XtGem Forum catalog
Uzairu badamasi

BARKA DA ZUWA SHAFI MAI ALBARKA

Alhamdulillah muna muku albishir insha Allah zamu dawo aiki gadan gadan!


Shafin farko

Haidar Ali
RASHIN LAFIYA DA KUMA HANIN LIKITA

Ali Khamenei4

T748: Akwai wasu likitoci wadanda hukumce-hukumcen shari'a ba su dame su ba sukan hana marasa lafiya yin azumi wai saboda cutarwa, to shin maganar irin wadannan likitoci hujja ce?

A: Idan har likita ba amintacce ba ne, kuma maganarsa ba ta haifar da nitsuwar zuciya, kana ba ta sa a ji tsoron aukuwar cuta ba, to ba'a lura da maganarsa. Idan kuwa ba haka ba to bai kamata a dau azumi ba.
749: Mahaifiyata kimanin shekaru sha uku kenan take fama da wata cuta, don haka ba ta iya yin azumi. Na san cewa dalilin rashin azumin nata yana da alaka da shan maganin da take yi ne. Tambaya ta a nan ita ce shin wajibi ne ta rama azumin da ta sha?

A: Matukar wannan gazawar nata ya samo asali ne daga rashin lafiya, to ba wajibi ne ta rama azumi ba.
T750: Saboda raunin jiki da nake da shi tun daga farkon lokacin balaga har zuwa shekaru sha biyu ba na yin azumi, to a halin yanzu mene ne hukumci na?

A: Wajibi ne ki rama azumin watan Ramalana da ba ki dauka ba saboda kin kai shekarar balaga. Idan kuma har shan ruwan (kin daukan azumin) azumin watan Ramalanan da kika yi da gangan ne ba tare da wata lalura ta shari'a ba, to kaffara ma ta hau kanki.
751: Wani likitan ido ya hana ni yin azumi yana cewa bai kamata in yi azumi ba saboda ciwon idon da nake tare da shi, to amma duk da haka sai ban yarda da wanann magana tasa ba na fara yin azumin. Amma na dinga samun matsaloli kala-kala, ta yadda a wasu ranakun zan yi azumin ba tare da jin wani ciwo ba, a wasu lokutan kuma na kan ji ciwo da yamma. To sai na shiga cikin damuwa da taraddadin shin ko in bar azumin ne ko kuma in hakura da zafin ciwon in ci gaba da azumin har faduwan rana. To tambaya a nan ita ce, shin tun farko ma wajibi ne in yi azumin? Sannan shin a ranakun da nake yin azumi a halin ina kokwanton zan iya kaiwa har faduwar rana ko ba zan iya ba to zan ci gaba da azumi ko a'a? Kana kuma yaya niyyata za ta kasance?

A: Idan har ka sami nitsuwa da kuma yakini kan maganar wani likita mai riko da addini, amintacce na cewa azumi zai cutar da idonka ko kuma ka zamanto kana tsoron cutuwa saboda azumi, to azumi bai wajaba a gare ka ba, kai bai ma halatta ka yi azumin ba. Ba ya inganta ka yi niyyar azumin idan kana tsoron zai cutar da kai, to amma idan ba ka tsoron wata cutarwa to babu matsala ga hakan, to amma kuma ingancin azumin naka ya ta'allaka ne da rashin cutarwar a hakika.
752: Ni na kasance ina amfani da tabarau ne na magani (wanda likita ya bani), a halin yanzu idanuwana sun yi rauni. Lokacin da naje wajen likita sai ya ce min matukar ban yi wani kokari ba (wajen magance matsalar idon) to za su ci gaba da raunana. To idan aka dauke min watan Ramalana wani hukumci ne ya hau kaina?

A: Matukar azumi zai cutar da idanuwanka, to ba wajibi ba ne ka dau azumi, kai wajibi ne ma ka sha ruwa. To idan kuma wannan cuta taka ta ci gaba har zuwa watan azumi na gaba, to rama azumin ma ba wajibi ba ne a gare ka. To sai dai wajibi ne ka ciyar da miskini guda na kowace rana guda da ka sha azumin.
754: A shekarar da ta wuce wani kwararren likita ya yi min tiyata a koda ta biyu inda daga baya ya hana ni yin azumi har zuwa karshen rayuwa ta, to amma a halin yanzu ba ni jin wata matsala, ina ci ina sha kamar da, ba na jin wani ciwo, to mene ne ya wajaba a gare ni?

A: Idan har kai kanka ba ka jin wani tsoron cewa azumin zai cutar da kai, kana ba ka da wata hujja ta shari'a a kan hakan to wajibi ne ka yi azumi.
755: Idan likita ya hana mutum yin azumi, to shin wajibi ne ya lizimtu da wannan magana tasa? Tattare da cewa wasu likitocin ba sa da masaniya kan hukunce-hukuncen shari'a. Shin aiki da maganarsa wajibi ne.

A: Idan har mutum ya samu nitsuwa da wannan magana tasa cewa azumi zai cutar da shi, ko kuma a sanadiyyar maganar likita sai ya ji tsoro kan cewa azumin zai cutar da shi, ko kuma hakan ya samu (wato tsoron cutarwa) daga wani sababi wanda masu hankali suka yarda da shi, to a wannan hali azumi ba wajibi ba ne a kansa.
766: Kananan tsakuwa sukan taru mun a cikin ....., kuma hanya guda kawai ta nesantar taruwarsu ita ce yawaita shan ruwa, wani likita mai kula da addini ya bayyana cewar lalle bai kamata in yi azumi ba. To a nan mene ne hukumcin da ya hau kaina dangane da azumin watan Ramalana?

Matukar magance wannan cuta ta ta'allaka ne da yawaita shan ruwa da sauran dangoginsa, to daukan azumi a gare ka ba wajibi ba ne.
767: Kamar yadda yake wajibi ne masu cutar sugari (diabetes) su dinga yin allurar insulin sau guda ko sau biyu a rana kamar yadda kuma wajibi ne su kula da yanayin yadda suke cin abinci ba tare da jinkiri ba don hakan zai zai haifar musu da matsaloli. Hakan ne ma ya sa wasu likitocin suke shawartarsu da su dinga cin abinci sau hudu a rana. Don haka muna so ka yi mana bayanin hukumcin azumin irin wadannan mutane?

A: Matukar sun san cewa nesantar abinci da abin sha tun daga fitowar alfijir har zuwa faduwansa zai haifar musu da matsala ko kuma suna tsoron hakan, to daukan azumi a gare su ba wajibi ba ne, kai bai ma halalta ba.



.
Copyright © 2018~2022.
( Uzairu Badamasi Sufi )
Harkarmusulunci@yahoo.com
All rights reserved

Bamu Da Alhakin Tallar Da Ake Sawa Akan Wannan Website Din