BARKA DA ZUWA SHAFI MAI ALBARKA
Alhamdulillah muna muku albishir insha Allah zamu dawo aiki gadan gadan!Mizanin Biyayya Cikin Maganganu
Sharhin hadisin da aka ruwaito
daga wajen Imam Muhammad
Al-Bakir (amincin Allah ya
tabbata a gare shi) wanda
Jagoran juyin juya halin
Musulunci Ayatullah Sayyid Ali
Khamenei ya yi a wajen darasin
‘Darsul Kharij' da ya gabatar a
ranar 3, Janairun 2011 (28,
Muharram 1432):
-------------------------------------------------------
" ﻋَﻦْ ﺃَﺑُﻮ ﺟَﻌْﻔَﺮٍ )ﻉ ( ﻳَﺎ ﺻَﺎﻟِﺢُ ﺍﺗَّﺒِﻊْ ﻣَﻦْ
ﻳُﺒْﻜِﻴﻚَ ﻭَ ﻫُﻮَ ﻟَﻚَ ﻧَﺎﺻِﺢٌ ﻭَ ﻟَﺎ ﺗَﺘَّﺒِﻊْ ﻣَﻦْ
ﻳُﻀْﺤِﻜُﻚَ ﻭَ ﻫُﻮَ ﻟَﻚَ ﻏَﺎﺵٌّ ﻭَ ﺳَﺘَﺮِﺩُﻭﻥَ
ﻋَﻠَﻰ ﺍﻟﻠَّﻪِ ﺟَﻤِﻴﻌﺎً ﻓَﺘَﻌْﻠَﻤُﻮﻥ "ﻛﺎﻓﻰ، ﺝ ،2
ﺹ 683
Daga Abu Ja'afar (a.s.) yana
cewa Ya Saleh ka bi (ka yarda
da) wanda ya ke sanya ka kuka
saboda zai zamanto mai nasiha
a gare ka, kada ka bi wanda ya
ke sanya ka dariya, don zai
zamanto maka mai yaudara ne.
Ga Allah za ku koma gaba
dayanku, sannan za ku sani".
(Al-Kafi, juzu'i na 2, shafi na 683)
Ya zo cikin Al-Kafi da Al-Tahzib
daga Imam Bakir (amincin Allah
ya tabbata a gare shi): mai
girma Imam Muhammad Bakir
amincin Allah ya tabbata a gare
shi yana cewa: Ka bi wanda
yake sanya ka kuka, saboda zai
zamanto mai nasiha a gare ka".
Wato wannan mutumin da ya ke
gaya maka maganganu masu
daci wadanda za su sanya ka
kuka, to shi din nan mutum ne
mai maka fatan alheri; ka yarda
da maganarsa. A nan kalmar ‘ka
bi' tana nufin ka saurare shi, ka
yarda da shi; ko da kuwa
magana ce mai daci da sosa rai,
to amma duk da haka dai lamari
ne da zai amfane ka.
Sannan kuma ya ci gaba da
cewa: "Ka da ka bi wanda ya ke
sanya ka dariya, don shi mai
yaudararka ne", wato kada ka
saurara da kuma bin maganar
mutumin da ya ke gaya maka
maganganu masu dadi, don ka
ji dadi da kuma sanya ka bude
bakinka da yin murmushi; to sai
dai shi din nan mai yaudara ne,
mai yaudararka ne, babu alheri
cikin hakan. Yana maka hakan
ne cikin bakin zuciya da
mummunan fata, to amma duk
da haka yana gaya maka abin
da zai faranta maka rai. Lalle ka
nesanci wannan mutumin. "Lalle
za ku koma zuwa ga Allah gaba
dayanku, sannan za ku sani; a
lokacin da kuka koma ga Allah
Madaukakin Sarki, za ku fahimci
abubuwan da suke cikin
zukatan juna.