Polly po-cket
Uzairu badamasi

BARKA DA ZUWA SHAFI MAI ALBARKA

Alhamdulillah muna muku albishir insha Allah zamu dawo aiki gadan gadan!


Shafin farko

Haidar Ali

Hanyoyin Tabbatar Da Ijtihadi Da Aalamiyya Da Kuma Gano Fatawa

Ali Khamenei4

T24: Shin wajibi bayan na gano cancantar wani mujtahidi ta hanyar shaidar adilai guda biyu in sake tambayan wasu kan hakan?

A: Shaidar adilai guda biyu daga cikin ma'abuta sani (Ahlul khibra) kan cancantar wani mujtahidi wanda ya cika sharuda ya wadatar, ba wajibi ba ne sai an sake tambayar wasu jama'a.
T25: Yaya ake zaben marja'i da kuma karban fatawoyinsa?

A: Gano ijtihadi ko kuma A'alamiyyar marja'in da ake masa takalidi ya kan faru ta hanyar gwaji, ko kuma ta hanyar ilimi kan haka ko da kuwa ilimin ya samu ne ta hanyar yaduwar labarin cikin mutane ko kuma ta hanyar samun nitsuwa ko kuma ta hanyar shaidar adilai biyu daga masana.
Ita kuwa fatawar mujtahidi akan same ta ne ta hanyar:
1. Ji daga gare shi.
2. Fadin adilai biyu kai ko da ma adali guda daya ne.
3. Fadin wani amintacce wanda ake nitsuwa da maganarsa.
4. Ta hanyar komawa ga risalarsa matukar ta kubuta daga kura-kurai.
T26: Shin wakilci wajen zaban marja'i misalin wakilcin mahaifi ga dansa ko malami ga dalibinsa ya inganta?

A: Idan har abin nufi da wakilcin shi ne mika aikin binciken marja'in da ya cika sharudda ga mahaifi ko malami ko wani na daban ne, to babu matsala cikin hakan, ra'ayinsa kan hakan kuma idan har ya ginu bisa ilimi ne sannan kuma aka sami kwanciyar hankali da shi da tabbas cikinsa, shari'a ta amince da shi kuma ya zama hujja.
T27: Na tambayi wasu malamai wadanda mujtahidai ne kan wane ne A'alam sai suka amsa min da cewa yin taklid wa wane (suka ambaci sunansa)yana wadatarwa, to shin yana halatta in dogara ga maganarsu tattare da jahilcina kan A'alamiyyarsa ko kuma ina shakkan hakan ko kuma ina da yakinin cewa shi ba a'alam ba ne saboda wasu mutane da su ma aka ba da irin wannan shaidar dangane da su, shin zan iya yarda da maganar wadannan mutane in yi takalidi wa wannan mujtahidi?

A: Idan har dalili na sharia (shaidar adilai biyu) ya tabbata kan A'alamiyyar mujtahidin da ya cika sharudda, matukar dai babu wata hujja ta shari'a da ta zo ta yi inkarin wannan shaidar, to ita wannan shaidar ta zama hujja ta shari'a wanda za a dogara a kan ta kana ba sharadi ba ne a ce sai an sami yakini ko nitsuwa a kan haka. Sa'an nan kuma ba wajibi ba ne a irin wannan hali a ce za a binciko wata shaidar da ta saba wa hakan.
T28: Shin ya halalta mutumin da ba shi da izinin nakalin fatawar wani marja'i daga wajensa ko kuma a wasu lokuta an san shi da ba da fatawar kuskure ya dauki nauyin nakalin fatawar mujtahidin ko kuma bayani hukumce-hukumcen shari'a? Shin me ya kamata mu yi a lokacin da wannan mutumin ya ke karanta mana hukumci daga littafin hukumce-hukumce na mujtahidi (risalatul Amaliyya).

A: Aikin nakalin fatawan mujtahidi da bayanin hukumce-hukumcen shari'a samun izini ba sharadi ba ne. Amma mutumin da yake yin kuskure cikin hakan ba ya halalta ya riki wannan aiki. A duk lokacin da ya fahimci ya yi kuskure wajen bayanin fatawar wajibi ne ya sanar da wadanda suka saurare shi wannan kuskure da ya yi. Ala kulli hal, bai inganta ga mai saurare yayi aiki da abin da ya ji ba har sai ya sami yakinin ingancin abin da aka fada masan



.
Copyright © 2018~2022.
( Uzairu Badamasi Sufi )
Harkarmusulunci@yahoo.com
All rights reserved

Bamu Da Alhakin Tallar Da Ake Sawa Akan Wannan Website Din