Tauhidi
Kasantuwa bawan Allah tana nufin 'yanci, yana nufin girma, yana nufin kama hanyar kamala, yana nufin amfani da ababe da suke tabbatar da kamala gwargwadon yadda za a iya da kuma amfanuwa.Fasalin Farko: Tauhidi Da Mahangarsa Kan DuniyaMa’anar Tauhidi A IstihalanceBisa al’adu da koyarwar Alkur’ani, tauhidi yana nufin Allah Madaukakin Sarki Shi kadai ba shi da wani abokin tarayya, Shi ne ya halicci duniya, Shi Ya halicci dan’adam, gudanar da duniya tana hannunsa ne, gudanar da dokoki na duniya suna hannunSa ne, dokokin da suke gudanar da rayuwar bil’adama duk suna hannunSa ne.
Tauhidi yana nufin yin imani da cewa wannan tsari mai ban mamaki (na duniya) da dokokin da suke gudanar da duniya da duniyar halitta, kama daga taurari daban-daban da suke sama zuwa rana har zuwa ga kananan ‘ya’yan halitta da suke jikin mutum da sauran jikkuna – wadanda ana iya kirkiro dubban tsare-tsare daga cikinsu – dukkaninsu gini da kuma aiki ne na tunani da kuma karfi guda sannan kuma ba haka kawai suka samar da kansa ba. Wannan imani wani lamari ne da duk wata lafiyayyiyar kwakwalwa sannan kuma duk wani mutum mai hankali da tunani wanda kuma ya yi nisa da halin na yarinta cikin tunani ko kuma wanda yake nuna rashin karfin gwuiwa cikin matakan da yake dauka ko kuma riga malam masallaci cikin lamurra zai amince da shi. Irin wannan tunani da karfi mai girma maras karshe wanda kuma ba za a iya siffanta shi ba da ya samar da irin wadannan abubuwa masu ban mamaki da kuma wahalar fahimta, ba kamar gunki kaza ba ne da mutum ya sassaka, ko kuma wani mutum mai iyaka da yake da’awar ubangijintaka ko kuma wata alama da aka kirkira; face dai zatinsa ne wanda shi kadai ne kuma mai karfin da ba ya gushewa wanda addinai suke kiransa da sunan ‘Allah’ sannan kuma suke fahimtarsa da alamunsa. A saboda haka tabbatar da wannan karfi da irada da irin tsarin da ke tattare da wannan yanayi mai ban mamaki; haka nan tabbatar da cewa shi wannan mai tsarin da ba shi da tamka wanda kuma ba za a iya siffanta shi ba, shi din nan ba kamar dukkanin kaskantattun abubuwan da mutane suke kerawa ba; face dai “Shi ne Allah, Wanda babu wani abin bautawa face shi, Mai mulki, Mai tsarki, Aminci, Mai amintarwa, Mai tsarewa, Mabuwayi, Mai tilastawa, Mai kamun kai. Tsarki ya tabbata a gare Shi daga abin da suke yi na shirkda da shi”.
Tauhidi yana nufin ‘yantar da mutum daga bauta da kuma mika wuya a gaban duk wani abu ko kuma wani mutum wanda ba Allah ba; wato katse duk wata sarka ta mulkin mallaka na bil’adama; wato kawar da tsoron masu karfi na shaidan da kuma na duniya; wato dogaro da irin karfi maras iyaka da Allah Madaukakin Sarki ya ba wa dan’adam sannan kuma ya bukace shi da ya yi amfani da shi a matsayin wata farilla wacce ba a saba mata; wato yarda da alkawarin Allah cikin nasarar da raunana za su samu a kan azzalumai da masu girman kai da sharadin tsayuwa da gwagwarmaya da kuma tsayin daka; wato mika zuciya ga rahamar Ubangiji da kuma yin watsi da yiyuwar shan kashi; wato amincewa da irin wahalhalu da hatsarin da ke kan tafarkin tabbatar da alkawarin Allah, wanda ya ke barazana ga dan’adam; wato sanya wahalhalun da ke kan wannan tafarki ga hisabin Ubangiji da kuma samun fatan cikin nasara ta Ubangiji wacce babu kokwanto cikin hakan; wato sanya ido kan manufa ta koli – wadda ita ce ‘yantar da al’umma daga duk wani nau'i na zalunci da nuna wariya da jahilci da shirka – a lokacin da ake gwagwarmaya; kullawa da kuma sauya irin gazawa ta daidaiku da kuma wacce ake fuskanta a kan tafarkin da ake kai. A takaice (tauhidi) yana nufin damfara kai da irin karfi na Ubangiji maras karshe da kuma kama hanyar isa ga manufa mafi girma tare da gagarumar fata. Dukkanin daukaka da girma da aka yi alkawari ga musulmi (bil’adama), duk suna karkashin inuwar irin wannan imani da gagarumar fahimta ce ta tauhidi. Ba tare da wannan gagarumar fahimta kuma ingantacciya ba da kuma gagarumar riko na akida da aiki da tauhidi ba, to babu wani guda daga cikin alkawurran Ubangiji ga musulmi (bil’adama) da zai tabbata.
Dalilin Samuwar UbangijiDaya daga cikin tushen sanin kai, wato karin sanin Allah shi ne cewa mutum ya fahimci kansa da kuma irin raunin da yake da shi da kuma tsayawa kyam wajen fuskantar abubuwa da zuciyarsa take so. Akwai wani abu cikin zuciyar mutum wanda shi kansa dalili ne na samuwar Allah. Mene ne wannan abin? Irin wannan shu’uri na neman Ubangiji, kaunar Allah, jan hankali na Ubangiji, dukkanin wadannan abubuwa suna cikin zukatan kowa, sai dai kawai shi mutum da ya gafala ne ba ya saninsu.
Abin da ya ke sanya mutum ya ke neman alakoki, kauna da kuma abubuwan janyo hankula, to tushen irin wannan kokari da kuma irin wannan shu’uri na zuciyar, shi ne irin wannan abin da ke janyo hankali na Ubangiji. To sai dai mutumin da ke cikin duhu da gafala, ba shi da irin wannan nasara da daukaka ta zuciya, bai fahimci hakan ba.
Matsayin Hankali Cikin Sanin AllahTauhidi ba shi ne kawai mu dinga cewa Allah yana nan ba, shi din ma Shi kadai ba su biyu ba. Wannan hoto ne na tauhidi. Badinin tauhidi, wani kogi ne wanda waliyan Allah suka yi nitso a cikinsa. Tauhidi wani kogi ne mai girman gaske; amma a cikin wannan kogi mai girman, muminai da musulmi da masu kadaita Allah suna ci gaba da tafiya bisa tafarkin tunani da amfani da hankali. Ko shakka babu hankali ko kuma tunani yana iya ciyar da mutum gaba. Ko da yake a matakai daban-daban, hankali yana samun abinci ne daga hasken wahayi da haske masaniyar (Ubangiji) da kuma koyarwar waliyan Allah; to sai dai abin da ke samun ci gaba shi ne hankali. Babu inda za a iya tafiya idan ba tare da hankali ba.
Tushe Na Asasi Na MusulunciDukkanin wata wahala da bala’in da ke fuskantar musulmi da al’ummar musulmi sun samo asali ne sakamakon rasa tushen rayuwa karkashin inuwar tauhidi. Tauhidi ba wai kawai wani lamari ne na kwakwalwa ba; tauhidi wani lamari ne na hakika da wani tsari na rayuwa. Tauhidi yana gaya wa musulmi yadda zai yi mu’amala da aboki da kuma makiyi, ya ya za mu yi da tsarin zamantakewa sannan kuma ya ya za mu rayu. Wasu suna zaton cewa imani da tauhidi, lamari ne da ya shafi rayuwa bayan mutuwa; alhali kuwa imani da tauhidi, lamari ne da ke gina wannan duniyar da kuma wannan rayuwar. Gwargwadon yadda mutane suka kama hanyar tauhidi da bautar Allah, to kuwa gwargwadon yadda sharrin dawagitai za su ragu musu. Bautan Allah da bautan wanin Allah lamurra ne da ba sa haduwa da junansu.
Tauhidi A Mahangar Musulunci A DuniyanceKowane addini yana da irin mahangarsa da irin fahimtarsa dangane da duniya, irin wannan mahanga da kallo da ya kebanta da shi da kuma yadda yake kallon duniya ana kiransa da mahanga ta duniya.
To tauhidi ma yana daga cikin mahangar Musulunci ta duniya, haka nan kuma yana daga cikin akida mai gina rayuwa a Musulunci; tauhidi tamkar ruhi ne da ke cikin kwarangwal din dukkanin dokokin Musulunci. Tamkar iska ce mai dadi da take cikin dukkanin bangarori na wannan ginin wanda sunansa Musulunci. Tamkar tsarkakakken jini ne da ke cikin dukkanin wannan jikin wanda sunansa Musulunci da kuma addini ne; akwai shi cikin dukkanin komai, babu wani hukumci a cikin Musulunci da za ka iya samu da ba za ka ga wata alama ta tauhidi a cikinsa ba.
