BARKA DA ZUWA SHAFI MAI ALBARKA
Alhamdulillah muna muku albishir insha Allah zamu dawo aiki gadan gadan!Fadaka Dangane Da Son Wani
Daga cikin wa'azozin Imam Ali bn Husaini (a.s):
وقال له رجلٌ: إنّي لأحبّك في اللّه حبّاً شديداً، فنكس عليه السلام ثمّ قال: الّلهم إنّي أعوذبك أن اُحَبّ فيك وأنت لي مبغض ثمّ قال له: أحبّك للذي تحبّني فيه
Wani mutum yace masa: "Hakika ni ina tsananin sonka saboda Allah", sai Imam Sajjad (a.s) ya sunkuyar da kai sannan yace: "Ya Allah ni ina neman tsarinKa a so ni saboda kai alhalin kana fushi da ni". Sai yace wa mutumin nan: "ina sonka saboda wanda kake so na dominsa"
(Tuhaful-Ukul shafi na 282).
Abin da ke da muhimmanci a lura da shi cikin wannan hadisi kuma darasi ne mai girma gare mu shi ne saurin fadaka dangane da hatsarin dake barazana ga mutum (cikin soyayyar mutane ga mutum saboda Allah). Don haka ne lokacin da wannan mutumi ya bayyana wa Imam Sajjad (a.s) cewa ina sonka saboda Allah, Imam Sajjad bai furta masa cewa na gode ba ko kuma ina gode wa Allah dangane da wannan soyayya ba, amma sai ya amsa masa da cewa: "Ya Allah ina neman tsarinka dangane da soyayyar mutane gare ni saboda da kai, alhali kana fushi da ni" hakan ba karamin hatsari ba ne gare mu. Saboda haka Allah ya kiyaye ya zame mutane suna zaton muna aiki ne domin Allah kuma a kan hanyarSa amma a hakika ba haka lamarin yake ba, wato zahirinmu da badininmu ba daya suke ba, ko kuma Allah yana fushi da mu saboda ayyukanmu. Wato mutane a nasu bangaren suna son mu saboda Allah sai dai Shi kuma Allah yana fushi da mu, Allah Ya kiyaye.