XtGem Forum catalog
Uzairu badamasi

BARKA DA ZUWA SHAFI MAI ALBARKA

Alhamdulillah muna muku albishir insha Allah zamu dawo aiki gadan gadan!


Shafin farko

Haidar Ali

Demokradiyya Ta Addini Da Kuma Demokradiyyar Yammaci

Ali Khamenei5

Fasali Na Farko: Tsarin Demokradiyya Na Addini

Mece ce Demokradiyya Da Kuma Iko Na Al’umma?

Demokradiyya tana nufin fifita kuri’a da ra’ayin mutane cikin siyasar gudanar da kasa. Shi kuma iko na al’umma yana nufin samar da wani tsari na siyasa da kuma fitar da masu gudanar da wannan tsari na siyasa daga cikin mutane. Hakikanin ma’anar hakan kuwa tana bayyana ne a wajen da aka ba wa mutane hakikanin damar daukan matsayi da kuma gudanar da abin da suka yi imani da shi sannan kuma zukatansu suke son suna masu la’akari da maslaha (ta kasa da al’umma).

Bangarori Biyu Na Demokradiyya (Iko Na Al’umma)

Demokradiyya tana da bangarori biyu: wani bangare na demokradiyyar shi ne cewa ana kafa gwamnati ne ta hanyar irada da kuri’un mutane; wato mutane ko kai tsaye ko kuma ta wata hanya su ne suke zaban gwamnati, ‘yan majalisa da manyan jami’an gwamnati; wannan bangare na zaben da mutane suke yi daya ne daga cikin bangarori biyu na tsarin demokradiyya na addini. Wajii ne mutane su zamnato suna so, su fahimta, su kuduri aniya sannan kuma su yi zaben don su sauke nauyi na shari’a da ke wuyansu. Idan ba tare da wannan masaniya da bukata ba, hakan ba ya zama takalifi na shari’a.
Daya bangare na demokradiyyar shi ne cewa bayan da aka zabi jami’an kasar, to su kuwa wadanda aka zaba din suna da wani nauyi da ayyuka a wuyansu wadanda wajibi ne su aiwatar da su. (Ana iya ganin wasu daga cikin nauyi da ayyukan da ke wuyan jami’an gwamnati a nan kasa, wato bangaren Hanyoyin Gyara Ayyukan Ma’aikatan Hukuma)

Ma’anar Demokradiyya Ta Addini

Tsarin demokradiyya na addini shi ne cewa iko na addinin Allah yana tafiya kafada da kafada da kuri’un mutane, da akidar mutane, da imanin mutane da bukata ta mutane da tausayawa ta mutane ne. Kamar yadda wani mutum ya ke ganin kansa a matsayin bawan Allah shi kadai kawai – “Kai muke bauta wa kuma Kai muke neman taimakonKa” – haka nan kuma ya ke nema daga wajen Allah Madaukakin Sarki da Ya sanya shi a bisa tafarkinSa da kuma bin tafarkin salihan bayi “Ka shiryar da mu ga hanya madaidaiciya. Hanyar wadanda Ka yi wa ni’ima"Bin tafarkin salihan bayi, yin biyayya ga fitattun bayin Allah na kwarai, yin biyayyar muminai maza da muminai mata ga Manzon Allah da kuma duk wanda shugabancin al’ummar musulmi yake hannunsa, mubaya’a ce ga imani, mubaya’a ce wa adini sannan kuma mubaya’a ce ga ababe masu tsarki. Ba mika wuya ce ga wani mutum ba; ba mika wuya ce ga irada da ra’ayin wani mutum ba ne. A Musulunci abin da ke iko, shi ne addini, addinin da a cikinsa aka yi la’akari da dukkanin abubuwan da za su tabbatar wa mutum da sa’ada; hakan kuwa lamari ne da ke wuyan shi kansa mutum.