Musulunci ya yi amana da cewa dukkanin wadannan abubuwa wadanda ake kira duniya, tun daga sama har zuwa kasa, kama daga manya abubuwa zuwa ga kananansu, kama daga mafi girman halittu masu rai da wadanda ba su da rai, har zuwa ga mafi daukaka da kuma karfin halittu masu rai sannan kuma mai hankali – wato mutum – dukkanin wadannan, ko ina cikin duniyar nan, dukkanin komai sun dogara ne da wani karfi mai girman gaske. Akwai wani abu wanda ya ke gefen wannan zahiri da mutum yake gani, wanda ke bayan abin da tabarau zai iya gani, wanda ya ke bayan dukkanin abubuwan da za a iya ji da kuma tabawa, akwai wata hakika a bayan dukkanin wadannan abubuwa wacce ta fi dukkanin hakika da kuma dukkanin wadannan abubuwa, dukkanin wadannan abubuwa suna hannun karfinsa ne. Wannan karfi madaukaki an ba shi suna, wanda shi ne ‘Allah’. A saboda haka duniya wata hakika ce wacce ita da kanta ba ta cin gashin kanta; ba ita da kanta ce ta samar da kanta ba; ba ita ta samar da kanta daga cikinta ba, face dai wannan karfin ne ya samar da wadannan abubuwa daban-daban – wanda a duk lokacin da ilimi ya samu ci gaba shi da kansa yake bayyanar da kansa – da kuma halitto su. Ba daga wani ya samo rayuwarsa ba, ba daga wani ya samo iliminsa ba. Shi din nan shi ne wanda dukkanin duniyar nan take hannunsa. Ya ya abubuwan da suka hadu suka yi duniya suke a gabansa? Shin abubuwan da suka hadu suka yi duniya, shi kenan daga lokacin da ya samar da ita sun zama tamkar yaron da uwarsa ta haife shi, sun rabu da shi kenan? A’a, ko da wasa; a kowane lokaci suna bukatarsa saboda tabbatuwa da ci gaba da wanzuwa, suna bukatar karfi da kudurarsa; kowa bawansa ne, dukkanin halittu bayi kuma halittarsa ne; yana iya juya komai, ya halicci kowa da irin tsarinsa, ya samar da kowa ne da irin sunna da tsarinsa; a halin yanzu ilimi yana ci gaba da gano wadannan abubuwa.
A mahanga ta Musulunci, tauhidi yana nufin duniya wacce take da mahalicci guda, a wata jumlar kuma wacce take da wani ruhi mai tsarki da kuma taushi. Duniya tana da wani Mahalicci wanda dukkanin bangarori na wannan duniyar ana kirga su a matsayin bayi da kuma halittu na wannan Ubangijin wanda kuma shi ne ya samar da su.
Matsayin Halittu A Mahanga Ta Tauhidin MusulunciMahangar tauhidi na Musulunci tana fadin cewa ne dukkanin halittu sun samo asali ne daga wani karfi guda, daga wata mabubbuga sannan kuma daga wani karfi guda. Kowa da kowa a gabansa bayi ne, kowa a gabansa ba shi da wani karfi, wajibi ne kowa ya mika wuya ga umurninsa, babu wani da yake da hakki tilasta karfinsa a kan wani, kamar yadda kuma babu wani da yake da hakkin tilasta wa wani abin da yake so
Kamar yadda mutum ba shi da hakkin tilasta ikonsa a kan wani, haka nan kuma ba shi hakkin mika kansa ga waniSaboda dukkanin bangarorin biyu (wato wanda ya tilasta wa wani ikonsa da kuma wanda ya yarda da ikon wanin) sun yi abin da ya saba wa hakika. Mutumin da ya hau kan doki ya zauna, sannan kuma ya sanya bayi suna binsa, ba shi da wani bambanci da wadannan bayin.
Halitta A Mahangar TauhidiA lokacin da mutum ya zama musulmi, dukkan komai a wajensa wani share fage sannan kuma hanya ce a gare shi. Hanya a gare shi ta isa ga wata duniya mai fadin gaske, ba wai duniya bayan mutuwa ba, duniya ta tunani da mahanga ta shi kansa mutum din wadda take da fadin gaske. Dukkanin komai a wajen mutum wata hanya da kayan aiki ne, don mutum ya sami damar samun yardar Allah. Rayuwar duniya, dukiya ta duniya, kwanciyar hankali na duniya, da kuma so da kauna ta duniya ba su da wata kima da girma a wajen shi. Wadannan abubuwa za su zamanto masu kima da girma a gare shi ne a lokacin da suka zamanto a tafarkin Allah ne. Amma idan har wannan kauna, wannan dukiya, wannan matsayi, wannan rayuwar, wannan da, wannan mutumci suka kasance ba a tafarkin Allah da kuma tafarkin sauke nauyin da ke kai ba, to kuwa ba su da wata kima a wajensa.
Mutum A Mahangar Duniya Ta MusulunciMutum a mahanga ta duniya ta Musulunci wata halitta ce wacce a tattare da ita akwai kwarewa da dama da ba a yi amfani da su ba. Wannan mutum din zai iya samun ci gaba a fagagen ilimi da masaniya da gano alamu da gaskiya ta halittu. A bisa tafarkin ababen da suke karfafa ruhi yana iya samun ci gaba maras iyaka, yana iya zama sama da mala’iku, sannan kuma yana iya samun damar isa ga dukkanin nau’oi na karfi da kai wa koluluwa ta karfi. Idan har ya bauta wa Allah, ya yi biyayya ga Allah, to kuwa wannan hanyar za ta kasance a bude a gare shi. Idan kuwa ya bauta wa wanin Allah, to kuwa za a daure masa fuka-fukansa ta yadda ba zai iya tashi ba. A dukkanin bangarori na ilimi, tauhidi yana bisa kololuwar tafarkin mutum sannan kuma mutum zai fahimci Allah. Musulman farkon Musulunci duk kuwa da irin jahilcin da yake iko a duniya a wancan lokacin, da kuma irin shirkar da take iko da duniya, amma duk da haka suka sami yin imani da tauhidi sannan kuma cikin ‘yanci suka sami hanyoyin nasara kuma aka bude musu hanyoyi na ilimi da masaniya, sannan kuma dukkanin bil’adama suka biyo bayana suka shiga cikin tafkin ilimi
wanda a yau duniya da dukkanin bil’adama sun sami ilimin da suke da shi ne sakamakon Musulunci da kuma tauhidi na Musulunci wanda shi ne a karon farko ya sanya kafafunsa cikin tafkin ilimi.Sirrin Ci Gaba Da Wanzuwar Tunanin TauhidiTsawon tarihin bil’adama yunkurin tabbatar da hukuma ta Ubangiji da kadaita (tauhidi) Allah sun fuskanci adawa da yawan gaske. Ya ya aka yi annabawan (Allah) suka sami nasara a kan makiyansu tsawon tarihi? Ta ya ya aka yi Bani Isra’ila suka sami iko a duniya bayan dukkanin irin wannan matsin lamba a kan annabi Musa da Shu’aib da Yusha’u da Haruna. Me ya faru annabin Musulunci - wanda a wancan lokacin shi kadai ne, sannan kuma dukkanin duniyar jahiliyya suna adawa da shi – amma ya sami damar zuwa Madina da kuma kafa hukuma a can sannan kuma ya janyo dukkanin duniya zuwa ga wannan tafarki na tauhidi da kuma haifar da wani sabon yunkuri a duniya? Sannan kuma ya ya aka yi juyin juya halin Musulunci na Iran, wanda kasashen gabashi da yammaci suke adawa da shi sannan kuma ba shi da wata kasa mai ba shi kariya a duniya face dai kawai al’ummomi, yayi nasara. Sirrin ci gaba da wanzuwar koyarwa ta tauhidi tsawon tarihi da kuma sirrin nasarar juyin juya halin Musulunci a Iran yana cikin wani batu guda ne shi ne kuwa cewa
akwai wadansu mutane a cikin bayin Allah da suke shirye su sadaukar da rayukansu don (koyarwar tauhidin ko kuma juyin) ya cimma madaukakiyar manufar da yake da ita. Neman shahada; idan har a ce babu son yin shahada (cikin zukata), haka nan kuma idan har da a ce babu rayukan da masu shi za su sadaukar da su ga tafarki mai girma; to da juyin juya halin Musulunci bai yi nasara ba haka nan kuma da Manzon Allah (s.a.w.a) bai yi nasara ba, sannan kuma da tauhidi bai samu irin nasarar da ya samu ba. Abin da ya sanya Allah Madaukakin Sarki ya sanya irin wannan yanayi ga dukkanin annabawan Allah da kuma addinai na Ubangiji: wato
“Hakika Allah ya saya daga muminai rayukansu da dukiyoyinsu, da cewa suna da Aljanna”To wannan ruhi na neman shahada a cikin al’ummomi shi ne ya ke sanya su samun nasara.
