BARKA DA ZUWA SHAFI MAI ALBARKA
Alhamdulillah muna muku albishir insha Allah zamu dawo aiki gadan gadan!Rabon Kwado Baya Hawa Sama
Manzon Allah (s.a.w.a) ya
ce:-
ﺍﻟﺪﻧﻴﺎ ﺩُﻭَﻝ ﻓﻤﺎ ﻛﺎﻥ ﻟﻚ ﺃﺗﺎﻙ ﻋﻠﻰ
ﺿﻌﻔﻚ ﻭﻣﺎ ﻛـﺎﻥ ﻣﻨﻬﺎ ﻋﻠﻴﻚ ﻟﻢ
ﺗﺪﻓﻌﻪ ﺑﻘﻮّﺗﻚ ﻭﻣﻦ ﺍﻧﻘﻄﻊ ﺭﺟﺎﺅﻩ
ﻣﻤﺎ ﻓﺎﺕ ﺍﺳﺘﺮﺍﺡ ﺑﺪﻧﻪ ﻭﻣﻦ ﺭﺿﻲ
ﺑﻤﺎ ﻗََََﺴَﻤﻪ ﺍﻟﻠﻪ ﻗﺮّﺕ ﻋﻴﻨﻪ
"Duniya wata aba ce mai
jujjuyawa, don haka abin da
ya kasance naka ne zai
same ka komai rauninka
kuwa. Abin da kuma ya
kasance daga gareta a
kanka ba za ka iya kare
kanka daga gare shi da
karfinka ba, wanda kuma ya
fitar da ransa daga kan abin
da ya kubuce masa, ya
hutar da jikinsa (ya huta),
wanda kuma ya amince da
rabon da Allah Ya ba shi,
yana cikin farin ciki da
kwanciyar hankali".
(Tuhaful-Ukul shafi na 40).
*****
A wannan hadisi za mu
fahimci cewa ababan kawa
na duniya abubuwa ne da
suke sassauyawa, ba dole
ba ne mu zaci abubuwa irin
su dukiya, matsayi, sukuni,
lafiya da kwanciyar hankali
da muke da su, za su ci
gaba da kasancewa tare
damu har karshen
rayuwarmu. Koda wasa,
akwai yiyuwar a kwace su
daga gare mu.
Duniyar da ake nufin cewa
idan mutum ya kaurace
mata ya hutar da kansa ita
ce duniya abar zargi. Wato
wacce mutum yake
nemanta ruwa a jallo don
biyan soyace-soyacen ransa,
ba wai madaukakan
abubuwa da za su kai
mutum zuwa ga alherorin
lahira da sauran abubuwan
rufin asiri na rayuwa ba ne.