Uzairu badamasi

BARKA DA ZUWA SHAFI MAI ALBARKA

Alhamdulillah muna muku albishir insha Allah zamu dawo aiki gadan gadan!


Shafin farko

Haidar Ali

Abubuwan Da Allah Yake So

Ali khamenei3

Daga cikin wa'azozin Imam Ali bn Husain Al-Sajjad (a.s):

ما من شىءٍ أحبّ إلى اللّه بعد معرفتهمن عفّة بطن وفرج، وما من شىءٍ أحبّ إلى اللّه من أن يسأل

"Babu wani abu da yafi soyuwa a wajen Allah bayan saninSa kamar kamewa ta ciki da farji, kuma babu wani abu da yafi soyuwa a wajen Allah irin a roke Shi".
(Tuhaful-Ukul shafi na 282).
Dalilin da ya sanya Imam Ali Sajjad (a.s) ya bayyana mafi soyuwar abu a wajen Allah bayan saninSa da cewa sai kamewa ta ciki da farji amma bai ambaci sauran ibadu na wajibai ba irin su salla shi ne cewa: kamewa daga sha'awar ciki da farji mataki ne na karya garkuwar abubuwan da suke fitinar da mutum, wanda a kullum rigakafi yafi magani, misalin haka shi ne mutumin da yake cin abinci mai kyau da gina jiki amma a bangare guda kuma sai waa kwayar cuta ta shiga cikin jikinsa, a fili yake cewa wannan kwayar cutar ba za ta yi wani tasiri ba.

A bangaren lamurran da suka shafi ruhi da ma'anawiya kuwa idan mutum ya zamanto mai yawan ibada amma sai aka samu kwayar cuta ta sabo da zunubai ta shiga cikin ruhinsa, to ko shakka babu za ta rage kaifin tasirin ibadunsa. Amma matukar bai bakanta madubin zuciyarsa da zunubi ba, to dabi'ar imaninsa da Allah zata shiryar da shi zuwa ga shiriya da kamala. Don haka barin zunubi shi ne mafi muhimmanci daga aikata ibada. Don haka ne Shaidan yake yawan sanya waswasi da ingiza mutum zuwa ga aikata sabo don ya samu damar hana shi yin ibadu, saboda lokacin da laifi yayi galaba a kan dan'Adam ibadunsa ba za su kusantar da shi ga Allah ba.
Don haka mafi soyuwar ayyuka shi ne barin laifuka biyu, na daya laifin ciki wanda yake da alaka da son duniya, tara dukiya da yawan buri, na biyu kuwa shi ne sha'awar jima'i.



.
Copyright © 2018~2022.
( Uzairu Badamasi Sufi )
Harkarmusulunci@yahoo.com
All rights reserved

Bamu Da Alhakin Tallar Da Ake Sawa Akan Wannan Website Din


XtGem Forum catalog