Hakkoki Na Dan’Adamtaka Da Zamantakewa Na Mace Da Namiji A Musulunci
Gabatarwa:Ana iya kallon ra’ayi da mahangar Musulunci dangane da wadannan jinsuna guda biyu (mace da namiji) ne ta mahanga biyu: mahanga ta farko ita ce mahanga ta asali ta dan’adamtaka, yanayin dan’adamtaka, hakikanin dan’adamtaka da kuma abubuwan da wadannan hakika da yanayi suka ginu a kai; shin a tattare da shi kansa mutum ne ko kuma cikin makomarsa ne da kuma hanyar da za ta iya kai shi wannan mutum din zuwa ga wannan makoma da kuma irin wannan matsayi mai girma da yake son isa gare shi; ko kuma wadanda suke da alaka da hakkoki na asasi na shi kansa mutum; a matsayin misali hakkin ‘yanci da yake da shi, ‘yancin amfani da hankali, hakki na takalifi – saboda a wata ma’ana shi kansa takalifi wani hakki ne – hakki na zabi da irada da kuma hakki na mallaka. A wasu lokuta ma Musulunci ya kan kalli mace da namiji sakamakon wasu abubuwan da suke bijirowa da kuma yanayi na rayuwarsu – wato a bangaren jiki, yanayin takalifi na zamantakewa da makamantan hakan - .
Bambanci Cikin Hakika Ta Dan’adamtakaAmma a mahanga ta farko (ta hakika ta dan’adamtaka), Musulunci ba ya ganin akwai wani bambanci tsakanin mace da namiji. Jinsi na mace ko namiji ba shi da komai kashin tasiri cikin hakan. Shin cikin asalin dan’adamtakarsu ne haka nan kuma babu wani bambanci cikin hakkoki na asasi da suke da shi: (namiji) yana da ‘yanci ita ma (mace) tana da ‘yanci; yana da hakki na zabe, haka nan ita ma tana da hakki na zabe, yana da takalifi a kansa, ita ma tana da takalifi a kanta, yana iya kai wa ga kololuwa ta matsayi na dan’adamtaka, ita ma tana iya kai wa; shi ma yana da hakkin neman ilimi, haka ita ma tana da wannan hakki na neman ilimi; yana da nauyi mai girma na jihadi fisabilillahi, ita ma tana da wannan nauyi na yin jihadi fisabillillah – wato kamar yadda jihadi yake wajibi a kan mace, haka yake a kan namiji; jihadi dai ba shi kawai daukan takobi (yaki) ba, akwai nau’oi daban-daban na jihadi; wasu nau’oi na jihadin ma sun fi wahala a kan daukan takobi da tafiya fagen daga. Mai yiyuwa ne wani mutum ya zamanto zai iya aikata wani nau’in, wani mutum kuma ya zamanto ba zai iya ba, to amma ala kulli hal jihadi fisabilillah wani lamari ne da ya zamana wajibi a kan mace haka nan kuma a kan namiji – takalifi na Ubangiji ai wata dama ce ta samun daukaka ga mutum, ta hanyar wannan takalifi ne mutum zai iya samun wannan daukaka. Don haka ya zamanto wajibi a kansa da kuma kanta. Dukkanin wadannan abubuwa ba tare da wani bambanci ba, suna da matsayi guda ne a wajen mace da namiji. A saboda haka ne a wajaje da dama Alkur’ani ya ke ambaton mace da namiji tare:
“Lalle musulmi maza da musulmi mata da muminai maza da muminai mata da masu tawali’u maza da masu tawali’u mata, da masu gaskiya maza da masu gaskiya mata, da masu hakuri maza da masu hakuri mata da masu tsoron Allah maza da masu tsoron Allah mata, da masu sadaka maza da masu sadaka mata, da masu azumi maza da masu azumi mata, da masu tsare farjojinsu maza da masu tsare farjojinsu mata da masu ambaton Allah da yawa maza da masu ambatonSa mata, Allah Ya yi musu tattalin wata gafara da wani sakamako