Fasali Na Biyu: Masu Inkarin Bautan Allah Shi KadaiKaramar Kofar Lalacewar Bil’adamaMafi girman zunubin da wani mutum ko kuma wata al’umma za ta iya fuskanta shi ne zunubin shirka wanda Allah Madaukakin Sarki Ya na gafarta wa dukkanin zunubai, to amma ba ya gafarta shirka.
“Lalle ne, Allah ba Ya gafarta a yi shirki game da shi, kuma Yana gafarta abin da yake bayan wannan ga wanda Yake so”(Suratun Nisa’ 4:48) to amma shirka duk da irin wannan girma da haibar da take da ita, tana daga cikin zunuban da masu aikata su suna da yawan gaske a duniya; hakan kuwa saboda sabanin da dama daga cikin sauran zunubai ba kowa ne ya fahimci hakikaninta ba. A saboda haka ne a cikin ruwaya aka raba shirka (gida biyu) bayyananniya da kuma boyayyiyar shirka. A saboda haka a wani lokaci a kan sami shirka cikin al’ummar jahiliyya, a wani lokaci kuma cikin al’ummar musulmi.
Shirka Cikin Al’ummar JahiliyyaA cikin al’ummar jahiliyya dukkanin komai shirka ne, dukkanin yunkurin al’umma, yunkuri ne da ke cike da shirka don kuwa mutanen da suke jagorantar al’ummar jahiliya wacce ba ta Musulunci ba, wasu mutane ne wadanda suke jan al’umma da shiryar da yunkurinsu zuwa ga wanin Allah. A saboda haka ne su kansu da kuma dukkanin mutanen da suke binsu suna tafiya ne bisa tafarkin fadawa wutar halaka.
A lokacin da aka gabatar da batun alaka da Allah da karfi mai girma da ke mulkan duniya cikin wata al’umma da take cike da shirka, a dabi’ance a irin wannan al’umma mutane za su rarrabu; wannan da wani ubangijin, dayan kuma da wani ubangijin na daban, shi ma na ukun da wani ubangijin na daban. Al’ummar da ta ginu bisa asasin shirka, a cikin kabilu daban-daban, hakan wata katanga ce wacce ba za a iya kutsawa cikinta ba sannan kuma akwai wani yanayi na rarrabuwa da ba za a iya hada shi ba.
Shirka A Cikin Al’ummar MusulmiA cikin al’umma ta Musulunci, duk da cewa halifofin Ubangiji ne ke jagorantar al’umma, amma duk da haka a kan samu shirka a cikinta. Misalin farko na shirka cikin al’ummar musulmi da kuma al’umma da take son ta zamanto ta Musulunci shi ne cewa jami’an da suke gudanar da wannan al’umma, saboda wasu dalilai ko kuma saboda rashin kula ko kuma saboda mummunan zato ga makoma ko kuma ga Musulunci da kuma musulmi, a shirye suke su kafa dokokin da ba na Ubangiji ba da kuma aiwatar da su. Hakan ya kan zama shirka, shirka kuma mai girma. A duk lokacin da aka sami wata al’umma wacce da sunan Musulunci sannan kuma wacce ta kumshi al’ummar musulmi, amma sai aka sami jagororinta mutane ne wadanda a shirye suke su yi watsi da hukumce-hukumce na Ubangiji saboda maslaharsu“Suna sayen tamani kadan da ayoyin Allah"wannan shirka ce cikin al’umma. Wannan al’umma duk kuwa da cewa al’umma ce da ta kumshi musulmi, to amma a bisa hakika wata shirka abar kyama ce take iko a cikin wannan al’umma
Wajibcin Fahimtar Ma’anar ShirkaImam Sajjad, amincin Allah ya tabata a gare shi, yana cewa: “Hakika Bani Umayya sun bude hanyar koyon imani ga mutane amma sun rufe kofar fahimtar shirka. Saboda idan har suka ja mutane zuwa ga shirka, mutane ba za su fahimta ba, saboba ba su san shirka din ba. Bani Umayya sun bar malamai da ma’abota addini cikinsu kuwa har da Imamai, amincin Allah ya tabbata a gare su, su yi magana dangane da salla, dangane da hajji, dangane da zakka, dangane da azumi haka nan kuma dangane da ibadu, su ci gaba da bayanin hukumce-hukumcen Ubangiji kan wadannan lamurra. Sun kasance suna barin kofa a bude a yi wa mutane bayani kan tauhidi da kuma annabci, to sai dai ba sa barin kofar karin haske kan ma’anar shirka da kuma misalan shirka din a bude don kada jama’a su fahimci wani abu. Saboda idan har aka sanar da mutane wani abu dangane da wadannan abubuwa, to cikin sauki za su fahimci cewa su din nan mushirikai ne sannan kuma za su fahimci cewa abubuwan da Bani Umayyan suke kiransu zuwa gare su, shirka ce. Cikin gaggawa za su fahimci cewa halifofin Bani Umayya dawagitai ne masu yin karen tsaye wa Allah, sannan kuma idan har wani ya yi musu biyayya, to alal hakika ya yi shirka. A saboda hakan ne ba sa barin mutane su sami ilimi dangane da shirka
Abubuwan Da Suke Sanya Mutum ShirkaAllamah Majlisi (r.a) yana fadi a cikin mujalladi na arba’in da takwas na littafin Bihar cewa: “Hakika ayoyin shirka, zahirinsu yana cikin gumaka ne sannan kuma badininsu yana cikin azzaluman halifofi, wadanda suka yi shirka tare da imaman gaskiya, suka hau matsayinsu” wato ayoyin shirka da suke cikin Alkur’ani zahirinsu yana cikin babin gumaka ne, wato wadannan gumaka masu nauyin tsiya da aka sassaka su daga itace, to amma badinsu da kuma tawilinsu yana cikin babin azzaluman halifofi ne, mutanen da cikin zalunci suke kiran kansu da sunan halifofi sannan kuma suke iko a kan duniyar musulmi, wato wadannan azzaluman halifofi sun kwatanta kansu da Imaman gaskiya wajen da’awar hukumar Musulunci da kuma iko a kan al’ummar musulmi. Shi kansa daidaita kai da wadannan halifofi na gaskiya, shirka ce da Allah, don kuwa wadannan imamai na gaskiya wakilan Allah ne sannan kuma suna magana ne da yawun Ubangiji, daga wajen Allah suke, to saboda sun sanya kansu a matsayinsu sannan kuma suka zamanto abokan hanayyarsu wajen da’awar Imamanci. A saboda haka sun kasance gumaka kuma dagutu, sannan kuma duk wani wanda ya yi musu biyayya, to kuwa ya zama mushiriki.
Da’awar Samun Da Ga Ubangiji Da Kore HakanAbin da Alkur’ani mai girma ya ke koyar da mutane a matsayin akida abu ne wanda yake da bakin magana cikin lamunce manufofi na Ubangiji. Abin da kuma yake kore mummunar akida shi ne abin da a mahangarsa yake tabbatar da bacin al’umma. Inkarin wata gurbatacciyar akida yana nufin kawar da lalataccen jijiyar jini a cikin al’ummar bil’adama ne. Aya ta 87 ta cikin Suratu Maryam tana fadin cewa:
“Kuma suka ce, “Mai rahama yana da da” kiristoci, yahudawa, mushirikan kuraishawa da mushirikan jazirar larabawa da mushirikan sauran wajaje suna cewa Allah yana da da. Wasu suna cewa Allah yana da diya (mace), wasu suna cewa yana da da namiji, wasu kuma suka ce yana da da da kuma diya, wasu suka ce yana da guda, wasu suka ce yana da su ba iyaka, shi mai iyali ne; wannan da’awa da ma’anar cewa a cikin halittun duniya akwai wani wanda alakarsa da Allah ba alaka ce ta bawa ba; alaka ce da uba da da. ‘Ya’yansa ne ba wai bayinsa ba, duk kuwa da cewa ba haka lamarin yake ba. Yahudawa suna cewa Uzair dan Allah ne, wato annabi Uzairu dan Allah ne, suna so ne su ce idan har dukkanin halittun duniya dukkanin bayin Allah ne, to amma shi Uzairu kan ba shi cikin hakan; shi kan ba bawan Allah ba ne, shi dan Allah ne, sanyin idon Allah ne. Su ma kiristoci haka su ke fadi dangane da Annabi Isa. Kafirai ma haka suke fadi dangane da Lata da Manata da Uzza, suna cewa su ‘ya’yan Allah mata ne; mushirikan Girka da Roma wadanda suke cewa Allah yana da ‘ya’ya, dukkaninsu haka mahangarsu take. Wato alal hakika wadannan layuka guda biyu da suka rika, daya layi ne na Allah, dayan kuwa layi ne na dukkanin bayin Allah da halittu – wadanda dukkaninsu sun mika wuya a gaban Allah – to amma su kan mai da wadannan layuka guda biyu zuwa uku, suna cewa Allah, bayin Allah da kuma ‘ya’yan Allah. Imani da cewa akwai wani mai hadawa tsakanin Allah da bil’ada a cikin al’umma lamari ne da ke da lalata a cikinsa.
