BARKA DA ZUWA SHAFI MAI ALBARKA
Alhamdulillah muna muku albishir insha Allah zamu dawo aiki gadan gadan!
Shimfida: Abin da ke biye
fassarar jawabin da Jagoran
juyin juya halin Musulunci
Ayatullah Sayyid Ali Khamenei ya
yi ne a wajen darasin 'Darsul
Kharij' inda ya yi sharhi kan
wasu hadisai guda uku da suka
yi magana kan kyawawan
halaye:
Da Sunan Allah Mai Rahama Mai
Jin Kai
Dukkan godiya ta tabbata ga
Allah Ubangijin talikai. Tsira da
amincin Allah su tabbata ga
shugabanmu Muhammad tare
da tsarkakan Alayensa; sannan
la'anar Allah ta tabbata ga
makiyansu gaba daya.
(A nan dai Jagora ya yi karin
haske ne dangane da isnadin
wadannan hadisai da kuma
inda aka ciro su, wanda mu na
ganin babu bukatar kawo su a
nan. Don haka za mu fara ne
daga inda ya fara bayani kan
hadisan)
To; zan fara magana kan
wadannan riwayoyi guda uku
ne da wannan gabatarwar da
zan yi, don hakan ya zamanto
mana abin lura insha Allahu. A
nan marigayi Al-Majlisi ya
nakalto wadansu riwayoyi cikin
littafin 'Al-Nawadir' wanda ni a
yau zan kawo uku daga cikinsu
a matsayin share fagen darasin
da zan gabatar. Daya daga cikin
wadannan riwayoyi ita ce
riwayar da take cewa: "Manzon
Allah, tsira da amincin Allah su
tabbata a gare shi da Alayensa
yana cewa: Wadanda suka riga
shiga inuwar al'arshi, sun sami
babbar rabo", wato sun ji
dadinsu mutanen da suka samu
nasarar zama ‘yan gaba-gaba
wajen zama a karkashin inuwar
al'arshin (Ubangiji). Saboda
al'arshin Ubangiji wani al'amari
ne na ruhi da ke nuni da
matsayi mai girma da daukaka
ta Allah Madaukakin Sarki. To a
nan ma'anar 'rigayya zuwa ga
al'arshi' tana nuni da irin
matsayi mai girma da bawa zai
sami a wajen Ubangijinsa. Mafi
girman abin da bawa zai yi
tunaninsa shi ne mutum ya sami
damar fakewa karkashin
al'arshin Ubangiji Madaukakin
Sarki. "Sai aka ce: Ya Manzon
Allah, su wane ne wadannan?"
wato wadansu mutane ne za su
zamanto a kan gaba wajen
shiga inuwar al'arshin Mai
rahama? "Sai ya ce: Su ne
wadanda suke yarda da gaskiya
idan suka ji ta". Wato su ne
mutanen da suke da wadannan
siffofi: Na farko shi ne a lokacin
da suka ji gaskiya, to za su
karbe ta, "Sannan kuma za su
fade ta idan aka tambaye su",
wani bangare na lamarin shi ne
cewa a lokacin da aka tambaye
su cewa 'mece ce gaskiya?" ba
tare da la'akari da wani abu ba
za su yi bayaninta, za su gabatar
da gaskiyar. Ku dubi wadannan
kalmomi guda biyu da kyau,
idan da a ce za a sami tabbatar
da wadannan abubuwa guda
biyu a wannan duniya ta mu ta
yau da ta nutse cikin fasadi -
wanda ko shakka babu akwai
kwakwala da zukata da lamirai
da hankula da za su iya fahimtar
wannan hakikar da kuma
gaskiya -, to ya ya duniyar za ta
kasance!
Mece ce gaskiya? Gaskiya ita ce
abin da aka gina halitta a kanta.
"Ba mu halitta su ba face da
manufa ta gaskiya" (Suratud
Dukhan 44:39). Gaskiya ita ce
tushen halittar Ubangiji; wato
ita ce dai wannan abin da ya
zama wajibi a samar da shi
sannan kuma wanda dukkanin
kokarin da masu kokari na
duniya tsawon tarihi suka yi
kokarinsu wajen isa gare shi. A
saboda haka gaskiya lamari ne
mai matukar muhimmancin
gaske. Ita ce dai wannan abin
da idan har aka fahimce shi
sannan kuma aka bi shi, to
kuwa ba za a sake ganin wani
abin ki da abin da ba a son
ganinsa a duniya ba.
Gwargwadon yadda (gaskiya) ta
tabbata, gwargwadon yadda
lamarin zai kasance. Shin
wannan karamin abu ne?! To
akwai wadansu mutane dai a
wannan duniyar wacce ta nutse
cikin fasadi wadanda suka
fahimci dukkanin hakan ko
kuma wani layi nasa ko kuma
kalma tasa. To idan har
wadannan mutane suka yarda
da hakan (abin da suka
fahimtar) sannan kuma suka yi
bayaninsa ga mutanen da suke
bukata, ku duba ku ga irin
abubuwan da za su faru a
duniya sannan kuma wani irin
gagarumin sauyi ne zai faru
cikin rayuwar bil'adama da
kuma duniya.
To sai dai bala'in yana cikin
cewa ne soyace-soyacen zuciya
ta dan'adam da kuma irin
sarkokin da aka sanya su a
wuyan dan'adam - "Wadanda
akwai kukumai a cikin
wuyoyinsu (Suratur Ra'ad 13:5) -
hakan ba zai ba su damar su
fahimci gaskiya ba sannan
kuma idan ma sun fahimce ta su
yarda da ita, sannan kuma idan
su yarda din su gaya wa
mutanen da suke bukatarta ba.