mai girma” (Suratul Ahzab 33:35). A nan maza ba za su iya cewa mu muna da irin wannan fifikon, ko kuma mace ta ce da wani dalili ya sa aka ba wa maza wannan fifiko, a’a. A dukkanin wadannan lamurra maza da mata daya suke a wajen Allah Madaukakin Sarki. A wasu wajajen ma Allah Madaukakin Sarki a lokacin da yake son gabatar da wata alama a gaban mutane, sai ya zabi wata mace. Zai iya zaban wani namiji; akwai manya mazaje masu girma da yawa; to amma sai ya zabi wata mace guda. Akwai wata ma’ana cikin hakan. Dangane da wadannan jahilan mutane da suke ganin akwai wani bambanci tsakanin mace da namiji, Alkur’ani mai girma yana fadin cewa:
“Kuma Allah Ya buga wani misali domin wadanda suka yi imani: matar Fir’auna” wato an gabatar da matar Fir’auna a matsayin misalin muminai. Yana iya kafa misali da annabi Musa, to amma sai ya kawo matar Fir’auna a matsayin misali
“Sa’ad da ta ce, Ya Ubangiji! Ka gina mini wani gida a wurinKa a cikin Aljanna”(Suratut Tahrim 66:11) A daya bangaren abu mara kyau kum a haka lamarin ya kasance:
“Allah Ya buga wani misali domin wadanda suka kafirta; matar Nuhu da matar Ludu” (Suratut Tahrim 66:10); an bayyana matan Nuhu da Ludu a matsayin misalin muggan mutane; wato babu wani bambanci tsakanin mace da namiji a fagen dan’adamtaka da daukaka da kuma a fagen takalifi da hakkoki; su din nan ‘yan adam ne.
Bambanci Cikin Yanayi Na Jiki Da Takalifi Na ZamantakewaMahanga ta biyu, ita ce kallon wadannan jinsi biyu a mahanga ta hakikaninsu na jinsuna guda biyu. AKwai wata hakika dangane da wadannan jinsuna guda biyu; a matsayin misali ba da nono ga jariri (shayarwa) wani nauyi ne da ke wuyan mace. Wajibi ne mace ta shayar da jarirai, namiji dai ba zai iya shayarwa ba. Ko kuma a matsayin misali kula da yaro, wani nauyi ne sannan kuma wani hakki ne – wato nauyi ne sannan kuma yana da wata ma'ana ta hakki – wanda lamari ne da ya ta'allaka ga mace. Ko kuma samar abin da za a ci a gida wanda nauyi ne dake wuyan namiji. Ko da a ce mace tana da dukkanin arzikin duniyan nan, ba wajibi ne a wuyan mace ta ciyar da gida da sauran bukatu na rayuwa ba. Wannan nauyi ne da ke wuyan namiji. Hakan ya samo asali ne daga hakikanin wadannan jinsuna guda biyu; wato Allah Madaukakin Sarki Ya halicci wadannan jinsuna guda biyu ne saboda maslaharsu, saboda ci gaba da wanzuwar zuriyarsu, saboda ci gaban wannan duniyar da kuma gudanar da wannan duniya yadda ta dace don haka ya halicce su da irin wannan jinsin da suke da shi. An halicci yanayi da jiki na mace da namiji ne gwargwadon yadda nauyin da ke wuyansu yake; an halicce su ne a yanayi biyu. Wadannan nauyi kuwa an tsara su bisa la'akari da wannan yanayi ne. Wanna hakikani na dabi'a – da ta hada da jiki da tausayinsu – gwargwadon irin nauyin da ke wuyansu sannan da kuma irin nau'i na hakkokin da ke wuyansu ne. A matsayin misali hakki na ciyarwa da tufatarwa da mace take da shi a wajen namiji. Hakkin ciyarwa da tufatarwa ba shi da alaka da talauci ko kuma yanayin ita macen wato saboda ba za ta iya yin wani abu ba, don haka wajibi ne a ba ta shi. A'a, mai yiyuwa ne mace za ta iya yin wani abu, za ta iya samun kudi, to amma ba wajibi ba ne a