Uzairu badamasi

BARKA DA ZUWA SHAFI MAI ALBARKA

Alhamdulillah muna muku albishir insha Allah zamu dawo aiki gadan gadan!


Shafin farko

Haidar Ali
HUKUNCE-HUKUNCEN WANKAN JANABA

Ali Khamenei4

T107: Shin ya halatta ga mai janaba ya yi salla da taimama kana da kuma najasar da ke jiki da tufafinsa idan lokaci ya yi kunci ko kuma ya jira har ya yi tsarki kana ya yi wanka sannan ya yi salla a matsayin ramako?

A: Idan har lokaci ba zai ba shi daman ya tsarkake jiki da tufafinsa ba, ko kuma ya canza tufafin ba, kana kuma ba zai iya salla tsirara ba saboda sanyi da makamancinsa, to sai ya yi salla a wannan hali cikin najasar amma tare da yin taimama wadda za ta zama a maimakon wankan janaba kuma ta wadatar kana ba wajibi ba ne ya rama ta.
108: Shin isar da maniyyi zuwa ga mahaifa ba ta hanyar jima'i ba yana haifar da janaba?

A: Janaba ba ta tabbatuwa da haka.
109: Shin wajibi ne ga mata bayan binciken da ake musu a cikin jikinsu ta hanyar amfani da kayan ayyukan likitanci da su yi wankan janaba .

A: Ba wajibi ba ne su yi wanka matukar dai maniyyi bai fito musu ba.
110: Idan har gwargwadon hashafan namiji ya buya a farjin mace, to amma maniyyi bai fita ba kana kuma macen ba ta kai kolin jin dadinta ba, to shin wanka ya wajaba a gare ta ne kawai ko kuma ga namijin ne kawai ko kuma wajibi ne a kansu su biyun ?

A: A bisa wannan yanayi da aka ambata wajibi ne gare su su biyun.
111: Dangane da mafarkin mata, shin a wani irin yanayi ne wankan janaba yake wajaba a gare su? Kana shin ruwan da yake fito musu yayin wasa da mazaje yana da hukuncin maniyyi ne? Kana kuma shin wajibi ne su yi wanka tattare da cewa basu kai ga jin dadinsu ba kana ba su ji mutuwar jiki ba? A takaice dai yaya janaba take tabbata ga mata ba tare da jima'i ba?

A: Idan mace ta ga alamar maniyyi a jikin tufafinta bayan farkawarta daga barci to wajibi ne ta yi wankan janaba to amma ruwan da yake fito musu yayin wasa da makamancinsa ba shi da hukuncin maniyyi, sai dai idan ya fito tare da mutuwar jiki da kuma isa ga jin dadi na koli.
112: Shin wanka yana wajaba ga budurwar da sha'awarta ta tashi ta hanyar karatun littafan batsa ko kuma ta wata hanya ta daban? To idan har wankan ya wajaba, to wane wankan ne ya wajaba a gare ta?

A: Karanta littattafan da suke motsa sha'awa bai halatta ba. Bisa dukkan hali dai wajibi ne gare ta ta yi wankan janaba idan har maniyyi ya fito mata.
113: Yayin da mace ta fahimci zuban wani ruwa cikin sha'awa lokacin wasa shin wajibi ne ta yi wankan janaba?

A: Idan har mace ta fahimci zuban maniyyi daga gare ta to wanka ya wajaba a gare ta, haka ma idan tana shakkan abin da ya fito din maniyyi ne ko kuma, a a matsawar dai ya fito ne tare da sha'awa ta musamman.
114: Idan mace ta yi wanka daga zarar saduwa da mijinta kana maniyyinsa ya ci gaba da zama cikin mahaifanta, shin wankanta yana nan da ingancinsa idan har maniyyin ya fito mata bayan wankan? Kana shin wannan maniyyi da ya fito bayan wanka yana da tsarki ko kuma a'a ?

A: Wannan maniyyi da ya fito mata najasa ne, sai dai idan har abin da ya fito mata din maniyyin mijin ne to ba ya wajabta wanka a karo na biyu.
115: Macen da ta samu janaba alhali tana cikin haila shin wajibi ne ta yi wankan janaba bayan ta sami tsarki ko kuma ba wajibi ba ne a gare ta tun da daman ba ta da tsarki?

