BARKA DA ZUWA SHAFI MAI ALBARKA
Alhamdulillah muna muku albishir insha Allah zamu dawo aiki gadan gadan!
Haidar Ali
GANGANTA ZAMA CIKIN JANABA
T772: Idan mutum ya zauna cikin janaba (saboda wasu wahalhalu) har aka kira sallar asuba, to shin ya halatta ya yi azumi a wannan ranar?
A: Babu wata matsala ga azuminsa idan dai azumin ba na Ramalana ko ramakonsa ba ne, to amma a azumin Ramalana ko ramakonsa, idan har ba zai iya wanka ba ne to dole ne ya yi taimama, idan har ya bar taimama, to azuminsa ba ya inganta.
773: Idan mutum ya yi azumi na wasu ranaku alhalin yana cikin janaba ba tare da ya san cewa tsarki daga janaba yana daga cikin sharadin azumi ba, to shin wajibi ne ya yi kaffaran wadannan ranaku da ya yi azumi a cikinsu da janaba, ko kuma ramakonsu kawai ya wadatar?
A: Dangane da yanayin da aka fadi ramako kawai yana wadatarwa.
774: Shin ya halalta mutumin da ya wayi gari (wato fitowar alfijir) cikin janaba ya yi wanka ya dauki azumin ramako ko na mustahabi?
A: Matukar mutum da gangan ya ci gaba da zama cikin janaba har alfijir ya keto, to azumin watan Ramalana da ramakonsa ba ya inganta a gare shi. To sai dai bisa karfaffiyar magana sauran azumi suna inganta a gare musamman azumin mustahabi.
775: Mutum ne ya tafi bakunta cikin watan Ramalana, to cikin tsakiyan dare sai ya yi mafarki, to don saboba shi bako ne ba shi da wasu tufafi, don haka sai ya kuduri aniyar yin tafiya washe gari don gudu daga azumin. To bayan kiran sallar asuba sai ya fito don yin wannan tafiya ba tare da aikata wani abin da ke bata azumi ba. Tambaya a nan ita ce: Shin kudura anniyar tafiya a wajen wannan mutum yakan sauke masa yin kaffara ko kuwa?
A: Kudura anniyar tafiya cikin dare kawai ba ya wadatarwa haka kuma yin tafiya da rana bai wadatarwa wajen kaffara daga gare shi idan har ya wayi gari cikin janaba-tattare da cewa ya san yana da janabar- ba tare da ya gaggauta yin wanka ko taimama kafin fitowar alfijir ba.
776: Shin ya halatta ga wanda ba shi da ruwa ko kuma dai wasu uzurorin na daban da suke hana wankan janaba (banda kurewar lokaci) da ya yi janaba da gangan cikin watan Ramalana?
A: Hakan yana halatta a gare shi idan har abin da ya hau kansa shi ne taimama, kana kuma yana da cikakken lokaci na yin taimamar bayan da ya yi janabar.
777: Mutum ne cikin watan Ramalana ya farka gabannin kiran sallar asuba, to amma bai san cewa ya yi mafarki ba, sai ya koma da barcinsa, to sai yayin da ake kiran sallar asuba ya gane cewa ya yi mafarki kuma ya tabbatar da cewa mafarkin nasa ya yi shi ne kafin kiran sallar, to mene ne hukuncin azuminsa?
A: Idan har bai gano hakan (wato janabar) ba kafin kiran sallar asuba din, to azuminsa ya inganta.
778: Idan mutum ya farka daga barci kafin kiran sallar asuba na watan Ramalana to sai ya ga ya riga ya yi mafarki, to amma sai ya ci gaba da barcinsa yana mai fatan cewa zai sake tashi don yin wanka, to amma sai ya wuce bai yi wanka ba har zuwa bayan fitowar rana wato ya jinkirta yin wankan har zuwa lokacin sallar azahar sannan ya yi wanka ya yi salla to shin mene ne hukuncin azuminsa?
A: Dangane da wannan tambaya wajibi ne ya rama wannan azumi, haka nan ihtiyati mustahabi shi ne ya yi kaffara daga baya.
779: Idan mutum ya yi shakka kafin kiran sallar asuba na watan Ramalana kan cewa shin ya yi mafarki ko kuma, to amma bai kula da wannan shakka tasa ba ya ci gaba da barcinsa, to sai dai da ya farka bayan kiran salla sai ya ga ashe ya yi mafarkin kuma kafin kiran sallar ne. To mene ne hukuncin azuminsa?
A: Idan har a farkawar tasa ta farko bai ga wata alama na mafarki ba, kawai tsammani ne yake yi, ba tare da ya tabbatar ba to azuminsa ya inganta, ko da kuwa daga baya ya bayyana masa cewa mafarkin ya yi shi ne kafin kiran sallar.
780: Idan mutum ya yi wanka da ruwa mai najasa a cikin watan Ramalana, to sai bayan sati guda sai ya fahimci cewa ruwan da ya yi wankan da shi mai najasa ne, to mene ne hukuncin azumi da sallarsa cikin wannan lokaci?
A: Sallarsa batacciya ce wajibi ne ya sake ta, to amma azuminsa ya inganta.
782: Idan mutum ya kwanta kafin kiran sallar asuba ko kuma bayansa sai janaba ta same shi cikin barci kuma bai farka ba sai bayan kiran salla, shin yana wani lokaci yake da shi na yin wanka?
A: A bisa yanayin wannan tambaya, janabar da yayi ba ta bata masa azumin wannan rana ba, to sai dai wajibi ne ya yi wanka don yin salla. Yana ina jinkirta wankan har sai lokacin da zai yi sallar.
783: Idan mutum ya mance yin wankan janaba don azumin watan Ramalana ko kuma sauran azumi na daban, sai tsakiyar rana ya tuna da hakan, to mene ne hukumcinsa?
A: Idan har aka mance yin wankan janaba cikin dare har alfijir ya keto wato mutum ya wayi gari da janaba to azuminsa na watan Ramalana ya baci, kuma bisa ihtiyati zai rama wannan azumi. To amma dangane da sauran azuma kuwa to azuminsa ba ya baci.
.
Copyright © 2018~2022.
( Uzairu Badamasi Sufi )
Harkarmusulunci@yahoo.com
All rights reserved