BARKA DA ZUWA SHAFI MAI ALBARKA
Alhamdulillah muna muku albishir insha Allah zamu dawo aiki gadan gadan!Yakini
Yazo cikin hudubar Shugaban muminai Imam Ali (a.s) da aka fi sani da "Dibaj" cewa:
عباداللّه، سلوااللّه اليقين، فإنّ اليقين رأس الدّين وارغبوا اليه في العافية فإنّ أعظم النعمة العافية فاغتنموها للدنيا والآخرة
"Ya ku bayin Allah, ku roki Allah yakini, saboda yakini shi ne tushen addini, kuma ku bukaci lafiya daga gare shi saboda (ita lafiya) ita ce mafi girmar ni'ima. Don haka ku ribace ta domin duniya da lahira".
(Tuhaful-Ukul shafi na 150).
Yakini yana da matakai, kowane mataki (daga cikin matakan) yana da wanda ya darashi. Don haka ne ma tsarkakan Imaman shiriya daga Iyalan gidan Manzon Allah (a.s), duk da cewa suna kan mataki madaukaki na yakini, amma suna neman Allah da ya kara azurta su da yakini.
A wannan hadisi an kwatanta yakini da "kai" saboda kamar yadda kai shi ne tushe kuma ginshikin motsi da rashin motsi a wajen dan Adam, shi ma yakini irin wannan rawar yake takawa a addinin mutum.
Za a iya samun yakini ta hanyoyi biyu kamar haka: Hanya ta farko ita ce tunani da zurfafa lura cikin akidar addini da hakikanin shari'ar Musulunci mai tsarki. Hanya ta biyu ita ce mika kai ga zatin Ubangiji mai tsarki da kaskantar da kai da biyayya gare shi.
Kalmar lafiya data zo cikin wannan ruwaya ba ita ce wadda muka sani a dabi'ar rayuwarmu da muke nema yau da kullum ba, wanda mutum yake fakewa da ita domin kada ya fita fagen yaki domin daukaka kalmar Allah, saboda kada ya fuskanci aiki mai girma da wahala a rayuwarsa. Face dai wannan lafiyar ita ce lafiya ta akida da aiki da take kare waswasin shaidan dana son rai. Mutumin da yake cikin fagen yaki dole ne ya dinga rokon Allah lafiya, wato ya dinga rokon Allah kada ya afka cikin shakka, tsorata da girgizar imani. Imam Sajjad (a.s) cikin addu'a ta ashirin da uku na littafin Sahifatul-Sajjadiyya yayi ishara da bangarori daban-daban na lafiya sannan kuma ya bukaci hakan daga wajen Allah Madaukakin Sarki.