Disneyland 1972 Love the old s
Uzairu badamasi

BARKA DA ZUWA SHAFI MAI ALBARKA

Alhamdulillah muna muku albishir insha Allah zamu dawo aiki gadan gadan!


Shafin farko

Haidar Ali
TABA SUNAYEN ALLAH DA KUMA AYOYINSA

Ali Khamenei4

T125: Mene ne hukuncin taba lamiran da suke komawa ga zatin Allah Ta'ala kamar lamirin da ke cikin (بسمه تعالى) "Bismihi Ta'ala" (wato "hi" da ya zo a wannan lafazi.)?

A: Lamiri ba shi da hukuncin lafazin sunan Allah.
126: A wasu lokuta akan rubuta ((الله da haka (ا...) to shin mene ne hukuncin taba wadannan kalmomi ba tare da alwala ba?

A: Wannan Alif (hamza) da wadannan digo guda uku ba sa da hukuncin sunan Allah don haka taba su da ba tare da alwala ba, ya halalta.
: 127: Makafi sukan yi amfani da rubutunsu da ake kira ‘Brel' wajen karatu da rubutu ta hanya shafa wadannan alamomi da hannayensu. To shin wajibi ne su zamanto cikin alwala yayin da suke karatun Alkur'ani da sunaye masu tsarki da aka rubuta da irin wannan rubutu ko kuma a'a?

A: Irin wadannan alamomi da aka yi da suke nufin haruffan asali ba su da hukumcin haruffan asali. Don haka ba wajibi ne a zamanto cikin alwala yayin taba su.
128: Mene ne hukuncin taba sunayen mutane kamar Abdullahi ko Habibullah ba tare da alwala ba?

A: Ba ya halatta ga mara alwala ya taba sunan Allah ko da kuwa ya kasance wani bangare ne na hadadden suna (kamar Abdullah).
129: Shin ya halatta ga mace mai haila ta sanya abin wuyan da aka rubuta sunan Manzon Allah (s.a.w.a) a jiki?

A: Sanya shi a wuya ba matsala, sai dai wajibi ne bisa ihtiyati kada sunan Manzon Allah (s.a.w.a) ya taba jikinta.
130: Shin haramcin taba rubutun Alkur'ani mai girma ba tare da alwala ba ya kebanta ne kawai idan rubutun na cikin Alkur'anin ne ko kuma ya hada da ko da yana jikin wani littafi ne daban, ko allo, ko katanga da dai sauransu?

A: Haramcin taba kalmomi da ayoyin Alkur'ani mai girma ba tare da alwala ba kawai ya kebanta da Alkur'ani ba ne, a'a ya hada da kalmomi da ayoyin Alkur'ani ko da kuwa a wani littafi na daban ne, ko cikin jarida, ko mujalla, ko allo ko kuma rubutu a jikin garu da dai sauransu .
131: A jikin wasu kwanuka da farantai da iyalanmu suke cin abinci an rubuta wasu ayoyin Alur'ani kamar ayatul kursiyyi, niyyarsu na yin hakan kuwa ita ce neman alheri da kuma albarka. To shin akwai wata matsala cikin hakan?

A: Babu matsala ga hakan, sai dai wajibi ne a kiyaye kada a taba ayoyin kur'ani ba tare da alwala ba.
132: Shin wajibi ne mutanen da suke rubuta sunayen Allah ko ayoyin Kr'ani ko sunayen Ma'asumai (a.s) ta hanyar injunan rubutu su kasance cikin alwala yayin rubutun?

A: Ba sharadi ba ne a kasance cikin alwala sai dai taba rubutun ba tare da alwala ba ba ya halatta.
133: Mene ne hukuncin amfani da kan sarki da ake amfani da shi wajen aika wasiku (stamp) wadanda aka rubuta musu ayoyin kur'ani, sannan mene ne hukuncin buga sunayen Allah da ayoyin Alkur'ani ko kuma buga tambarin wasu cibiyoyi da suke dauke da Alkur'ani a cikin jaridu da mujalu da ake yadawa kowace rana?

