BARKA DA ZUWA SHAFI MAI ALBARKA
Alhamdulillah muna muku albishir insha Allah zamu dawo aiki gadan gadan!Kiyaye Aboki da Ladar Hakan
Sharhin hadisin da aka ruwaito
daga wajen Imam Ja'afar al-
Sadik (amincin Allah ya tabbata
a gare shi) wanda Jagoran juyin
juya halin Musulunci Ayatullah
Sayyid Ali Khamenei ya yi a
wajen darasin ‘Darsul Kharij' da
ya gabatar a ranar 17, Janairun
2011 (12, Safar 1432):
--------------------------------------------/
ﺍﻻﻭﻝ: » ﻋَﻦْ ﺃَﺑِﯽ ﻋَﺒْﺪِ ﺍﻟﻠَّﻪِ ﻉ ﻗَﺎﻝَ ﺇِﻥَّ ﺍﻟﻠَّﻪَ
ﺗَﻌﺎﻟﯽ ﻟَﻴَﺤْﻔَﻆُ ﻣَﻦْ ﻳَﺤْﻔَﻆُ ﺻَﺪِﻳﻘَﻪ
ﺍﻟﺜﺎﻧﯽ: »ﻗَﺎﻝَ ﺃَﺑُﻮ ﻋَﺒْﺪِ ﺍﻟﻠَّﻪِ ﻉ ﻟَﺎ ﺗُﻔَﺘِّﺶِ
ﺍﻟﻨَّﺎﺱَ ﻓَﺘَﺒْﻘَﻰ ﺑِﻠَﺎ ﺻَﺪِﻳﻖ
ﺷﺎﻓﯽ، ﺻﻔﺤﻪ 65
Riwayar Farko: "Daga Abi
Abdillah (a.s) yana cewa: Hakika
Allah Madaukakin Sarki zai kare
wanda ya kare abokinsa"
Riwaya Ta Biyu: Abu Abdillah
(a.s) yana cewa: Kada ka dinga
binciken mutane don sai ka rasa
aboki".
(Al-Shafi, shafi na 65)
Gajerun Riwayoyi Guda Biyu:
Ya zo cikin Al-Kafi, daga Imam
Sadik (amincin Allah ya tabbata
a gare shi) yana cewa: "Daga
Abi Abdillah (a.s) yana cewa:
Hakika Allah Madaukakin Sarki
zai kare wanda ya kare
abokinsa". Wato Imam Sadik
amincin allah ya tabbata a gare
shi yana cewa: Allah
Madaukakin Sarki zai kare
mutumin da ya kare abokinsa.
Ko da yake abin da ake nufi ba
wai shi ne kawai kariya ta jiki
ba - duk da cewa hakan yana
iya zama daya daga cikin
misdakin hakan - wato ya kiyaye
masa mutumcinsa, ya kiyaye
masa matsayin da yake da shi,
ya kiyaye masa matsayar da ya
dauka da kuma kula da hakan.
To kuwa Allah Madaukakin Sarki
zai kare irin wannan mutumin. A
Musulunci dai haka irin wannan
'yan'uwantaka da abokantaka
suke da irin wannan
muhimmanci. Idan har kuka kula
da abokinku, kuka kiyaye shi, to
kuwa Allah Madaukakin Sarki zai
ba ku ladar hakan, wanda shi
ne zai kiyaye ku. To sai dai yana
da kyau a fahimci cewa kiyaye
aboki ba yana nufin mutum ya
dinga kare zunubin da kuma
kura-kuran da ya aikata ba ne;
kamar yadda hakan yake
faruwa cikin ayyuka na
kungiyanci da jam'iyya da kuma
tafarki ta yadda wajibi ne a
kare irin kura-kuran da mutum
ya yi saboda suna cikin jam'iyya
guda ne ko kungiya guda. A'a
wannan ba shi ne abin da ake
nufi ba. Hakan ba kiyaye mutum
ba ne; hakan alal hakika
ha'intar sa ne, sannan da sa shi
cikin matsala ne. Face dai abin
nufi a nan shi ne kiyaye
mutumcin mumini wanda yake a
matsayin dan'uwan mutum na
imani. Wannan ita ce riwaya ta
farko.
Daya riwayar kuma wacce ita
ma daga Al-Kafi din ne, an
ruwaito ne daga wajen Imam
Sadik (a.s) tana cewa ne: "Kada
ka dinga binciken mutane don
sai ka rasa aboki", wato kada ku
dinga bincike da sanya ido kan
ayyukan mutane, kada ku dinga
neman sanin abin da ke
gudana. Kada ku zamanto masu
neman ganin kura-kuran
mutane da aibinsu. Idan har
hakan ta faru, to za ku zamanto
marasa abokai. Kowane mutum
dai yana da nasa aibin. Don
haka idan har kuka zamanto
masu binciken ayyukan da
mutane suke yi to za ku
zamanto ku kadai ba tare da
abokai ba.