T:91: Na yi alwala amma da niyyar sallar magariba ne, to shin ina taba Alkur'ani mai girma da sallar lisha da wannan alwalar?
A: Idan har an yi alwala kamar yadda ya dace, to matukar dai alwalar ba ta baci ba, aikata duk wani aikin da ke bukatar alwala da wannan alwalar ya halalta.
92: Mutumin da ya sanya wa kansa gashin kanti, idan cire shi zai zama da wahala a gare shi, to shin ya halatta ya yi shafa a kan wannan gashi (yayin alwala) .
: Ba ya halatta a yi shafa a kan gashin kanti, wajibi ne a kawar da shi dan shafan kai. Amma idan har an an dasa gashin ne a jikin fatan kai sannan kuma kawar da shi yana da wahalan gaske da a bisa dabi'a ba za a iya jurewa ba, to yin shafa a kansa ya halalta.
93: Wani ya gayi min cewa: Yayin alwala sau biyu kawai ake zuba ruwa a fuska, amma yin hakan sau uku yana bata alwala. Shin hakan gaskiya ne?
A: Dangane da wanke gabobi lokacin alwala, wankin farko wajibi ne, na biyu kuma ya halalta, wani abu sama da hakan ba ya halalta. Sai dai yana da kyau a san cewa abin lura wajen ayyana kowani wanki shi ne niyyar mutum. Ko da ya zuba ruwa da yawa amma da niyyar wanki guda babu matsala cikin hakan.
94: Yayin alwala ‘irtimasi', shin yana halalta mu sanya hannaye da fuskarmu sau da yawa a cikin ruwa ko kuma sau biyu ne kawai ya halalta?
A: Sau biyu ne kawai ya halalta. Na farkon wajibi na biyun kuma halal sama da haka bai halalta ba. Amma dangane da hannaye wajibi ne yayin da mutum zai fitar da su daga cikin ruwan ya zamanto yayi niyyar wanke su wanki na irin na alwala, don ya samu damar shafa da ruwan.
95: Shin ana iya kirga man da a bisa dabi'ar jikin mutum ya kan fito a kan gashin kai ko fatansa a matsayin hajib(abin da ke hana isar ruwa ga fata).
: Ba'a kirga shi a matsayin hajib sai idan ya kai matsayin da zai hana isar ruwa zuwa ga fatar jiki ko kuma gashi.
96: Tsawon lokaci nayi ba na shafa kafafuna daga kan yatsuna, na kan shafa kan kafata ne da wani sashi na yatsun kawai. Shin hakan ya inganta? Idan bai inganta ba, to shin dole ne in sake sallolin da na yi da irin wannan alwalar?
A: Matukar shafan kafa ba ta hada da kan yatsu ba, to alwala ba ta yi ba, wajibi ne a sake sallolin da aka yi. Amma idan har shakku mutum yake yi kan cewa shin yayin da yake alwala yana shafa ne daga ‘yan yatsunsa ko kuma a'a? To alwala da sallolin da ya yi sun inganta.
97: Yayin shafan kafafu, har zuwa ina ne za a shafa din?
A: Dole ne a yi shafan kafa har zuwa wajen da ya dan taso sama na kafar mutum wanda ake kira da tudun saman kafa.
98: Mene ne hukumcin alwala a masallatai da ma'aikatun gwamnati da gwamnatocin sauran kasashen musulmi suke ginawa?
A: Ya halalta, babu wani hukumci na shari'a da ya hana hakan.
99: Idan aka sami idaniyar ruwa tana bubbugowa daga wani guri (kasa) wanda yake gurin mallakar wani mutum ne to idan muna so mu jawo wannan ruwa ta hanyar amfani da bututun ruwa zuwa wani guri da ke da nisar kilomitoci hakan zai tilasta mana bi da wadannan bututu cikin filin wannan mutumin da kuma filayen wadansu mutane, to idan har wadannan mutane ba su yarda da hakan ba, shin ya halatta ayi amfani da wannan ruwa dan alwala da wanka da sauran ayyukan tsarki?
A: Babu matsala wajen amfani da ruwan idan har idaniyar ruwa tana wajen da ba mallakan wani ba ne sannan kafin gudanar ruwan akan kasa aka ja shi zuwa cikin wadannan bututu da kai shi inda ake son kai shi sannan kuma yin hakan ba a ganinsa a matsayin amfani da kayan wani.
100: Ma'aikatar ruwa ta kafa dokar hana sanya amfani da na'urar da ke kara karfi zuwan ruwan famfo, to sai dai a wasu yankunan ruwan ba ya zuwa da karfi don haka ya zama dole mutanen yankin su yi amfani da irin wannan na'ura matukar suna son ruwan ya isa zuwa ga saman gidajen sama. To haka muke son ka amsa mana wadannan tambayoyi guda biyu:
1- Shin ya halalta a sanya na'urar da ke karfi zuwan ruwa don a sami damar amfani da ruwa sosai?