wuyanta ta kashe ko da kobo guda daga cikin dukiyar da take da ita wajen tafiyar da rayuwar da take yi tare da mijinta ba. Idan har tana so za ta iya kashe wannan kudin ne a wani wajen na daban babu kuma wata matsala cikin hakan; to amma shi namiji ba shi da irin wannan hakkin. Irin wannan mahanga ta Musulunci dangane da mace da namiji ta samo asali ne daga irin dabi'arsu. Allah Madaukakin Sarki ya samar da wani irin yanayi na dabi'a ne bisa asasin maslaha da hikima don dai rayuwa ta tafi yadda ake so tsakanin mace da namiji, don su sami damar gudanar da duniya (rayuwarsu) yadda ta dace. Ya sanya wasu ayyukan a wuyan mace sannan wasu kuma a wuyan namiji; haka nan kuma ya sanya wasu hakkoki ga mace sannan wasu hakkokin kuma ga namiji. A matsayin misali hijabin da aka dora wa mace ya fi tsanani a kan hijabin da aka dora wa namiji. Duk kuwa da cewa a wasu wajajen ma wajibi ne namiji ya kiyaye wasu hijabobin ta yadda wajibi ne ya suturce wasu bangarori na jikinsa; to amma a wajen mace kan an fi tsananta hakan, ko me ya sa? Don kuwa dabi'a da kuma siffofin da mace ta kebanta da su, siffofi ne na kyawu cikin halittu, sannan kuma matukar dai ba a so al'umma ta lalace da kuma gurbata sannan kuma kada fasadi ya shigo cikin, to wajibi ne a kiyaye wannan jinsin cikin sutura. A irin wannan bangaren kan namiji ba kamar mace ya ke ba, namiji yana da 'yanci sosai (sama da mace). Hakan ya samo asali ne saboda irin dabi'arsu sannan da kuma irin yadda Allah Madaukakin Sarki Ya tsara gudanar da duniya.
Dalilin Bambancin Diyyar Mace Da Ta Namiji A MusulunciDaya daga cikin dalilan bambamcin da ke tsakanin mace da namiji, shi ne batun dukiya da tattalin arziki, wanda hakan yana yin tasiri a wasu wajajen; to amma dangane da lamarin kisasi akwai wadansu abubuwa guda biyu: na farko, rai ne a gaban rai. A nan kan babu wani bambanci tsakanin wadannan jinsuna guda biyu. Idan mace ta kashe namiji, ko kuma namiji ya kashe mace, wajibi ne a aiwatar da kisasi a kansu. Babu inda aka ce idan namiji ya kashe mace, to hukumcinsa kaza ne; idan kuma mace ta kashe namiji, hukumcinta kaza ne; a'a, hukumcin dukkaninsu shi ne kisasi, wajibi ne a yi musu kisasi; wato a mahanga ta muhimmancin da rai yake da shi –
"Duk wanda ya kashe rai…kamar ya kashe dukkanin mutane ne gaba daya"- babu wani bambanci tsakanin mace da namiji.
To amma a bangaren dukiya akwai bambanci tsakanin mace da namiji; don kuwa namiji yana da wani fifiko na kudi da aka ba shi. Wannan fifiko na dukiya da aka ba wa namiji, saboda irin nauyi na kudi da ke wuyansa ne; ba wai kawai cikin lamarin da ya shafi iyali ba, face ma dai saboda a mafi yawan lokuta samar da dukiya da kudi ta hanyar namiji ne. Hakan ba shi da wata alaka da kima ta mutum. A matsayin misali a lokacin da ku ke neman leburan da zai muku wani aiki na gini a gidanku, sannan sai kuka tafi (inda leburori suke) kuka ga wadansu mutane goma suna tsaye suna jira. A cikinsu akwai mutane masu karfi sannan da kuma wadanda suke da ilimi. To ku din wannan mutum mai karfi ne za ku ba shi kudi ku kawo shi gidan na ku don ya yi muku wannan aikin. To amma a lokacin da kuke son ku karantar da 'ya'yanku ko kuma a