BARKA DA ZUWA SHAFI MAI ALBARKA
Alhamdulillah muna muku albishir insha Allah zamu dawo aiki gadan gadan!Abokantaka Da Hidima Maras Gori
Sharhin hadisin da aka ruwaito daga wajen Imam Ja'afar al-Sadik (a.s.) wanda Jagoran juyin juya halin Musulunci Ayatullah Sayyid Ali Khamenei ya yi a wajen darasin ‘Darsul Kharij' da ya gabatar a ranar 21, Disambar 2010 (15, Muharram 1432):
--------------------------------------------------------
"عَنْ أَبِی عَبْدِ اللَّهِ (ع) قَالَ سَمِعْتُهُ يَقُولُ الْمُؤْمِنُونَ خَدَمٌ بَعْضُهُمْ لِبَعْضٍ قُیل وَ كَيْفَ يَكُونُونَ خَدَماً بَعْضُهُمْ لِبَعْضٍ قَالَ يُفِيدُ بَعْضُهُمْ بَعْضاً..." الكافي، ج 2 ص167
"Daga Abi Abdillah (a.s.) yana cewa: Muminai masu hidima wa junansu ne. Sai a ka ce ya ya za su zamanto masu hidima wa junansu. Sai ya ce: Suna amfanar junansu".
(Al-Kafi, juzu'i na 2, shafi na 167)
Ya zo cikin littafin Al-Kafi daga wajen Al-Sadik (amincin Allah ya tabbata a gare shi) yana cewa: Muminai masu hidima wa junansu ne. To wadanda suke wajen dai sun yi mamakin hakan suna masu cewa ta yaya? Dukkanin mutanen masu hidima wa juna ne? Ko kuma a irin kalmomin da aka saba da su a wannan zamanin kowa boyi-boyin dan'uwansa ne (juna) ne? "Sai suka ce: ta ya ya za su zamanto masu hidima wa junansu" wato ta ya ya za a yi wadansu su zamanto masu hidima wa wasu na daban? Wato a matsayin misali (ana nufin) su tafi gidajen junansu su yi wa juna aiki kenan? Sai ya ce: "Suna amfanar junansu" a saboda haka amfanar da wani mumini da zai yi wa wani na daban, yana a matsayin yin hidima ne. Don haka babu wani gori cikin wannan hidimar da mutum zai yi. Wannan shi ne abin da ake son nuni da shi.
Idan har muka yi hidima da kuma amfanar junanmu, shin a fagen da muke tare ne - a matsayin misali a matsayinmu na mutanen gari, a cikin kasuwa da kan tituna, gwargwadon matsayin mu a cikin al'umma ko kuma a fage na daban - ko kuma sauran mutane wadanda suke da wani matsayi mai girma cikin al'umma; a matsayin misali shugaban wata cibiya, to bai kamata mu zamanto masu gori wa sauran mutane ba. A ra'ayina lamari mai muhimmanci da ke cikin wannan hadisin ba wai kawai shi ne cewa wajibi ne mutane su amfanar da junansu ba ne; face dai wajibi ne ya zamanto babu gori cikin irin wannan hidimar da aka yi, don kada mu bata wannan hidimar da muka yi da gori.