Ring ring
Uzairu badamasi

BARKA DA ZUWA SHAFI MAI ALBARKA

Alhamdulillah muna muku albishir insha Allah zamu dawo aiki gadan gadan!


Shafin farko

Haidar Ali

Siffofi Tsakanin 'Yan Shi'a

Ali khamenei3

Sharhin hadisin da aka ruwaito daga wajen Imam Muhammad Al-Bakir (amincin Allah ya tabbata a gare shi) wanda Jagoran juyin juya halin Musulunci Ayatullah Sayyid Ali Khamenei ya yi a wajen darasin ‘Darsul Kharij' da ya gabatar a ranar 27, Disambar 2010 (21, Muharram 1432):
------------------------------------------------------

"قَالَ أَبُو جَعْفَرٍ (ع) أَ يَجِي‏ءُ أَحَدُكُمْ إِلَى أَخِيهِ فَيُدْخِلُ يَدَهُ فِی كِيسِهِ فَيَأْخُذُ حَاجَتَهُ فَلا يَدْفَعُهُ فَقُلْتُ مَا أَعْرِفُ ذَلِكَ فِينَا فَقَالَ أَبُو جَعْفَرٍ (ع) فَلاَ شَيْ‏ءَ إِذاً قُلْتُ فَالْهَلاَكُ إِذاً فَقَالَ إِنَّ الْقَوْمَ لَمْ يُعْطَوْا أَحْلَامَهُمْ بَعْد..."

