BARKA DA ZUWA SHAFI MAI ALBARKA
Alhamdulillah muna muku albishir insha Allah zamu dawo aiki gadan gadan!Siffar Aboki Na Imani
Sharhin hadisin da aka ruwaito
daga wajen Imam Ja'afar al-
Sadik (amincin Allah ya tabbata
a gare shi) wanda Jagoran juyin
juya halin Musulunci AyatSayyid Ali Khamenei ya yi a
wajen darasin ‘Darsul Kharij' da
ya gabatar a ranar 11, Janairu
2011 (5, Safar 1432):
--------------------------------------------------------
" ﻗَﺎﻝَ ﺃَﺑُﻮ ﻋَﺒْﺪِ ﺍﻟﻠَّﻪِ )ﻉ ( ﺍﺧْﺘَﺒِﺮُﻭﺍ ﺇِﺧْﻮَﺍﻧَﻜُﻢْ
ﺑِﺨَﺼْﻠَﺘَﻴْﻦِ ﻓَﺈِﻥْ ﻛَﺎﻧَﺘَﺎ ﻓِﻴﻬِﻢْ ﻭَ ﺇِﻟَّﺎ ﻓَﺎﻋْﺰُﺏْ ﺛُﻢَّ
ﺍﻋْﺰُﺏْ ﺛُﻢَّ ﺍﻋْﺰُﺏْ ﻣُﺤَﺎﻓَﻈَﺔٍ ﻋَﻠَﻰ ﺍﻟﺼَّﻠَﻮَﺍﺕِ
ﻓِﯽ ﻣَﻮَﺍﻗِﻴﺘِﻬَﺎ ﻭَ ﺍﻟْﺒِﺮِّ ﺑِﺎﻟْﺈِﺧْﻮَﺍﻥِ ﻓِﯽ ﺍﻟْﻌُﺴْﺮِ
ﻭَ ﺍﻟْﻴُﺴْﺮ"
ﺷﺎﻓﯽ، ﺻﻔﺤﻪﻯ 652
"Abu Abdillah (a.s) yana cewa:
Ku gwada 'yan'uwanku da
siffofi biyu, idan har sun
kasance tare da su, (shi kenan)
idan kuwa ba haka ba, ku
nesance su, ku nesance su
sannan ku nesance su, (su ne
kuwa): kiyaye salla a kan
lokacinta da kuma kasantuwa
tare da 'yan'uwa cikin tsanani
ne ko kuma cikin jin dadi".
(Shafi, shafi na 652)
Ya zo cikin Al-Kafi, daga wajen
Imam Sadik (a.s) yana cewa: "Ku
jarraba 'yan'uwanku da siffofi
biyu". A nan 'yan'uwan da aka
ce ba wai kawai ana nufi
wadanda kuke tare da kuma
rayuwa tare da su ba ne. Wato
mutanen da ka ke son ka dauke
su a matsayin 'yan'uwanku da
kuma wadanda za su zamanto
abokanku, na kurkusa da ku,
wato wadanda kuke son ku
zaba da kuma wannan matsayi,
to wajibi su zamanto suna da
wadannan siffofi guda biyu,
"Idan har suna da wadannan
siffofi guda biyu", wato idan har
suna da wadannan siffofi guda
biyu to lamarin ya fi kyau. "Idan
kuwa ba haka ba, to a nesance
su, kuma a nesance su, kuma a
nesance su". Kamar yadda ya zo
ne cikin Alkur'ani "Gwargwadon
zarra ba ta nisanta daga gare
Shi" (Suratus Saba 34:3). Ku
nesance su.
Mene ne wadannan siffofi guda
biyun: " kiyaye salla a kan
lokacinta". Siffar farko ita ce su
kasance masu kiyaye salla a kan
lokacinta. Ko shakka babu ana
nufin lokacinta na fadhila ne. In
kuwa ba haka ba, idan har aka
ce sakakken lokacinta kawai, to
har karshen lokacinta ma ai
lokaci ne, idan har mutum bai yi
haka ba (wato bai yi salla ba har
sai da lokacinta ya fita), a
wannan lokacin kan ya zamanto
fasiki. Yana so ne ya ce masu
salla cikin lokacinta na fadhila.
Marigayi Ayatullah Bahjat
(yardar Allah ta tabbata a gare
shi) wanda a lokuta da dama
mun sha jin wannan lamari
daga bakinsa. Ni kai na na sha ji
sannan kuma wadansu ma sun
nakalto min - ya kan ce
malaminsu - daga dukkan alamu
yana nufin marigayi Aghaye
Kadhi ne a matsayin misali - ya
gaya masa cewa idan har wani
ya kiyaye salla cikin lokacinta, to
lalle zan zamanto lamuni wajen
ceto shi ko kuma a matsayin
lamuni dangane da samun
madaukakin matsayi; wata
magana dai makamanciyar
hakan. Ni din nan a wani lokaci
na taba tambayarsa cewa
wajibi ne sallar ta zamanto da
kyau kan ko? sai ya ce: Na'am, e
haka ne, salla wacce ta dace
tare kuma da kula da Ubangiji,
sannan kuma a farkon lokacinta.
Idan har mutum ya kiyaye
hakan, to hakan wani lamari ne
da ke daukaka mutum da kuma
kai shi zuwa ga matsayi na koli
na tauhidi. Wannan ita ce siffa
ta farko.
"Kasantuwa tare da 'yan'uwa
cikin tsanani ne ko kuma cikin
jin dadi ". Siffa ta biyu wata siffa
ce ta zamantakewa. Siffa ta
farko siffa ce ta daidaiku,
tsakanin mutum ne da
Ubangijinsa; amma wannan ta
biyun tsakaninsa ne da sauran
mutane. Mutumin da siffarsa za
ta kasance mai taimakon
'yan'uwansa, shin cikin tsanani
ne ko kuma cikin yalwa. To
wannan tsanani da kuma yalwa
(dai tana iya daukan yanayi
biyu), shin shi kansa wanda za a
taimaka masa din ne ya ke cikin
tsanani da yalwa ko da kuma
yana cikin tsananin ne, yana
cikin wahala, to zai taimaka
masa. A matsayin misali yana
cikin talauci ne, ba shi da kudi,
zai taimaka masa. Ko dai zai iya
saukaka masa, ya taimaka masa
da harshensa, ya taimaka masa
ta hanyar kare mutumcinsa;
sannan kuma mai yiyuwa ne
abin nufi da tsanani da yalwa
din shi ne na mai taimakawan
ne, wato shin shi ma mai
taimakon yana cikin yalwa ne ko
kuma kumci. Don kuwa akwai
wadansu mutane da suke a
shirye su taimaka wa mutum, a
lokacin da yake cikin yanayi mai
kyau; a lokacin da idanuwa suka
koma kan mutum, a shirye suke
su taimaka masa, lalle za su
taimaka masa. Amma daga
lokacin da dukkanin idanuwa
suka janye daga gare shi, to su
ma sai su juya masa baya.
Wadansu daga lokacin da
duniya ta juya wa mutum baya
su ma sai su juya masa bayan.
A'a, ba haka lamarin ya kamata
ya kasance ba. Cikin kowane irin
hali da yanayi a taimaka wa
mutum.