A nan ne matsalar take. Idan
har hakan ta faru, to ku duba ku
ga irin gagarumin abin da zai
faru mana. Alal hakika akwai
bukatar a fadi cewa: "Wadanda
suka riga shiga inuwar al'arshi"
don kuwa aiki ne mai wahala.
Kada ku yi nisa sosai. Ko da
yake, gaskiya a mizani na
duniya, tana da wadanda suka
santa da masu yada ta da masu
kokarin hana wanzuwarta da
wadanda suke rowanta da
masu kore ta da masu kafirce
mata da kuma masu boye ta. A
bisa mahangar al'ummar da
muke rayuwa a cikinta, tana da
wasu nauyi da alamu da
abubuwan da suke nuni da ita,
sannan kuma a dan tsukekken
wajen da mu ke rayuwa ma
tana da wasu alamu da
abubuwan da suke nuni da ita
da kuma wasu siffofi. Dukkanin
wadannan abubuwa suna da
muhimmanci. Bai kamata a ce
wane mai boye gaskiya ne ba,
saboda a matsayin misali ya
kasance mai inkarin gaskiyar
annabci ko gaskiyar tauhidi ko
kuma gaskiyar magana kaza a
fage na duniya ba, don haka
la'ananne ne. To amma ni din
nan da hakika ta bayyana min
sannan kuma take hannuna da
kuma wajen da nake rayuwa
amma sai na yi inkarinta da
kuma boye ta sannan kuma ba
na ma kare ta, sannan kuma
idan ma an gabatar min da ita
ba zan amince ba, to ba na cikin
wancan hukumcin. Hakan ba
abu ne abin yarda da shi ba. A
saboda haka "Wadanda suke
yarda da gaskiya idan suka ji
sannan kuma su yi bayaninta
idan aka tambaye su" ta hada
da kowa, a duk inda yake a
duniya.
Sannan kuma "suna wa mutane
hukumci tamkar hukumcin da
suke yi wa kawukansu". To
wannan ma daya ne daga cikin
alamun gaskiya wacce take da
wahalar gaske. A wajen wasu
mutane wasu daga cikin
gaskiyar ba wani lamari ne mai
bakanta rai sosai ba, face ma
dai abin faranta rai ne a wajen
ma'abota gaskiya. To amma
gaskiyar da take zama mai
wahala da sosa rai ga kowa, ita
ce gaskiyar da idan har wani
mutum ya yi aiki da ita, to lalle
ya bayar da jarabawa mai
kyaun gaske.
"Suna wa mutane hukumci
tamkar hukumcin da suke yi wa
kawukansu" wato suna hukumci
wa mutane kamar yadda suke yi
wa kansu, babu wani bambanci
tsakaninsu da sauran mutane.
Wannan tana daga cikin
gaskiyar da take da wahalar
gaske. Don kuwa mu din nan
daliban addini da malaman
addini na Shi'a albarkacin tsarin
Jamhuriyar Musulunci sannan
kuma kafin ma a tsayar da
wannan tsari na Jamhuriyar
Musulunci, tsawon tarihin ilimin
fikihun shi'anci sannan kuma
sakamakon irin kokari da
abubuwan da suka faru cikin
tarihi mun kasance a yanayi mai
kyau wajen tabbatar da gaskiya
da kuma fada da karya. A halina
yanzu ma sakamakon kafa
Jamhuriyar Musulunci da kuma
wannan gwamnati mai albarka
ta Ubangiji da kuma Alkur'ani,
alhamdu lillahi lamarin ma ya
karu ne. A saboda haka wannan
hadisin yana da muhimmanci a
gare mu sannan kuma akwai
darussa da yawa a cikinsa a
gare mu.
Ya kamata ku dinga tunawa
sannan kuma bai kamata
malamai da daliban addini su
mance da wadannan kalmomi
guda uku ba. A duk inda suka ga
gaskiya, su yarda da ita, ko da
yake bisa ingantacciyar fahimta.
Wato abin da suka fahimce shi
tsakaninsu da Allah ba tare da
wani bangaranci da kuma son
zuciya ba a matsayin gaskiya. A
duk inda aka tambaye su
sannan kuma aka bukace su da
su yi bayaninsa, to lalle su yi
bayanin. Batu na uku kuma,
wanda kuma ana iya cewa daya
ne daga cikin mafiya wahala da
bayyana cikin lamari na biyu
(wato za su fadi gaskiya idan
aka tambaye su) ko kuma na
farko (wato wadanda suke
yarda da gaskiya idan suka ji
ta), shi ne cewa a yayin
hukumci, su sanya kansu su a
matsayi guda da sauran
mutane. Duk wani irin hukumcin
da ya yi wa mutane - ko dai
wanda ya yi daidai da abin da
suke so ko kuma akasin hakan -
to haka ya kamata ya aikata a
kansa.
Hadisi na gaba (na biyu), shi ma
dai da wannan isnadin ne
"daga Ali, amincin Allah ya
tabbata a gare shi, yana cewa:
An ce wa Manzon Allah (tsira da
amincin Allah su tabbata a gare
shi da Alayensa) cewa: mene ne
yake nesantar da shaidan daga
gare mu". Wato wani abu ne
yake iya nesantar da Shaidan
daga gare mu? Ko da yake kun
san cewa Shaidan dai ya hada
har da Ibilis. Su kansu
wadannan masu karfi da suke
da tasiri da kawo sharri da
fasadi da kawar da mutane
daga kan tafarki madaidaici
wadanda (a wani lokaci) suke
bayyana cikin tufafi daban-
daban, a wani lokaci cikin tufafi
na mutum, a wani lokaci kuma
cikin tufafin da ba na mutane
ba, a wani lokaci kuma cikin
soyace-soyacen zuciya a wani
lokaci kuma a shakali na Ibilis.
