Uzairu badamasi

BARKA DA ZUWA SHAFI MAI ALBARKA

Alhamdulillah muna muku albishir insha Allah zamu dawo aiki gadan gadan!


Shafin farko

Haidar Ali

Abokantaka

Ali khamenei3

Imam Ali (a.s) yana cewa:

إنّ أحسن ما يألف به الناس قلوب اودّائهم ونفوا به الضّغن عن قلوب أعدائهم حسن البشر عند لقائهم والتفقد في غيبتهم والبشاشة بهم عند حضورهم

"Lalle mafi kyawun abin da mutane za su yi amfani da shi wajen kwantar da zukatan masoyansu da kawar da kiyayya daga zukatan makiyansu shi ne kyakkyawar tarba gare su yayin da suka hadu da neman yadda suke a lokacin da saduwa ta yi wuya a tsakaninsu da kuma sakin fuska gare su a yayin da ake tare waje guda".
(Tuhaful- Ukul shafi na 218).
Sakin fuska da fara'a da iya cudanya da mutane matakai ne da suke janyo soyayya a tsakanin mutane da hada zukatansu waje guda. Ya zo cikin ruwaya cewa: "Nuna kauna rabin hankali ne". Wannan hadisi yana da muhimmancin gaske ga dukkanin jami'ai a hukuma ta Musulunci musamman ma malaman da suke kula da ma'aikatu da cibiyoyi. Saboda ma'aikata da jami'ai dake gudanar da aiki a ma'aikatu ko cibiyoyi ba su zama daya ba matakin imaninsu, sau da dama halin sanyaya gwiwa ko nuna rashi kula gare su zai iya sanadiyyar taba addininsu da raunana imaninsu. Haka nan kuma sabanin hakan idan aka samu wata kyakkyawar dabi'a (daga wajen wani jami'i) zai yi sanadiyyar janyo mutum ga addini da riko da shi gami da kyakkyawar fata ga Musulunci. Domin 'mumini fara'arsa a fuskarsa take, bakin cikinsa kuwa a zuciyarsa".


.
Copyright © 2018~2022.
( Uzairu Badamasi Sufi )
Harkarmusulunci@yahoo.com
All rights reserved

Bamu Da Alhakin Tallar Da Ake Sawa Akan Wannan Website Din


Teya Salat