Uzairu badamasi

BARKA DA ZUWA SHAFI MAI ALBARKA

Alhamdulillah muna muku albishir insha Allah zamu dawo aiki gadan gadan!


Shafin farko

Haidar Ali

Muhimmancin Samun Mai Tunatarwa

Ali khamenei3

Daga cikin wa'azozi da nasihohin Imam Sajjad (a.s):

ابن آدم! إنّك لاتزال بخير ما كان لك واعظ من نفسك وما كانت المحاسبة من همّك وما كان الخوف لك شعاراً والحذر لك دثاراً


Ya dan Adam ! ba ka gushe ba kana cikin alheri matukar kana da mai maka wa'azi tare da kai daga zuciyarka. Kuma hisabi ya kasance daga cikin abin damuwarka, tsoro ya kasance abin ambatonka kuma tsantseni ya zame maka mayafi".
(Tuhaful-Ukul shafi na 280).
Duk da cewa mutum bai wadatu daga wa'azin sauran mutane ba, amma wa'azin da yake daga cikin zuciyarsa shi ne mafificin wa'azi, domin kowani ya san dukkan siffofi da aibin da yake da su sama da sauran mutane. Saboda haka wajibi ne dukkanin himmar mutum ta kasance wajen yin hisabi wa kansa. Ba dalili ba ne idan wadansu ba su mana hisabi ba, shi kenan sai mu zauna ba tare da yi wa kanmu hisabi ba. Saboda hisabi wa kai yana kare mutum daga kura kurai a nan gaba.
Abin nufi da tsoro a nan shi ne tsoron Allah da azabarsa gami da mummunan aikin mutum, bawai tsoron mutane da masu mulkin kama karya ba.
Tsantseni yana nufin rigakafi, tsantseni ba yana nufin mutum ya kauracewa ayyuka ba ne, a'a dole ne ya shiga fage a dama da shi sai dai ya zame yana taka tsantsan cikin al'amuransa, wanda hakan shi ne ake nufi da tsoron Allah.


.
Copyright © 2018~2022.
( Uzairu Badamasi Sufi )
Harkarmusulunci@yahoo.com
All rights reserved

Bamu Da Alhakin Tallar Da Ake Sawa Akan Wannan Website Din


Pair of Vintage Old School Fru