Kyawawan Halaye 4 (Mutum Da Kyawawan Halaye)
Rukuni Na Asasi Na Mutum MusulmiMutum musulmi ba wai kawai shi ne mutumin da ya yi imani da Musulunci da aikata ayyukan Musulunci ba, face dai kyawawan halaye na Musulunci ma daya ne daga cikin rukunai na asasi; idan kuwa ba haka ba ko da a ce mutum ya kasance mai riko da akidar Musulunci da kuma aiki da ma'anar salla da azumi da makamantan hakan, to amma sai ya zamanto mai hassada, marowaci, matsoraci, mai fatan sharri, maras karfin gwuiwa da irada, to wannan ba mutum ne musulmi ba. Mutum musulmi wajibi ne ya zamanto a dukkanin bangarori uku – bangaren tarbiyya, bangaren ilimi haka nan bangaren aiki – ya zamanto mai aiki.
Tushen Matsalolin MutumIdan har muka dubi tushen matsalolin da bil'adama suke fuskanta, to lalle za mu ga cewa hakan yana komawa ne ga gurbatar zukatan bil'adama. A duk inda aka sami rauni da matsaloli ko dai saboda sabani ne ko kuma saboda kwadayi da handama da son duniya ko kuma saboda bakin halin mutane a kan junansu ne ko kuma saboda tsoro da nuna rauni da tsoron mutuwa, ko kuma saboda kwadayi da sha'awa da son jin dadi ne. Wadannan su ne tushen matsalolin da bil'adama suka fada ciki.
Dalilan Gushewar Al'adu Da Al'ummomiGushewar al'adu ya samo asali ne sakamakon kauce wa hanya. A lokacin da al'adu suka kai koluluwarsu, amma sakamakon rauni da kauce wa hanya da suka fuskanta sai ya zamanto su da kansu sun kama hanyar rugujewa. Mu dai a yau muna ganin alamun irin wadannan rugujewa na al’adu cikin al’adun kasashen yammaci, wanda ala’adu ne na ilimi ba tare da kyawawan halaye ba, abin duniya ba tare da abubuwan da suke kyautata ruhi ba sannan kuma addini da karfi ba tare da adalci ba.
Faduwar al’ummu a ko da yaushe ba wani lamari ne da yake faruwa haka nan siddan ko kuma kwatsam ba; wani lamari ne da ke faruwa sannu a hankali. Idanuwan masu tunani irin na yammaci a kasashen Amurka da Turai suna ganin iri wannan lamari da ke faruwa sannu a hankalin. A cikin wancan al’ummar, matashi yana kwadayin rayuwa ba tare da wani nauyi ko kan iyaka ba, rayuwar rashin kunya sannan kuma yana kaunar aikata munanan laifuffuka da wuce gona da iri, sannan kuma ya kutsa cikin fasadi da munanan halaye. Irin wadannan matasa a cikin kowace al’umma, komai irin ilimi da masaniyar da suke da su, za su zamanto masu kawar da kafafu da kuma tushen wannan al’umma kamar yadda gara suke yi.
Al’umma Da Kyawawan HalayeAbabe Masu Kima Na Asali Na Wata Al’ummaMutumcin kowace al’umma yana cikin yanayi kyawawan halayenta ne; wato alal hakika tushe na asali na wata al’umma shi ne tushen kyawawan halayenta sannan kuma dukkanin komai ya ginu ne bisa hakan.