Ibilisai dai wasu gungu ne na
shaidanu wadanda akwai kissar
su cikin Alkur'ani mai girma. To
sai dai ba su ne kawai ba. Su din
nan shaidanu ne na aljannu
haka nan kuma cikin mutane
wadanda a wani lokacin
hatsarin da suke da shi bai gaza
na wadancan ba. A saboda
haka Shaidan wata ma'ana ce
ta gaba daya. To wasu
abubuwa ne suke nesantar da
su daga gare mu? "Sai ya ce:
Azumi saboda Allah yana
bakanta fuskarsa". Dalilin hakan
kuwa shi ne cewa azumi ya kan
ruguza irin wannan girman kai
da take tattare da mutum
wanda ya ke batar da mutum
da kuma kawo karshen irin
wannan girman kan. "Sannan
sadaka kuma tana karya
(gadon) bayansa" don kuwa ita
sadaka wani lamari ne da ke
nuni da kawar da idon mutum
da kuma rufe ido kan
abubuwan da ya mallaka.
Wannan ma lamari ne mai
muhimmanci: "Sannan soyayya
saboda Allah Madaukakin Sarki
da kuma kula da ayyuka na
kwarai suna tumbuke
tushensa". Wadannan abubuwa
guda biyu su ne mafiya
muhimmancinsu. Na farko shi ne
'So saboda Allah. Wato mutum
mai tausayi, ya zamanto mai
juyar da so da kaunarsa zuwa
ga bangare na Ubangiji. Idan
har kuna son wani mutum ne, to
wajibi ne wannan soyayya ta
zamanto saboda Allah, ba wai
saboda duniya ba. Ku sanya
soyayyarku ta zamanto saboda
Allah ne. Ko da yake riwayar nan
ta "Soyayya saboda Allah da
kuma kiyayya saboda Allah"
riwaya ce mai fadin gaske. A
cikin littafin Al-Kafi da sauran
littafa akwai cikakken babi
dangane da wannan siffar.
"Da kuma kula da ayyuka na
kwarai". Abin da yake da
muhimmanci shi ne cewa
mutum ya kula da ayyuka na
kwarai. Wato ci gaba da
gudanar da ayyuka na kwarai
ba tare da katsewa ba. Wannan
magana da take cikin Du'a
Kumail da take cewa "da
dawwama cikin sadarwa da
kai", wato mutum ya zamanto a
ko da yaushe mai ci gaba da yin
hidima wa Allah Madaukakin
Sarki. Wannan ci gaba ba tare
da katsewa ba lamari ne mai
muhimmancin gaske. Idan har
aka sami wadannan abubuwa
guda biyu, wanda daya daga
cikinsu yana da bangare ne na
tausayi da zuciya dayan kuma
yana da bangare na aiki ne, to
za a "tumbuke tushensa", wato
za a tumbuke tushen shaidan ko
kuma za a kawar da shi.
"Istigfari kuma yana katse
jijiyoyinsa", wato neman gafarar
Ubangiji yana yanke jijiyoyin
Shaidan. A saboda haka daga
cikin abubuwan da suke ruguza
Shaidan, shi ne istigafari.
Istigafari ko kuma neman
gafara daga wajen Allah
Madaukakin Sarki, wanda ya zo
a wajaje daban-daban cikin
Alkur'ani mai girma sannan
kuma a kowane waje an
ambaci amfani na musamman
da hakan yake da shi. Wannan
ruhi na istigfari da neman
gafara, lamari ne mai
muhimmancin gaske; don kuwa
hakan yana a matsayin nuna
damuwar mutum ne ga kura-
kuran da ya aikata. Duk wani
mutum da yake ganin kansa a
matsayin wanda ba shi da kura-
kura da zunubi sannan kuma
yake zaton cewa babu wani
mummunan aikin da ya aikata,
to ba ma zai yi tunanin neman
gafara ba. Shi kansa tunanin
neman gafara, hakan yana
nufin cewa mu din nan muna da
kura-kurai, muna da nakasi da
zunubi ne.
Wannan lamari ne da ya zama
wajibi ga kowane mutum; don
kuwa a dabi'ance babu wani
mutum da ba shi da laifi da
kuma kura-kurai. "Kuma da Allah
Yana kama mutane da
zaluncinsu, da bai bar wata
dabba ba a kan kasa" (Suratun
Nahl 16:61). Allah Madaukakin
Sarki Yana kau da kai daga
(ayyukan) bayinsa ne, idan
kuwa ba haka ba, idan da a ce
zai kama bayinsa saboda
zalunci da munanan ayyukan da
suke yi to da babu wani mutum
da zai saura a bayan kasa: "da
bai bar wata dabba ba a kan
kasa". A nan dai dabbar da ake
magana ana nufin mutum ne,
don kuwa ana magana ne kan
mutane. A saboda haka, a mafi
yawan lokuta mu kan aikata
zunubai daban-daban wadanda
a mafi yawan lokuta su kan
samo asali ne saboda son zuciya
wasu kuma daga cikin su
saboda jahilci ne da rashin
hangen nesan mu ne. A saboda
haka lura da neman gafarar
Ubangiji, damuwa ne da
zunubin da mutum ya aikata
sannan kuma wajibin damuwa
da zunubin shi ne gyara ayyuka.