wani lokacin da kuke zaune haka kawai ba tare da aiki ba kuna son ku faranta wa 'ya'yanku rai, to ba za ku kawo wannan saurayi mai karfi gidan na ku ba. Za ku ba wa wannan masanin ne kudi da kawo shi gida. A saboda haka za ku zabi mutum ne gwargwadon yadda zai iya gudanar muku da aikin da kuke son a yi muku. Namiji dai saboda fagen tattalin arziki da dukiya ne; amma ba wai cewa mace ba ta da hakki ba ne; me ya sa, mace dai tana da ayyukanta da yawa, mace tana da lamarin haihuwa, tana da nauyin shayarwa, tana da yanayi na jiki, da yanayi na ruhi da kuma yanayi na tausayi, ba za ta iya shiga kowane fage ba, ba ta da karfin gudanar da dukkanin komai. Ita din nan a bangaren dukiya da tattalin arziki da sauran ayyukan da suka shafe ta, suna haifar mata da wasu 'yan matsaloli da iyakoki; to amma shi namiji ba shi da irin wadannan iyakoki alal hakika ma an samar da shi ne don daukan nauyin wadannan lamurra na tattalin arziki. Bisa wannan misalin, a wannan fagen ana ba da wannan fifiko ne ga wannan mutum mai karfi; wato idan har aka ce za a ba wa wannan mutum mai rauni a matsayin misali tuman (sunan kudin Iran ne) dubu a kowace rana, to za a ba wa mutum mai karfi tuman dubu da dari biyar ne. Ma’anar ba shi tuman dubu da dari biyar ba tana nufin cewa shi wannan mutum mai karfi ya fi mai rauni kima ba ne; face ma’anar hakan kimar da yake da ita cikin wannan aikin ta fi na wancan din ne. A matsayin misali idan har ana son a ba da wani fifiko saboda kula da yara, to a nan fifikon zai kasance ne ga mace. Idan har ana so a ba da wani fifiko saboda shayarwa, to za a ba wa mace ne wannan fifikon. A saboda haka dangane da lamarin da ya shafi diyya, akwai bambanci cikin diyyar mace da diyyar namiji; to sai dai hakan ba saboda cewa kimar namiji ya fi na mace ba ne; a’a akwai kisasi a kan kowa – rai a gaban rai – to amma da yake a fagen kudi ne, to a mafi yawan lokuta namiji ya fi zama mai gudanar da aiki da kuma samar da dukiya, diyyarsa ta bambanta da ta mace. To amma dukkanin wadannan abubuwa sun ginu ne bisa la’akari da akasariyar mutane; idan kuwa ba haka ai mai yiyuwa ne a sami wata mace wacce ta fi wani adadi mai yawa na maza karfi. A matsayin misali shi ne kissar abin da ya ga gudana a farkon Musulunci tsakanin wata mace da wani mawaki yayin da ta bukace mawakin da ya tashi ya kashe wani bayahude; to amma sai mawakin ya ji tsoro inda ya ja da baya; a wannan lokacin sai wannan mace ta tashi da kanta ta dauki makami ta buge wannan bayahuden da kawar da shi alhali shi kuwa wannan mawakin matsoraci ya ci gaba da karkarwa. Muna da irin wannan misali a baya da kuma a yanzu; a wannan zamani na mu ma sannan kuma a baya ma muna da irin wadannan misalai; to amma wadannan ba yanayi ne na gaba daya ba. Ba a kafa hukumci na gaba daya a kan yanayin da ba kasafai ake samunsa ko kuma yake faruwa ba, ana kafa dokoki da hukumce-hukumce ne bisa abubuwan da suka fi yawa. A saboda haka a bangaren dan’adamtaka na wannan lamarin – wanda kima ce ta rai – mace da namiji daidai suke. To amma a bangaren kima ta dukiya da abin duniya – wanda yake da alaka ta gaba daya ta yanayin samar da dukiya – akwai bambamci a tsakaninsu.