Idan har aka tabbatar da kyawawan halaye cikin wata al’umma, to kuwa za a tabbatar da adalci na zamantakewa a cikinta; za a gina al’ummar sannan kuma mutane za su rayu cikin aljanna ko da kuwa suna cikin wannan duniyar ce. A wannan duniyar, mafi girman laifuffukan da ake aikatawa a kan bil’adama sun samo asali ne daga munanan halaye da fasadin da suke cikin halaye da dabi’un daidaikun mutane. Mafi girman adalci na zamantakewa suna da alaka ne da kyawawan halaye. Duk kuwa da cewa wani bangare mai yawa na hakan suna da alaka ne da dokokin da aka kafa cikin wannan al’ummar. To amma dokoki ba tare da cewa mutane suna da kyawawan halaye na Ubangiji da Musulunci ba, ba za su haifar da wani abin a zo a gani ba. A yau din nan akwai wadansu mutane masu yawa wadanda suke da kudaden shiga masu yawan gaske, to amma shin wajibi ne su sarrafa dukkanin wadannan kudade wajen biyan bukatun kansu? Wannan dabi’a ce ta abin duniya. Wannan dabi’a ce ta Shaidan. A jumlar da tafi dacewa wannan dabi’a ce ta dabbanci. Don kuwa ita dabba duk abin da take da shi, mallakanta ita kadai ne. To amma kyawawan halaye na mutum musamman ma dai kyawawan halaye na Musulunci ba sa ganin hakan a matsayin abin da ya dace. Abin da mutum ya ke da shi, to bayan ya biya bukatarsa ta wajibi, to ya sarrafa shi wajen biyan bukatun al’ummar da suke rayuwa tare da shi.
Kan Iyaka Tsakanin Al’ummar Musulunci Da Al’ummar JahiliyaA wani lokaci a kan sami wata al’umma wacce mutanen da suke cikinta mutane ne da suke da kyawawan halaye. Daidaikun mutanen wannan al'umma mutane ne masu yafuwa, masu tunani, masu hankali, masu alheri da kyautatawa, masu taimakon juna, masu hakuri da jurewa matsaloli, masu hakuri da wahalhalu, masu kyawawan halaye da kyakkyawar mu’amala da sauran mutane sannan kuma masu sadaukarwa a duk inda sadaukarwar ta zamanto wajibi. Haka nan kuma mai yiyuwa ne a samu wasu akashin hakan. Wato a samu mutane wadanda alakar su da junansu ba alaka ce ta tausayi da mutumci da adalci da kyawawan halaye ba, rayuwar ta zamanto an gina ta ne bisa asasin amfanin da mutum zai samu kawai. Wato mutum zai zauna da dan’uwansa ne kawai a lokacin da ya zama hakan ya yi daidai da amfanin da zai samu. Idan kuwa har ba haka ba, to a shirye ya ke ya kawar da wancan din. Wannan ma wani nau'i ne na wata al’ummar. Wannan al’umma, al’umma ce ta jahiliya wacce ta bambanta da al’ummar da a cikinta ake kula da kyawawan halaye wacce ake kiranta da al’ummar Musulunci. Aiko Manzon Allah (tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi da alayensa) tana da irin wannan siffa ce ta kyawawan halaye. A saboda haka ana iya cewa daya daga cikin kan iyakokin da kuma abubuwan da suke bambanta Musulunci da jahiliya shi ne batun kyawawan halaye.
Kyawawan Halaye Da RayuwaAljannar Da Take Doron KasaMusulunci dai yana bukatar ganin mutane sun zamanto masu tausayi da damuwa da makomar junansu da kuma kaunar juna da kiyaye ababen amfanin junansu su nuna damuwa da irin wahalhalu da kura-kuran da junansu suke ciki, su dinga addu’a ga junansu sannan kuma su dinga mu’amala da junansu cikin rahama da tausayi;
“kuma suka yi wa juna wasiyya da tausayi”(Suratul Balad 90:17). Wannan yanayi na abokantaka, wannan alaka ta tausayi, alaka ta so da kauna tsakanin ‘yan’uwa, tsakanin abokai, tsakanin ‘yan’uwa mata, tsakanin dukkanin al’ummar musulmi, fatan alheri, tunani na alheri, dukkanin wadannan wasu sifofi masu kyau ne kuma abin yabo; wajibi ne a karfafa su a cikinmu. Mafi munin siffar da take tattare da mutum ita ce cewa mutum ya sanya kansa da kuma maslaharsa a matsayin tushen tunaninsa sannan kuma ya zamanto a shirye ya ke ya sanya adadin mutane masu yawan gaske cikin hatsari da kuma wahala saboda biyan wata bukata ta kashin kansa.
