Uzairu badamasi

BARKA DA ZUWA SHAFI MAI ALBARKA

Alhamdulillah muna muku albishir insha Allah zamu dawo aiki gadan gadan!


Shafin farko

Haidar Ali

Horas Da Kai Kan Kyawawan Dabi'u

Ali khamenei3

Shugaban muminai Imam Ali (a.s) yana cewa:

ذلّلوا أخلاقكم بالمحاسن وقوّدوها إلى المكارم وعوّدوا أنفسكم الحلم

"Ku horas da dabi'arku da abin yabo, ku jagoranceta zuwa ga kyawawan dabi'u, kuma ku tarbiyantar da kanku da hakuri".
(Tuhaful-Ukul shafi na 224).
Kalmar تـذليل tana nufin horaswa da sabarwa.
A halayya ta dabi'a ta dan'Adam (wato mutumin da bai samu tarbiya), akwai wasu abubuwa masu kawo cikas da ba sa tafiya kafada da kafada da rayuwar tasa. Don haka nauyin dake kansa shi ne kokari wajen kawar da wadanann abubuwa sannan kuma yayi kokarin tarbiyantar da wannan dabi'ar da kyawawan dabi'u madaidaita. Misali siffar karfin zuciya da mutum yake da shi ya karkatar da ita zuwa ga jarumtaka kuma kada ya sake siffar ta zame abin suka a kansa misalin mai kasada. Hakan kuwa yana bukatar sanin kyawawan siffofi da zage damtse domin kai wa gare su. Amma kudurta niyya kawai ga wadannan kyawawan siffofi ba tare da tashi tsaye ba mataki ne da ba zai ba da sakamako mai kyau ba. Sai dai akwai wani abu kuma wanda da mutum zai same shi da zai kai ga samun sauyi na ban mamaki a tsarin halittarsa na dan Adam, wannan abu kuwa shi ne son Ubangiji. Matukar zuciyar mutum ta kama hanyar Allah Madaukakin Sarki, to ta kama dahir kuma za ta ga ta iya samun abin da ake samunsa cikin shekara dari cikin dare guda.
A wani bangare kuma yana cewa mutum yayi kokarin sabar wa kansa da hakuri da juriya.
Hakuri dai ba yana nufin rashin fushi ne ba kawai, face dai yana da ma'anar da take dauke da juriya gwargwadon yadda mutum zai iya. Don haka wajibi ne mutum ya dauki matakin juriya kan duk wani abin da zai sanya shi yin fushi ko wurgashi cikin tarkon girman kai ko farin ciki da annashuwa marassa tushe.



.
Copyright © 2018~2022.
( Uzairu Badamasi Sufi )
Harkarmusulunci@yahoo.com
All rights reserved

Bamu Da Alhakin Tallar Da Ake Sawa Akan Wannan Website Din


Disneyland 1972 Love the old s