BARKA DA ZUWA SHAFI MAI ALBARKA
Alhamdulillah muna muku albishir insha Allah zamu dawo aiki gadan gadan!Shugabanci
Yana daga cikin wasiyar Imam Ali (a.s) ga Kumail bn Ziyad cewa:
يا كميل! لست واللّه متملقاً حتى أطاع ولاممنياً حتى لاأعصى ولا مائلاً لطعام الأعراب حتى انحل امرة المؤمنين وادعى بها
"Ya Kumail! Wallahi ban kasance mai fadanci ba domin a mini biyayya, kuma ban zama mai alkawura marasa tushe ba don kada a saba mini. Sannan kuma ban karkata zuwa ga abincin larabawan kyauye ba don in karbi ragamar shugabancin muminai in yi da'awarsa".
(Tuhaful-Ukul 175).
A wannan bangare na wasiya, Imam Ali (a.s) yayi watsi da dabi'ar da ‘yan duniya suke amfani da ita wajen samarwa kansu mulki da karfafa shi da tabbatar da ci gabansa.
Yin fadanci da lallabi ba su takaita ga masu mulki da dukiya da masu matsayi kawai ba, a wasu lokutan mai mulki ma yana rusuna wa al'umma kai har wa daidaikun mutane da suke karkashinsa da musu fadanci domin su ci gaba da yi masa biyayya. Yana mai cewa: Ni ba zan taba rayar da kyakkyawar fata a zukatan mutane da yi musu alkawurran marasa tushe don su yi min biyayya. Kuma ban kasance ina cin abinci mai sauki na mutanen kyauye don in yi amfani da hakan wajen samun kansu da shugabantar muminai.
Don haka dole ne mu fahimci cewa wannan magana ta fito ne daga bakin mutumin da yake cin abinci mafi sauki sannan ya zaba wa kansa rayuwa mafi wuya da wahala. Amma duk da haka yake cewa: ba ina hakan ne don shugabanci ko nuna kai ba. Wannan ba karamin al'amari ba ne mai muhimmanci gare mu da dole ne mu dau darasi daga gare shi, don niyyarmu da manufarmu su zama tsarkakku dangane da duk wani aiki da zamu gudanar. Wato duk ayyukan da zamu gudanar su zamanto domin Allah ne kawai.