Al’ummar da a cikinta aka kawar da hassada, rowa, rashin mutumci, aikata laifuffuka, handama, mummunan fata, kulla makirci da fatan sharri ga juna a cikinta, alal hakika wata aljanna ce a doron kasa; ‘don kuwa aljanna ita ce wajen da babu cutarwa a cikinsa”. Aljanna waje ne na al’ummar musulmi, idan har aka samu tsarkake zuciya.
Alakar Dukiya Da Kyawawan HalayeWadansu mutane cikin wauta suna sanya ido kan wadansu kasashe masu dukiya suna cewa wadannan kasashe suna da dukiya amma ba su da addini da kuma kyawawan halaye; mu ma dai wannan hanyar ya kamata mu kama. Suna zaton cewa dukiyar da suka samun ta samo asali ne saboda rashin riko da addini da kuma kula da kyawawan halayen da suka yi! Wannan kuskure ne. Duk wata kasar da ta zamanto mai dukiya da kuma karfi, hakan ya samo asali ne saboda wasu dalilai na musamman da suke samar da dukiya da kuma samar da karfi. A duk inda aka sami tunani da aiki da kokari, to kuwa za a sami wani abu, wannan wata sunna ce ta Ubangiji. Hatta mutanen da suke neman duniya kawai ba tare da abubuwa masu karfafa ruhi ba, matukar suka zamanto suna da tsari na gudanar da aiki da kuma kokari to lalle za su sami abin da suke nema:
“Dukkansu Muna taimakon wadannan da wadancan daga kyautar Ubangijinka” (Suratul Isra’ 17:20) wannan magana ce ta Alkur’ani. A duk lokacin da aka yi aiki da kokari saboda abin duniya, to kuwa za a sami dukiya da karfi; to amma ba za a sami sa’ada ba.
Kyawawan Halaye Da GudanarwaGwargwadon yadda za ku iya ku mayar da tsarin gudanarwarku (yadda ake shugabanci) ya zamanto na Musulunci. Gudanarwa irin ta Musulunci, tana nufin kyawawan halaye na Musulunci bugu da kari kan tsayin daka irin ta gudanarwa.
Gwargwadon yadda za ku iya, ku yi kokari mai da gudanarwa ku ta zamanto ta Musulunci. Gudanarwa ta Musulunci, tana nufin kyawawan halaye na dan'adam bugu da kari kan tsayin daka irin na gudanarwa. Shin ba ku ga fadin Allah Madaukakin Sarki ba ne inda yake cewa:
"Sa'an nan kuma idan ka yi niyyar zartarwa, to, ka dogara da Allah" (Suratu Al Imrana 3:159)? Allah Madaukakin Sarki yana gaya wa ManzonSa cewa: Ka girmama ra'ayin wadannan mutane. Sakamakon shan kashin da musulmi suka yi bayan yakin Uhudu, sun kasance cikin bakin ciki sosai. Ka yi shawara da su, ka yi mu'amala mai kyau da su; to amma
"idan ka yi niyyar zartarwa, to, ka dogara da Allah", wato a duk lokacin da ka yi azama, to shi kenan ka dogara da Allah, ka kama hanya. Wannan ita ce gudanarwa da kuma shugabanci: ka nuna kyawawan halaye, to amma kuma ka zamanto mai kaifin wuka, ka nuna tsayin daka na gudanarwa da shugabanci sannan kuma ka dogara da Allah a kowane yanayi; ka nemi alheri daga wajen Allah Ubangijin talikai sannan kuma ka dogara da Shi.
Ilimi Da Kyawawan HalayeWajibcin Tafiyar Ilimi Kafada da Kafada Da Kyawawan HalayeMai neman ilimi yana bukatar kyawawan dabi'u na wajibi. Gwargwadon yadda mai neman ilimi ya zamanto mai irin wadannan kyawawan halaye da tsoron Allah, to kuwa gwargwadon yadda zai sami ilimi da kuma yarda da ilimin da kuma girmama shi bugu da kari kan amfanuwa da shi. Wajibi ne ilimi ya zamanto tare da kyawawan halaye, haka nan wajibi ne ci gaban masana'antu da ilimi da abubuwan duniya su zamanto tare da kyawawan halaye. Haka nan kuma komawa ga Ubangiji shi ma lamari ne da ke tabbatar da kyautatuwar halaye.
