XtGem Forum catalog
Uzairu badamasi

BARKA DA ZUWA SHAFI MAI ALBARKA

Alhamdulillah muna muku albishir insha Allah zamu dawo aiki gadan gadan!


Shafin farko

Haidar Ali
HUKUNCE- HUKUNCEN SHIGA BAYAN GIDA

Ali Khamenei4

T81: Irin kabilun nan masu yawo daga guri zuwa guri (kamar fulani) idan ba su mallaki ruwan da za su yi tsarki da shi ba, to shin suna iya amfani da itace ko tsakuwa wajen tsarkake wajen fitan fitsari? Sannan kuma shin suna yin salla da hakan?
A: Wanin ruwa ba ya tsarkake wajen fitar fitsari. To amma sallar mutumin da ba zai iya tsarkake jikinsa da ruwa ba, sallarsa ta inganta.
82: Mene ne hukuncin tsarkake mafitar fitsari da bayan gida da ruwa kadan ma'ul kalil .

: Ihtiyati wajen wanke mafitar fitsari da ruwa kadan shi ne a wanke shi sau biyu, amma mafitar bayan gida wajibi ne a wanke shi har sai ainin najasar da alamunta ta gushe.
83: A bisa al'ada wajibi ne ga mai salla bayan gama fitsari ya yi istibra'i to amma ni ina da wani ciwo a al'aura ta, yayin da nake istibra'i jini ya kan fito min a dalilin mammatse shi da nake yi kana ya hadu da ruwan da nake amfani da shi wajen tsarkin sannan ya najasta min jiki da tufa, kana idan har ban yi istibra'i ba to ina sa tsammanin warkewan ciwon, kuma abu ne sananne cewa ciwon zai ci gaba da wanzuwa idan na ci gaba da istibra'i saboda mammatse al'auran da nake yi. Don haka nake so ka min bayani shin zan yi istibra'i ko kuma a'a?

A: Shi dai istibra'i ba wajibi ba ne, idan ma har zai cutar to ba ya halatta a yi shi. Na'am idan har ba'a yi istibra'i ba bayan gama fitsari sai wani danshi mai rikitarwa ya fito to ana daukansa a matsayin fitsari ne.
84: A wasu lokuta wani danshi (ruwa) mai kama da fitsari ya kan fito ma mutum ba tare da son sa ba bayan fitsari da kuma istibra'i. To shin wannan danshin najasa ne ko kuma yana da tsarki? Kana idan mutum ya fahimci hakan bayan wani lokaci, to mene ne hukuncin sallolin da ya riga ya yi? Sannan shin wajibi ne a nan gaba ya binciki fitar wannan danshi da ke fita ba tare da zabinsa ba?
: Idan wani danshi ya fito bayan istibra'i kana aka yi shakkan kasantuwarsa fitsari to bai da hukuncin fitsari, yana da tsarki, ba wajibi ba ne a yi wani bincike.
85: Don Allah ko za ka mana karin bayani kan nau'oin ruwa da suke fitowa daga jikin mutum.

A: Danshin ruwan da a wasu lokuta yake fitowa bayan maniyyi ana kiransa da' wazi", kana ruwan da ke fitowa a wasu lokuta bayan fitsari ana kiransa da "wadi". Sannan ruwan da ke fitowa a wasu lokuta bayan wasanni tsakanin ma'aurata biyu ana kiransa da "mazi". Dukkan wadannan ruwa masu tsarki ne, ba sa warware tsarki.
86: Sakamakon cutar da nake da ita a hanyar fitsarina, don haka bayan na yi fitsari da yin istibra'i, fitsarin ba ya yankewa na kan ga danshin ruwa. Don haka na tafi wajen likita don magani amma bayan magani na wani lokaci ban sami sauki ba. A irin wannan hali mene ne hukumcin shari'a da ya hau kaina?

A: Bayan istibra'i ba a damuwa da shakkan da ake yi kan fitar fitsari. Idan har kana da yakinin cewa fitsari ne yake fita maka dis-dis, to dole ne ka yi aiki da hukumcin mutumin da fitsari yake yawan fita masa da aka yi bayaninsa cikin Risalar marigayi Imam Khumaini (r.a), babu wani karin hukumci kan hakan.
87: Ya ya ake istibra'i kafin wanke wajen fitar bayan gida?

A: Babu bambanci tsakanin yadda ake istibra'in wajen fitar bayan gida kafin tsarkake shi da bayan tsarkake shi
88: Aiki a wasu kamfanoni da cibiyoyi: ya ta'allaka da gudanar da wasu bincike kan lafiyar mutum da hakan ya kan kai ga bude al'aura a wani sa'i, to shin hakan ya halatta idan akwai bukatuwa ga aikin?

: Ba ya halatta ga mutum ya bude al'aura gaba ga wani mutum ko da kuwa aikin da za a ba shi ya taallaka da hakan ne sai dai idan barin aikin zai sa shi cikin halin kaka nikai, kana kuma ya zama dole ne ya yi hakan.
89: Yayin biyan bukata, sau nawa ne ake wanke wajen fitar fitsari kafin ya tsarkaka?

A: Bisa ihtiyati na wajibi ana wanke wajen fitar fitsari sau biyu ne da ruwa kadan kafin ya tsarkaka.
90: Ya ya za mu tsarkake wajen fitan bayan gida?

A: Ana tsarkake wajen fitan bayan gida ne ta hanyoyi biyu: Na farko a wanke shi da ruwa har najasar ta kawu, to daga nan ci gaba da zuba ruwa ba wajibi ba ne. Na biyu shi ne a tsarkake shi da tsakuwa guda uku ko wani tsumma da makamantan hakan, idan har najasar ba ta kawu da tsakuwa guda ukun ba sai a sanya wasu tsakuwa a kawar da shi sosai. Sannan kuma ana iya amfani da bangarori uku na tsakuwa guda ko tsumma maimakon ukun.



.
Copyright © 2018~2022.
( Uzairu Badamasi Sufi )
Harkarmusulunci@yahoo.com
All rights reserved

Bamu Da Alhakin Tallar Da Ake Sawa Akan Wannan Website Din