Ring ring
Uzairu badamasi

BARKA DA ZUWA SHAFI MAI ALBARKA

Alhamdulillah muna muku albishir insha Allah zamu dawo aiki gadan gadan!


Shafin farko

Haidar Ali

Imani

Ali Khamenei2

Manzon Allah (s.a.w.a) ya
ce:-
ﺛﻼﺙٌ ﻣﻦ ﻛﻦّ ﻓﻴﻪ ﺍﺳﺘﻜﻤﻞ ﺧﺼﺎﻝ
ﺍﻹﻳﻤﺎﻥ: ﺍﻟﺬﻱ ﺇﺫﺍ ﺭﺿﻲ ﻟﻢ ﻳُﺪﺧِﻠﻪ
ﺭﺿﺎﻩ ﻓﻲ ﺑﺎﻃﻞ ﻭﺇﺫﺍ ﻏَﻀِﺐَ ﻟﻢ
ﻳﺨﺮﺟﻪ ﺍﻟﻐﻀﺐ ﻣﻦ ﺍﻟﺤﻖّ ﻭﺇﺫﺍ
ﻗﺪﺭ ﻟﻢ ﻳﺘﻌـﺎﻁ ﻣﺎ ﻟﻴﺲ ﻟﻪ
"Abubuwa uku duk wanda
ya mallake su ya cika siffofin
imani: Wannan da idan ya
amince (da wani),
amincewar ba zata sanya
shi ya afka cikin bata ba,
wanda idan kuma yayi fushi
(to) fushinsa ba zai sanya
shi yayi watsi da gaskiya ba,
wanda idan kuma ya samu
matsayi, ba zai dauki abin
da ba hakkinsa ba".
(Tuhaful-Uqul shafi na 43).
*****
Wannan hadisin ba yana
nufin imani ya takaita kan
wadannan siffofi uku ba ne
kawai, amma abin da yake
nufi shi ne, duk wanda ke
da wadannan halaye, to
alama ce dake bayyana
cewa yana da sauran
halayen imani, domin
kowane daya daga cikin
siffofi uku suna kumshe da
tarin kyawawan siffofi.
Bai kamata kauna da
soyayyar da mutum yake yi
wa wani, ta kai shi ga
afkawa cikin bata da goyon
bayansa kan rashin gaskiya
ba. Haka nan idan mutum
yana fushi da wani ka da
wannan fushin ya sanya shi
ya fice daga da'irar gaskiya.
Wato ka da fushin ya sanya
shi ya hana wanda yake
fushi da shi hakkinsa da ya
cancanta. Kuma idan ya
samu matsayi ka da ya
aikata abin da ba hakkinsa
ba ne.



.
Copyright © 2018~2022.
( Uzairu Badamasi Sufi )
Harkarmusulunci@yahoo.com
All rights reserved

Bamu Da Alhakin Tallar Da Ake Sawa Akan Wannan Website Din