Idan har aka dauka cewa al'umma tana da kyawawan halaye, to amma kuma ba ta ilimi, to wannan rashin ilimin zai ja ta zuwa ga halaka. Saboda kuwa makiya za su iya zuwa su tilasta wa wannan al'umma ilimi da take bukata wadanda za su iya karo da juna da kyawawan halayenta. Na'am wannan al'umma za ta iya hakuri na dan wani lokaci na rashin irin wannan ilimi, to amma dai daga karshe wajibi ne ta bukace shi. Irin wannan yanayi shi ne ya ke jijjiga tushe da kuma kawar da shi. To idan wata kasa da wata al'umma ta zamana tana da jami'a mai kyau, to amma ba ta da kyawawan halaye da abubuwan da suke kyautata ruhi, ya ya yanayin zai zamanto? Hakan ya ma fi wancan din muni! Don kuwa a irin wannan yanayi, ilimi zai sami ci gaba a wannan kasar; to sai dai ba a tafarkin tabbatar da manufa mai kyau ba. Zai zamanto ilimi ne a tafarkin yin hidima wa zalunci, girman kai, wariya, rashin tausayi hatta ma ilimi wajen hidima wa ha'inci da ababe masu kima na kasa. Haka lamarin zai kasance.
Raba Ilimi Da Kyawawan HalayeDalilin da ya sanya a yau irin ilimin da kasashen yammaci suke da shi ya gagara ceto bil'adama shi ne cewa hakan bai yi daidai da 'yan'adamtaka ba ne. A duk inda aka sami ilimi, to amma sai aka rasa lamiri da kyawawan halaye da abubuwan da suke karfafa ruhi da irin shu'uri na dan'adam, to kuwa mutane ba za su amfana da wannan ilimin ba. Ilimi ba tare da kyawawan halaye ba, zai zamanto makami mai guba ne, zai cutar da mutanen da ba su ci ba su sha ba; zai zama makami wanda zai cutar da fararen hula a kasashen Labanon da Palastinu da aka mamaye da sauran yankuna na duniya; zai zamanto sinadari mai guba a Halabja da sauran yankuna na duniya wanda zai kawar da mata da kananan yara da matasa da mutane da dabbobi! Dukkanin wadannan abubuwa daga ina suka zo? Wadannan sinadarai masu kisa, sun fito ne daga wadannan cibiyoyi na ilimi na wadannan kasashe na ATurai! Su ne wadanda suka samar da wadannan sinadarori sannan suka ba wa wancan gwamnatin wacce ba ta lura sosai. Makamai da nau'oi daban-daban na abubuwan da ilimi ya samar a yau sun gagara kuma ba za su iya ma ba wajen sanya bil'adama zama cikin kwanciyar hankali, da sanya iyalai cikin farin ciki da samun sa'ada sannan kuma 'ya'ya da mata da kananan yara su ji dadin rayuwa; hakan kuwa saboda ilimi ba ya tafiya ne tare da dan'adamtaka.
Kyawawan Halaye Na LikitanciWajibi ne likita ya ba wa batun kyawawan halaye muhimmancin gaske ta bangarori biyu: daya shi ne ta bangaren karba sannan dayan kuma ta bangaren mikawa. Akwai kyawawan halaye na Musulunci a wajen da ake koyarwa. Wato a samar da wani yanayi na kyawawan halaye cikin harkar koyarwa: ya ya za a koyar, irin yanayin koyarwar, a ina za mu koya sannan don me za mu koya; dukkanin wadannan abubuwa a fagen koyarwa kenan. 'Allah Ya yi rahama ga mutumin da ya aikata (koyi) wani abu sannan ya kware a kansa" to a cikin koyarwa ma akwai hakan. Wato a koyi abu da kyau sannan kuma a ko da yaushe ya zamanto ana neman abu mai kyau ne, hakan wata marhala ce ta kyawawan halaye.
