pacman, rainbows, and roller s
Uzairu badamasi

BARKA DA ZUWA SHAFI MAI ALBARKA

Alhamdulillah muna muku albishir insha Allah zamu dawo aiki gadan gadan!


Shafin farko

Haidar Ali

Munanan Dabi'u

Ali khamenei3

Imam Ali (a.s) yana cewa:

من استطاع أن يمنع نفسه من أربعة اشياء فهو خليق بأن لاينزل به مكروهٌ أبداً قيل: وما هنّ يا أميرالمؤمنين! قال: العجلة واللجاجة والعُجب والتّواني

"Duk wanda ya iya hana kansa wasu abubuwa hudu, to ya kubuta daga afkawa cikin tsautsayi har abada. Sai aka ce wasu abubuwa ne Ya Shugaban muminai? Sai ya amsa da cewa: Gaggawa, taurin kai, girman kai da rashin kula".
(Tuhaful- Ukul shafi na 222).
Duk wanda ya nisanta kansa daga wadannan siffofi hudu, shi kadai ne ko kuma wata jama'a ce ta shugabanni da jagorori, to babu wani hatsari da tsautsayi na bacin rai da zai auku a kansu:
1- Gaggawa, wato yanke shawara cikin hanzari ko gudanar da wani aiki ba tare da la'akari da abin da zai je ya komo ba. (Amma gaggawa a nan ba tana nufin yin sauri wajen gudanar da aiki ba ne).
2 - Taurin kai, daya ne daga cikin matsaloli masu hatsari da bala'i dake addabar al'umma. Wato dagewa kan abu ko matsin lamba kan rashin gaskiya kan wani abu da aka furta ko mataki da aka dauka kuma mutum ba a shirye yake ya janye daga kan matakin ba ko da kuwa ya tabbatar da rashin ingancinsa.
3 - Girman kai, wato yaudaran kai da fankama da mutum yake yi domin ya lullube tawaya da rauninsa, wani lokaci ma ya dinga fankama kan kyawawan ayyukansa.
4 - Rashin kula da lalaci da nuna rauni kan muhimmin lamari, wanda aikin da ya kamata mutum ya gudanar a yau sai ya jinkirta shi zuwa gobe da haka zai janyo mai da hannun agogo baya.
Sakamakon gogayya da kwarewata ta tsawon shekaru da suka gabata da na samu na kai ga fahimtar cewa wannan jawabi na Shugaban muminai Imam Ali (a.s) tabbas jawabi ne da ya kumshi dukkanin hikima, sannan kuma dukkanin cutarwa da hasara da al'umma take fama da su sun samo asali ne daga wadannan al'amura. Don haka muna rokon Allah da Ya sa mu dace da mikewa domin gwagwarmaya tare da tallafawa daga gare shi wajen kaurace wa wadannan munanan siffofi.



.
Copyright © 2018~2022.
( Uzairu Badamasi Sufi )
Harkarmusulunci@yahoo.com
All rights reserved

Bamu Da Alhakin Tallar Da Ake Sawa Akan Wannan Website Din