Bayar Da Fatawa Da Kuma Limancin MaceKo da yake wasu daga cikin wadannan ayyuka da aka bayyana su a cikin fikihu - a matsayin misali lamarin bayar da fatawa – lamari ne da za a iya nazari kansa da kuma sauya shi. Mu dai ba za mu iya gaskata cewa daya daga cikin sharuddan mai ba da fatawa shi ne ya zamanto namiji ba. Mai yiyuwa ne ya zamana cewa mace ce ya kamata ta ba da fatawa cikin wadansu lamurran. Akwai wadansu lamurra wadanda yake ni da ku a matsayinmu na maza ba za mu iya fahimtarsu ba. Komai irin karin bayanin da aka yi mana, ba za su zamanto a fili ba a gare mu; mace ce kawai za ta iya gano shi. Mai yiyuwa ne mutum ya ce dangane da wannan lamari cikin lamurran da suka shafi mace, mace ta bayar da fatawa. Ala kulli hal, mu dai ba ma so mu dauki abubuwan da ake fadi cikin fikihu dangane da bambancin da ke tsakanin mace da namiji ya zamanto wani abu da aka sallama masa; a’a, wasu daga cikinsu lamurra ne da aka sallama musu – a matsayin misali wannan lamari na diyya – wasu kuma ba wai an sallama musu ba ne lamurra ne da za a iya sake nazari kansu; a matsayin misali lamarin fatawa, alkalanci kai hatta ma lamarin limancin salla; wanda wasu daga cikin manyan malamanmu irin su Imam, yardar Allah ta tabbata a gare shi, - kamar yadda zan iya tunawa – ba sa ganin mace tana iya limanci; to sai dai mu kan ba mu yarda da hakan ba. A saboda haka, lamarin ba shi ne cewa wajibi ne mu amince da dukkanin abin da aka fadi cikin fikihu dangane da sabanin da ke tsakanin mace da namiji ba tare da bayyanar da ra’ayinmu a kai ba. A’a, wasu daga cikin wadannan abubuwan, abubuwa ne da za a iya nazari kansu, wasu kuma ba lamurra ne da za a iya soke su ba.
Tafsirin Ayar “Maza masu tsayuwa ne a kan mata”A lokacin bukin daura auren wadansu matasa, Ayatullah Sayyid Ali Khamenei ya yi karin bayani dangane da aya ta 34 ta cikin Suratun Nisa'i da ke cewa:
“Maza masu tsayuwa ne a kan mata saboda abin da Allah Ya fifita sashensu da shi a kan sashe, kuma saboda abin da suka ciyar daga dukiyoyinsu” inda ya yi gajeren bayani kan nauyin da ke wuyan mace da namiiji cikin iyali da kuma bambancin da ke tsakaninsu. Ga kadan daga cikin abin da ya ce din:
Wannan aya tana bayani ne kan cewa shugabancin gida da kuma kula da shi yana wuyan namiji ne. Wajibi ne namiji ya fita ya yi aiki. Ciyar da iyali yana wuyansa ne. Duk dukiyar da mace take da ita mallakanta ne, to amma ciyar da gida ba yana wuyanta ba ne.
Sai dai kuma lamarin ba shi ne mu ce wajibi ne mace ta yi biyaya ga namiji a dukkanin wajaje ba. A’a, wannan wani lamari ne da babu shi cikin Musulunci haka nan kuma cikin shari’a. Ayar
“Maza masu tsayuwa ne a kan mata”ma’anarta ba ita ce cewa wajibi ne mace ta yi biyayya ga mijinta cikin dukkanin komai ba, a’a! ko kuma ba kamar yadda turawa da wadanda suke binsu ido rufe suke fadi ba na cewa wajibi ne mace ta zamanto dukkan komai, wajibi ne namiji ya yi mata biyayya. To wannan ma kuskure ne.
Dukkaninsu dai abokan tarayya da zama ne na juna. A wani wajen a kan sami namiji ya nuna gazawa haka nan a wani wajen kuma macen ta nuna gazawa. A wani wajen wani ya yi watsi da abin da ya ke so, a wani wajen shi ma dayan ya yi haka, don dai su sami damar rayuwa tare.
To amma dai Allah Madaukakin Sarki Ya sanya bambanci na dabi’a a tsakanin mace da namiji. Allah Madaukakin Sarki ya sanya mace mai taushin yanayi ne. (A matsayin misali) Wasu daga cikin hannuwa suna da girman gaske, don haka suka dace sosai wajen daga wani dutse daga kasa, amma idan har suna so su dauki wani wani dan karamin abu, babu tabbas din cewa za su iya.
Amma wasu daga cikin hannayen suna da taushi kuma ‘yan kanana ne. Ba za su iya daukan dutse ba, to amma za su iya tattara wadannan ‘yan kananan zinaren da suka zube a kasa (cikin sauki). To haka mace da namiji suke. Kowane guda daga cikinsu yana da nauyin da ke wuyansa. Ba za a iya cewa nauyin da ke wuyan wannan yafi girma da nauyi ba. Dukkanin nauyin da ke wuyansu yana da girma. Dukkanin biyu wajibi ne. Haka Allah Madaukakin Sarki Ya sanya su cikin tarayya da junansu.