A: Ba matsala wajen bugawa da kuma yada ayoyin Alkur'ani da sunayen Allah da makamancinsu, sai dai wajibi ne ga wanda suka isa ga hannunsa ya kiyaye hukunce-hukuncen shari'a na rashin wulakanta su da kuma najasta su, da taba su ba tare da alwala ba.
134: A kan rubuta sunan Allah ko ayoyin Alkur'ani a cikin wasu jaridu, to shin ya halatta kunshe abinci da su ko kuma zama a kansu ko kuma shinfida abinci a kansu ko kuma sanya su a kwandon shara, musamman bisa la'akari da matsalar samun wata hanya da za a kiayye su?
: Idan har ana ganin hakan a matsayin wulakanci ne to ba ya halalta. Amma idan ba a ganin hakan a matsayin wukalanci to ba matsala.
135: Mene ne hukuncin jefa abubuwan da suke kunshe da sunayen Allah cikin kogi ko kuma rafi? Shin za'a kirga hakan a matsayin wulakantawa?

A: Ba matsala wajen jefa su cikin kogi ko rafi idan har jama'a ba sa ganin hakan wulakanci ne.
136: Shin sharadi ne yayin jefar da takardun jarabawar da aka riga aka gyara su a cikin kwandon shara ko kuma kona su a tabbatar da rashin kasantuwar sunayen Allah da ma'asumai (a.s) a jikinsu? Sannan shin jefar da takardun da ba'a yi amfani da daya bangarensu ba almubazzaranci ne?

A: Yin bincike ba wajibi ba ne, idan dai har mutun bai san da cewa akwai sunan Allah a jikin takarda ba to jefar da ita cikin shara ba matsala. Amma takardun da aka yi amfani da wani bangare nasu kana za'a iya amfani da daya bangaren wajen rubutu ko kuma amfani da shi wajen wani aiki, to konawa ko kuma jefar da ita akwai matsala a cikinsa.
137: Wadanne sunaye masu albarkan da wajibi ne a girmama su kana haramun ne a taba su ba tare da alwala ba.

A: Ba ya halatta a taba sunayen zatin Allah madaukakin sarki, da kuma sunayen siffofin da suka kebantu da Allah Ta'ala ba tare da alwala ba kana kuma ihtiyat a nan ya wajabta cewa sunayen Annabawa (A.S) da kuma sunayen lmamai (A.S) su ma suna da wannan hukunci da muka ambata.
138: Wadansu hanyoyi ne sharia ta yadda da su wajen gogewa ko shafe sunaye masu albarka da ayoyin kur'ani yayin bukatar hakan? Kana mene ne hukuncin kona takardun da suke da sunayen Allah ko ayoyin Alkur'ani a jikinsu idan har bukatan rabuwa da su da taso?

: Ba wata matsala wajen binne su cikin kasa, ko kuma mayar da su gari, to amma kona su akwai matsala, idan ana ganin konawa a matsayin walakantarwa ne to ba ya halatta, sai dai idan yin hakan ya zama lalura kana ba za'a iya yanke ayoyin Alkur'anin ko sunaye masu albarka ba.
139: Mene ne hukuncin yayyanke sunaye masu albarka da ayoyin Alkur'ani ta yadda babu wasu haruffa guda biyu da suka hade ballantana su karantu? Shin caccanza yanayin rubuta su ta hanyar kara wasu haruffa a kansu, ko kuma shafe wasu haruffa yana wadatarwa wajen goge su da kuma faduwar hukuncinsu?

A: Irin wannan yayyankewa da aka ambata idan har ana iya kirgashi a matsayin wulakantawa to ba ya halalta. Idan kuwa ba haka ba, to matukar yayyankewar ba ta sanya shafe rubutun sunan Allah ko ayoyin kur'anin ba ba ta wadatarwa. Kamar yadda canza yanayin shakalin rubutun ba ya wadatarwa wajen gusar da wannan hukunci akan haruffan da aka zana su da nufin rubuta sunan Allah. Na'am bai yi nisa ba ace hukuncin yana iya faduwa bayan canza shakalin haruffan, ta hanyar ba shi hukuncin shafewa ko da yake ihtiyat shi ne a nisanci yin hakan.



.
Copyright © 2018~2022.
( Uzairu Badamasi Sufi )
Harkarmusulunci@yahoo.com
All rights reserved

Bamu Da Alhakin Tallar Da Ake Sawa Akan Wannan Website Din