Tushen Tsarin Demokradiyyar Da Yayi Daidai Da Hankali

A bisa asasi demokradiyya ta samo asali ne daga Musulunci. Musulunci shi ne wanda ya kafa tushen demokradiyya na hakika wanda kuma ya yi daidai da hankali. A lokacin Manzon Allah (s.a.w.a) dukkanin mutane ne daya bayan dayansu suka zo suka yi masa mubaya’a; maza da matansu. A wancan lokacin ma mace ba ta da wani matsayi. Ba wai kawai a Saudiyya ba, a cikin larabawa ma an bar mace a baya ne, kai a gidan sarautar Iran da Roma ma ba sa ba wa mace damar bayyanar da ra’ayinta; to amma Manzon Allah (s.a.w.a) ya karbi umurni daga wajen Allah na cewa “Idan mata muminai suka zo maka suna yi maka mubaya’a a kan ba za su yi shirki da Allah ba” (Suratul Mumtahana 60:12), wato a lokacin da mata muminai suka zo wajenka don su yi maka mubaya’a, wajibi ne su yi mubaya’ar bisa wannan tushe (da ke cikin wannan aya ta sama), kamar yadda maza suke zuwa su yi mubaya’ar. Mata ma sun zo suka yi mubaya’a, maza ma sun zo suka yi mubaya’ar. Zukata sun hadu da junansu, azama sun hadu waje guda sannan kuma tauhidi da kadaita Allah ta bayyana tsakanin shi kansa Annabi da sauran daidaikun mutane da muminai. Na’am suna nuna kauna ga Annabi; to amma hakikanin lamarin ba shi ne Annabin ba.

Dalilin Rikon Mutane Ga Shugabanni A Duniyar Musulmi

A Musulunci dai mutum ba shi ne abin dubawa ba. Bai kamata wani ya yi kira zuwa ga wani mutum ba. Babu wani mutum da a shi kan kansa ba tare da ya dogara da wani abu mai tsarki ba ya zamanto ya sami tausayawa da kauna da sadaukarwar wani mutum na daban ba. Tun daga farko dai musulmi sun saba da hakan; har zuwa yanzu kuma haka lamarin yake. Musulmi suna nuna so da kaunar su ga duk wani abin da suka ji cewa lalle yana da alaka da wani tushe mai tsarki wanda shi ne Musulunci. Haka lamarin ya kasance tare da Manzon Allah (s.a.w.a) haka zukata suka kasance suna da alaka da wannan mai girman. Wannan shi ne demokradiyya.

Hanyoyin Gyara Ayyukan Ma’aikatan Hukuma

A yau mafi kyawun abin da za a iya amfani da shi wajen gyara halaye da dabi’un jami’an gwamnati shi ne tsarin demokradiyya na addini. Yayin da yake magana da Malik Al-Ashtar Amirul Muminin (a.s) yana cewa: “Ina gargadinka dangane da yin gori ga talakawanka saboda wata kyautatawa da ka yi musu ko kuma karin gishiri cikin ayyukan da ka aikata ko kuma ka saba alkawarin da ka yi musu. Saboda gori yana bata aiki mai kyau da ka yi, karin gishiri kuma ya kan tafiyar da hasken gaskiya sannan saba alkawari ya kan haifar da fushin Allah da fushin mutane”. Wato yana cewa ne: kada ka dinga yin gori wa mutane cewa ni na yi muku kaza ko kuma ina so in yi muku kaza; ko kuma ka kara gishiri cikin magana kan abin da ka aikata; a matsayin misali ka aikata dan wani aiki, shi kenan sai ka kambama shi sannan kuma bai kamata ka yi alkawari sannan ka saba ba. Daga nan kuma sai ya ce idan har kuka yi gori, to hakan zai bata alherin da kuka yi. Ita kuwa kambama aiki tana tafiyar da hasken gaskiyar (abin da aka aikata din ne); wato ita kanta gwargwadon gaskiyar da ke tare da aikin da ka aikata din, to mutane za su ga wannan aikin shi ba shi da wata kima. Idan har kuka karya alkawari, hakan zai zamanto abin fushi sannan kuma zunubi a wajen Allah da kuma wajen mutane “Ya girmama ga zama abin kyama a wurin Allah, ku fadi abin da ba ku aikatawa” (Suratus Saff 61:3) “Ka kula da adalci na Ubangiji da mutane cikin kanka da kebantattun cikin iyalanka da kuma wadanda suke karkashinka na daga talakawanka”, wato kada ka kebance su da wani abu ban da sauran mutane. Wato ka bude dama ga wadansu mutane na musamman ta hanyar amfani da wani kamfani da wata hanya ta samun kudi saboda kawai wadannan mutane abokanka ne ko kuma jininka ne ko kuma na kurkusa da kai ne. Wadannan suna daga cikin ayyukan da suke kafar ungulu ga demokradiyya “Ya kamata mafi soyuwan al’amari a gare ka ya zamanto matsakaicinsu cikin gaskiya, wanda yafi haduwa cikin adalci da kuma cika wajen yardar mutanen da suke karkashinka”, wato ka nemi aikata ayyukan da suka yi nesa da wuce gona da iri ko kuma gazawa sannan kuma ka sanya adalci ya zamanto cikin dukkanin al’amurran mutane; wato gwargwadon yadda fagen samun damar mutane da kuma abubuwan amfaninsu ya karu to kuwa yarda da farin cikinsu ma zai karu. Kada ka zamanto mai neman yardar wadannan mutane na musamman kawai – wato ma’abota dukiya da karfi - . Daga nan kuma sai ya ce: “don kuwa rashin yardar sauran mutane ya kan tafiyar da yardar ‘yan kadan”, wato ko da ka sami yardar zukatan masu kudi da iko amma kuma ka bakanta wa sauran mutane rai, to kuwa wannan rashin amincewa ta mutane za ta kawar da wancan farin ciki na wadancan kebantattun mutane – wato masu kudi da ikon. “haka kuma rashin yardar ‘yan kadan ya kan bace cikin yardar sauran mutane”, amma idan har ba ka kula da masu dukiya da iko ba, za su yi fushi da kai, to ka bar su su yi fushin. “Ya kan bace”, wannan fushin na su zai gushe.