Wajibi ne kowane mutum a ko
da yaushe ya zamanto mai
kyautata ayyukansa. Idan har
aka sami wannan yanayi na
gyara ayyuka, to a nan za a sami
kamala. A saboda haka, sharadi
na asali na kamalar mutum, shi
ne wannan gyara wanda
neman gafara yana daga cikin
abubuwa masu muhimmanci a
wannan fagen. A saboda haka
ne a ka ba wa istigfari matsayi
mai girman gaske.
Yanzu kuma bari in karanta
riwaya ta uku sannan daga
baya kuma in dan fadi wasu
jumloli biyu zuwa uku dangane
da wannan riwayar. Ita ma dai
da wannan isnadi ne tana
cewa: "Manzon Allah, tsira da
amincin Allah su tabbata a gare
shi da Alayensa, yana cewa: Ina
wa al'umma ta wasicci da
abubuwa guda biyar, (ina musu
wasicci da ji da biyayya...." A
mafi yawan lokuta dai a kan
kawo ‘ji' da ‘biyayya' tare ne;
amma a nan kan an raba su.
Daga dukkan alamu a wannan
wajen ba a yi amfani da ‘ji' da
‘biyayya' da ma'ana guda ba.
Idan ma har a wasu wajajen ‘ji
da biyyya' (wato amincewa) sun
zo tare ne, to a nan kan ‘ji' ba
biyayya ba ne. ‘Ji' yana nufin
lura da abu, ji da nuna
damuwa'. Lamari na farko shi
ne wannan. Abu na farko da
al'ummar Shi'a take bukata shi
ne nuna damuwa. Wajibi ne
wannan al'umma ta zamanto
mai sanya ido da kuma nuna
damuwa da abubuwan da suke
gudana a duniya. Mai yiyuwa ‘ji'
a nan yana ishara ne da
wannan lamarin. Lalle bai
kamata a dinga nuna halin ko in
kula da fadin, ‘duk abin da ya
faru, ya faru mana', ‘me ya
dame mu' ‘mu dai babu abin da
za mu iya' 'mene ne na mu cikin
wannan lamarin'. Babban dalilin
da ya sanya wannan gini mai
albarka (Jamhuriyar Musulunci)
ya zamanto mai karfi shi ne
cewa akwai gagarumin
bambanci tsakanin wannan
babban bawan Allah (Imam
Khumaini) da sauran mutane shi
ne cewa shi din nan har abada
bai taba fadin: ‘Ina ruwana ba',
ya kasance mai sanya ido kan
abubuwan da ke faruwa a cikin
al'umma. Akwai mutane da
dama da suke sanya ido, amma
wasu kuma ba sa ganin hakan,
ba sa fahimta, ba sa damuwa
da hakan. Da dama ba sa
damuwa; amma su kan ce ‘Ina
ruwanmu' ‘mu dai abin da ya
dame mu za mu aikata'.
Wannan babban bawan Allah
bai taba fadin cewa ‘ina
ruwana ba'. A saboda haka ne
ya zamanto Imami kuma
shugaban al'umma. Lalle ya
dace da shugabanci, a saboda
haka ne ya samar da wannan
tushe mai cike da albarka.
Wannan shi ne aiki na farko.
Daga nan kuma sai ‘biyayya'.
Biyayya ga wane mutum? 'Ga
wanda ya cancanci a yi masa
biyayya' ga wanda wajibi ne a yi
masa biyayya. Wajibi ne kowane
mutum a kuma ko ina yake
sannan kuma kowane mukami
yake da shi, wajibi ne ya yi
biyayya ga mutumin da ya
cancanci a yi masa biyayya.
Babu batun taurin kai da fadin
cewa ‘ina ruwa na' da
sauransu. Idan dai har al'ummar
musulmi za ta yi aiki da wasiyyar
Annabi, to wajibi ne ta yi biyayya
ga wanda a shar'ance ya
wajaba a yi masa biyayya.
Kishiyar biyayya kuwa ita ce
sabawa wanda ayar nan mai
girma da ta zo cikin Suratul Al
Imran aya ta 152 ta ja kunne
dangane da hakan, a lokuta da
dama na sha yin bayanin kan
hakan.
Daya daga cikin lamurran da
suke haifar da rashin nasara da
shan kashi - wanda ana iya
ganin zahirin hakan a yakin
Uhudu - shi ne lamarin saba wa
umurni, wato rashin biyayya.
Wadancan mutanen (a lokacin
yakin Uhudu) sun saba wa wani
umurni ne na Annabi (s.a.w.a);
sai abin da ya faru ya faru. A
lokacin Jamhuriyar Musulunci, a
duk inda aka ga wata alama ta
rashin biyayya, to kuwa an
fuskanci matsaloli. A duk inda
aka yi biyayya, to kuwa an sami
ci gaba da kuma alheri.
Daga nan kuma sai 'da hijira'. Ko
da yake hijira tana da matakai.
Mai yiyuwa ne a wani lokaci
abin da Annabi ya ke nufi da
hijira shi ne kafa al'umma ta
Musulunci wanda wajibi ne a
fitar da mutane daga irin
rayuwar da larabawan (wancan
lokacin) suke yi a 'Jazirar
larabawa' da kuma samar da
wata sabuwar al'umma. Har
zuwa lokacin da mutane ba su
zamanto masu wayewar kai ba,
to kuwa babu yadda za a iya
gudanar da koyarwar Ubangiji
da Musulunci a kansu ba da
kuma isar da su zuwa ga wani
waje ba.
Daya daga cikin matakan shi ne
hijira zuwa ga 'Darul Hijra'.
Bayan hakan kuma sai hijira
zuwa ga garuruwa wato lokacin
da kabilu daga wajaje daban-
daban bisa umurnin Manzon
Allah (s.a.w.a) suka bar wajajen
da suke zuwa ga garuruwa.
