BARKA DA ZUWA SHAFI MAI ALBARKA
Alhamdulillah muna muku albishir insha Allah zamu dawo aiki gadan gadan!Hanyoyin Hana Samun Ikon Shaidan
Sharhin hadisin da aka ruwaito
daga wajen Imam Ja'afar al-
Sadik (amincin Allah ya tabbata
a gare shi) wanda Jagoran juyin
juya halin Musulunci Ayatullah
Sayyid Ali Khamenei ya yi a
wajen darasin ‘Darsul Kharij' da
ya gabatar a ranar 16, Janairun
2011 (11, Safar 1432):
-------------------------------------------------
«ﻗَﺎﻝَ ﺍﻟﺼَّﺎﺩِﻕُ ﺟَﻌْﻔَﺮُ ﺑْﻦُ ﻣُﺤَﻤَّﺪٍ ﻉ ﻣَﻦْ
ﻟَﻢْ ﻳَﻜُﻦْ ﻟَﻪُ ﻭَﺍﻋِﻆٌ ﻣِﻦْ ﻗَﻠْﺒِﻪِ ﻭَ ﺯَﺍﺟِﺮٌ ﻣِﻦْ
ﻧَﻔْﺴِﻪِ ﻭَ ﻟَﻢْ ﻳَﻜُﻦْ ﻟَﻪُ ﻗَﺮِﻳﻦٌ ﻣُﺮْﺷِﺪٌ
ﺍﺳْﺘَﻤْﻜَﻦَ ﻋَﺪُﻭَّﻩُ ﻣِﻦْ ﻋُﻨُﻘِﻪ «
ﺷﺎﻓﯽ، ﺻﻔﺤﻪ 652
Imam Sadik Ja'afar bn
Muhammad (a.s) yana cewa:
Duk wanda ba shi da mai yi
masa wa'azi daga cikin
zuciyarsa da kuma mai
tsawatarwa daga shi kansa
sannan kuma ya zamanto ba shi
da wani na kusa da shi da zai
shiryar da shi, to kuwa ya ba wa
makiyinsa dama a kansa".
(Al-Shafi, shafi na 652)
Daga Sadik (amincin Allah ya
tabbata a gare shi), wato Imam
Ja'afar Sadik amincin Allah ya
tabbata a gare shi yana cewa:
"Duk wanda ba shi da mai yi
masa wa'azi daga cikin
zuciyarsa da kuma mai ba shi
umurni daga shi kansa sannan
kuma ya zamanto ba shi da
wani na kusa da shi da zai
shiryar da shi, to kuwa ya ba wa
makiyinsa dama a kansa". Abu
na farko da zai ba wa mutum
karfin tsayin daka a gaban a
gaban abokin gabansa - wanda
a nan ana nufin Shaidan ne - da
kuma hana shi samun iko a
kansa, shi ne cewa: ya sami ‘mai
masa wa'azi daga cikin
zuciyarsa", wato ya dinga yi wa
kansa wa'azi daga cikin
zuciyarsa. Duk wata zuciyar da
take a farke kuma mai ambaton
Allah, za ta dinga yi wa mutum
nasiha, za ta dinga yi masa
wa'azi. Daya daga cikin mafi
kyawun hanyoyi da mutum zai
bi wajen tilasta wa zuciyarsa ta
zamanto mai masa wa'azi ita ce
ta hanyar wadannan addu'oi,
addu'oin da aka ruwaito su
daga wajen Imamai - wadanda
suke cikin Sahifatus Sajjadiya da
sauran addu'oin - haka nan
kuma tashin asuba; wadannan
abubuwa su kan zamanto masu
nasiha da wa'azi ga zuciyar
mutum. A saboda haka abu na
farko shi ne ‘mai wa'azi daga
zuciya".
(Abu na biyu kuma shi ne): "mai
tsawatarwa daga cikinsa", wato
ya zamanto yana da wani mai
tsawatarwa a tattare da shi,
mai hana shi (mummunan abu),
mai ja masa kunne. Idan har ya
rasa wadannan abubuwa guda
biyu "sannan kuma ya zamanto
ba shi da wani na kusa da shi
da zai shiryar da shi", wato ya
rasa wani aboki, wani na
kurkusa wanda zai dinga
shiryar da shi, ya taimaka masa,
ya dinga nuna masa hanya -
wanda hakan shi ne abu na uku
- wato idan mutum ya rasa abin
da zai dinga shiryar da shi da
sanya ido kan ayyukansa, (to
lalle akwai matsala). Wajibi ne
ya sami wani aboki, kamar
yadda aka fadi cewa: "Wanda
ganinsa ya kan tuna muku da
Allah". Idan har bai sami hakan
ba "to kuwa ya ba wa makiyinsa
dama a kansa", to ya mika
kansa ne ga abokin gabansa; ya
ba wa abokin gabansa wani
karfi ne da zai sami damar
amfani da shi wajen juya shi
yadda yake so. Wanda abin nufi
da abokin gaba a nan shi ne
Shaidan. Lalle wadannan
abubuwa ne da wajibi ne a
samar da su. Mutum ya sami mai
yi masa nasiha daga cikinsa.
Mafi kyawun wanda zai yi wa
mutum nasiha, shi ne shi kansa
mutum din; don kuwa mutum ba
zai yi korafi wa kansa ba. Duk
wani mutumin da zai yi wa wani
mutum nasiha, idan har ya dan
tsananta, to kuwa wannan
mutumin zai yi korafi. To amma
idan har shi kansa mutum din
ne ya yi wa kansa nasiha; ya ja
kunnen kansa da kansa, ya
zargi kansa da kansa, to
wannan lamari ne mai tasirin
gaske. Mutum ya yi wa'azi da
tsawatar da kansa. Idan kuwa
har mutum bai sami hakan ba,
to mutum ya nemi wani aboki
ko dan'uwansa ya rike shi
hannu bibbiyu (wato ya
zamanto mai shiryar da shi).