Halalcin Tsarin Siyasa A Musulunci

Hakikanin tsarin demokradiyya na addini shi ne cewa wajibi ne ya zamanto ana gudanar da shi ne bisa shiryarwa ta Ubangiji da kuma irada ta mutane sannan kuma ta ci gaba. A Musulunci mutane wani rukuni ne na wannan halalcin, ba wai dukkanin tushen halalcin ba. Tsarin siyasa a Musulunci, baya ga ra’ayi da bukatar mutane, ya kuma ginu bisa wani tushe na daban wadanda su ne tsoron Allah da kuma adalci. Idan har mutumin da aka zaba saboda shugabanci ya zamanto ba shi da tsoron Allah da adalci a tattare da shi, to ko da dukkanin mutane sun zabe shi, to a wajen Musulunci wannan hukuma ba halaltacciyar hukuma ba ce; yawan mutane ba shi da ma’ana a nan. Imam Husaini, amincin Allah ya tabbata a gare shi, yana cewa: “Wallahi babu shugaba face sai mai hukumci da gaskiya (adalci)” shugaba a cikin al’ummar musulmi haka nan hukuma a Musulunci ba za su iya zama shugaba ko hukuma ba har sai sun kasance masu aiki da adalci; da hukumci da adalci. Matukar (shugaba) bai yi aiki da adalci ba, ba shi da halalci ko wane ne kuwa ya nada shi ko kuma ya zabe shi.

Tushen Demokradiyya A Musulunci

Lamari na asasi da a koda yaushe na kasance ina jaddada shi, shi ne cewa babu tazara da bambanci tsakanin kishin addini a tsarin Musulunci da kuma kishin talakawa. Kishin talakawa a tsarin Musulunci, yana da tushe na Musulunci. A yayin da muka ce 'tsarin Musulunci' babu yadda za a iya rufe idanuwa kan mutane. Tushe da asasi na hakkin mutane a cikin wannan zaben shi ne dai Musuluncin; a saboda haka tsarin demokradiyya na addini yana da falsafa da kuma tushe.
A cikin tsarin demokradiyya na addini sannan kuma cikin shari'a ta Ubangiji akwai wannan batu na cewa wajibi ne mutane su zamanto masu kaunar wani shugaba. Matukar dai ya zamanto abin yardarsu to yana da hakkin ya yi shugabanci. Ya ku musulmi, me ya sa kuri'ar mutane ta zamanto abar la’akari? Suna cewa saboda mu din nan musulmi ne; saboda mun yi imani da Musulunci, sannan kuma saboda a Musulunci ra'ayin mutane bisa asasin karama ta mutane a wajen Allah Madaukakin Sarki abin lura ne. A Musulunci babu wani shugabanci ko iko a kan mutane da ya zamanto abin yarda sai dai idan Allah Madaukakin Sarki ne Ya ayyana hakan. Mu dai a duk lokacin da muka sami wata alaka cikin batutuwa daban-daban na fikihu da ke da alaka da wilaya ta shugaba, wilaya ta alkali ko kuma wilaya ta mumini – wanda yake da nau'oi daban-daban na wilaya – sai mu yi shakka shin akwai wani dalili na shari'a ta karfafa irin wannan wilaya ko kuma a'a, mu kan ce a'a; me ya sa? Saboda asalin lamarin shi ne rashin wilayar. Wannan ita ce falsafar Musulunci. Wannan wilaya za ta zamanto abar yarda ce a lokacin da shari'a ta yarda da ita. Yardar shari'ar kuwa tana cikin cewa ne wannan mutumin da yake da wilayar wajibi ne ya zamanto yana da wannan dacewar wato adalci da kuma tsoron Allah sannan kuma mutane suna son sa. Wannan ita ce falsafar demokradiyya ta addini wacce tana da karfi sosai. Wani mutum mumini yana iya yarda da wannan falsafar da dukkanin imani sannan kuma ya yi aiki da hakan. Babu shubuha da taraddudi cikin hakan.

