80s toys - Atari. I still have
Uzairu badamasi

BARKA DA ZUWA SHAFI MAI ALBARKA

Alhamdulillah muna muku albishir insha Allah zamu dawo aiki gadan gadan!


Shafin farko

Haidar Ali

Siffofi Na Musamman Na Hakikanin Aboki

Ali khamenei3

Sharhin hadisin da aka ruwaito daga wajen Imam Ja'afar al-Sadik (amincin Allah ya tabbata a gare shi) wanda Jagoran juyin juya halin Musulunci Ayatullah Sayyid Ali Khamenei ya yi a wajen darasin ‘Darsul Kharij' da ya gabatar a ranar 10, Janairu 2011 (5, Safar 1432):

--------------------------------------------------
"عَنْ أَبِی عَبْدِ اللَّهِ )ع( قَالَ لَا تَكُونُ الصَّدَاقَةُ إِلَّا بِحُدُودِهَا فَمَنْ كَانَتْ فِيهِ هَذِهِ الْحُدُودُ أَوْ شَيْ‏ءٌ مِنْهَا فَانْسُبْهُ إِلَى الصَّدَاقَةِ وَ مَنْ لَمْ يَكُنْ فِيهِ شَيْ‏ءٌ مِنْهَا فَلَا تَنْسُبْهُ إِلَى شَيْ‏ءٍ مِنَ الصَّدَاقَةِ فَأَوَّلُهَا أَنْ تَكُونَ سَرِيرَتُهُ وَ عَلَانِيَتُهُ لَكَ وَاحِدَةً وَ الثَّانِی أَنْ يَرَى زَيْنَكَ زَيْنَهُ وَ شَيْنَكَ شَيْنَهُ وَ الثَّالِثَةُ أَنْ لَا تُغَيِّرَهُ عَلَيْكَ وِلَايَةٌ وَ لَا مَالٌ وَ الرَّابِعَةُ أَنْ لَا يَمْنَعَكَ شَيْئاً تَنَالُهُ مَقْدُرَتُهُ وَ الْخَامِسَةُ وَ هِيَ تَجْمَعُ هَذِهِ الْخِصَالَ أَنْ لَا يُسْلِمَكَ عِنْدَ النَّكَبَات "

شافی، ص 651
Daga Abi Abdillah (a.s.) yana cewa: Abokantaka ba ta kasancewa sai da iyakokinta. Duk (abokantakar) da ta zamanto da irin wadannan kan iyakoki ko kuma wani abu daga cikinsu, to ku dauke ta a matsayin abokantaka. Duk wacce kuwa ta zamanto ba ta da irin wadannan abubuwa, kada ku dauke ta a matsayin abokantaka. Na farko badini da zahirinsa (abokin) su zamanto maka daya. Na biyu ka dinga ganin abin da zai zamanto ado a gare ka a matsayinsa abin ado a gare shi sannan kuma abin da zai bakanta ka a matsayin abin da zai bakanta shi. Na uku kada mulki ko dukiya su sauya shi daga gare ka. Na hudu kada ya hana ka wani abin da karfinsa zai iya aikatawa. Na biyar wacce ta hada dukkanin wadannan siffofi ita ce kada ya barka (kai kadai) yayin wata wahala".

