Uzairu badamasi

BARKA DA ZUWA SHAFI MAI ALBARKA

Alhamdulillah muna muku albishir insha Allah zamu dawo aiki gadan gadan!


Shafin farko

Haidar Ali

Mayar Da Amana Da Kiyayeta

Ali khamenei3

Cikin wasiyarsa ga Kumail bn Ziyad, Imam Ali (a.s) yana cewa:

يا كميل! إفهم واعلم إنّا لانرخص في تركِ أداء الأمانة لأحدٍ من الخلق فمن روى‏ عنّا في ذلك رخصةً، فقد أبطل وأثم وجزاءُه النار بما كذب، اقسم لسمعت رسول اللّه (صلى الله عليه وآله وسلّم) يقول لي قبل وفاته بساعةٍ مراراً ثلاثاً: يا اباالحسن أدّ الأمانة إلى البرّ والفاجر فيما جلّ وقلّ حتى الخيط والمخيط


"Ya Kumail! Ka fahimta kuma ka san cewa mu ba mu sassauci ga wani daga cikin bayin Allah dangane da mayar da amanar da aka ba shi. Don haka duk wanda ya ruwaito daga gare mu wata ruwaya kan hakan (wato yin sassauci wajen mai da amana) hakika ya bata kuma yayi laifi kuma sakamakonsa wuta ce dangane da karyar da yayi. Na rantse da Allah Manzon Allah (s.a.w.a) ya gaya min 'yan sa'oi kafin wafatinsa ya gaya min har sau uku cewa: Ya Abal- Hasan! Ka mai da amana ga mai shi, mai biyayya ne ko fajiri, na abu mai yawa ne ko kadan, har zare da allura".
(Tuhaful-Ukul shafi na 175).
Mayar da amana (ga masu ita) lamari ne mai muhimmancin gaske a koyarwar Musulunci. Ko da kuwa abu ne maras kima aka ba wa mutum amanarsa, dole ne yayi kokakin kare wannan amanar sannan ya mai da ita ga ma'abucinta a lokacin da ya bukata, shin wanda ya ba da amanar mumini ne ko fajiri kuma koda kafiri ne.
Amma yana da kyau a san cewa amana ba ta takaita kan dukiya ba kawai, face dai ta hada ma har da duk wani nauyi (aiki) da ya rataya a wuyarmu ko sirrin wasu da muka sani, dukkansu amana ce da suka zama wajibi mu kare su.



.
Copyright © 2018~2022.
( Uzairu Badamasi Sufi )
Harkarmusulunci@yahoo.com
All rights reserved

Bamu Da Alhakin Tallar Da Ake Sawa Akan Wannan Website Din


XtGem Forum catalog