Mataki na gaba, shi ne mataki na gabatar (koyar) da abin da aka karanto (ga masu bukata). Wato wajen da za ka yi gaba da gaba da mara lafiya (a asibiti) ko kuma dalibi a jami'a. Hakan wani mataki ne na daban; nan din ma wani waje ne na ayyukan kyawawan halaye. Akwai batutuwa masu kyau da jan hankula cikin wasiyyar 'Hippocrates' (likitan nan dan kasar Girka). Ko da yake abin ya fi shafan mara lafiya ne, wato kan yadda za a yi mu'amala da mara lafiya wanda hakan daya ne daga cikin bangarori biyu na kyawawan halaye.
Kyawawan Halaye Da SiyasaA duniya wani abu ne da aka amince da shi na cewa wajibi ne duk wani mutumin da yake da jagoranci na al'umma a wuyansa ya zamanto yana da wasu halaye da dabi'u na musamman! Girman kai, samun rayuwa ta jin dadi da kashe kudi, son ado, tilasta ra'ayinsa da son ransa da makamantan hakan. Wadannan abubuwa ne da al'ummomin duniya suka amince da su, na cewa duk wani mutumin da yake jagoranci ya zamanto yana da su. Hatta a kasashen da aka aiwatar da juyin juya hali, ma'abota juyin juya halin da a jiya suke rayuwa karkashin tanti da kuma boye kansu a cikinsa, to amma daga lokacin da suka sami mulki, shi kenan sai yanayin rayuwarsu ta sauya haka nan yanayin dabi'ar hukumarsu sai ta sauya, yanayinsu ya zamanto irin na sauran sarakuna da shugabannin kasashen duniya.
Imam Khumaini (r.a) ya sauya wannan tunani na kuskure sannan kuma ya tabbatar da cewa wani jagora abin kauna ta wata al'umma ko kuma ta musulmin duniya yana iya gudanar da wata rayuwa da take cike da gudun duniya, sannan kuma maimakon karbar baki a wata gagarumar fadar da aka yi mata kawa, zai iya karbansu a wata Husainiya sannan kuma ya yi mu'amala da mutane da tufafi da harshe da kyawawan halaye na annabawa.
Akwai wadansu abubuwa guda biyu da suke barazana ga siyasa: daya daga ciki shi ne raba siyasa da kyawawan halaye sannan kuma a hana ababe masu kyautata ruhi da daukaka samun gindin zama cikinta; wato shaidanu su sami iko a kan siyasa; son zuciyar mutane su zamanto su ne masu rike da siyasa; azzalumai da masu son amfani da karfi su zamanto su ne masu gudanar da siyasa da jan ta zuwa nan da can. Idan har wannan bala'i ya fada wa siyasa, to a wannan lokacin dukkanin bangarori na zamantakewa na al'umma za su cutu daga wannan bala'in. Wani bala'in da ke fuskantar siyasa shi ne cewa mutane masu karamin tunani, masu tunani irin na yara da kuma rauni su zamanto su ne masu gudanar da siyasa, sannan kuma iko na siyasa ya tashi daga hannun mutanen da suke da kwarewa ya koma hannun mutanen da ba su da kwarewa.