Hakan alal hakika wani abu ne kawai da suke fakeewa da shi wajen sanya bayin (Allah) maimakon su zamanto bayin Allah, sai su zamanto bayin wani na daban.Dalilin Da Ya Sanya Masu Akidar Abin Duniya Suke Inkarin TauhidiMutumin da ya yi imani da Allah yana cewa ne abin da ke bayan abin da mutum yake gani hakika ce sannan kuma ya fi abin da yake gani a zahiri girma. Idan har babu hakan to kuwa da wadannan abubuwa ba su faru ba. Shi kuwa mai akidar abin duniya cewa ya ke yi a’a, mu dai ba za mu yi imani da duk wani abin da ba ma ganinsa ba. Mu dai dukkanin binciken da muka gudanar a dakunan bincike ba mu ga wata alama ta abin da wadanda suka yi imani da kadaitakar Ubangiji suke fadi ba. Masu akidar abin duniya sun yi imani da cewa duk wani abin da ya ke bayan wannan duniyar babu hakika ko samuwa cikinsa. Saboda ba su yi imani da akida ta Ubangiji ba, shi ya sa suke fadin hakan. Saboda shi ya yi imani da cewa babu yadda za a iya tabbatar da irin wannan gini na duniya da gudanar da rayuwar bil’adama da tabbatar da adalci da kawar da nuna bambanci in ba karkashin inuwar tunani na abin duniya ba, saboda haka ne suke adawa da akidar imani da Allah.
Idan har kamar yadda yake a cikin tunanin wadancan mutane da suka yi imani da wasu akidu ko kuma saboda ba su da wani dalili mai karfi na tunani kan samuwar Ubangiji don haka suke inkarin Ubangiji ko kuma ba su yi imani da shi ba; a mafi yawan lokuta ma kafa hujja na tunani ba yana hannun daya bangaren lamarin ba ne
Wajen kore samuwar Ubangiji babu wani dalili, a yanzu ne ko kuma a baya. Babu wani wanda ya ke cewa saboda dalili kaza don haka babu Allah. Cikin dukkanin masu akidar abin duniya – tun daga ranar farko har zuwa yau din nan – babu wani mutum guda da yake cewa ni dai zan iya tabbatar da cewa babu Allah saboda dalilai kaza; duk wani wanda ya ke da wani abin fadi a wannan fagen to ya fadi ni dai bai tabbata min cewa akwai shi ba; ban fahimta ba, ni dai ban yarda da samuwar dalili ba. Alkur’ani mai girma ma yayi nuni da wannan hakika, inda ya ke cewa:
“kuma su ba kome suke yi ba face suna yin zato” (Suratul Bakara 2:78) su din nan ba abin da suke nema face zato, idan kuwa ba haka ba, ba za su iya inkarin Allah da dalili ba.
Dalilin Riko Da Akidar Abin DuniyaDalilin riko da abin da masu akidar abin duniya suka yi imani da shi, shi ne cewa mutumin da ya yi imani da abin duniya yana zaton cewa a yau wannan akida ta sa ita ce za ta gudanar da duniya yadda ya kamata. Suna cewa ita ce za ta iya kawar da zalunci, ita ce za ta iya kawar da nuna bambanci da wariya, sannan kuma ita ce za ta iya tumbuke tushen zalunci da babakere. Mutumin da ya yi imani da abin duniya yana cewa ne addini ba zai iya yin hakan ba. Mene ne dalilinsu na cewa addini ba zai iya yin hakan ba? Saboda ba su san komai ba dangane da koyarwa ta addini face dai abin da suke gani mutanen da suke kan tituna da kasuwa suna aikatawa; ba su da masaniya kan hakikanin koyarwa ta addini. Idan har aka tambaye shi cewa mene ne addini, zai kawo maka sunayen wasu mazhabobi ya ce wadannan su ne addini, tun da dai suna sanya mutum cikin maye, saboda wadannan sun yi daidai da zalunci da azzalumai, don sun gagara magance matsalolin da mutane suke fuskanta. A kan sami wani lokaci mutum ya kan sami kansa yana fuskantar irin wannan tunani, to mafi kyawun amsar da ta dace da wannan tambaya shi ne cewa na’am, idan har ka sami wani addini da ya ke tafiya kafada da kafada da azzalumi, yake aiki tare da mulkin kama karya, ba ya kasancewa tare da wanda aka zalunta, ya gagara magance matsalar mutane, bai taba amfanin duniya da lahirar al’umma ba, idan har ka sami irin wannan addini, to a inda ka same shi ka yi inkarinsa; kada ka taba amincewa da wannan addinin. Saboda idan har addini ya fito daga wajen Allah ne ba zai taba zama haka ba.
Ya Ya Ake Biyayya Ga Shaidan“Kuma lalle ne, shaidanu, hakika, suna yin ishara zuwa ga masoyansu domin su yi jayayya da ku” (Suratul An’am 6:121) shaidanu da cibiyoyin ashararanci suna yin ilhami ga masoyansu da abokansu don su dinga jayayya da ku. Shaidanu da masu yada fasadi da lalata a bayan kasa suna kwadaitar da ‘yan amshin shatansu da masoyansu da wadanda suka mika musu wuya don su zo wajenku su yi bahasi da ku, su dinga jayayya da ku. To wani nauyi ne ya hau kanku dangane da wadannan abokan shaidan din?
“Kuma idan kuka yi musu da’a, lalle ne ku, hakika, masu shirka ne” (Suratul An’am 6:121), wato idan har kuka yi musu biyayya, kuka bi su, to kun zama mushirikai. Biyayya ga shaidan yana nufin tushen ashararanci ko kuma biyayya ga abokan shaidan yana nufin ‘yan amshin shatansu, kayan aikinsu, abokansu, wadanda suke tare da su a sansani guda, sannan kuma yaransu. Yin biyayya a gare su yana sanya mutum ya zamanto mushiriki
“Kuma idan kuka yi musu da’a”,wato idan kuka yi musu biyayya,
“lalle ne ku, hakika, masu shirka ne”,lalle kun zama mushirika.
Shin Allah Madaukakin Sarki Yafi Son Wasu Mutane?“Kuma Yahudu da Nasara sun ce: “Mu ne diyan Allah, kuma masoyanSa” (Suratul Ma’ida 5:18), wato yahudawa suka ce mu din nan ‘ya’yan Allah ne kuma masoyansa, daga baya kuma a lokacin da Allah Madaukakin Sarki ya ke ba su amsa dangane da daya daga cikin munanan ayyukansu sai ya amsa musu. Wato ya amsa musu sannan kuma ya mayar musu da martani yana cewa:
“to don me kuke kashe annabawan Allah gabannin wannan, idan kun kasance masu bayar da gaskiya"(Suratul Bakara 2:91), wato idan har da gaske ne kuna da irin wannan abokantaka da kusaci da Allah, to me ya sa kuke kashe masa annabawansa? Me ya sa kuke kashe masa zababbun bayinsa? Yahudawa suna cewa mu din nan ‘ya’yan Allah ne don haka muna da wani fifiko. To Musulunci dai cewa ya ke yi lalle wannan magana kuskure ne. A wani wajen kuma yana cewa:
“Ka ce, “Ya ku wadanda suka tuba (yahudu) idan kun riya cewa lalle ku ne zababbun Allah ba sauran mutane ba, sai ku yi gurin mutuwa idan kun kasance masu gaskiya” (Suratul Juma’a 62:6), wato idan har abin da kuke fadi na cewa ku din kuna da wata alaka ta abokantaka da kauna tsakaninku da Allah gaskiya ne, to ku yi kwadayin mutuwa ma don ku bar wannan rayuwa ta duniya da take cike da damuwa, don ku koma wajen Allah wanda yake kaunarku sannan kuma kuke da alaka da shi. Daga nan kuma sai ya c
“Kuma ba za su yi gurinta ba har abada "(Suratul Juma’a 62:6), lalle ba abu ne mai yiyuwa ba wadannan mutane su yi gurin mutuwa. Bayahude din ne zai yi maka gurin mutuwan?!
