Polly po-cket
Uzairu badamasi

BARKA DA ZUWA SHAFI MAI ALBARKA

Alhamdulillah muna muku albishir insha Allah zamu dawo aiki gadan gadan!


Shafin farko

Haidar Ali

Tsarkake Zuciya Yayin Aiki

Ali khamenei3

Daga cikin wasiyar Imam Ali (a.s) ga Kumail bn Ziyad:

يا كميل! ليس الشّأن أن تصلّي وتصوم وتتصدّق، الشّأن أن تكون الصلوة بقلبٍ نقىّ وعمل عنداللّه مرضيّ و خشوع سوىّ وانظر فيما تُصلّي وعلى ماتصلّي ان لم يكن من وجهه وحلّه فلا قبول


Ya Kumail! Muhimmi ba shi ne (ka yi) salla da azumi da sadaka ba, abin da yake muhimmi shi ne sallar ta kasance da zuciya tsarkakekkiya da aiki wanda zai zamanto karbabbe a wajen Allah da tawali'u. Ka yi dubi (ka ga) don me kake salla kuma a kan me kake sallar. Idan sallar ba don Allah ba ce, kuma a waje da ba na halal ba, to sallar ba ta karbu ba".
(Tuhaful-Ukul shafi na 174).
Daga wadannan jumloli da Shugaban muminai ke bayyana wa amintaccen dalibinsa dangane da zahiri da badini gami da hakikanin ayyuka, za a iya fahimtar cewa duk wani aiki yana dauke da jiki da ruhi, matukar babu ruhi, to jiki ya mutu kuma ba shi da wani muhimmanci. Saboda haka babu wani amfani da bawon (wani abu) zai yi ba tare da abin da ke cikinsa ba. Don haka ne ma Imam Sajjad (a.s) ke cewa: Ya Allah Ka azurta ni da zuciya mai rinjaye.
Yayin salla, yadda aka yi ta yana da muhimmancin gaske. Don haka dole ne a gudanar da salla da zuciya tsarkakekkiya kuma cikin tawali'u, domin ta zame aikin da Allah zai amince da shi. Amma sallar da za a yi ta a waje na kwace da ba na halal ba, Ubangiji baya karbarta.
Duk da cewa wannan ruwaya tana magana ne kan salla, amma dukkanin ayyuka haka suke. Har gudanar da ayyukan siyasa dole ne su kasance da nufin wanzar da gyara a tsakanin al'ummar musulmi, duk wani abu sabanin hakan haka, Allah ba zai amince da shi ba.


.
Copyright © 2018~2022.
( Uzairu Badamasi Sufi )
Harkarmusulunci@yahoo.com
All rights reserved

Bamu Da Alhakin Tallar Da Ake Sawa Akan Wannan Website Din