BARKA DA ZUWA SHAFI MAI ALBARKA
Alhamdulillah muna muku albishir insha Allah zamu dawo aiki gadan gadan!Kula Da Hakkokin Muminai
Sharhin hadisin da aka ruwaito daga wajen Imam Ja'afar al-Sadik (amincin Allah ya tabbata a gare shi) wanda Jagoran juyin juya halin Musulunci Ayatullah Sayyid Ali Khamenei ya yi a wajen darasin ‘Darsul Kharij' da ya gabatar a ranar 26, Disambar 2010 (20, Muharram 1432):
--------------------------------------------/
"عَنْ أَبَانِ بْنِ تَغْلِبَ قَالَ كُنْتُ أَطُوفُ مَعَ أَبِی عَبْدِ اللَّهِ (ع) فَعَرَضَ لِی رَجُلٌ مِنْ أَصْحَابِنَا كَانَ سَأَلَنِی الذَّهَابَ مَعَهُ فِی حَاجَةٍ فَأَشَارَ إِلَيَّ فَكَرِهْتُ أَنْ أَدَعَ أَبَا عَبْدِ اللَّهِ ع وَ أَذْهَبَ إِلَيْهِ فَبَيْنَا أَنَا أَطُوفُ إِذْ أَشَارَ إِلَيَّ أَيْضاً فَرَآهُ أَبُو عَبْدِ اللَّهِ ع فَقَالَ يَا أَبَانُ إِيَّاكَ يُرِيدُ هَذَا قُلْتُ نَعَمْ قَالَ فَمَنْ هُوَ قُلْتُ رَجُلٌ مِنْ أَصْحَابِنَا قَالَ هُوَ عَلَى مِثْلِ مَا أَنْتَ عَلَيْهِ قُلْتُ نَعَمْ قَالَ فَاذْهَبْ إِلَيْهِ قُلْتُ فَأَقْطَعُ الطَّوَافَ قَالَ نَعَمْ قُلْتُ وَ إِنْ كَانَ طَوَافَ الْفَرِيضَةِ قَالَ نَعَمْ قَالَ فَذَهَبْتُ مَعَهُ ثُمَّ دَخَلْتُ عَلَيْهِ بَعْدُ فَسَأَلْتُهُ فَقُلْتُ أَخْبِرْنِی عَنْ حَقِّ الْمُؤْمِنِ عَلَى الْمُؤْمِنِ فَقَالَ يَا أَبَانُ دَعْهُ لاَ تَرِدْهُ قُلْتُ بَلَى جُعِلْتُ فِدَاكَ...."
شافی، جلد 1، حدیث 1506
"Daga Abban bn Taglib ya ce: Na kasance wata rana ina dawafi tare da Abi Abdillah (a.s) sai wani mutum daga cikin mutanen mu ya yi min ishara da wata bukatarsa da ya ke son mu tafi tare mu magance ta. Sai na ji ba na son in bar Abu Abdullah (a.s) in tafi tare da shi. A daidai lokacin da na ci gaba da dawafi sai ya sake min ishara, a nan sai Abu Abdullah (a.s) ya gan shi. Saa ya ce min Ya Abban, shin ka san wancan mutumin ne. Sai na ce na'am, sai ya ce wane ne shi, sai na ce daya ne daga cikin mutanenmu. Sai ya ce shin shi din nan yana kan tafarkin da kake kai ne?. Sai na ce na'am. Sai ya ce to ka tafi wajensa. Sai na ce in katse dawafin. Sai ya ce: na'am. Sai na ce ko da dawafi na wajibi ne. Sai ya ce na'am. Sai ya ce sai na tafi tare da shi. Daga baya sai na tafi wajensa na tambaye shi, na ce ka bani labari dangane da hakkin mumini a kan (dan'uwansa) mumini. Sai ya ce Ya Abban, ka bari kawai kar ka sake nanatawa. Sai n ace: Na'am raina ya zamanto fansa a gare ka...
(Shafi, juzu'i na 1, hadisi na 1506)
Ya zo cikin Al-Kafi daga "Daga Abban bn Taglib ya ce: Na kasance wata rana ina dawafi tare da Abi Abdillah (a.s) sai wani mutum daga cikin mutanen mu ya yi min ishara da wata bukatarsa da ya ke son mu tafi tare mu magance ta". Wato Abban bn Tablib yana fadin cewa: daya daga cikin mutanenmu - wato daga cikin 'yan'uwa 'yan Shi'a - ya bukace ni da in taimaka masa wajen tafiya tare da shi don biya masa wata bukatarta.