Fasaha Da Kyawawan HalayeTauhidin Kyawawan Halaye Da FasahaIdan har mutum abin girmamawa da daukaka ne, to kuwa zuciya da kwakwalwa da kuma tunaninsa ma abin girmamawa da daukaka ne. Ba komai ne za a dinga gaya wa mai saurare ba, saboda kawai yana zaune yana sauraren maganganun wani masanin fasaha. Wajibi ne masanin fasahan ya yi dubi cikin abin da yake son gabatarwa. Abin lurar shi ne kwayawan dabi’u da daukaka. Akwai wani abin da na taba karantawa – ina zaton – daga cikin maganganun Romain Rolland (marubuci dan kasar Faransa wanda aka haife shi a ranar 29 ga watan Janairun 1866 – (sannan ya mutu a ranar) 30, ga Disamba 1944) inda aka ce a cikin wani aiki na fasaha, kashi daya cikin dari ne aiki na fasaha, kashi casa’in da tara cikin dari na kyawawan halaye ne; ko kuma idan muka yi taka tsantsan muna iya cewa: kashi goma cikin dari fasaha, kashi casa’in cikin dari kyawawan halaye ne. Ni dai ina ganin wannan ba ingantacciyar magana ba ce. Idan aka tambaye ni, ni zan ce ne kashi dari cikin dari fasaha, sannan kashi dari bisa dari kyawawan halaye. Wadannan abubuwa ne da ba sa karo da junansu. Wajibi ne a gabatar da aiki cike da yanayi na fasaha dari bisa dari sannan kuma kashi dari bisa darinsa su zamanto suna da abubuwa masu daukaka da girmama mutum sannan kuma cike da kyawawan abubuwa. Abin da yake damun wasu daga cikin mutane masu kishi a wannan fage na fasaha shi ne cewa masanin fasaha yana fakewa da ‘yancin tunani ko kuma ‘yanci na fasaha, ya yi watsi da abubuwan da suka shafi kyawawan halaye. Wannan lamari ne mai muhimmancin gaske.
Ababen Da Suke Kawo Cikas Wa Kyawawan Halaye‘Yanci Ba Tare Da Kyawawan Halaye BaTsarin demokradiyyan yammaci wani tushe da falsafa ne na tsarin sassauci. Suna cewa ne saboda mutum yana da ‘yanci, don haka wannan ‘yancin yana sanyawa ya zamana babu mulkin kama-karya sannan a samu tsarin jamhuriya. To da ya ke wannan ‘yancin ma’ana ce ta sassauci, ‘yanci ne sakakke. Wato idan har mutane suka dau matsaya, za su iya amincewa da abin da dari bisa dari zai zamanto mai cutarwa a gare su. Ku dauki mutanen Ingila a matsayin misali, sun amince da batun luwadi a majalisarsu, sun amince da cewa auren muharramar (mutum) daidai ne. A nan dai babu hankali cikin hakan wanda bai kamata su amince da hakan ba; amma wajibi ne su amince da hakan. Mene ne bambancin luwadi da kuma auren muharrama? A nan dai babu hikima cikin wannan aikin. A yau idan har majalisar Amurka ko kuma ta Ingila sun kuduri aniyar cewa ana iya auren muharrama, to shi kenan babu kuma batun irin kishi na namiji a wannan bangaren. A saboda haka babu wata hikima da hankali da yake hukumci a kan wannan ‘yancin. Idan har suka ce daga yanzu zuwa sama ‘yanci ya saba wa kyawawan halaye, sai mu ce wani kyawawan halayen kuma? Babu wani kyawawan halaye, suna da ‘yanci! Don kuwa hikimar da ke cikin tsarin sassauci ‘yanci ne wanda babu wani abin da zai kayyade wannan ‘yanci da ake da shi in dai ba ‘yancin ya yi karo da asasin ‘yanci na gaba daya ba ne. Wannan shi ne kawai abin da ba za su amince da shi ba. Alal hakika demokradiyyar yammaci wanda ta ginu ne bisa falsafar sassauci ita da kanta ta tabbatar da rashin ingancinta. Saboda a irin wannan yanayin mai yiyuwa ne dukkanin ababe masu kima na kyawawan halaye na wata al’umma su lalace. To a yau mutanen da suka yi imani da wannan tunani, ba a shirye suke su amince da hakan ba; to sai dai abin da ya zama wajibinsu shi ne hakan.
Nesantar Kyawawan HalayeMutanen kasashen yammaci su da kansu suka ruguza tushen kyawawan halaye. Tun shekaru hamsin zuwa sittin din da suka gabata suka sanya tushen kyawawan halaye bisa hanyar rugujewa. Wato tun lokacin da suka sanya lamarin ‘yanci na daidaiku da kuma ci gaba ba tare da wani haddi da kan iyaka ba da kuma cewa kowane mutum yana da ‘yancin ya aikata dukkanin abin da ya ga dama, sannan kuma daga dukkanin abin da yake son ya ji dadi da shi yana iya ji, tun daga wancan lokacin wancan al’umma ta lalace a bangaren al’adu. Hakan lamari ne da ke nuni da cewa su din nan suna cikin mawuyacin hali a bangaren al’adu da kuma yanayi na mutane.
