Old school Swatch Watches
Uzairu badamasi

BARKA DA ZUWA SHAFI MAI ALBARKA

Alhamdulillah muna muku albishir insha Allah zamu dawo aiki gadan gadan!


Shafin farko

Haidar Ali
HUKUNCE-HUKUNCEN RUWA

Ali Khamenei4

T70: Idan sashin kasa na ruwa mara yawa (al'maul kalil) wanda yake gangarowa daga sama ba da karfi ba ya shafi najasa, to shin sashin samansa yana nan da tsarki ko kuwa?

A: Sashin sama na ruwan da yake gangarowa yana da tsarki idan dai har gangarowar tasa ta kasance ta yadda za'a iya kiranta gangarowa ce daga sama zuwa kasa.
71: Shin wajibi ne yayin wanke tufafi mai najasa da ruwa mai gudu ko kuma ruwan kur a matse shi a wajen ruwan kafin ya tsarkaka ko kuma yana ma iya tsarkakuwa idan aka matse shi a cikin ruwan?

A: Matsewa ko jijjigawa a cikin ruwan ya wadatar.
72: Yayin wanke darduma ko ‘carpet' mai najasa da ruwan famfo, shin saduwar ruwan da wurin najasar kawai ya kan tsarkake su ko kuma sai an fitar da ruwan wankin daga jikinsu?

A: Yayin tsarkake abu mai najasa da ruwan famfo, fitar ruwan wankin ba sharadi ba ne face dai mujarradin isar ruwan ga wurin da ya najastu bayan gushewar najasar da share ruwan wankin da hannu yayin da ruwan famfon yake zuba, ya wadatar.
73: Mene ne hukuncin alwala da kuma wanka da ruwan da a dabi'ansa shi mai kauri ne? Misali kamar ruwan teku da saboda yawan gishirin da ke cikinsa ya mai da shi mai kauri.

A: Kaurin ruwa saboda kasantuwan gishiri a cikinsa ba ya hana a kira shi "Ruwa Mudlak". A shar'ance abin da ke tabbatar da kasantuwan ruwa "mutlaki" shi ne idan har jama'a za su kira shi da sunan mutlaki.
74: A wasu lokuta a kan sanya wa ruwa wani sinadarin da ke sanya shi ya zamanto da launin madara, to shin wannan ruwa ya zama "ma'ul Mudaf" ruwa wanda ya cudanya? Shin mene ne hunkuncin alwala ko tsarki da shi?

A: Hukuncinsa ba hukuncin "ma'ul Mudhaf" (ruwan da ya cudanya) ba ne.
75: Idan ruwa mai gishiri-gishiri ya tafasa, shin ana iya alwala da ruwan da ya taru na daga tururinsa?

A: Idan har abin da ya taru na daga wannan za'a iya kiransa "ma'ul Mudlak" (wato ruwa mutlaki) to ana iya amfani da shi.
76: Yayin tsarkake tafin kafa ko kuma takalmi, sharadi ne mutum yayi tafiya na kimanin taku sha biya. To shin hakan yana nufin bayan kawuwar najasar ne ko kuma taku sha biyar din kawai ya wadatar ko da kuwa najasar tana nan? Sannan shin idan najasar ta kawu da taku sha biyar shi kenan kafar ko takalmi ya tsarkaka?

A: Mutumin da tafin kafarsa ko kasan takalminsa ya najastu saboda tafiya a kan kasa, to idan yayi tafiya a kan busasshiyar kasa mai tsarki na kimanin taku goma to kafar tasa ko kuma takalmin ya tsarkaka amma da sharadin cewa najasar ta kawu.
77: Shin tafiya kan titin da sanya masa kwalta yana tsarkake tafin kafa ko kasan takalmin da ya najastu?

A: Kasar da aka sanya mata kwalta da makancinta ba ta tsarkake tafin kafa ko kuma kasan takalmi.
78: Shin rana tana daga cikin abubuwa masu tsarkakewa? Idan tana daga ciki, shin wasu sharudda ne suke tattare da shi.

A: Saukar rana kan kasa da sauran abubuwan da ba a iya daukansu irin su gine-gine da abubuwan da aka kafa su irinsu katako, kofa, taga da sauransu takan tsarkake su amma da sharadin cewa kafin ranar ta sauka an kawar da asalin najasar sannan kuma ranar ce ta busar da najasar.
79: Yaya za'a iya tsarkake tufafi masu najasan da launinsu yake zuba a cikin ruwan yayin tsarkake su?

A: Idan dai har zuban launin ba zai iya canza ruwan ya koma "mudaf" ba, to za'a iya tsarkake su ta hanyar zuba ruwa a kansu.
80: Mutum ne ya zuba ruwa a langa dan wankan janaba, to yayin da yake wankan sai wani sashi na ruwan da ke zuba daga jikinsa ya kasance yana komawa cikin langar, to shin hakan yana najasta ruwan? Shin akwai wani abin da zai hana ni gama wankan da wannan ruwan?

A: Idan har ruwan da ke zuba cikin langar yana zuba ne daga sashin jikinsa dake da tsarki, to ruwan yana da tsarki kuma babu wani abin da zai hana shi karasa wankan da shi.



.
Copyright © 2018~2022.
( Uzairu Badamasi Sufi )
Harkarmusulunci@yahoo.com
All rights reserved

Bamu Da Alhakin Tallar Da Ake Sawa Akan Wannan Website Din