuciya. Nasara da samun babban rabo – wato mutum ya kai ga manufa ta asali da yake son isa gare ta – ya damfara ne da tsarkin zuciya.
Girman Aikin Imam Khumaini (r.a)Girma da daukakar da aikin Imam Khumaini (r.a) yake da ita ta samo asali ne sakamakon alakar da yake da ita da Allah da kuma tsarkake zuciyarsa da ya yi. Imam (r.a) ya kasance mutum ne mai tsarkin zuciya. Makiyansa na ciki da waje sun yarda da wannan siffa tasa sannan kuma suna fadin cewa shi din nan mutum ne mumini. Daya daga cikin fursunoni Amurkawa da aka yi garkuwa da su na tsawon kwanaki dari hudu da arba'in da hudu a Iran (wato jami'an ofishin jakadancin Amurka da aka tsare su a Iran bayan nasarar juyin juya halin Musulunci da kuma kame ofishin jakadancin Amurka da wasu dalibai suka yi samun ayyukan leken asiri da suke gudanarwa a wajen) da kuma dukkanin abubuwan da suka biyo baya wadanda sun faru ne a kan idon Imam, a hirar da suka yi da manema labarai yana cewa: ni dai ba mutum ne wanda zan yi farin ciki saboda rasuwar Imam ba. Shi ya kasance mutum ne mai kyawawan halaye irin nasa, sannan kuma babu wani mutum da ya kai shi.
Kyawawan Halaye Da Kasashen YammaciYanci Daga Kyawawan HalayeAbin da a kasashen yammaci aka dauke shi a matsayin take, a matakin farko shi ne batun 'yancin mace. 'Yanci dai yana da ma'ana mai fadi; ya hada da samun 'yanci daga zama fursunan yaki, haka nan kuma ya hada da 'yanci daga kyawawan halaye – don kuwa kyawawan halaye wani kaidi ne – haka nan kuma 'yanci ne daga irin mummunan tasiri na masu ba da aiki wadanda suke jan mace zuwa ga aikin leburanci da kuma ba ta 'yan wadansu kudade, haka nan kuma ya hada da 'yantuwa daga dokokin da suke hana mace zama mai biyayya ga mijinta. 'Yanci dai yana iya kumsar dukkanin wadannan ma'anoni.
Kyawawan Halaye Cikin Tsarin Sassauci Na YammaciA kasashen yammaci saboda kyawawan halaye wani lamari ne da ya shafi bangare guda, saboda haka 'yanci ya zamanto ba shi da wani takunkumi ko kan iyaka. Me ya sa? Ku din nan da kuka yi imani da wasu kyawawan halaye, ba ku da hakkin ku soki wani mutumin da yake cin mutumcin wadannan abubuwa da kuka yi amanna da su; don me yiyuwa ne shi bai yarda da kuma daure kansa da wadannan abubuwa ba. A saboda haka babu wani haddi ga batun 'yanci; wato a bisa la'akari na ruhi da kyawawan halaye, babu wani haddi da kan iyaka. ‘Yanci dai a sake yake haka nan ba tare da wani haddi da takunkumi ba. Me ya sa hakan? Don kuwa babu wata tabbatacciyar hakika; don kuwa a mahangarsu hakikanin kyawawan halaye wani lamari ne da ya shafi wani bangare guda.
Dangane da abin da ya shafi akida da kyawawan halaye, kasashen yammaci masu akidar abin duniya suna da matsayarsu; haka nan a fagen karfi da dukiya – wanda wani bangare ne na irin amfanin da ake samu – matsayarsu wani abu ne na daban. A duk inda kasashen yammacin suka ga cewa za su iya samun karfi da kuma dukiya, ko kuma akwai wani mai adawa, to su kan shiga wannan fage da dukkan karfinsu da kuma amfani da tursasawa, ba sa taba nuna sassauci. To amma a babin akida da kyawawan halaye kan a'a, alal akalla a kan takarda da kuma fagen ikirari da fatar baki mutane ne masu sassauci da nuna halin ko in kula; wato hakan ba shi da wani muhimmanci a wajensu. Kowane mutum kowace irin akida yake da ita, kowane irin kyawawan halaye yake da shi, babu ruwansu! Ko da yake a wasu wajajen mutum ya kan iya ganin cewa a cikin lamurran da suka shafi al'adu a samu lokutan da su kan zamanto masu tsaurin ra'ayi da rashin nuna sassauci. Wato a duk inda yake da alaka da tattalin arzikinsu ko kuma fagen siyasa ko kuma siyasarsu ta fadada da neman samun karfi, za ka ga cewa suna tsayawa kyam wajen bin wannan lamarin. To amma yanayin aikinsu shi ne cewa a babin akida da al'adu ba su nuna wata damuwa ko kuma tada jijiyoyin wuya ko kuma daukar matsaya. A cikin lamurran da suka shafi kyawawan halaye kan babu wani abin da ke hana 'yanci. A matsayin misali yunkurin luwadi da madigo a kasar Amurka daya ne daga cikin yunkurin da suke yawo; suna ma alfahari da shi; su kan gudanar da zanga-zangogi a kan tituna, su kan buga hotunansu cikin mujallu; cikin alfahari suke fadin cewa kasurgumin dan kasuwa kaza ko kuma dan siyasa wane dan wannan kungiyar ne; babu wani wanda yake jin kunya ko kuma inkarin hakan. Sama da hakan, wasu daga cikin mutanen da suke adawa da hakan, su kan fuskanci mayar da martani mai kaushi daga wajen wasu kafafen watsa labaran suna cewa wannan yana adawa da luwadi da madigo. Wato kyawawan halaye ko da wasa ba sa taba ayyana kan iyaka ga 'yanci.
Dabi'ar Neman Yaki A Kasashen TuraiAkwai wani yanayi mai ban mamaki wanda yake gudanar da yanayin halaye da dabi'un al'umma a kasashen Turai. A saboda haka ne a lokacin da ka kalli 'yan wasu karnoni na baya-bayan nan da suka wuce za ka ga cewa kasashen Turai sun fuskanci mafi muni da wahalar yakukuwa. Tsawon tarihi an samun abkuwar mummunan yaki tsakanin kasashen turai – a matsayin misali tsakanin kasashen Jamus da Faransa - . A duk lokacin da suka zamanto ba sa cikin yaki da wata kasa wacce ba ta Turai ba, to za ka ga cewa suna cikin fada da junansu; amma a duk lokacin da suka fuskanci wata kasa wacce ba ta turai ba, za su hada kansu waje guda kan wannan kasar wacce ba ta Turai din ba. Wato da'irar su haka take a killace. Ya zuwa yanzu dai kasashen Turai sun haifar da yakukuwan duniya guda biyu. Haka nan kuma dukkanin kakkasa kasashen duniya bayan wadannan yakukuwa guda biyu da aka yi, shin a kasashen Turai din ne ko kuma a kasashen da ba na Turai din ba wato a yankunan gabas ta tsakiya, Balkan, Afirka da yankunan larabawa, turawan ne dai suka yi hakan; wadannan wadansu dabi'u ne kautattu.