Fasali Na Uku: Tasirin Mahangar Tauhidi Dangane Da DuniyaAlamun IbadaA wani lokaci a kan sami wani mutum yana ibada ta yadda shi da kansa yana ganin kansa a matsayin wani mutum mai tsarki wanda yake da wani karfi da ya saba irin wanda aka san shi. Tamkar irin gumaka ko kuma tsarkakan limaman da shekara da shekaru ake bauta musu. Bautawa abubuwan da tun da farko suke da tsarki da girma da irin wannan yanayi na tsarkin ruhi, a matsayin misali kiristoci wadanda sakamakon irin girmama Annabi Isa al-Masihu, amincin Allah ya tabbata a gare shi, ko kuma ga mahaifiyarsa mai tsarki Maryam, amincin Allah ya tabbata a gare ta, da suke yi su kan rusuna wa gumakan Al-Masihun ko kuma Maryam da aka yi, suna kuka da kuma bauta musu. Ibada ba wai kawai ita ce mutum ya dinga rusuna da kuma yin sujada da ruku’u da neman taimako a gaban wani abu da yake ganinsa a matsayin mai tsarki ba; akwai wani aikin kuma na daban wanda shi ma za a iya kiransa da sunan ibada sannan kuma ana iya kiransa da ma’ana ta biyun. Mece ce ma’ana ta biyu ta ibada? Ma’ana ta biyu ta ibada wacce kuma ake samunta cikin kamus na farisanci sannan kuma ta kasance tana yawo a bakunan mutane ita ce biyayya.
Biyayya ga kowane mutum a yanayi na shi kadai ba tare da wani kaidi ko sharadi ba, ibada ce a gare shi.Bisa al’ada ta Alkur’ani bauta wa wata halitta wacce ba Allah ba – shin wannan halitta wani karfi ne na siyasa ko na mazhaba ko wani abin da ke tattare da mutum irin su zuciyarsa, ko kuma wani abin da ke wajen samuwar mutum din ko kuma wani mutum ne da ake girmama shi saboda lamari na siyasa ko adddini – yana nufin yi musu da’a. Duk wani wanda ya yi da’a wa wani ko kuma wani abu na daban, to kuwa ya yi masa ibada ne.
Bautar Allah Da Bautar ShaidanImam Jawad (a.s.) yana cewa: “Duk wanda ya saurari mai magana, to ya bauta masa”, da’irar ibada tana da fadin gaske, ba wai kawai yin biyayya ba ne face dai hatta mika daya daga cikin ababen da mutum yake ji da su ga wani mutum yana a matsayin yi masa ibada. Shin mutum ba zai iya sauraren maganganun gaskiya ba kenan? A saboda haka wannan hadisi ya ci gaba da cewa: “Idan har mai maganar yana magana ne a madadin Allah, lalle ya bauta wa Allah”, wato idan wanda ya ke magana da kuma janyo zukatan mutane zuwa gare shi yana magana ne da harshen Ubangiji, mutane suka mika masa zukatansu, suka ba shi tunaninsu, lalle sun bauta wa Allah ne. (Hadisin ya ci gaba da cewa) “Idan mai maganar yana magana ne da harshen Ibilis, to ya bauta wa Ibilis”, amma idan har wannan mai maganar yana magana ne da harshe na Shaidan, yana magana ne da yawun Iblis, ya zamanto yana bahasi ne sabanin abin da ya yi daidai da hankali da tunani na Ubangiji da kuma magana kan hakan, sannan kuma mutane suka kasance suna saurarensa, a cikin wannan yanayi ya kasance ya shagaltu da ibada da yin da’a wa Ibilis, wato shi din nan kansa Shaidan ne. Shi kansa wanda ya ke irin wannan magana Shaidan ne ba wai wakilin Shaidan ko kuma kakakin Shaidan ba; a ma’ana ta Alkur’ani haka Shaidan yake.
Al’umma Ta TauhidiA lokacin da tauhidi ya shigo cikin wata al’umma dukkanin bayi za su zamanto a bangare guda. A cikin al’umma ta tauhidi, wacce a lokacin da Ubangijin halitta, Rayayye tsayayye mai karfi wanda dukkanin wani yunkuri da abubuwan da suke duniya sun ta’allaka da shi ya zamanto mai juya lamurra, to mutane – shin bakaken fata ne ko farare ko kuma wadanda suke da kabilu daban daban da kuma mabambantan yanayi na zamantakewa – za su zamanto tare da juna; don kuwa sun kasance suna da alaka da Ubangiji ne, sun kasance sun riki wani waje ne sannan kuma suna samun taimako ne daga wani waje guda. Hakan shi ne sakamako na tabbas na tauhidi. A irin wannan mahangar, ba wai kawai bil’adama suna da alaka da junansu ba ne, face dai ta hanyar mahanga ta tauhidi, abubuwa da bangarori na duniya da dabbobi, abubuwa marasa rai, sama da kasa da dukkanin abubuwa, dukkaninsu suna da alaka da junansu sannan kuma dukkaninsu suna da alaka da mutum. A saboda haka, dukkanin abin da mutum yake gani sannan kuma yake jinsa a jiki da kuma fahimtarsa, wani fage da wata duniya da kuma wani gungun jama’a ne da suke rayuwa a wata duniya lafiyayyiya da kuma wani fage da ke cikin aminci.
Alamu Na Al’ummar MusulunciAbin nufi da al’ummar Musulunci shi ne irin wannan al’umma wacce a cikinta bautar Allah take iko a kan dukkanin wadanda suke cikin wannan al’umma, ko kuma dukkanin abubuwan da ke gudana da kuma hanyoyin da ake bi a cikin wannan al’umma suna daidai ne da umurnin Ubangiji da kuma yadda yake so. Ana iya ganin alamun bautan da wata al’umma take yi wa Allah cikin wasu ‘yan abubuwa. Idan har aka sami wadannan abubuwa a cikin wata al’umma to kuwa wannan al’umma baiwar Allah ce, sannan kuma wannan tsari, tsari ne na Ubangiji:
shi ne cewa hukumce-hukumcen Ubangiji su zamanto su ne masu iko, mutane su zamanto masu aiki da dokokin Ubangiji ba wai dokokin da suke cike da son zuciyan wadansu mutane wadanda suka ginu bisa asasi na kuskure ba. Alkur’ani mai girma da hukumce-hukumcen Ubangiji su zamanto su ne suke tsara wadannan dokoki.
Na Farko bayin Allah su zamanto su ne suke iko da irin wannan al’umma ba wai masu hamayya da Allah ba. Kada dawagitai su zamanto su ne suke iko a kan wannan al’umma, wadanda suke kira zuwa ga kansu, wadanda suke ganin kansu a matsayin wadanda wajibi ne a yi musu ibada amma ban da Allah, mutanen da suka zama tamkar Fir’auna da Namarudu da sauran dawagitan da suka kasance tsawon tarihi wadanda suke son mutane su zamanto masu bauta musu sannan kuma kada zukatansu su zamanto sun san Allah, kada su zamanto su ne masu iko a kan al’umma, bayin Allah su zamanto su ne suke iko.
Na Biyu Na Ukushi ne cewa adalci ya zamanto shi ne yake a cikin wannan al’umma, a cikin al’ummar da zalunci ya zamanto shi n eke iko wannan ba al’umma ce ta Ubangiji ba.
Na Hudu shi ne cewa a cikin wannan al’umma ya zamana ana girmama mutane. A cikin wannan al’umma bil’adama abin girmamawa ne, ba a mai da mutum ya zamanto wani kayan aiki ba; a dinga ganin dan’adam a matsayin wata halitta ce wacce ita ce mai gudanar da duniya sannan kuma mafi daukakan halittun duniya, ba wai kawai a matsayin halittar da manufarta ita ce cika cikinta ba. Idan har kwakwalwarsa ba ta fahimta ba, shi kenan ba ta fahimta ba, idan har zuciyar ba ta son isa ga manufar da ake son isa gare ta ba, shi kenan. Mutum dai a cikin al’umma abin girmamawa ne, fadin da Allah Madaukakin Sarki yake yi na cewa
“Lalle mun karrama Bani Adama” ba wai wani fulako ne kawai ba, hakan wani asasi ne, wani tushe ne ga al’ummar musulmi. A duk inda ba a yi aiki da wannan asasi ba, to ba al’ummar Musulunci ba ce. A duk inda mutum ya zamanto kaskantacce, a duk inda mutum ya zamanto mai biyan bukatar zuciya da manyan masu karfi na duniya, a duk inda mutum ya zamanto ba shi da hakkin ya yi tunani, ya yi karatu da kuma zaban tafarkin da ya kamata ya rika – wato tafarkin Allah – to wannan waje ba al’ummar Musulunci ba ne.