Tsarkin Tsarin Demokradiyya

'Yancin mutane da dogaro da ra'ayoyinsu da kuma demokradiyya da ma'anarta ta hakika, a wajen mu wani lamari ne mai tsarki, me ya sa? Ba wai saboda falsafa akidar sassauci ba, face dai saboda Allah Madaukakin Sarki Wanda Shi ne Mahalicci kuma mamallakimu ya fadi cewa: "Dukkanin mutane 'yantattu ne, kada ka zamanto bawan wani alhali kuwa Allah Ya halicce ka da" Allah ne ya fadi hakan. Idan Amirul Muminin (a.s) da fadi magana, wato fadin Allah ne; Idan Annabi ya fadi magana, fadin Allah ne; kawai dai ta bakinsu ne aka ji. Halifa na biyu ma ya taba gaya wa daya daga cikin ma'aikatansa – wanda shi ma ya kasance a wancan yanayi – cewa: 'Ka bautar da mutane alhali kuwa Allah Ya halicce su 'ya'ya". Wannan wani tushe da falsafa ce ta demokradiyya ta hakika. Mafi muhimmancin alamar 'yanci ita ce cewa mutane su zamanto su ne za su zaba wa kansu makomarsu. Wannan shi ne tushen demokradiyya.

Haduwar Bautar Allah Da Kishin Talakawa

Sabon abin koyi na tsarin demokradiyya na addini ya gabatar wa bil'adama wata sabuwar hanya wacce a cikinta aka ceto rayuwar mutum daga bala'i na gwamnatocin da aka gina su bisa asasin mulkin kama karya na daidaiku da kungiyanci ko kuma wanda ya ginu bisa tsoma bakin masu bautan zinare da 'yan babakere da kuma nutsewa cikin kogin abin duniya da yada fasadi da nesantar ababen da suke kusata mutum da Ubangiji, da kuma nuna rashin ingancin ra'ayin cewa akwai karo da juna tsakanin bautan Allah da kishin talakawa cikin aiki. Wannan sabon abin koyi cikin girma da wanzuwarsa da kuma karfin wajen cimma manufar da ake son cimmawa wata hujja ce a kan gwamnatocin da suke fakewa da sunan kishin talaka suke nesantar da mutane da Allah da ababen da suke kusata mutane zuwa gare Shi sannan kuma da sunan demoradiyya suke makure mutane da sanya su a aljihunsu. A al'ada ta Musulunci, mafi alherin mutane shi ne wanda ya ke amfanar mutanen. Tsarin demokradiyya na addini, sabanin tsarin demokradiyya na son nuna kai da yaudarar mutane, tsari ne na yin hidima wa mutane tsakani da Allah ba tare da gori ba, hidima da jin cewa ana sauke wani nauyi ne da ke wuya ne tare kuma da tsarkin zuciya.