2- Idan har hakan bai halalta ba, to mene ne hukumcin alwala da wankan da aka yi da irin wannan ruwa?
A: A irin wannan yanayi da tambayar ta nuna sanya irin wannan na'ura da amfani da ita ba ya halalta, akwai matsala cikin alwala da wankan da aka yi da ruwan da aka samu ta wannan hanya.
101: Yayin wanke fuska da hannaye lokacin alwala idan da mutum zai dinga budewa da kuma rufe famfon da yake alwala da shi, to mene ne hukuncin wannan taba famfo da yake yi da hannunsa mai danshi.
A: Babu matsala ga hakan, ba ya cutar da ingancin alwala. To amma bayan gama wanke hannun hagu kafin yin shafa da shi idan da mutum zai sanya shi a kan ruwan da ke kan famfon to akwai matsala wajen ingancin alwalarsa idan dai har aka dauka ruwan da ke hannunsa da ruwan da ke famfon sun cudanya.
102: Shin muna iya amfani da wani ruwan da ba na alwala ba wajen yin shafa? Sannan kuma shin dole shafan kai ya zamanto da hannun dama sannan kuma daga saman kai zuwa kasa?
A: Shafan kafa da kai dai dole ne ya zamanto daga danshin ruwan alwala da ya saura a hannu ne, idan har babu sauran danshin to ana iya shafo danshin ruwan da yake jikin gemu ko gira a yi shafan da shi. A bisa ihtiyati ana shafan kai ne da hannun dama. To amma shafan kai daga sama zuwa kasa ba dole ba ne.
103: Wasu mata suna da'awar cewa sanya jan farce akan farce ba ya hana alwala, kana kuma yin shafa akan safa mara kauri (shara-shara)yana halatta. Mene ne fatawarka kan hakan?
A: Idan har jan farcen yana hana isar ruwa zuwa ga faratu to alwala ta baci. Sannan shafa akan safa ba ya inganta komi shara-sharanta.
104: Saboda ciwon shan inna da na samu a kafata sai ya zamanto ina amfani da wani takalmi na musamman da kuma sanduna biyu wajen tafiya. To saboda cire wadannan takalma yayin alwala ba zai yiwu ba, don Allah ina son ayi min bayani kan abin da ya wajaba a kaina dangane da shafan kafa?
A: Idan har cire takalmin dan shafan kafa zai zamanto kunci gare ka, to shafa a kansa ya wadatar kana ya inganta.
105: Yaya mutum mai yawan waswasin alwalarsa zai yi salla, ko karatun Alkur'ani da ziyarar kabarin Ma'asumai (a. s)?
: Ba'a damuwa da shakkan tsarki bayan alwala. Ya halatta ya yi salla da karatun Alkur'ani da ziyara matukar dai bai sakankance da bacin alwalarsa ba.
106: Shin gudanar ruwa ga dukkan gabobin hannu sharadi ne na ingancin alwala ko kuma shafansu da sauran danshin da ke jikin hannu ya wadatar?
A: Ma'aunin tabbatuwar wankewa shi ne isar da ruwa ga dukkan gabobi ko da kuwa ta hanyar shafa hannu ne. To amma shafa da danshin da ke hannu kadai ba ya wadatarwa.
107: Yayin shafan kai, shin shafan gashi da danshin hannu ya wadatar ko kuwa wajibi ne danshin ruwan ya taba fatan kai?
: Shafan fatar kai (yayin alwala) ba wajibi ba ne, face dai shafa gashin gaban kai ya wadatar.
108: Mene ne hukuncin jinkirtawa tsakanin gabobin alwala ko wanka?
A: Rashin gaggautawa a cikin wanka ba matsala ba ce to amma a alwala idan har jinkirtawar zai kai ga bushewar gabobin da aka riga aka wanke to alwala ta baci.
109: Mutumin da tusa yake yawan fita masa, me ya kamata ya aikata yayin alwala da salla?
A: Idan har ba zai iya rike alwalarsa har zuwa karshen sallarsa ba, kana kuma sassake alwala yayin salla zai zamanto kunci a gare shi, to ya hatatta ya yi salla guda da alwala guda, wato ya takaita da alwala guda ga kowace salla ko da kuwa alwalar ta baci yayin sallar.
110: Wasu mutanen da ke zaune a gungun gidajen da jama'a suke da yawa sukan ki biyan kudaden da ake Tarawa don gudanar da lamurran gidajen da suka hada da biyan kudaden ruwa da na masu gadi da sauransu. Shin azumi da salloli da sauran ibadun da suke yi a wajen ya inganta?
A: Wajibi ne kowani guda daga cikin mutanen da suke wajen ya biya kudaden da suke kansa. Idan har ya ki biyan kudaden ruwa to akwai matsala cikin alwala da wankan da yake yi, kai ba su ma inganta ba.
