XtGem Forum catalog
Uzairu badamasi

BARKA DA ZUWA SHAFI MAI ALBARKA

Alhamdulillah muna muku albishir insha Allah zamu dawo aiki gadan gadan!


Shafin farko

Haidar Ali

Fadawa Tarkon Yabon Mutane

Ali khamenei3

Yana daga cikin wa'azozin Imam Ali bn Husain Al-Sajjad (a.s) cewa:


كم من مفتونٍ بحسن القول فيه، وكم من مغرورٍ بحسن الستر عليه، وكم من مستدرجٍ بالإحسان عليه

"Sau nawa ake fadin kyakkyawar magana kan maha'inci, kuma sau nawa mutum ya kan yi gururi saboda kyakkyawar sitirar da aka yi masa, kuma sau nawa ake wa mutum istidraji ta hanyar kyautata masa".
(Tuhaful-Ukul shafi na 281).
Sau nawa ake samun mutanen da suke fada tarkon yabo da kyawawan maganganun da mutane suke yi a kansu. Don haka bai kamata mutum ya rudu da abubuwan da mutane suke fadi (na yabo da kyakkyawar shaida) a kansa ba har ya sanya shi ya gafala daga kyakkyawar hukuncin da ya cancance shi ba. Hakan lamari ne mai muhimmancin gaske musamman ga jami'an gwamnati.
Har ila yau bai kamata mutumin da Allah Madaukakin Sarki ya rufa masa asiri dangane da munanan ayyukansa ya rudu da hakan ba har yayi tsammanin cewa za a ci gaba da rufa masa asiri dangane da munanan ayyukan nasa. Sau nawa Allah Madaukakin Sarki ke tona irin wadannan asirai tun a nan duniya, idan kuma har a rayuwar duniya Allah bai tona su ba saboda tausayi da kyautatawarsa, to a ranar kiyama (wato ranar da zahirin mutane zai fito fili) asiri zai tonu. Don haka ne tsarkakan Imaman Ahlulbaiti (a.s) kamar yadda ya zo cikin addu'ar watan Sha'aban suke rokon Allah da cewa: "Ya Ubangijina kada ka tona ni a ranar kiyama a gaban masu shaida".
Kuma sau nawa mutanen da suke cikin ni'imar Ubangiji suke cikin tarkon istidraji (kama mutum a hankali a hankali), Allah Madaukakin Sarki na cewa: "Za mu yi musu istidraji daga inda ba su sani ba".
Don haka kada yawan yabon mutane da rufin asirin Ubangiji da kyautar ni'imarsa gare mu su sanya mu gafala daga sahihin hukunci kanmu.



.
Copyright © 2018~2022.
( Uzairu Badamasi Sufi )
Harkarmusulunci@yahoo.com
All rights reserved

Bamu Da Alhakin Tallar Da Ake Sawa Akan Wannan Website Din