Na Biyar shi ne cewa kada a sami bambanci da wariya cikin wannan al’umma, bai kamata launin fata, fari ko baki, ko balarabe ko ba’ajame ko kuma dan wannan kabila da wancan ko kuma dan wannan gida da wancan su zamanto abubuwa ne da za su zamanto masu bambance tsakanin mutane ba. Ya zamanto ana ganin mutum ne a matsayinsa na mutum, sannan kuma abin da ke bambance mutane ya zamanto shi ne tsoron Allah kamar yadda dukkanin wadannan abubuwa suka kasance a farkon Musulunci.
Na Shidashi ne cewa daga cikin alamu na al’umma ta Ubangiji kuma ta Musulunci shi ne jihadi saboda Allah. Al’ummar da babu jihadi a cikinta, babu kokari saboda Allah, to wannan al’umma ba za ta zamanto ta Musulunci ba.
Tasirin Tauhidi Cikin Gina Tushen Tattalin Arzikin Al’ummaA cikin al’umma ta tauhidi, wajibi ne kowa da kowa ya zamanto yana da dukkanin abubuwan da ake bukatarsu a cikin al’umma. Ba wai wajibi ne dukiyar da kowa ya ke da ita ta zamanto daya ba, babu yadda za a ce mutane su zamanto daidai cikin dukiyar da suke da ita ba. To sai dai wajibi ne a ba wa dukkanin mutane damar amfanuwa da damar da ake da ita a cikin al’ummar. Mai yiyuwa ne wani ya fi wani wayo, wani kuma ya zamanto malalaci. Idan har wani ya fi yin aiki, to kuwa zai fi samun kudi. To amma ba za a zo a dauki wani abu daga cikin wannan kudi nasa a ba wa wani na daban don kudadensu su zamanto daidai ba. Face dai abin so shi ne a ba wa dukkanin al’umma dama iri daya na yin karatu, koyon aiki da kuma yin aikin. A daidaita mutane wajen amfanuwa da damar da ake da ita.
Tasirin tauhidi cikin gina tattalin arzikin al’umma shi ne cewa wajibi ne a sami yanayi na daidaito tsakaninsu, ba wai su zamanto abu guda ba; face dai yanayi na daidaito. Irin wannan al’umma wacce Amirul Muminin (a.s) a farkon halifancinsa ya bayyana ta a matsayin dalilin da ya sanya shi amincewa da halifancin, inda ya ke cewa: “ba don alkawarin da Allah ya daukar wa malamai na kada su zuba ido da yin shiru a kan zaluncin azzalumi da kuma zaluncin da ake yi wa wadanda aka zalunta ba”, wato Allah Madaukakin Sarki ya dora wa malamai dam asana nauyin cewa kada su yi shiru dangane da zaluncin azzalumai da kuma zaluncin da ake yi wadanda aka zalunta ba. Lalle wajibi ne hakan ya zamanto shi ne asasi na tsarin tattalin arziki na Musulunci sannan kuma dukkanin batutuwan da suka shafi tattalin arziki na Musulunci su zamanto sun ginu bisa wannan asasi ne. Wannan yanayi na daidaito, ya samo asali ne daga imanin mutane da Allah. Idan har babu Allah, idan har wannan duniya ba ta da wani mai iko a kan mutane, idan har duk abin da mutane suka samu wani abu ta hanyar amfani da karfin da suke da shi sannan suka mayar da shi mallakansu, to kuwa yanayin al’ummar su zai zamanto wani abu ne na daban.
Mahangar tauhidi cikin lamuran da suka shafi dukiyar al’umma ta tauhidi wanda hakan daya ne daga cikin kudurin tauhidi kamar yadda Alkur’ani ya bayyana hakan
“kuma ku ba su wani abu daga dukiyar Allah wannan da Ya ba ku”(Suratun Nur 24:33), dukiyar da Allah ya ba ku, dukiyar Allah da ya ba wa masu abin hannu su ba da su a wajajen da ake bukatarsu. Dukkanin abin da suke da shi na Allah ne, mutane ba su wuce wadanda aka ba su ajiya ba.
“Dukiyar Allah da muka sanya ta ajiya a wajen mutane”; dukiyar da Allah ya ajiye ta amana a wajen mutane. Wannan shi ne asasi da kuma wajibi na mahangar tauhidi.
Tasirin Tauhidi Cikin Halayen Al’ummaKo shakka babu yanayin tunani da mu’amalar daidaikun mutanen da suke rayuwa cikin al’umma da tsari na tauhidi da ‘yan’uwansu da kuma dukkanin mutane, da kuma dabi’arsu da rayuwarsu ta daidaiku tana da wani irin yanayi wanda ya saba wa irin yanayin mutane da suke rayuwa cikin al’ummar da tsarin da ya ginu bisa abin duniya ne yake mulkanta. Su din nan (wadanda suke rayuwa karkashin tsari na tauhidi) suna rayuwa ne tare da Allah, suna bukata ne daga wajen Allah, suna kaunar Ubangiji, suna tsoron Allah, suna neman mafaka daga wajen Allah, su din nan suna ganin kansu ne a matsayin bayin Allah, suna nuna so da kauna da tausayawa ga bayin Allah, ba sa zaluntar bayin Allah, ba sa musu hassada, ba sa hadama, dukkanin kyawawan halayen da aka ambata cikin littafan kyawawan dabi’u sun samo asali ne daga imani da Allah da kuma kyawawan halaye na Musulunci, imani da Allah.
Tasirin Tunanin Tauhidi Cikin Al’ummar MusulmiCikin share fagen bahasin zamantakewa na Musulunci akwai wani lamari abin lura wanda kula da shi zai taimaka wa mutum cikin dukkanin bahasinsa na zamantakewa na Musulunci, wannan abu kuwa shi ne cewa wani irin tasiri ne tunani na Musulunci da akida ta Musulunci da tauhidi yake da shi wajen gina al’umma da tushen zamantakewa na al’umma na Musulunci; wato wadannan mutanen da suka yi imani da Allah, mene ne bambancinsu da wadanda ba su imani da Allah ba. Shin imani da Allah yana cikin cewa ne mutane su yi imani da Allah cikin zuciya da maganganunsu, su zamanto masu sanya Allah cikin dukkanin mu’amalarsu ta daidaiku irin su salla, zakka, fadin gaskiya, nesantar karya da sauran batutuwa na daidaiku, to amma babu wata matsala wajen su rayu cikin kowace irin al’umma ko kuma a’a. Wajibi ne imani da Allah ya tabbatar da kansa cikin dukkanin rayuwar al’umma. Ko shakka babu imani da Allah bai takaita kawai cikin kyautata zukata da kwakwalan mutane ba ne, face dai imani da Allah yana nufin gina duniyar da ta yi imani da hakan ne. Imani da tauhidi da imani da Allah suna da tasiri cikin tsarin hukumar al’umma wacce ta yi imani da kadaitakar Allah cikin tafarkin tattalin arziki wannan al’umma haka nan kuma cikin tafarkin kyawawan dabi’un daidaikun mutanen da suke cikin wannan al’ummar. A cikin al’ummar da ta yi imani da Allah, to wajibi ne hukuma ta zamanto mai riko da koyarwar addini. Wato wajibi ne addinin Musulunci da shari’ar Musulunci da hukumce-hukumce Musulunci su zamanto masu iko a kan rayuwar al’umma sannan kuma masu gudanar da wadannan hukumce-hukumce su zamanto mutane ne da suka dace wadanda suke da wadansu siffofi guda na asali. Na farkonsu shi ne cewa su dauki wadannan hukumce-hukumce, wadannan shari’a, wadannan ilmin fikihu na Musulunci sama da komai, su zamanto kuma sun san wadannan hukumce-hukumce na Ubangiji. Siffa ta biyu ita ce cewa wannan mutumin masanin Ubangiji da fikihu na Ubangiji ya zamanto yana da karfin da zai iya nesantar zunubi da kura-kurai da gangan da kuma kauce wa hanya, wato wadannan abubuwa da a urfi na al’adar Musulunci ake kiransa da adalci.
Tushen ‘Yanci Cikin Al’adar MusulunciTushen ‘yanci cikin al’adun Musulunci, shi ne mahangar duniya ta tauhidi. Tushen tauhidi da irin wadannan ma’ana da yake da shi yana tabbatar da ‘yancin da mutum yake da shi. Wato duk wanda ya yi imani da kadaitakar Ubangiji sannan kuma ya yi imani da tauhidi, to wajibi ne ya sanya mutum ya zamanto mai ‘yanci. Maganar farko ta dukkanin annabawa ita ce cewa ku yi biyayya ga Allah sannan ku nesanci dagutu da mutanen da su ba Allah ba ne amma su ke son su mai da mutane su zama bayi
“Ku bauta wa Allah, sannan ku nesanci dagutu”. A saboda haka ‘yanci a Musulunci ya ginu ne bisa tushen tauhidi. Ruhin tauhidi shi ne cewa wajibi ne a kawar da bautan wanin Allah. Tushen ‘yanci a Musulunci shi ne shaksiyya da kima na mutum wanda mutum bai san kowa ba in ba Allah ba, alal hakika tushen ‘yancin mutum shi ne tauhidi da sanin Allah. Mutumin da ya ke da ‘yanci a al’adar Musulunci ba zai iya ba kuma ba shi da hakkin ya yi biyayya wa wanin Allah.
