BARKA DA ZUWA SHAFI MAI ALBARKA
Alhamdulillah muna muku albishir insha Allah zamu dawo aiki gadan gadan!Hanyoyi Uku: Ihtiyati Da Ijtihadi Da Taklidi
T1: Shin taklidi lamari ne na hankali kawai ko kuma yana da wani dalili na shari'a?
A:Takilidi yana da dalili na shari'a sannan kuma hankali yana hukumta cewa mutumin da ba shi da cikakkiyar masaniya kan hukumce-hukumcen addini da ya koma wajen wani mujtahidi da ya cika sharudda don sanin wadannan hukumce-hukumce.
T2 : A, fatawarka, shin aiki da"ihtiyati" shi ya fi ko kuma yin "taklidi"?
A: Kasantuwar aiki da"ihtiyati" ya ta'allaka ne da sanin wuraren da ya dace da shi, da kuma yanayin aiki da shi ("ihtiyat") sannan kuma hakan yana bukatar sarrafar lokaci mai yawa, don haka abin da ya fi shi ne yin taklid ga mujtahidin da ya cika sharuddan taklid.
T3: Mene ne haddin da'irar ihtiyati cikin hukumci tsakanin fatawoyin fukaha'u (manyan malaman fikihu da ake taklidi da su)? Shin ana iya shigar da fatawoyin fukaha'un da suka gabata?
A: Abin nufi da ihtiyati a wannan waje shi ne kiyaye dukkanin abubuwan da suka zo cikin fikihu ta yadda mukallafi zai sami kwanciyar hankalin cewa yayi aiki da nauyin da ke kansa (ya sauke nauyin dake kansa).
T4: Nan ba da jimawa ba ‘ya ta za ta cika shekarun balaga, daga nan kuma wajibi ne ta zabi marja'in da za ta masa taklidi, tattare da cewa gano hakan babbar matsala ce, don haka mene ne ya wajaba a kan mu?
A: Idan har ita da kanta ba za ta iya gano abin da ya wajaba a kanta ba dangane da wannan al'amari, to a nan abin da ya hau kanka shi ne shiryar da ita.
T5: Sanannen abu ne wajen fukaha'u cewa ayyana maudhu'in hukumci yana hannun shi kansa mukallafi ne, aikin mujtahidi shi ne ayyana hukumci. To sai a wasu lokuta mujtahidan sukan ba da ra'ayinsu wajen ayyana maudhu'in hukumcin, shin wajibi ne a yi koyi da mujtahidin wajen ayyana maudhu'in?
A: Ayyana maudhu'i yana wuyan mukallafi ne, koyi da mujtahidi wajen ayyana maudhu'i ba wajibi ba ne sai dai idan har mutum ya sami kwanciyar hankali kan ingancin ayyana maudhu'in (da mujtahidin yayi) ko kuma shi kansa maudhu'in yana daga cikin maudhu'an da ayyana su yana bukatar fitar da shi daga masdarori na shari'a (wato intinbadi).
T6: Mutumin da ya nuna gazawa wajen neman ilimin hukumce-hukumcen shari'a da yake bukata, shin ya aikata sabo ne ?
A: Idan har gazawa wajen neman ilimin hukumce-hukumcen zai iya kai shi ga barin wajibi ko kuma aikata haramun, to lalle ya aikata sabo.
T7: Wasu mutane wadanda ba sa da cikakkiyar masaniya yayin da muka tambaye su kan cewa wani marja'i suke yi wa "taklidi", sukan amsa da cewa mu ba mu sani ba, ko kuma su ce muna wa wane (taklidi) ne. Sai dai kuma ba sa ganin cewa dole ne su koma ga risalarsa dan su yi aiki da ita, to anan mene ne hukuncin ayyukansu?
A: Idan har ayyukan nasu sun yi daidai da "ihtiyat" ko kuma da abin da ya dace ko kuma ga fatawar mujtahidin da daman wajibi ne su koma gare shi, to ayyukan sun inganta.
T8: Cikin mas'alar da mujtahidi A'alam ya ba da fatawar wajibcin ihtiyadi a cikinta, shin muna iya komawa ga mujtahidin da ke biye masa wajen A'alamiyya (fifikon marja'i bisa sauran' yan' uwansa), sannan idan shi ma fatawarsa tamkar ta farkon ce wato wajibcin ihtiyati, shin muna iya komawa ga mujtahidi na uku dake biye wa na biyun wajen A'alamiyya. Idan shi ma fatawarsa tamkar na biyun farko ne shin muna iya komawa ga wanda ke biye masa haka dai haka dai...don Allah a yi mana karin bayani kan wannan mas'ala.
A: A mas'alar da mujtahidi A'alam ba shi da fatawa, to babu matsala a koma ga mujtahidin da yake da bayyananniyar fatawa amma bisa la'akari da ka'idar bin A'alam bayan A'alam.