Idan da a ce ba su yi hijira ba,
ko da a ce sun kasance cikin
jihadi, to kuwa ba za a ba su
abin da aka samu na daga
ganima ba. Akwai hakan ma
cikin riwayoyin mu. Da yardar
Allah za mu zo wajen a cikin
'Babin jihadi' sannan kuma za
mu yi bahasi kan sa.
Yin hijira zuwa ga inda ya
wajaba a yi hijirar, wato rashin
damfara kai da wani waje guda.
Mai yiyuwa ne misdakin wannan
hijirar a wajen daliban addini
da malamai masu girma da suke
cikin makarantar hauza shi ne
hijirar da suke yi zuwa
garuruwa daban-daban na
musulmi don isar da sakon
Musulunci.
Akwai wadansu mutane da za
su iya ci gaba da zama a
garuruwa da ci gaba da shiryar
da mutanen da suke wajen.
Akwai wadansu dubban ko
kuma daruruwa irin su da suke
ci gaba da zama a Kum sannan
kuma babu wani abin da zai
faru. Mafi girman abin da za su
yi dai shi ne su ba da darasi,
wanda idan ma ba su karantar
din ba, wadannan mutanen da
suke zuwa azuzuwan na su za
su iya zuwa wajen wasu
malaman su yi karatu. Wato za
su iya yin wannan karatun a
can. A yau a kasar mu, akwai
wadansu garuruwa da kauyuka
da suke bukatar malamin
addini, wanda wajibi ne
malaman addini su tafi can din.
Ko da yake ba tare da wani
sharadi ba. Don kuwa wasu su
kan gaya mana cewa wajibi ne
a samar mana da abu kaza
kafin mu tafi. Ba wai muna
cewa ne babu bukatar a kula da
abubuwan da rayuwa take
bukatar su na duniya ba. Tabbas
akwai bukatu. To amma wajibi
ne a dauki wadannan a
matsayin bukatu na wajibi. To a
ko ina dai akwai irin wadannan
abubuwan. A saboda haka bai
kamata a sanya wadannan
abubuwa a matsayin sharadi
ba. Wajibi ne su tafi da kuma yin
himma.
Ko da yake hakan ma dai ba wai
wani aiki ne na daidaikun
mutane ba. Mai yiyuwa ne
mutane hamsin su ce: "Shi
kenan yanzu ya tabbata don
haka wajibi ne mu tashi mu tafi"
sannan sai su tashi su tafi. To;
mutane hamsin sun aikata
wannan aikin, daga baya aikin
zai tsaya. Wajibi ne makarantar
hauza ta Kum sannan kuma
sauran makarantun hauzar ma
su biyo sahu su mayar da
wannan aikin ya zamanto wani
yunkuri mai ci gaba da
wanzuwa. Su kama hanya su
tafi. Yana da kyau shugabannin
makarantar hauza da fitattun
(malaman) hauza su kama
wannan aikin. Da farko dai su
fara daga kansu. Akwai
wadansu daga cikin manyan
mutane wadanda idan suka tafi
wani gari na daban, to kuwa
kasantuwarsu a can za ta fi
zama mai amfani a kan
zamansu a Kum. Akwai irin
wannan yanayi hatta dangane
da manyan malamai. To, a
matsayin misali a sami wani
mutumin kamar Ayatullah Milani,
yardar Allah ta tabbata a gare
shi, wanda ya kasance a Karbala
da Najaf, akwai kuma irin su da
yawa a Najaf da Karbala din, ya
taso ya zo Mashhad da samar
da babbar makarantar Hauza.
Alal hakika kasantuwar marigayi
Ayatullah Milani (a Mashhad)
wata albarka ce ta Ubangiji ga
makarantar hauzar Mashhad. To
shi din nan dai yana iya ci gaba
da zama a Karbala har karshen
rayuwarsa. A wancan lokacin
akwai manyan malamai irin sa a
can. Wasu daga cikinsu idan ma
ba su kasance sama da shi ba a
fagen ilimi, to mai yiyuwa ne a
wasu fagagen sun kasance a
gabansa. To amma duk da haka
ya zo Mashhad sannan kuma
hakan ya zamanto abin albarka.
A saboda haka, wannan
magana, hatta ga mutane irin
su marigayi Ayatullah Milani
haka take; don a rage taruwa
waje guda. Ita kanta wannan
hijira, hijira ce zuwa ga wajen
da ake bukatar (mutum): zuwa
ga garuruwa, makarantun
hauza, zuwa ga manyan hauzozi
da kanana, daga baya kuma
zuwa cikin cibiyoyin gwamnati,
cikin ofisoshi cikin kamfanoni -
wajajen da ake da irin
wadannan bukatu - daga nan
kuma zuwa ga wajen kasar nan.
Mai yiyuwa ne a yau, daya daga
cikin alamun da suke tabbatar
da hijira, yana iya zamantowa
wannan lamarin.
"Da kuma jihadi" jihadi dai wani
aiki ne mai cikakken amfani
wanda ake iya samun sa a
yanayi da fagage daban-daban.
A farkon ‘babin jihadi' mun fadi
cewa jihadi ba wai kawai
daukan takobi da shiga fagen
yaki ba ne. Abin da ke nuni da
jihadi shi ne dai wannan abin
da ake kira da ‘gwagwarmaya'.
A na cewa wane mutum ne dan
gwagwarmaya; wane kuma ba
dan gwagwarmaya ba.
Marubuci dan gwagwarmaya,
marubuci wanda ba dan
gwagwarmaya ba. Malami dan
gwagwarmaya, malami wanda
ba dan gwagwarmaya ba.