Fasali Na Biyu: Demokradiyya Ta Yammaci

Karin Bayani Kan Demokradiyyar Yammaci

Demokradiyyar yammaci ta ginu ne bisa tushen akidar sassauci (akidar nan ta yarda da 'yanci na daidaikun mutane da kuma hakki guda). Suna cewa ne tun da mutum yana da 'yanci, to wannan 'yanci yana tabbatar da cewa kada ya zamanto mai mulkin kama karya ya zamanto mai akidar jamhuriya. To wannan 'yanci wanda yake da ma'ana ta sassauci, ‘yanci ne wanda ya ke sakakke ba tare da wani kaidi ba. Wato idan har mutane suka kuduri aniya, to za su iya amincewa da wani lamari wanda dari bisa dari mai cutarwa ne a gare su. A matsayin misali mutanen Ingila kamar yadda majalisarsu ta amince da halalcin luwadi da madigo, sai su kuduri aniyar cewa wajibi ne a halalta amfani da heroin da auren muharrama. To a nan kan babu hankali cikin cewa kada su saurara; wajibi ne su yarda da hakan. Mene ne bambancin da ke tsakanin luwadi da auren muharrama? A nan dai ba su da wani abin da ya yi daidai da hankali dangane da wannan aikin. Idan har a yau majalisar Amurka ko kuma majalisar Ingila su ka yanke shawarar cewa ana iya auren muharrama, to a nan ina batun kishi na mazantaka kuma. A saboda haka babu wani hankali cikin wannan 'yancin da ake magana. Idan har suka ce daga yanzu zuwa sama kan wannan 'yancin ya saba wa kyawawan halaye, sai mu ce wasu kyawawawan halaye kuma? Babu batun kyawawan halaye ai, suna da 'yanci. Saboda falsafar akidar sassauci ita ce 'yanci sannan kuma babu wani kan iyaka da haddi da zai takaita wannan 'yancin, sai dai idan har 'yancin ya ci karo da ‘yanci na daidaikun mutane ‘. Wannan kan shi ne jan layinsu da ba za su iya tsallake shi ba. A hakikanin gaskiya demokradiyyar yammaci ta hanyar dogaro da wannan hikima da falsafa ta akidar sassauci tana tabbatar da rashin wani abu mai amfani da take da shi ne. Ta haka ne za su iya kawar da dukkanin wasu al'adu masu kyau na wata al'umma. A yau mutanen da suka yi imani da wannan tunani, ba a shirye suke su amince da wannan lamarin ba; to amma abin da hakan yake tabbatarwa shi ne wannan abin.

Sigar Demokradiyyar Yammaci

Cikin dukkanin abubuwan da a yau a duniya aka sanshi da sunan demokradiyya akwai wata siga da aka santa. A cikin demokradiyya ta yammaci, sigarta ita ce manufa da bukata ta masu hannu da shuni da masu juya makomar al'umma. A karkashin wannan sigar ce ake girmama ra'ayi da kuri'un mutane da kuma aiwatar da su. Idan har mutane suka zabi wani abin da ya saba wa amfanin wadannan masu jari da masu mulki da karfin tattalin arziki – wadanda su ne suke gudanar da siyasar duniya – to babu wani lamuni da ke nuni da cewa wannan tsari na demokradiyyar zai amince da wannan bukata ta al'umma. Akwai wata siga tsayayyiya da take gudanar da dukkanin wadannan tsari na demokradiyya. A kasashen ‘yan gurguzu da suke gushe – wanda su ma suna kiran kansu kasashen demokradiyya - wannan shi ne sigar jam’iyyar da take mulki. Duk wani abin da ya saba wa wannan siga da bukata da siyasar jam’iyyar da take mulki, to kuwa babu wani abin da kuri’a da ra’ayin al’umma zai iya yi.

Manufar Demokradiyyar Yammaci

Tsarin demokradiyya na kasashen yammaci, tsari ne da ya sha kashi wanda kuma ya tsufa sannan kuma matsalolin da suke tattare da shi sun fito fili. Irin wannan tsarin demokradiyyar ya ginu ne bisa son mulki. Wadansu kungiyoyi biyu ne ko kuma jam’iyyu biyu ne suke fuskantar junansu; idan har da za a tambaye su me kuke son cimmawa ne, za su ce muna so ne mu sami karfi da mulki. To ku yi me da wannan karfi idan kuka same shi? Shin za ku karfafa da kyautata irin kyawawan halayen mutane ne? za ku kara daukaka abubuwan da suke kusata mutane da Ubangiji ne? za ku kyautata rayuwar mutane ne? Za ku kawo karshen take da zahirorin lamurra ne? A’a, ba haka lamarin ya ke ba; wata jam’iyya ce kawai take so ta ci gaba da rike mulki da karfi har zuwa wasu shekaru. Babu wani abu mai kima da ya dame su; babu batun girmama dan’adam; babu batun daukaka dan’adam a cikinsu. A yau a duniya hatta a kasashe irin su Amurka – wanda muryarta ta fi ta sauran tashi sama – ba a tabbatar da irin wannan demokradiyya ta yammaci ba!