كافى، ج 2، ص 174
Abu Ja'afar (a.s) ya ce: Shin wani daga cikinku zai zo wajen dan'uwansa ya sanya hannunsa cikin jakarsa ya dauki abin da ya ke bukata ba tare da ya hana shi ba. Sai ya ce Lalle ban san hakan ba a tsakaninmu. Sai Abu Ja'afar (a.s) ya ce: A saboda haka babu wani abu kenan. Sai ya ce: Don haka mun halaka kenan. To lalle al'umma ba su kai ga inda ya kama su kai ba kenan....
(Al-Kafi, juzu'i na 2, shafi na 174)
Ya zo cikin Al-Kafi, daga Imam Bakir (amincin Allah ya tabbata a gare shi) yana cewa: Shin wani daga cikinku zai zo wajen dan'uwansa ya sanya hannunsa cikin jakarsa ya dauki abin ya ke bukata ba tare da ya hana shi ba". Wato mai girma Imam Muhammad Al-Bakir (amincin Allah ya tabbata a gare shi) yana tambayar daya daga cikin sahabbansa ne - a gabatarwar ba a ambaci ko waye wannan sahabin ba, kuma wace tambaya ya yi sannan kuma daga ina ya zo ba; babu dukkanin wadannan abubuwa cikin wannan riwayar - cewa shin a inda ka ke haka lamarin yake cewa wani daga cikinku zai zo wajen dan'uwansa na addini ya sanya hannu cikin aljihunsa, ya dauki dukkanin wani abin da ya ke bukata daga aljihun, sannan kuma ba zai yi fushi ba? Shin kun kai wannan matsayi da aljihunku zai zamanto a bude ga kowa?
Marigayi Hazruddeen ya nakalto cewa Sheikh Khidhr a lokacin marigayi Kashif al-Gita' ya kasance daga cikin manyan malamai sannan kuma mutum ne wanda mutane suke girmamawa. Yana fadin cewa a ranar idi, mutanen Najaf da kabilun da suke wajen da sauransu wadanda suke kauna da kuma girmama Sheikh Khidhr su kan zo gidansa da kawo masa kyaututtuka - su kan zo da kudi da zinare - suna gabatar masa da su, haka yake barinsu a gabansa. Daga nan sai Sheikh Ja'afar Kashif al-Gita' ya shigo. A fili yake cewa a wancan lokacin Sheikh Ja'afar bai kai ga matsayin shugabanci ba. Sai ya shigo ya zauna sannan sai idanuwansa suka kai kan wadannan kudade da kuma zinare. A hankali a hankali dai lokacin azahar ya yi, mutane suka watse. Sai Sheikh Ja'far ya tashi ya baza wani bangare na abayarsa, ya kwashe wasu daga cikin wadannan kudade da zinariya da suka zuba a cikin abayar tasa, ya ce sai an jima, ya tafi. Sheikh Khidhir dai ya kale shi amma bai ce komai ba; tamkar dai babu wani abin a zo a gani da ya faru!!
To wannan kissar dai da na nakalto tana da ci gaba, wanda hakan ma ya fi daukan hankali. Ala kulli hal Imam dai yana tambaye ne cewa shin haka kuke dangane da kudaden da kuka mallaka na kashin kanku, wato idan ku na zaune da wani daga cikin abokanku, shin zai iya zuwa ya sanya hannu cikin aljihunku, sannan ya debi abin da yake bukata na kudi daga ciki ya tafi ya bar saura ya kama hanyarsa, kuma ku din nan ba za ku ji wani abu ko kuma ku yi fushi ba? Shin akwai irin wannan yanayin a tattare da ku? Sai ya ce: Ni dai ban san ko akwai hakan ba. Wato shi wannan mai riwayar yana cewa ne lalle ba haka yanayin yake ba a wajenmu. Sai ya ce: Don haka babu wani abu kenan tattare da ku, wato babu wani labari a tattare da ku kenan.
To a nan dai bari in kara wani abu cewa wancan dai lamari ne da ya danganci zamanin Imam Bakir (amincin Allah ya tabbata a gare shi). Saboda a wancan lokacin ana cikin kafa al'ummar ‘yan Shi'a ne a hankali a hankali. Don kuwa bayan waki'ar Ashura, tsawon wadannan shekaru 33 zuwa 34 wanda lokaci ne na Imam Sajjad (amincin Allah ya tabbata a gare shi), a hankali a hankali ne a ke ci gaba da tara al'umma. Bayan wannan waki'a ta Ashura, irin gagarumin abin da aka yi ya sanya 'yan Shi'a warwatsewa; wasu sun koma (inda suka fito), wasu kuma sun ja da baya, wasu kuma sun janye wilayar da suka mika wa Ahlulbaiti, kowane guda dai da hanyar da ya gudu. Tsawon wadannan shekaru 34, a hankali a hankali ne mutane suka fara tattaruwa da dawowa. A zamanin Imam Bakir (amincin Allah ya tabbata a gare shi) ne suka fi taruwa. Saboda haka wancan lamari ne da yake da alaka da wancan lokacin ne da Imam Bakir ya ke cewa haka ya kamata jama'a ta 'yan Shi'a ta kasance a duk fadin duniyar musulmi. Haka ya kamata su zamanto cikin so da kaunar junansu.
A lokacin da Imam ya ce 'Don haka babu wani abu kenan' - wato babu wani labari; wato abin da ya kamata a yi ba a yi shi ba - don haka sai wannan mutumin da ake magana da shi ya ji tsoro; "sai ya ce to don haka mun halaka kenan" to halaka dai a wannan wajen da kuma wajaje da dama ba tana nufin halaka da aka saba da ita ba ce ta mutuwa da lalacewa ba ne; tana nufin shiga cikin mawuyacin yanayi ne. A saboda haka ma'anar kalmar ita ce mun shiga cikin yanayi mai wahala kenan Malam? Shi kenan babu wani abin cewa kenan. Wato har ya zuwa yanzu dai ba mu kai irin wannan matsayi da ake bukata ba. A saboda haka kalmar ba tana nufin halaka da muke fadi na kawuwar abu ba ne, da kuma azabar Allah ba ne; a'a, face dai da ma'anar cewa har ya zuwa yanzu dai ba ku kai matsayin da ake son ku kai ba ne.



.
Copyright © 2018~2022.
( Uzairu Badamasi Sufi )
Harkarmusulunci@yahoo.com
All rights reserved

Bamu Da Alhakin Tallar Da Ake Sawa Akan Wannan Website Din