Dalibin jami'a da daliban addini
‘yan gwagwarmaya, dalibin
jami'a da na addini wanda ba
dan gwawarmaya ba. Al'umma
‘yar gwagwarmaya da kuma
wacce ba ‘yar gwawgarmaya
ba. A saboda haka jihadi yana
nufin gwagwarmaya da kuma
kokari.
A yayin gwagwarmaya akwai
wadansu abubuwa guda biyu
da suka zamanto wajibi: daya
daga ciki shi ne cewa wajibi ne
ya zamanto akwai kokari da
yunkuri cikin hakan. Mutum dai
ba zai iya yin gwagwarmaya a
kan gado da wajen hutunsa ba!
Wajibi ne ya zamanto akwai
kokari da motsawa cikin
gwagwarmaya. Duk kuwa da
cewa a wani yanayin akwai
gwagwarmaya da son zuciya; to
sai dai misalan da muke kawo
wa muna magana ne kan
gwagwarmaya ta zamantakewa
da makamantan hakan. A
saboda haka da farko dai wajibi
ne ya zamanto akwai kokari da
motsi da yunkuri cikin hakan. Na
biyu shi ne ya zamanto akwai
masu nuna kiyayya ga hakan.
Duk wata gwagwarmayar da ba
ta da makiya tattare da ita, ba
ta da ma'ana. A saboda haka,
jihadi yana tare da wadannan
rukunai guda biyu ne: na farko
shi ne a sami kokari da yunkuri
a cikin hakan; na biyu kuma shi
ne ya zamanto yana tinkarar
makiya ne. Idan wani mutum ya
yunkura da kuma tinkarar
abokinsa, to wannan ba jihadi
ba ne; face dai fitina da tada
hankali ne. Idan har wani ya
yunkura saboda fada da
gwamnatin gaskiya, wajen fada
da alheri da amfanin
gwamnatin gaskiya, ya yi ta
kokari da jihadi, to wannan
fitina ce da fada da hukumar
gaskiya; wannan ba jihadi ba
ne. To wannan yunkuri da
kokarin da ake yi, ta kowane
yanayi kuwa ya kasance - shin
ta hanyar rubutu, magana, littafi
ko kuma ta hanyar yada
karararraki da kokarin cin
fuskar wadansu mutane ne -
dukkanin wadannan abubuwa
neman tada fitina da rikici ne,
wasu daga cikin yanayinsu ma
yana a matsayin fada da addini
da gaskiya ne. Idan dukkanin
wadannan abubuwa suka
zamanto wajen fada da makiyin
Allah da kuma makiyi ne ‘ta
bakin Allah da Manzonsa da
Waliyansa, amincin Allah ya
tabbata a gare su", to a nan ne
zai iya zama ‘jihadi saboda
Allah'. Wannan shi ne irin jihadin
da Manzon Allah (s.a.w.a) ya ke
kira zuwa gare shi. A saboda
haka ragwantaka da zaman
dirshan ba tare da wani yunkuri
da kuma ba wa lamurra
muhimmanci ba alheri ba ne ga
al'ummar annabi. Abin so dai shi
ne jihadi a ko da yaushe.
"Da jama'a; ‘taron jama'a'. Daga
nan sai ya ce: "Duk wanda ya ke
kira da irin kira ta jahiliya, to
kuwa yana da wani dutse daga
cikin duwatsun Jahannama";
wato dutse daga cikin
duwatsun wutan jahannama
yana kan mutumin da ya ke kira
zuwa ga jahiliya. Jahiliya dai ita
ce tsarin da ya kasance kafin
Musulunci. Kafin tsarin
Musulunci, tsari ne na jahiliya
ake gudanarwa. Tsarin da ba na
Musulunci ba, tsari ne na jahiliya.
To; mu din nan a matsayin mu
na daliban addini da kuma
makarantar hauza, wajibi ne mu
yi la'akari da wadannan
abubuwa da na fadi. A yau na
karanto mana wasu riwayoyi
guda uku ne, hakan kuwa don
in yi nuni da irin muhimmancin
da kyautata zuciya da kuma
tabbatar da kyawawan halaye a
cikin makarantun hauza suke da
shi ne. Ya ku malamai! idan har
wani mutum ya samo ilimi, ya
zamanto mujtahidi, ya zamanto
ya sami matsayi na koli na ilimi,
amma kuma ba a shirye yake ya
amince da gaskiya ba; son
zuciya ta yi nasara a kansa,
soyace-soyacen zuciyarsa sun
rufe masa abubuwan da suke a
fili, to ba wai ma kawai wannan
mutumin ba shi da wani amfani
ga duniyar musulmi ba ne, face
ma dai shi din nan mai cutarwa
ne (gare su) kai a wani lokacin
ma cutarwarsa ta fi na jahilai. A
yau idan ma har aka sami wani
mutum ya zama ya fi kowa ilimi,
to amma sai ya gagara fahimta
da kuma ganin irin yadda a yau
tsarin Musuluncin da aka kafa
shi a Iran, wanda ya kafu bisa
gaskiya da kuma yadda aka
kawar tsarin jahilci wanda ya
ginu bisa zunubi da fasikanci da
zalunci - kamar yadda a yau
dukkanin gwamnatocin da suka
ginu bisa fasikanci da fajirci,
kama daga babbar shaidaniya
Amurka har zuwa ga kawayenta
abokanta, da dukkanin lalatattu
na duniya suke fada da wannan
tsarin - amma sai ya gagara
fahimtar dukkanin wadannan
abubuwa, a wani lokaci ma
bakinsu ya kan zo daya da
wadancan mutanen da kuma
share musu fage da faranta
musu, to babu alheri tattare da
wannan mafi ilimin. Allah wadai
da wannan malamin da yake
farin ciki a lokacin da yake
ganin gidajen radiyo na makiya
Musulunci suna yabonsa saboda
fada da yake yi da tsarin
Musulunci. Wajibi ne ya yi kuka!
