BARKA DA ZUWA SHAFI MAI ALBARKA
Alhamdulillah muna muku albishir insha Allah zamu dawo aiki gadan gadan!Sharuddan Takalidi
T9: Shin ya halatta yin "taklidi" ga mujtahidin da ba marja'i ba kana bai da risala?
: Idan har ya tabbata ga baligi cewa shi mujtahidi ne da ya cika sharudda, to babu wata matsala ga hakan.
10: Shin ana iya yin takalidi ga mutumin da a daya daga cikin babukan fikihu ne kawai misali babin salla da azumi ya kai matsayin ijtihadi?
A: Fatawar mujtahidin da a wasu babukan fikihu ne kawai ya kai matsayin ijtihadi a kan kansa ne take hujja, akwai matsala cikin wasu su yi takalidi da shi, duk da cewa ingancin hakan ba abu ne da za a iya kore shi ba.
11: Shin yin taklidi ga malamai (mujtahidai) na wasu kasashe ya halatta ko da kuwa saduwa da su ba zai yiwu ba?
A: Ba sharadi ba ne ga mujtahidin da ake masa taklidi ya kasance kasa daya ko gari daya da mai yi masa taklidi (mukallafi).
12: Shin akwai wani bambanci tsakanin adalcin da ake bukata wajen mujtahidi da marja'in da ake masa takalidi da adalcin da ake bukata wajen limamin (sallar) jam'i ta bangaren tsanani ko rauni?
A: Bisa la'akari da muhimmancin da matsayin marja'iyya yake da shi wajen fitar da fatawa, bisa ihtiyadin wajibi sharadi ne mujtahidin da ake masa takalidi, baya ga adalci, ya zamanto yana da karfin yin galaba a kan zuciyarsa da kuma nesantar duniya.
13: Bisa la'akari da cewa wajibi ne mujtahidin da za a yi masa takalidi ya zamanto adali, to me ake nufi da adali?
A: Adali shi ne mutumin da tsantsaininsa (tsoron Allansa) ya kai matsayin da ba ya aikata sabo da gangan.
14: Shin masaniyar yanayin zamani da halin da ake ciki tana daga cikin sharuddan ijtihadi?
: Me yiyuwa ne hakan ya zamanto sharadi cikin wasu mas'alolin.
15: Bisa ga ra'ayin lmam Khumaini (r.a) na cewa dole ne marja'in da za'a yi masa takalidi ya kasance masani ne kan al'amurran siyasa, tattalin arziki, aikin soja, zamantakewa da shugabanci baki daya da kasancewarsa masani kan hukunce- hukuncen ibadu da mu'amaloli. To mu a halin yanzu bayan mun kasance muna takalidi da lmam Khumaini (r.a) sai muka ga ya zama wajibi- bisa la'akari da irin shiryarwar da muka samu daga wajen wasu manyan malaman kana kuma da abin da muka gani da kanmu- mu koma gare ka don yin takalid, ta yadda zai zamanto kenan mun hada shugabanci da kuma marja'iyya, to shin mene ne kake gani?
A: Sharuddan cancantar marja'in da za'a masa takalidi suna nan an yi cikakken bayaninsu a cikin littafin Tahrirul Wasila da sauran littattafa. To amma al'amarin gano wadannan sharudda da kuma zaben wanda ya dace dan yi masa takalidi daga cikin Fukaha'u to ya ta'allaka ne ga shi kansa mukallafin.
16: Shin Aalamiyya sharadi ne cikin takalidi ko kuma a'a? kana yaya ake gane Aalamiyya?
: A bisa lhtiyat wajibi ne yin takalid ga A'alam cikin mas'alolin da fatawoyinsa suka saba da fatawoyin sauran maraji'ai. Kana A'alamiyya shi ne wani marja'i ya kasance ya fi sauran maraja'ai kudurar sanin hukumce hukumcen Ubangiji da kuma kuduran ciro hukumce-hukumcen daga inda ake ciro su. Sannan kuma masaniyarsa kan zamaminsa gwargwadon yadda zai yi tasiri cikin ayyana maudhu'an hukumce-hukumcen shari'a da kuma yadda zai fitar da ra'ayin fikihunsa ya fi na sauran.
17: Shin za'a iya hukunta, taklidin wanda ya yi takalidi ga wanda ba A'alam ba saboda zaton cewa shi A'alam din bai mallaki sharuddan taklid ba, shin za a hukunta irin wannan taklidi da cewa bai inganta ba ?
: Ba ya halatta bisa ihtiyat yin taklidi ga wanda ba A'alam ba cikin mas'alolin da aka samu sabani a cikinsu saboda kawai zaton rashin mallakan sharuddan A'alamiyya ga A'alam.
18: Yayin da aka bayyana wasu malamai da cewa su ne A'alam a cikin wasu mas'aloli (ta yadda ko wani daya daga cikinsu A'alam ne a cikin wasu takamammun mas'aloli). Shin ya halatta komawa gare su ko kuma a'a?
A: Rarraba takalidi babu matsala a cikinsa, ballantana idan har A'alamiyyar kowane daya daga cikinsu ta zamana akan mas'alar da yake masa takilidi ne to a wannan hali wajibi ne bisa ihtiyat ya rarraba taklid idan har fatawoyinsu sun bambanta.
19: Shin ya halatta takalidin wanda ba A'alam ba tare da cewa akwai a'alam?
: Taklidin wanda ba A'alam ba cikin mas'alolin da fatawoyinsa ba su saba wa fatawoyin A'alam ba babu matsala cikinsa.
20: Mene ne ra'ayinka dangane da shardanta A'alamiyyar marja'i, sannan kuma mene ne dalilin hakan?
: Matukar aka samu yawaitar fukaha'un da suka cika sharudda amma kuma suka sami sabani cikin fatawa, to biya ihtiyati, dole ne mukallafi yayi takalidi da A'alam sai dai idan ya tabbata cewa fatawarsa ta saba wa ihtiyati sannan fatawar wanda ba A'alam din ba ta yi daidai da ihtiyatin. Hujjar wajibcin yin takalidi wa A'alam ta ginu ne bisa tushen hankali da hukumci na hankali. Saboda hujjar fatawar A'alam ga mai takalidi yakini ne shi kuwa zancen wanda ba A'alam ba zato ne.
21: Wane ne ya wajaba mu yi masa takalidi?
: Ga mujtahidin da ya cika sharuddan ba da fatawa da kuma marja'iyya, kana kuma ya kasance A'alam a bisa ihtiyat.
22: Shin ya halatta a yi takalidi ga mamaci a farkon farawa?
: Dangane da fara yin takalidi bai kamata a bar ihtiyati wajen fara takalidi da rayayyen mujtahidi wanda yake A'alam ba.
23: Shin yin taklidi ga mujtahidin da ya rasu, ya dogara ne kan taklidin rayayyen mujtahidi ko kuma a'a?
: Halaccin taklidin mamaci a farkon farawa, ko kuma ci gaba da takalidin mamaci duka ya ta'allaka ne da izinin rayayyen mujtahidi A'alam