Al’ummar Amurka ma, duk da irin dukiyar da take da ita mai yawa, da irin abubuwan rayuwa masu yawa da suke da su da kuma irin ci gaba na ilimi da suke da shi, amma suna fuskantar matsalar rashin ababe masu kyautata ruhi da kyawawan halaye wanda hakan shi ne dalilin faruwar irin wadannan munanan ayyukan laifuffuka da suke faruwa a can. Hakan kuwa sakamako ne na nesantar ababe masu kyautata ruhi. Ta ya ya za a iya a ce wata uwa, za ta kashe ‘ya’yanta saboda wata sha’awa mai gushewa da kuma wata kaskantacciyar bukata?!
Idan har saboda jin dadi na kashin kai mutum zai iya aikata irin wannan mummunan aiki, me ya sanya ake matsin lamba da kuma yin barazana dangane da muggan kwayoyi? Zuciyar wani mutum tana son amfani da muggan kwayoyi; da wani dalili ne za a hana shi?! za su saura ba su da amsar da za su fadi. A lokacin da tushen kyawawan halaye na wata al’umma ya ruguje, to babu abin da za a iya yi. Wannan shi ne yanayin da a halin yanzu suke ciki.
Munanan HalayeDalilin da ya sanya wadansu mutane saboda neman abin duniya suke shiga cikin rayuwa mai wahala ta ruhi da aikata munanan halaye da kwadayi da handama da rowa shi ne cewa hakan sakamako ne na nesantar irin koyarwa ta Ubangiji da ababen da suke kyautata ruhi da kuma tauhidi, wanda yake kiran mutane zuwa ga al’umma guda. Irin wannan duniya da take cike da ababen jin dadi sannan kuma abin so. Haka lamarin ya ke a cikin al’umma da kuma fage na duniya.
Tushen dukkanin matsalalolin da al’ummomi, jami'ai, manya da kanana suke fuskanta shi ne son zuciya da bauta mata da kuma samar da yanayi na fir'aunanci cikin zuciyar. A wani lokaci a kan sami mutum a cikin jikinsa – wato a zahirinsa – babu wani abin da ke nuni da fir’aunanci a tattare da shi; to amma a cikin zuciyarsa akwai fir’aunanci. Soyace-soyacen zuciya, bautar kai, sanya kai a matsayin tushen komai da kuma sanya dukkanin abin da ya ke so a matsayin tushen komai, wadannan su ne tushen mafi yawa daga cikin lalata ta rayuwa da ake fuskanta. A saboda haka wajibi ne a kama hanyar tsarkake zuciya.
Tasirin Rubewar Kyawawan Halaye Cikin IyaliA duk inda kafafun sha’awa da iskanci da lalacewar kyawawan halaye suka kafu, to kuwa za a samu rubewar iyali. A duk lokacin da aka ci gaba da hakan, abin da zai faru shi ne abin da a yau ake ganinsa a fili a cikin kasashen yammaci. Musamman ma a wasu wajajen da iskanci da lalata ya zamanto ruwan dare gama duniya. A irin wadancan al’umma iyali ba shi da wata ma’ana ta hakika. Idan ma a wani lokaci miji da mace suna son su rayu tare da junansu, to wajibi ne su sanya wani lokaci da dukkaninsu za su kasance a gida don su sami lokacin da za su zauna tare da ‘ya’yansu, su sha shayi, wato yanayi na iyali dai ba zai sake samun irin wannan yanayi na so da kauna ba. A saboda haka batu na farko shi ne cewa su nuna wa junansu so da kuma yarda da junansu.
.
Copyright © 2018~2022.
( Uzairu Badamasi Sufi )
Harkarmusulunci@yahoo.com
All rights reserved