Tauhidi, Daidaita Mutane Cikin HakkokiTauhidi, Daidaita Mutane Cikin HakkokiMa’anar umurnin Ubangiji ba shi ne ma’anar da ke cikin littafi ba; ko da yake umurnin Allah yana cikin littafin Allah ne, amma littafi wani abu ne sannan kuma umurni wani abu ne na daban. Umurnin Allah, shi ne wannan umurni da Allah ya yi wa bayinSa. Don tsara rayuwar bil’adama Allah Madaukakin Sarki ya gabatar da wasu dokoki, wato Allah Madaukakin Sarki ya tsara wani tsari wanda wajibi ne mutane su bi wannan tafarkin. Mene ne wannan tafarkin? Wannan yunkurin shi ne dai wannan lamarin da annabawa tun daga na farkonsu zuwa na karshensu suka yi kira zuwa gare su, wanda kuma shi ne wannan abin da koyarwar Musulunci ya ginu a kai, shi ne tauhidi, wato girmama dan’adam, wato daidaita mutane a fagen hakkoki, a fagen dabi’a, a fagen dokoki da sauransu. Wannan shi ne dai tsarin da aka tsara tsawon tarihi wanda a cikinsa ne ake samun kamala, to amma akwai wani yunkurin da kuma wani umurnin da kuma wata yarjejeniya da Allah ya kulla da bayinSa.
Mene ne dawagitai suke aikatawa? Dawagitai suna sauya wadannan yunkuri ne. Allah yana kira ne zuwa ga tauhidi, wato kada bayi su dinga bauta wa junansu, su bauta wa Allah, amma dawagitai sai su zo su sauya lamarin, su sanya mutane su dinga bauta wa bayi, su dinga bauta wa junansu a matsayin misali. Allah Madaukakin Sarki Ya kasance yana kiran mutane ne zuwa ga girmama mutum da ababe masu kima na mutane, sannan kuma tsarin Allah ya ginu ne bisa hakan, su kuwa dawagitai sun gina tsarinsu ne bisa tushen kaskantar da mutane da wulakanta su. A yau a cikin al’adu na abin duniya da ke gudana a kasashen yammaci mutane suna jin cewa lalle sun rasa Ubangiji cikin rayuwarsu. Saboda kuwa akwai wadansu mutane wadanda suke son cika alkawarin Ubangiji amma an nesanta su da kuma sauya su. Tsare-tsaren dagutu da suka saba wa na Ubangiji su kan mai da mutum ya zamana ya mance da Allah, ba wai kawai ma sunan Allah da hakikaninsa ba ma za su je ga kunnuwansu ba ne, a wani lokacin ma sun yi imani da Allah amma dai suna mancewa da hakkin Ubangiji, wato ba su san mene ne matsayin Allah cikin al’umma ba.
Sharadin Ceto (Rabauta)Ceto shi ne dai wannan rabauta da ya zo cikin maganar Manzon Musulunci inda ya ke cewa “Ku ce La ilaha illallah ku sami rabo”, wato ku ce La’ila illah, sai ku rabauta; ceto daga tunani na kuskure, daga munanan halaye, daga mika zuciya da munanan abubuwan da suka daure zukata sannan kuma sama da hakan tsira daga azzaluman da suke zaluntar bil’adama. Wato idan har tunani da kwakwalwa da zuciya da akidar wata al’umma suka zamanto a cike to amma kuma ya zamana azzalumai da ‘yan mulkin mallaka da ‘yan jari hujja ko kuma wata cibiya kaza mai karfi na ja’irci suka zamanto suna iko a kansu, to kuwa wannan ceto da rabauta da suke da su ba su cika ba. Rabauta na gaba daya ita ce rabauta cikin zuciya, cikin kwakwalwa, cikin kyawawan halaye, cikin al’umma, siyasa da ababen da suke kyautata ruhi. Irin wannan rabauta ita ce manufar addini, manufar tauhidi da kuma La ilaha illallah.
Aljannar Masu Kadaita UbangijiBarci da ci da sha da magana da kasuwanci da motsa jiki da karatu da ayyuka na siyasa da zamantakewa da sauran ayyuka na duniya, dukkanin wadannan abubuwa a wajen bayin Allah salihai suna yin su ne don cimma wannan manufa ta isa ga Allah Madaukakin Sarki. Sakamakon kama wannan hanyar, to Aljanna ta kan kasance a gefen mutum. A irin wannan rayuwar ta Musulunci da tauhidi da riko da ababen da suke kyautata ruhi, ba a samun karo da juna da fada da kuma sabani. Nazariyar tauhidi cikin shi kansa mutum ta kan samar da aljanna.
Tauhidi Cikin Tsari Na SiyasaTauhidi yana nufin ba ya halatta a bauta wa wani mutum wanda ba Allah ba. Wanin Allah ko shi wane ne dagutu ne sannan kuma kishiyar Ubangiji ne. A saboda haka ne a tsari na siyasa na kasar nan, a duk inda aka yi batun biyayya wa wani mutum, ya samo asali ne daga biyayya ga Allah, yin biyayya wa wanin Allah (cikin abin da ya saba wa umurnin Allah) kuskure ne. Wannan shi ne tushen tsarin Musulunci.
Tunanin da ya ke cike da shirka ko kuma tunani na dagutu da shaidan – wanda dagutu wata kalma ce ta daban ta Shaidan; Shaidan yana nufin karfi mai samar da sharri da fasadi da kauce wa hanya; dagutu ma yana nufin mai dagawa, wato wannan sharri da fasadi da kauce wa hanya; dakarun dagutu yana nufin wannan tunani na dagutu, tunani na shaidan – suna yin tasiri cikin halaye na daidaikun mutane, cikin halaye na jama’a da kungiya, cikin yadda ake kafa wani tsari na zamantakewa.
Fadadar MahangaMutum mai kadaita Ubangiji yana da mahanga mai fadi da kuma fadaddiyar zuciya; ya tsira daga kuncin mahanga da rashin hangen nesa da kuma kallon lamurra da ido na kurkusa. Mutum mai kadaita Allah ba ya cewa ni dai na sha kashi a fage kaza ko kuma sansaninmu a fage kaza ya ci baya kuma daga karshe dai za mu sha kashi. Shi dai ya san cewa tunani na tauhidi tsawon rayuwar mutum yana da wani kan iyaka. Fagen tunanin mutum mai kadaita Ubangiji cikin lamurran da suka shafi abubuwa na duniya ba su takaita kawai cikin ‘yan wasu kaskantattun abubuwa ba. Mutum mai kadaita Allah a duk lokacin da ya dubi kansa zai ga cewa baya da bukatu na abin duniya, akwai kuma wadansu dubban bukatu masu girma da daukaka na dan’adam; dukkanin tunani da kuma bukatunsa ba su takaita cikin ‘yan wadannan kaskantattun abubuwa ba. Mutum mai kadaita Ubangiji a duk lokacin da ya yi dubi zai ga cewa lalle akwai wata makoma mai fadi maras karshe a gabansa; mai kadaita Allah ba wai kawai da lahira ya damu ba, don kuwa yana ganin wannan duniya a matsayin wacce take da alaka da lahira. Yana ganin lahira da duniya a matsayin wasu abubuwa da suke juyawa tare, sannan kuma ba ya ganin mutuwa a matsayin wata katanga ta rayuwa, baya ganinta a matsayin karshen wannan hanya, face dai yana ganinta ne a matsayin wata hanyar wucewa zuwa ga duniyar da ta fi girma da fadi. Dukkanin wadannan abubuwa ne da suka kebanci tauhidi. Mutumin da ba mai kadaita Allah ba, duk yadda ya zamanto mai sadaukarwa, duk yadda ya zamanto mai kula da kyawawan akidu na bil’adama, dukkanin wadannan abubuwa a wajensa masu karewa ne bayan mutuwa; alhali a wajen mutum mai kadaita Allah mutuwa mafari ne na wata sabuwar rayuwa mai girma da fadin gaske sannan kuma wani waje ne mai kyau da jan hankula. Wani mutum mai akidar abin duniya, idan har ya zamanto mai tsananin sadaukarwa, a shirye ya ke ya jefa kansa cikin wani wajen da ya ke ganin cewa akwai mutuwa da halaka a wajen. To amma wani mutum mai kadaita Allah, idan har ya zamanto mai tsananin sadaukar da kai ko da ma bai kai irin wannan yanayi na sadaukarwa ba kuma ba ya ma so ya yi irin wannan sadaukarwar, to a wajensa fadawa cikin wannan waje da mara kadaita Allah ya ke ganinsa a matsayin halaka ya fi sauki, don kuwa shi ba ya ganin wajen a matsayin halaka, yana ganin wajen ne a matsayin wani waje wanda ya fi fadi ga rayuwar mutum.