To ko mai kuwa irin ilimin da
yake da shi, don kuwa hakan ba
ilimi ba ne, jahilci ne. Ba haske
ba ne, duhu ne. Don kuwa idan
har ya kasance haske ne, to da
a matakin farko da ya shiryar da
irin wadannan mutane. Irin
wadannan mutane - wadanda
idan ma har akwai su, alhamdu
lillahi, su din nan ‘yan kadan ne,
‘yan tsiraru ne - saboda son
zuciyar su a shirye suke su take
maslaha ta gaba daya ta
al'umma. Hatta ma ba za su iya
goyon bayan tsarin Musulunci
ba. Ko kuma sama da haka -
Allah ya kiyaye - su yi fada da
shi. Idan har muka ga irin
wadannan mutane, to wajibi ne
mu ba wa batun tsarkake
zukatan mu muhimmanci. Idan
har muka kalli irin kumaji na
ilimi da ake da shi a makarantar
hauza, amma kuma hakan ya
gagara cike gurbin da ake da
shi a tsarin Musulunci kamar
yadda ya dace, to wajibi ne mu
ba wa lamarin kyautata zuciya
karin muhimmanci. Saboda
kuwa idan har aka tabbatar da
kyawawan halaye da tsarkake
zuciya a cikin makarantun
hauza, to wajibi ne duk wani
abin da za a fadi ya zamanto
mai amfani ga mutane da kuma
al'umma.
Lalle ina son in kara jaddadawa
dangane da lamarin tsarkake
zuciya. Ya ku malamai!
Makarantun hauzozinmu cike
suke da matasa masu tsarkin
zuciya. Da wuya ka sami wani
wajen da ake da irin wadannan
matasa. A makarantun hauza
irin su Kum, akwai dubban
matasa masu tsarkin zuciya,
wadanda suka yi watsi da
ababen kyalkyalen wannan
duniya maras kima sannan
wasu daga cikin su sun kasance
misdakin wannan jumla da ta zo
cikin addu'ar nan mai girma ta
Al-Nudba da take cewa "bayan
ka yi musu sharadi (kasancewa)
masu tsoron Allah da gudun
duniya a cikin wannan duniya
kaskantacciya da kuma irin
kyalkyalin da ke cikinta". To da
kyau; taruwar wadannan
matasa salihai, masu tsarkin
zuciya kuma muminai masu
tsarki da haske a wannan
makarantar hauza, lalle lamari
ne mai ban mamaki da kuma
burgewa.
Daya daga cikin ayyuka da
nauyin da ke wuyan makarantar
hauza shi ne a matakin farko
kiyaye irin wannan ruhi na
tsarki da kusaci da Allah da ke
tattare da wadannan dalibai
matasa da kuma tabbatar da
shi. Na biyu, shi ne kara karfafa
hakan; da kara irin hasken da
hakan yake da shi. Wannan
wani lamari ne wanda na ke
son ya zamanto an lura da shi a
dukkanin makarantun hauza. Ko
da yake lalle an lura da hakan;
to sai dai muna so ne a kara shi.
A yau duniyar nan, duniya ce da
ta lalace, hakan ya yadu zuwa
ko ina. Babu wata katanga da
garkuwa da aka sanya; in dai
ba isar da sako mai kyau da
kuma yin bayani ba. To waye ya
kamata ya aiwatar da wannan
bayani da isar da sako mai kyau
din? Mutanen da suke tsaye da
kafafunsu. Wadannan kuwa su
ne dai wadannan matasa da
malamai wadanda suke koyon
ilmummuka na adini da kuma
yin bayanin hakan. Wadannan
mutane a bangaren kyawawan
halaye da ababen da suke
kusata mutum da Ubangiji suna
tsaye sosai da kuma yin tasiri.
Batu na gaba, wanda shi ma
lamari ne na biyu a makarantar
hauza shi ne lamari na ci gaban
ilimi da kuma mayar da shi ya yi
daidai da zamani. Ya ku
malamai! Ni dai ina son in sanar
da ku cewa manyan malamai
irin su Ma'abocin Jawahir (wato
Sheikh Muhammad Hasan Al-
Najafi, yardar Allah ta tabbata a
gare shi wanda aka haifa a
shekarar 1201 ya kuma rasu a
shekarar 1266 hujiriya), daya
daga cikin siffofin da ya kebanta
da ita shi ne cewa shi din nan
ya kasance mutum ne mai
tunani irin na sauyi da sanya
fikihu ya yi daidai da
zamani......Ala kulli hal, wannan
mutumin ya kasance mai sabbin
tunani. Shi din nan yana da
fatawa - ko kuma a wajen da
babu fatawar, yana da wadansu
maganganu wadanda suka yi
kama da fatawa - wanda mai
yiyuwa ne kafin sa babu wani
daga cikin fukaha' da suka fadi
hakan, ko kuma alal akalla bai
fito fili ba. Daya daga cikin
wadannan lamurra shi ne batun
‘fara jihadi a zamanin fakuwar
(Imam Mahdi)' wanda lamari ne
da ya shahara a tsakanin
malaman fikihu na da na cewa
hakan ba ya halalta. Amma shi
kuma ya yi bahasin lamarin
wanda sakamakon hakan shi ne
halalcin hakan. To wannan dai
sabuntawa cikin lamurra ne.
Hakan Ma'abocin Jawahiri ya
kasance cikin lamurra daban-
daban. Malamin fikihu yana iya
zama abin koyi kuma sananne
idan yana da irin wannan ruhi.