To a lokacin dai Abban bn Taglib ya kasance yana cikin dawafi ne tare da Abu Abdullah (Imam Sadik) amincin Allah ya tabbata a gare shi. "Sai ya yi min ishara" Sai wannan dan'uwan wanda yake son in tafi tare da shi don biyan wata bukata ta sa ya yi min ishara da in zo alhali kuwa ina cikin dawafi ne. Sai ya ce zuciya ta dai ba ta son in bar Abu Abdillah (amincin Allah ya tabbata a gare shi) in tafi wajensa. Lalle kan wace irin dama da falala ce wannan a ce mutum ya sami damar yin dawafi tare da wani Imami Ma'asumi. Sai ya ci gaba da cewa ina cikin wannan dawafin dai yayin da na zo inda yake sai ya sake min wannan ishara ta in zo mu tafi. A nan kan sai idanuwan Abu Abdillah suka gan shi. Sai ya ce: "Ya Abban, shin ka san wancan mutumin ne min" wato sai ya ce Ya Abban shin wannan mutumin yana da wani aiki da kai ne? Sai ya ce masa na'am sai ya ce wane ne shi? Sai na ce "daya ne daga cikin mutanen mu"; wato daga cikin mu yake, yana daga cikin 'yan Shi'anmu. Sai ya ce: "shin shi din nan yana kan tafarkin da kake kai ne", wato shin yana da irin wannan akidar da kake da ita a babin imamanci? Sai na ce masa na'am. Sai ya ce to shi kenan ka tafi wajensa ka ga abin da yake cewa. Sai na ce masa shin in katse dawafin? Wato ni dai ina cikin wannan yanayi na ibada ne, ina dawafi ne, shin in yanke dawafin? Sai ya ce na'am. A nan ku duba ku gani wannan fakihin - Abban dai fakihi ne - yana so ne ya yi amfani da wannan damar da ya samu wajen tambayar wata mas'ala ta fikihu. Don haka sai ya ce sai na tambaye shi ko da kuwa dawafi ne na farilla, in katse ta in tafi? Sai ya ce masa na'am. Wato ko da kuwa tsakiyar dawafi ne na farilla, idan har wani dan'uwanka yana da wani aiki da kai, yana da wata bukatar da yake son ka biya masa, to wajibi ne ka katse dawafin ka tafi. Sai ya ce "sai na tafi tare da shi", wato sai na yi biyayya, na katse dawafin, na tafi tare da wancan mutumin.
(Sai ya ci gaba da cewa) "To daga baya kuma sai na zo wajensa na tambaye shi", wato daga baya dai bayan ya dawo sai ya tafi wajen Imam yna tambaye shi cewa "ka bani labari dangane da hakkin mumini a kan (dan'uwansa) mumini" wato ya tambayi Imam cewa wane irin hakki ne wannan (da mumini yake da shi a wuyan dan'uwansa) wanda ya ke sanya mutum ya katse dawafinsa na wajibi? Wato ya yi tambaye ne dangane da hakkokin mumini (a kan dan'uwansa mumini). Sai Imam (a.s) ya ce: Ya Abban ka bari kar ka sake (tambaya)" wato ka bari kar ka sake wannan tambayar. Sai na ce masa rai na ya zamanto fansa a gare ka, don me ya sa ba zan yi tambaya ba. Na ci gaba da dagewa dai har sai da Imam (a.s) ya fara fadin hakkokin muminai. Dalilin da ya sanya Imam ya ce masa kada ya sake tambaya, ya bar lamarin haka saboda a lokacin da ka san abu, to kuwa za ka fada cikin matsala, don kuwa dole ne ka aikata shi. Hadisin dai yana da tsawo ba ma so mu kutsa cikinsa. Akwai wani hadisin ma makamancin wannan da aka ruwaito shi daga wajen Mu'alla bn Khanis wanda shi ma ya tambayi Imam Sadik (a.s) hakkokin mumini.
To dangane da bangarori daban-daban na riwayar dai na fadi, sannan dangane da wajiban wannan riwayar kuwa akwai bahasosi da yawa da aka yi. Fadin hakan kuwa yana da muhimmancin ne a gare mu wajen kula da hakkokin muminai.