Halalcin Tsarurrukan Siyasa Na Yammaci

Tsarin demokradiyya na yammaci – wato tsarin demokradiyyar da ta ginu bisa akidar sassauci – yana da wata hikima da ta kebance shi. Wannan lamari kuwa shi ne cewa tushen halalcin hukuma da wani tsari shi ne kuri’a da ra’ayin mafi yawan mutane. tushen wannan tunani ma shi ne dai wannan tunani na akidar sassauci; tunanin ‘yanci na daidaikun mutane wanda ba shi da wani kan iyaka da haddi na kyawawan halaye in ban da kan iyaka na cutar da ‘yancin sauran mutane. Wannan shi ne tunani akidar sassauci ta kasashen yammaci: ‘yanci na mutum da daidaiku a dukkanin fagage wanda daga karshe yake kai wa ga kafa tsari na siyasa na kasa. Da yake a cikin kowace al’umma akwai ‘yan tsiraru da kuma mafiya rinjaye, babu wata mafita face dai ‘yan tsiraru su bi mafiya rinjaye. Wannan shi ne tushen deomokradiyyar kasashen yammaci. Idan har wani tsari ya zamanto yana da wannan abu, to wannan tsarin da a mahangar tsarin demokradiyya na yammaci yana da halalci, idan kuwa wani tsari ya rasa hakan, to ba shi da halalci.


Fasali Na Uku: Demokradiyya A Tsarin Jamhuriyar Musulunci ta Iran

Amfani Da Kwarewar Bil’adama

A yau a tsarin Jamhuriyar Musulunci, bisa koyarwa ta Musulunci, muna amfani ne da kwarewa ta dan'adam. Mu a Musulunci muna da tsarin demokradiyya; kwarewa ta dan’adam ya zuwa wani haddi ya sami damar aiwatar da hakan bisa tsari na majalisa. Ba tare da bata lokaci ba muka riki tsarin majalisa; ba mu yi watsi da tsarin majalisa ba. Koyarwa ta Musulunci ta kasance mai kyakkyawan dubi da kallo ga dukkanin kwarewar da dan’adam ya samu kuma ya yi amfani da su tsawon shekara da shekaru, wato Musulunci ya amince da yin riko da wadannan kwarewa sai dai kawai wajibi ne su zamanto sun yi daidai da tushe da asasi na Musulunci. Wannan shi ne abin da a yau aka tabbatar da shi a kasar Musulunci ta Iran.

Alakar Jamhuriya Da Musulunci A Tsarin Jamhuriyar Musulunci ta Iran

A wannan kasa da kuma wannan tsari, Musulunci da jamhuriya suna tafiya ne tare. Jamhuriyar mu ta samo asali daga Musulunci sannan kuma Musuluncinmu ba zai bari ya zamanto babu demokradiyya a wannan kasa ta mu ba. Mu ba ma so mu koyi jamhuriya daga wajen wani; tuni Musulunci ya koya mana hakan. Wannan al’umma, tana riko da Musulunci ne sannan kuma ta yi amanna da jamjhuriya. A cikin kwakwalwar wannan al’umma sannan kuma a cikin wannan tsarin Allah da mutane suna tare ne sannan kuma Allah Madaukakin Sarki Ya ba mu wannan dacewar inda mutane suka yi riko da wannan tafarkin. Wannan al’umma, wannan tsari, wannan siga da kuma wadannan dokoki na kasa sun sami nasarar kiyayye Musulunci da kuma jamhuriya.