Shi ma marigayi Ayatullah
Burujerdi yardar Allah ta
tabbata a gare shi wanda a
zamaninsa ya zamanto koli ne
na ilmin fikihu, shi ma haka ya
kasance. Haka nan Imam
(Khumaini) yardar Allah ta
tabbata a gare shi ma ya
kasance.
Wajibi ne a sami ruhin ci
gabantar da ilim da fikihu.
Na'am a wani lokaci ba a za iya
samar da lamurra ta hanyar
fatawa kawai ba; to babu
matsala. Su yi bahasi na ilimi. Ni
dai a wani lokaci na kan ga
wasu mutane cikin wani bahasi
na fikihu suna kawo sabbin
abubuwa. A bangare guda sai
ka ga wasu suna ta sukan su da
cewa me ya sa ku din nan kuke
fadin irin wadannan
maganganu? A baya-bayan nan
akwai wadansu malamai masu
girma da suke da sabbin tunani,
suna gabatar da wadansu
maganganu wadanda babu
matsala cikin gabatar da su.
Wajibi ne ya zamanto an sami
juriyar sauraren maganganun
wasu; ko da kuwa wannan
malamin bai kai matsayin bayar
da fatawa ba. Mai yiyuwa ne
wasu su amince da hakan; su
fitar da fatawa. A saboda haka
ne ma na bukaci malaman Kum
da su dinga buga wata mujalla
ta fikihu da yada ta. Wannan
mujallar wacce za a dinga
gabatar da sabbin tunani da
ra'ayoyi na fikihu.
Ko da yake wadannan masu
girma ba su aikata hakan ba. An
sami wasu daga cikin matasa
da suka yi wani abu a wannan
fagen, ko da yake ba wani
gagarumin aiki ne ba, to amma
dai abin a yaba musu ne.
Saboda kuwa sun yi wani abu a
wannan fagen. Amma har ya
zuwa yanzu ana iya yin wannan
aiki mai girma. Ko da ma a ce an
samar da mujallu biyu zuwa uku
ne na fikihu ba su yi yawa ba. A
sami mujalla ta falsafa. Alhamdu
lillahi akwai mujalla ta ilimin
akida; ko da yake adadi kadan
ake bugawa kuma ba a ma
santa sosai ba. Mai yiyuwa ne
wasu daga cikinku ko sunanta
ma ba ku taba ji ba ko kuma
ganinta ba. To amma alhamdu
lillahi ni na ganta, sannan kuma
ina gode wa mutanen da suke
yin wannan aikin. Lalle wajibi ne
a dinga gabatar da sabbin
tunani cikin ilmummuka na
Musulunci a kowace rana a cikin
hauza. Wanda ya fi muhimmanci
cikinsu shi ne a fagen fikihu.
Batu na uku shi ne cewa wajibi
ne makarantar hauza ta
zamanto a sahun farko na
gagarumin yunkurin al'umma.
Kamar yadda kuka ga manyan
maraja'anmu irin su marigayi
Ayatullah al-Uzma Golpayagani,
marigayi Ayatullah al-Uzma
Najafi sannan a yau kuma irin
su Ayatullah al-Uzma Araki, Allah
ya kara masa tsawon rai, shin a
zamanin Imam (Khumaini)
yardar Allah ta tabbata a gare
shi ne ko kuma bayansa har
zuwa yau din nan, sun kasance
a sahun farko ne. Duk wani abin
da ya faru a cikin wannan
al'umma za ku ga cewa suna
sahun gaba-gaba ne. A ranar
zabe, tun da sanyin safiya za ka
ga marigayi Ayatullah
Golpaygani da marigayi
Ayatullah Mar'ashi suna da cikin
na farko-farkon da suke kada
kuri'ar su. Aikin su, wani aiki ne
da ke nuni da wani lamari mai
muhimmanci. Na'am ana iya
kada kuri'a da yamma ma. To
amma kada kuri'a tun da sanyin
safiya wata alama ce da take
nuni da wani abu. Ku din nan
dai kun ga yadda Imam, yardar
Allah ta tabbata a gare shi, ya
kasance mutum mai kula ainun!
Yanayinsa dai a fili yake.
Maraja'an Kum haka suka
kasance. Cikin manyan ayyuka;
lokacin yaki, kasantuwa a fagen
daga, kwadaitar da mutane
tafiya fagen daga, ayyuka na
tattalin arziki da sauransu, a ko
da yaushe sun kasance a sahun
farko-farko ne. Lalle haka ya
wajaba hauza ta kasance. Duk
wanda yake makarantar hauza,
amma sai ya zamanto yana wa
tsarin Musulunci da hukumce-
hukumcen Alkur'ani - wadanda
aka tabbatar da su a aikace a
wannan kasar - da kuma
hukumar Musulunci wacce aka
kafa ta sakamakon kokarin
mutane, sai ya zamana yana
wani irin kallon taro sisi a gare
su, to kuwa ya zamanto bako, to
wane ne shi kuwa. Wajibi ne
daliban makarantar hauza su
dinga jin kansu a matsayin
wadanda suke sahu na gaba-
gaba, wanda alhamdu lillahi a
ko da yaushe haka lamarin ya
ke. Wato a ko da yaushe daliban
hauza matasa da malamai da
sauran manyan malamai na
hauza sun kasance a sahu na
gaba-gaba ne; to a nan gaba
ma haka ya wajaba su zamanto.
Insha Allahu, muna rokon Allah
albarkacin shiriyarwar manyan
malamanmu, da ya sanya
wannan tsari na Musulunci ya
kai ga kamalar da yake son
kaiwa.