111: Mutum ne ya yi wankan janaba, to sai bayan awa 3 zuwa 4 ya so ya yi salla to amma bai san cewa shin wankansa ya baci ne ko kuma a'a, to shin akwai matsala idan ya yi alwala don samun kwanciyar hankali (ihtiyat)?
A: A bisa wannan yanayi da ka ambata sake alwala ba wajibi ba ne, to amma yin "ihtiyat" ya halatta.
112: Mene ne hukuncin wata gaba daga cikin gabobin alwala da ta najastu bayan wanke ta amma kafin idar da alwalar?
A: Hakan ba ya cutar da ingancin alwala, na'am wajibi ne a tsarkake wannan gabar idan za'a yi salla.
113: Shin kasantuwar digo- digon ruwa akan kafa yana cutarwa yayin shafa?
A: Wajibi ne a busar da wurin shafa daga duk wani digo na ruwa kafin yin shafan.
114: Shin shafan kafar dama yana faduwa idan har hannun daman mutum a yanke yake daga asalinsa?
A: A'a ba ya faduwa, face dai wajibi ne a yi shafan da hannun hagu.
115: Mutumin da yake da ciwo ko karaya a daya daga cikin gabobin alwalarsa, wani hukumci ne ya hau kansa?
: Idan mutum yana da ciwo ko karaya a daya daga cikin gabobin alwalarsa sannan kuma saman ciwon a bude yake (wato babu bandeji) sannan kuma isar da ruwa zuwa ciki ba zai cutar da shi ba, to wajibi ne ya wanke wajen. Amma idan har wankewa zata cutar da shi to wajibi ne ya wanke gefe-gefen ciwon. A bisa ihtiyati matukar shafa kan ciwon ba zata cutar ba to ya shafa din.
116: Mene ne hukumcin mutumin da yake da ciwo a wajen shafansa?
A: Idan ba zai iya shafa wajen shafan ba to a nan wajibi ne ya yi taimama maimakon alwala. Amma idan har zai iya sanya tsumma kan ciwon sannan ya shafi kansa, to a bisa ihtiyati bayan taimamar sai ya yi alwala ta hanyar irin wannan shafan.
117: Mene ne hukuncin mutumin da ya jahilci karyewar alwalarsa sai bayan ya gama ya fahimci hakan?
: Wajibi ne ya sake alwalar, haka kuma ya sake duk wani aikin da ke bukatar alwala kamar salla da ya yi da wannan alwalar a baya.
118: Mene ne hukumcin mutumin da yake da ciwo a daya daga cikin gabobin alwalarsa kuma jini yana ci gaba da fitowa ko da kuwa ya sa bandegi ne?
A: Wajibi ne ya sanya wani abu misali leda a kan ciwon (a matsayin bandegi) ta yadda jini ba zai dinga fitowa ba.
119: Shin share ruwan alwala bayan idarwa makaruhi ne? Kana rashin sharewar mustahabi ne?
: Idan har an kebance wa wannan aiki wani kyalle na musamman ne, to babu wata matsala ga hakan.
120: Shin irin launi da mata suke shafawa akan gashin kai da giransu don rina su yana bata alwala ko wanka?
A: Idan har ba shi da maikon da zai hana isar ruwa ga gashin, shi dai kawai launi ne, to ba ya bata alwala ko wanka.
121: Shin ruwan biro yana daga cikin abubuwan da suke hana isar ruwa ga fata, ta yadda kasantuwarsa a hannu kan iya bata alwala?
: Idan har yana hana isar ruwa ga fata to yana bata alwala, gane hakan kuwa yana hannun mukallafi ne.
122: Idan danshin shafa kai ya hadu da danshin fuska, shin alwala ya kan baci?
: Bisa la'akari da cewa shafan kafa wajibi ne ayi shi daga sauran danshin ruwan alwala da ya rage a hannu. Don haka wajibi ne yayin shafa kai a kula kada hannu ya isa zuwa ga goshi ta yadda ba zai hadu da danshin da ke fuska ba, don kada danshin hannu wanda za'a shafa kafa da shi ya hadu da danshi fuskar.
123: Mene ne hukuncin ruwan da ake kokwantonsa cewa fitsari ne ko maniyyi wanda ya fito bayan mutum ya yi fitsari da kuma istibra'i kana kuma ya yi alwala?
A: A wannan yanayi wajibi ne a hada alwala da wanka don a sami yakini kan tsarki.
124: Muna fatan za'a mana bayanin bambancin da ke tsakanin alwalan maza da na mata?
: Babu wani bambanci tsakanin mace da namiji wajen ayyukan alwala da kuma yanayin alwalar, sai dai kawai mustahabi ne ga maza yayin wanke damtsensu su fara da wajensa, su kuma mata mustahabi ne su fara da cikinsa.