Kawar Da Tsoro Daga Zuciyar Mai Kadaita AllahMafi muhimmancin tasiri na ruhin tauhidi a kan wani mutum shi ne kada ya ji tsoron makiya a kan tafarkin Allah, a kan tafarkin sauke nauyin da ke wuyansa, a kan tafarkin abin da yake ganinsa a matsayin manufar samuwarsa.Dangane da wannan lamari a cikin Alkur’ani mai girma an kirayi muminai da cewa:
“Kada ku ji tsoronsu, ku ji tsoro Na” Ku kawar da tushen tsoron wasu daga cikin zukatanku, ku ji tsorona, duk wani mutumin da ya ke jin tsoron Allah, to kuwa babu wani mutum da zai ji tsoronsa. Duk mutumin da ya zamanto mai kadaita Allah sannan kuma ya yi imani da Allah, to kuwa tsoro zai kawu daga zuciyarsa, tsoro da razana su ne suke kawar da duniya da kuma lahirar masu su daga gare su. Tsoron talauci shi ne yake sanya mutum tsoron ba da sadaka; tsoron rashin jin dadin (duniya) shi ne abin da ya ke sanya mutum aikata munanan laifuffuka da kaskantar da kansa. Tsoron rasa wannan rayuwa maras kima shi ne ya ke sanya mutum mika kai ga wannan rayuwa mai karshe; ya lalata rayuwa ko kuma kawar da ita.
Karfin Tauhidi Wajen Fada Da DagutuWata rana manzon sojojin Musulunci ya shigo fadar gidan sarautar Sasaniyawa. Lokacin da wannan mutumi wanda ya ke sanye da yankwanannun tufafi ya shigo wannan fada mai karfin gaske na siyasa, shin ya ji tsoro? Ya zo ne da tunanin jayayya? A’a. A irin wannan yanayi, idan irin wannan karamin mutum wanda ba shi da komai ya samu kansa a gaban wani sarki mai irin wannan karfi na duniya na wancan lokacin, za a ga cewa dukkanin himmarsa ita ce ko zai sami yadda zai sami kusaci da wannan mai karfin, ko da kuwa ta hanyar dadin baki da nuna tsoro da kuma kaskantar da kai ne. To shin haka lamarin ya kasance? Ko da wasa. A lokacin da ya matsa gaba ya isa gaban kujerar Yazdigar (sarkin wancan lokacin) ta yadda kafafunsa suka matso kusa da taba kujerar mulkin ya yi hakan ne saboda ya ga cewa Yazdigar ba zai zo ya karbi takardar da take hannunsa ba. Ya zo da wani sako ne, wasu sun zo su karbi sakon, amma ya ce ba zan ba ku ba, lalle wa shi zan ba wa. To da ya ke shi ba zai tashi ya zo ya karbi wani abu a wajen wani balarabe ba don haka ya zama wajibi ne ya matso gaba. Don haka sai ya tafi gaba har zuwa inda gadon mulkin ya ke, ya mika masa takardar. Sarkin na Iran ya ce me ya kawo ka? Sai ya ce:
“Don mu ‘yantar da mutane daga bautan bayi zuwa ga bautan Allah sannan kuma daga tsanani na duniya zuwa ga fadada da jin dadi na duniya da lahira”.Nauyin Tauhidi Cikin RayuwaDa farko dai wajibi ne imani da duk wani tunani da kuma duk wata akida ta addini ya zamanto bisa sani da fahimta ne, ya zamanto cikin fahimta ne ba wai kawai ido rufe ba; na biyu wajibi ne imani ya zamanto tare da wasu nauyin da ke wuya. Wajibi ne duk wani abin da za a yi imani da shi ya zamanto wani abu ne wanda zai sanya wa mutum nauyi cikin rayuwa da kuma ayyukansa – shin ayyuka ne na daidaiku ko kuma ayyuka na jama’a, shin abubuwan da suka shafi shi kansa mutum ne ko kuma wadanda suka shafi al’umma, ko kuma wanda ya shafi bil’adama ko kuma wanda ya shafi makomar tarihi ne. Ana yin imani da tauhidi ne cikin fahimta da masaniya wanda nauyi na takalifi yake tare da shi sannan kuma akwai wani nauyi a tattare da shi.
Nauyin da tauhidi ya ke sanya wa a wuyan mai kadaita Allah yana daga cikin nauyi mafi girma da tasiri cikin akidoji na Musulunci da kuma addini.
Nauyi na farko shi ne cewa Allah Madaukakin Sarki ne kawai ake bauta masa. Na biyu nauyin da tauhidi ya ke dora wa ma’abocinsa shi ne (samar da) wata al’umma da ta yi imani da tauhidi, wasu gungun mutane wadanda suke cikin wannan al’umma wadanda kuma suke da wasu hakkoki, dukkaninsu suna rayuwa ne karkashin wasu hakkoki. Dukkaninsu suna tafiya bisa wata hanya da kuma nau'i na dama da kuma wani nau'i na hakkoki na rayuwa.
Shiri Wajen Kare Tunani Na TauhidiTsawon tarihi a kan sami yaki da jidali tsakanin gaskiya da karya, ba wai wani lamari ne da ya kebanci wannan zamanin ba. Yaki tsakanin yunkuri guda biyu na alheri da sharri sun ta’allaka ne da samuwar wadannan abubuwa guda biyu. Allah Madaukakin Sarki yana fadin cewa:
“Kuma ba domin tunkudewar Allah ga mutane ba, sashensu da sashe, hakika, da an rusa sauma’o’i da majami’oi” (Suratul Hajj 22:40), wajibi ne wadansu da suka sami karfi sakamakon dogaronsu da Allah da kuma halittu na duniya su yi fada da wadansu wadanda suke kare tafarkin fasadi a bayan kasa. A saboda haka fada tsakanin alheri da sharri ya zamanto daga cikin abubuwan da suke faruwa na yau da kullum cikin tarihi; bambancin da ke cikin addinai da tunani na Ubangiji da waninsu yana cikin cewa ne a wajen addinan Allah yaki wani aiki ne saboda Allah; ba wani aiki ne wanda ake yinsa haka nan ido rufe ba, ba wani aiki ne na neman karfi maras manufa ba; jihadi ne a tafarkin Allah. A saboda haka ne Manzon Allah (s.a.w.a) tsawon shekaru goma – wato tsawon lokacin hukumarsa a garin Madina – ya yi yakukuwa kimanin saba’in da kafirai da masu adawa. Tsawon wadannan shekaru goma Manzon Allah (s.a.w.a) bai zauna haka kawai cikin kwanciyar hankali ba. Sannan kuma a bisa hakan ne al’adu da kyawawan halaye na Musulunci suka ci gaba da zama cikin tarihin. A fili yake sosai sannan kuma a dabi’ance dawagitan duniya ba za su taba barin wani yunkuri na tabbatar da gaskiya ya ci gaba da wanzuwa a duniya ba, don haka suke son kawar da shi daga tushe. Idan har wannan fure mai kamshi na tunanin Ubangiji da kuma tauhidi ya ci gaba da zama haka kawai ba tare da kariya ba, to kuwa da hannun masu fadi a ji sun yi kokarin kawar da shi. A lokacin da mutum ya yi imani da cewa gwagwarmaya da yaki a tafarkin Allah – wanda alal hakika ba da kariya ce ga ababe masu kima na Ubangiji da kuma abubuwa masu kyautata ruhi – wata lalura ce, to share fagen wannan yaki ma wata lalura ce. Wannan batu na cewa wajibi ne musulmi su zamanto cikin shirin yaki a tafarkin Allah lamari ne da ya zo cikin Alkur’ani mai girma:
“Kuma ku yi tanadi dominsu na abin da kuka sami ikon yi” (Suratul Anfal 8:60), wato ku yi shirin da kuma tanadar duk wani abin da za ku iya tanada domin fuskantar makiya
“na wani karfi kuma da ajiye dawaki”wato duk wani karfi da ya zama wajibi sannan kuma wanda za ku iya, wajibi ne ku tanade shi, domin ta hakan
“don ku tsoratar da makyin Allah da kuma makiyinku da shi”wato don ku sami damar tsoratar da makiyin Allah da makiyin al’ummar musulmi da irin wannan shiri da kuka yi.
.
Copyright © 2018~2022.
( Uzairu Badamasi Sufi )
Harkarmusulunci@yahoo.com
All rights reserved