(Al-Shafi, shafi na 651)
Ya zo cikin littafin Al-Shafi daga Imam Sadik (amincin Allah ya tabbata a gare shi) cewa: "Abokantaka ba ta kasancewa sai da iyakokinta". Imam yana cewa ne abokantaka tana da iyakoki wanda idan aka sami wadannan layuka na asali da kuma kan iyakoki, to kuwa wannan abokantaka wacce take da alamu (da wasu nauyi) da yawa na shari'a da ‘yan'uwantaka ta shari'a, to wadannan alamu da za su tabbata a kan wannan abokantakar, idan kuwa ba haka ba, to wadannan abubuwa ba za su tabbata a kan wannan abokantakar ba. "Duk (abokantakar) da ta zamanto da irin wadannan kan iyakoki ko kuma wani abu daga cikinsu, to ku dauke ta a matsayin abokantaka", wato ko da ma a ce ba a sami dukkanin wadannan siffofi da iyakoki ba, to wajibi ne a samu wasu daga cikinsu kafin abokantakar ta tabbata. "Duk wacce kuwa ta zamanto ba ta da irin wadannan abubuwa, kada ku dauke ta a matsayin abokantaka. Na farkonta badini da zahirinsa su zamanto maka daya", wato duk wata abokantakar da ta zamanto ba ta da wadannan iyakoki ko kuma wasu daga cikinta, to kada ku dauke ta a matsayin abokantaka. Na farko shi ne cewa zahiri da kuma badinin (wannan abokin) wajibi ne su zamanto maka abu guda. Wato bai kamata lamarin ya zamanto a zahiri zai nuna maka abokantaka da so da kauna ba, amma a badini ya dinga nuna maka kiyayya da gaba ba. Wannan shi ne sharadi na farko.
"Na biyu ka dinga ganin abin da zai zamanto ado a gare ka a matsayinsa abin ado a gare shi sannan kuma abin da zai bakanta ka a matsayin abin da zai bakanta shi"; na biyu shi ne ya dinga daukan duk wani abin da zai zamanto ado a gare ka tamkar na sa ne; haka nan kuma abin da zai zamanto aibi a gare ka a matsayin abin da zai aibanta shi. (A matsayin misali) idan har ka sami wani matsayi na ilimi, ko kuma ka aikata wani fitaccen aiki mai kyau wanda hakan zai zamanto abin yabo a gare ka, to ya dauki hakan a matsayin abu mai kyau a gare shi da daukansa tamkar shi ne abin ya shafa. Idan kuma abin Allah ya kiyaye, kana da wani abu, kana da wata siffa ko wani aiki wanda zai zamanto aibi a gare ka, to ya dauki hakan a matsayin abin da zai zamanto aibi a gare shi; wanda ko shakka babu akwai wani lamarin da ya zamanto wajibi ya aikata da suka hada da: ya yi kokari wajen ganin ya kawar da hakan, ya yi kokari wajen boye hakan. Bai kamata lamarin ya zamanto cewa yana nan yana jiran dako ne ka aikata wani mummunan abu, shi kenan sai ya yi ta farin ciki saboda hakan. To idan lamarin ya zamanto haka to lalle ba za a kira hakan a matsayin abokantaka ba.
"Na uku kada mulki ko dukiya su sauya shi daga gare ka"; (na uku) shi ne cewa kada yanayinsa ya sauya saboda wani mulki, ko wata hukuma ko wani shugabanci ko kuma wani kudi, ko wata dukiya, da ya samu, kada ya sauya maka. Wasu dai haka suke; su kan yi abokantaka da mutum, amma daga lokacin da suka sami wata dukiya ko wasu kudade ko kuma wata rayuwa mai kyau, shi kenan tamkar ba su san mutum ba. Kai ka ce ba su taba saninsa ba. Lalle mun ga irin wadannan mutane. To lalle bai kamata lamarin ya zamanto haka ba. Kada samun dukiya ko wani mukami ya zamanto ya sauya mutum, kada ya sauya yanayinsa.
"Na hudu kada ya hana ka wani abin da karfinsa zai iya aikatawa", (na hudu shi ne cewa) kada ya yi maka rowan duk wani abin da ya ke da karfin yi maka shi. Wato idan har akwai wata hidima ko wani taimako ko wata shiga tsakani ko wata shawara kai ko wani irin aiki ne zai iya maka da kuma samar maka da wani abin alheri, to lalle kada ya yi maka rowan sa.
"Na biyar wacce ta hada dukkanin wadannan siffofi ita ce kada ya barka (kai kadai) yayin wata wahala"; (na biyar shi ne cewa) a lokacin da kake cikin wata matsala ta rayuwar duniya, lalle kada ya yi watsi da kai. (Idan) har ka fuskanci wata matsala, ko wani ciwo ya kama ka ko ka fada cikin wata wahala ta rayuwa; kai nau'oi daban-daban dai na matsaloli da wahalhalu, - kuna iya ganin hakan dai a wannan zamani na mu; matsaloli na siyasa da tattalin arziki da mutumci da dai sauransu; muna ganin nau'oinsu daban-daban wadanda a baya dai ba ma ganinsu, amma a halin yanzu kan ga su nan muna ganinsu a gabannin idanuwanmu, jarrabawa kala-kala - to bai kamata ya barka kai kadai a irin wannan yanayin ba. Lalle ya kamata ya taimaka maka.



.
Copyright © 2018~2022.
( Uzairu Badamasi Sufi )
Harkarmusulunci@yahoo.com
All rights reserved

Bamu Da Alhakin Tallar Da Ake Sawa Akan Wannan Website Din