BARKA DA ZUWA SHAFI MAI ALBARKA
Alhamdulillah muna muku albishir insha Allah zamu dawo aiki gadan gadan!Kunya
Manzon Allah (s.a.w.a) ya
ce:-
ﺍﻟﺤﻴﺎﺀُ ﺣﻴﺎﺀﺍﻥ ﺣﻴﺎﺀُ ﻋـﻘـﻞٍ ﻭﺣﻴﺎﺀ
ﺣﻤﻖٍ ﻓﺤﻴﺎﺀ ﺍﻟﻌـﻘـﻞ ﺍﻟﻌﻠﻢ ﻭﺣﻴﺎﺀُ
ﺍﻟﺤُﻤﻖِ ﺍﻟﺠﻬﻞ
"Kunya ta kasu kashi biyu:
Kunya ta hankali da kunya
ta wawanci. Kunya ta
hankali ita ce ilimi, yayin da
kunya ta wawanci ita ce
jahilci".
(Tuhaful-Ukul shafi na 45).
*****
Kunya ta hankali ita ce
mutum ya zame yana jin
kunya kan asasi na hankali,
misali mutum ya ji kunyar
aikata laifi, ko ya ji kunyar
mutum mai mutunci da ake
girmamawa. Irin wannan
kunyar ilimi ce. Wato dabi'a
ce ta masu hankali. Ita
kuwa kunya ta jahilci ita ce
jin kunyar tambaya ko
neman ilimi ko kuma jin
kunyar gudanar da ibada
da makamantansu. Misali
mutum ya ji kunyar yin
sallah a wasu wajaje da ya
samu kansa ciki. Irin
wannan kunya dabi'a ce ta
jahilai.