Demokradiyya A Mahangar Imam Khumaini (r.a)

A mahanga ta siyasa ta Imam Khumaini (r.a), dan’adam yana da kima da karama kamar yadda kuma yake da karfi da kuma amfani. Sakamakon samun wannan kimar da kuma karama shi ne cewa wajibi ne ra’ayin mutane ya zamanto ya taka gagarumar rawa na asasi wajen tsara makomar wata al’umma. A saboda haka demokradiyya a mahangar Imam Khumaini (r.a) – wadda ta samo asali ne daga koyarwa ta Musulunci – tsarin demokradiyya na hakika ne. Mutane su ne suke zaban tafarkin da suke so ta hanyar kada kuri’arsu da kuma irada da kuma son zuciyarsu; sannan kuma su zabi shugabannin da suke son su jagorance su. A daya bangaren kuma Imam ta hanyar riko da karfin ra’ayin mutane ya yi amanna da cewa ta hanyar karfin mutane ana iya yin tsayin daka a gaban duk wani karfi mai son wuce gona da iri na duniya; sannan kuma haka nan din ya tsaya kyam. A cikin mahanga ta siyasa ta marigayi Imam Kumaini, demokradiyya ta samo asali ne daga koyarwa ta addini; ta samo asali ne daga “Kuma al’amarinsu shawara ce a a tsakaninsu” (Suratush Shura 42:38) sannan daga “Shi ne Wanda Ya karfafa ka da taimakonsa, kuma da muminai” (Suratul Anfal 8:62)

Yanayin Tsarin Musulunci A Iran

Ni dai a lokuta da dama na sha jaddada cewa wajibi ne mu samara da yanayin tsarinmu da ruhinsa da kuma abin da ya kumsa daga Musulunci; ba wai daga wajen ‘yan kasashen waje ba; wato dukkanin al’adun da suka yarda da su da maganganu da tunaninsu da suke yada shi a duniya, wato abubuwan da su suka yarda da su, to wajibi ne ma sauran al’ummomi su amince da su. Bai kamata mu mika kai ga tunanin wadansu mutane dangane da mu ba; wajibi ne mu ci gaba da neman abin da ya dace da maslaha da kuma bukatarmu sannan da kuma abin da muka yi imani da cewa shi ne gaskiya. Hakan shi ne hukumce-hukumce na Musulunci da adalci na Musulunci da kuma tafarkin Musulunci. Wannan shi ne abin da muka tabbatar da tsarin mu na Musulunci a kansa sannan kuma muka kira shi da demokradiyya ta addini. Demokradiyya ta addini tana nufin manufa, ababe masu kima na Musulunci da kuma aiwatar da dokoki da hukumce-hukumce na Musulunci. Idan har aka gudanar da wadannan dokoki, to kuwa za a sami adalci da daidaito na addini da dukkanin ma’anarsa cikin al’umma. A tsarin jamhuriyar Musulunci demokradiyya da girmama ra’ayin al’umma wani nauyi ne na addini. Jami’ai suna da wani nauyi a wuyansu na kiyaye wannan lamarin, sannan kuma za su ba da amsa a gaban Allah Madaukakin Sarki.

Alakar Mutane Da Jami’ai

Mai yiyuwa a cikin al’ummomin da a halin yanzu muke da labarinsu da kuma abin da muka sani na irin alakar da ke tsakanin al’umma da gwamnatoci da jami’ansu, to lalle ba mu ga wata al’umma irin al’ummar Iran wacce alakarta da jami’an gwanmati ba wai kawai alaka ce da ofisoshi da cibiyoyi na gwamnati ba, wato alakar da ake samunta kawai a lokacin zabe shi din ma a wani yanayi na musamman ba. Alakar mutane da jami’an gwamnati, wata alaka ce ta so da kauna da kuma imani da akida, wato sun yarda da jami’an. Wannan lamari ne mai matukar muhimmancin gaske wanda sama da komai yana tabbatar da irin karfafaffen tsarin demokradiyyar da ake da shi a cikin tsarin jamhuriyar Musulunci. Wannan tsarin demokradiyya wanda alaka ce tsakanin mutane da jami’an da masu gudanar da lamurran kasa, wata alaka ta bangarori biyu wacce take tare da so da kauna da imani na cikin zuciya da kuma akida. Hakan kuwa shi ne mafi kyawun yanayin wata hukuma ta al’umma.

.
Copyright © 2018~2022.
( Uzairu Badamasi Sufi )
Harkarmusulunci@yahoo.com
All rights reserved

Bamu Da Alhakin Tallar Da Ake Sawa Akan Wannan Website Din