A: Wajibi ne gare ta ta yi wankan janaba bugu da kari kan wankan hailar, ko da yake wankan janaba kawai yana wadatarwa, sai dai ihtiyat shi ne ta daura niyyar wankan biyu.
116: A wani irin hali ne za'a iya hukunta ruwan da ya fito wa mutum da cewa maniyyi ne?

A: Idan har ya biyo bayan sha'awa, da mutuwar jiki da kuma tunkuda yayin fitowa, to yana da hukuncin maniyyi.
117: A wasu lokuta bayan wanka za'a iya ganin sauran sabulu da ya makale a cikin faratun hannu ko na kafa, wanda ba'a iya ganinsa yayin wankan amma bayan fitowa daga bayan gida sai kaga farin sabulun ya bayyana, to mene ne abin yi? Bisa la'akari da cewa wadansu su kan yi wanka ko alwala tare da cewa sun jahilci hakan ko kuma ma hankalinsu bai kai ga hakan ba, kana tare da cewa ba'a da yakinin cewa ruwa ya ratsa wannan farin?

A: Dan kawai kasantuwan fari-farin sabulu wanda ya bayyana bayan gabobin jiki sun bushe bai cutar da ingancin alwala ko wanka, sai idan hakan zai hana tabbatuwan wanke fata.
118: Wani ya gaya min cewa: Wajibi ne kafin yin wanka a tsarkake jiki daga najasa, kana kuma ya ce wai tsarkake jiki dai dai lokacin da ake wanka, wato kamar a tsarkake shi daidai lokacin kana cikin wanka daga maniyyi yana bata wanka, to shin wajibi ne sai na sake Sallolin da na yi su a baya dan kuwa ni dama na jahilci wannan lamari.

: Wajibi ne ya zama an raba tsakanin tsarkake jiki da kuma wankan janaba, to amma ba wajibi ba ne a tsarkake dukkan jikin kafin fara wankan, face dai wajibi ne kowace gaba ta zan tana da tsarki yayin wanke ta, dan haka da mutun zai zan gabansa tana da tsarki kafin wanke ta, to wanka da sallarsa duk sun inganta, to amma fa idan da gaba za ta zama ba ta da tsarki kafin wanke ta, to wanka da sallar ba su inganta ba, wajibi ne ya sake su.
119: Idan mutum yayin wankan janaba sai ya yi wani abin da ke bata alwala, to shin wajibi ne ya faro wankan daga farko ko kuma ya karasa wanka kana daga baya ya yi alwala?

A: Ba wajibi ba ne ya koma ya faro wankan daga farko ba, face dai sai ya karasa wankan, to amma wajibi ne ya yi alwala yayin yin salla ko kuma wani aiki da yake bukatan alwala.
120: Idan wanka iri daban-daban wajibai ko mustahbbai ko dukkansu suka taru wa mutum, shin wanka guda ya kan wadatar?

: Idan har a cikinsu akwai wankan janaba, kuma ya kudura niyyar wankan yana wadatarwa daga sauran hakana wanda ya yi wanka guda daya da niyyar dukkan wanka da ke kansa to ya isar masa kan sauran.
121: Shin wani wanka ba na janaba ba yana wadatarwa daga alwala?

A: A'a ba ya wadatarwa.
122: Idan mutum ya san cewa idan har ya sadu da matarsa ba zai sami ruwan wanka ba, ko kuma lokaci ba zai ishe shi ya yi wanka kana ya yi salla ba, to shin ya halatta ya kusanci matar tasa?

: Idan har zai iya yin taimama a wannan hali, to babu wata matsala ga saduwa da matar tasa.
123: Ni dai saurayi ne dan shekara ashirin da biyu, to a kwanan nan sai gashina ya zama yana zuba wanda hakan ya jawo min matsala, to daga baya sai na kuduri aniyar na sa gashin kanti. To abin tambaya a nan shi ne: Mene ne hukuncin wankana idan har wannan gashi zai hana isar ruwa ga wasu bangarori na fatar kaina domin shi wannan gashin za a yi dashensa ne a kaina?

A: Idan har wannan gashi da aka dasa ba za, a iya cire shi ba, ko kuma kawar da shi din zai jawo maka cutarwa ko kunci, kana kuma ba za ka iya isar da ruwa zuwa ga fatar kan naka ba, to wankan tare da shi ya inganta.



.
Copyright © 2018~2022.
( Uzairu Badamasi Sufi )
Harkarmusulunci@yahoo.com
All rights reserved

Bamu Da Alhakin Tallar Da Ake Sawa Akan Wannan Website Din


XtGem Forum catalog