XtGem Forum catalog
Uzairu badamasi

BARKA DA ZUWA SHAFI MAI ALBARKA

Alhamdulillah muna muku albishir insha Allah zamu dawo aiki gadan gadan!


Shafin farko

Haidar Ali
ABUBUWAN DA SUKE BATA AZUMI

Ali Khamenei4

T:758: A tsakaiyar rana cikin watan Ramalana sakamakon waswasin Shaidan sai na yanke shawarar karya azumi na, to kafin in bata azumin sai na yi wani tunani sai na janye wannan shawarar da na yi, to mene ne hukumcin azumin nawa? Sannan kuma idan hakan ya faru ne a wata rana wacce ba ta watan Ramalana ba fa?

A: Matukar mutum ya kuduri aniyar bata azuminsa a wata rana ta watan Ramalana ta yadda ba ya tunanin ci gaba da azumin to azuminsa ya baci, sake shawarar ci gaba da azumin ba shi da wata fa'ida. To amma matukar shakka yake yi shin ya karya din ko kar ya karya, wato har ya zuwa yanzu bai yanke shawarar karya azumin ba ko kuma ya kuduri aniyar aikata wani aiki mai bata azumi amma bai riga da ya aikata ba. To a dukkanin wadannan halaye biyu akwai matsala cikin ingancin azumin nasa. Ihtiyati wajibi shi ne ya cika azumin daga baya kuma sai ya rama. Sauran azumin wajibi - irin su nazari na musamman da sauransu - hukumcinsu daya ne da wannan.
759: Idan mutum yana azumi sai jini ya fito masa a bakinsa, to hakan ya bata masa azumi ?

A: Hakan ba ya bata azumi, to amma wajibi ne ya kare wucewar jinin zuwa makogwaronsa.
760: Mene ne hukumcin shan taba da makamantanta yayin azumi?

A: Ihtiyati na wajibi ne shi ne mai azumi ya nesanci duk wani hayaki na taba da kuma muggan kwayoyi da ake jansu ta hanci ko kuma sanya su a kasar harshe.
762: Akwai wani nau'in magani da masu cutar 'athma' da suke da matsalar numfashi suke amfani da shi wanda ake fesa shi cikin baki wanda zai ba wa mara lafiya damar jan numfashi sosai. A wasu lokuta mara lafiyan yana bukatar amfani da irin wannan magani sau da yawa a rana guda, shin azumin mutumin da yake amfani da irin wannan magani ya inganta? Musamman bisa la'akari da cewa idan ba tare da wannan magani ba mai cutar ba zai iya yin azumi ba ko kuma zai zama da wahalar gaske.

A: Matukar dai wannan magani ya wuce makogwaro ko da kuwa iska ce dake tare da magani to akwai matsala cikin ingancin azumin. Sannan idan kuma yin azumi ba tare da amfani da wannan magani ba zai yiyuwa ba ko kuma akwai wahala cikin hakan, to ya halalta a yi amfani da shi. To sai dai ihtiyati shi ne kada ya aikata wani abu daga cikin abubuwan da suke karya azumi. Idan kuma har zai iya (ba tare da amfani da wannan abu ba) to zai rama azumin.
763: A mafi yawan ranaku yawun dake bakina ya kan zo ya hadu da jinin dake jikin labbana, a wasu lokuta ba na sanin shin yawun da nake hadiyewa yana hade da jinin ne ko a'a? To mene ne hukumcin azumina a irin wadannan ranaku? Ina fatan za ka min karin bayani.

A: Idan har jinin labben ya shige cikin yawun (ta yadda ba za a iya bambanta shi da yawun ba) to ana masa hukumci da tsarki, don haka hadiye shi babu matsala kuma ba ya bata azumi. Haka nan idan ana shakkun kasantuwan yawun da jinin, to babu wata matsala cikin hadiye shi kuma ba ya bata azumi.
764: Wata rana daga cikin ranakun watan Ramalana na dauki azumin watan Ramalana to amma bayan suhur sai ban wanke bakina da man goge baki ba to sauran abincin da ya saura a baki na ya wuce zuwa cikina, ba da so na ba to shin wajibi ne in rama azumin wannan rana?

: To idan har ba ka san da kasantuwar sauran abincin a jikin hakwaranka ba ko kuma ba ka san ya wuce zuwa makogoronka ba, kana kuma ba da gangan ka hadiye ba, to rama azumi a gare ka ba wajibi ba ne.
765: Mutumin da jini ya kan yawaita fitowa a jikin lebbensa, shin azuminsa ya karye? Sannan kuma shin zuba ruwa a kansa ta hanyar amfani da wani kwano ya halalta?

A: Fitan jini daga lebben mutum matukar ba a hadiye ba ba ya bata azumi. Haka nan zuba ruwa a kai ta hanyar amfani da kwano ko makamancinsa ba ya bata azumi.
767: Muna bukatar ka yi mana bayani kan hukuncin yin allura yayin da mutum yake cikin azumin watan Ramalana?

A: Babu wata matsala ga yin allura sai dai in allurar ta kasance ta sanya wa maras lafiyan abinci ne, to bisa lhtiyati wajibi ne a nesance ta yayin da ake azumi.
770: Mene ne hukumcin mijin da ya bukaci yin jima'i da matarsa cikin watan Ramalana sannan kuma ta amince?

A: Hukumcin shan azumi da gangan ya hau kansu, don haka baya ga rama wannan azumi kaffara ta hau kansu dukkansu biyun.
771: Mutumin da ya yi wasa da matarsa cikin ranakun watan Ramalana, shin hakan yana cutar da azuminsu?

A: Matukar dai hakan bai kai su ga fitar da maniyi ba, to babu abin da ya sami azuminsu. Amma idan har maniyi ya fito, to hakan bai halalta ba kuma yana karya azumi.



.
Copyright © 2018~2022.
( Uzairu Badamasi Sufi )
Harkarmusulunci@yahoo.com
All rights reserved

Bamu Da Alhakin Tallar Da Ake Sawa Akan Wannan Website Din