XtGem Forum catalog
Uzairu badamasi

BARKA DA ZUWA SHAFI MAI ALBARKA

Alhamdulillah muna muku albishir insha Allah zamu dawo aiki gadan gadan!


Shafin farko

Haidar Ali
FITAR DA MANIYYI DA GANGAN

Ali Khamenei4

T784: Mene ne hukumcin mutumin da ya karya azuminsa ta hanyar wasan jin dadi (da azzakarinsa) har ya fitar da maniyyi (istimna') ko kuma ta hanyar cin wani abu ko shan wani abu na haramun?

A: Dangane da wannan tambaya wajibi ne ya yi azumi guda sittin ko kuma ya ciyar da miskinai sittin. Ihtiyati mustahabi shi ne cewa ya hada dukkanin biyun.
785: Idan mutum ya san cewa istimna'i yana karya azumi amma da gangan sai ya aikata haka. To shin hada kaffarori ya wajaba a kansa?

A: Matukar ya yi istimna'i da gangan sannan kuma maniyi ya fito masa, to hada kaffarori bai wajaba a kansa ba, to sai dai bisa ihtiyati na mustahabi ya hada kaffarorin.
786: A cikin watan Ramalana ne ba tare da kasantuwar wata alama ta istimna'i ba, kawai saboda ina magana ne ta wayar tarho da wata mace muharrama ta sai kawai na ji maniyyi yana zubo min. To bisa la'akari da cewa tattaunawar da muke yi ba da nufin jin dadi ba ne, ina son don Allah a amsa min wadannan tambayoyi nawa: Shin azumina ya baci ko kuma a'a? Idan har ya baci to shin kaffara ya hau kaina ko kuma a'a?

A: Matukar fitan maniyyi sakamakon magana da wata mace ba shi daga cikin al'adarka, sannan kuma maganar taka ba da niyyar jin dadi ko motsa sha'awa ba ne, wato a takaice dai maniyyin ya fito maka ne ba tare da nufi ba, to ba ya bata azumi, babu kuma wani abin da ya hau kanka.
787: Mutum ne ya saba shekara da shekaru yana yin istimna'i cikin watan Ramalana da ma waninsa. To mene ne hukumcin salla da azuminsa?

A: Istimna'i dai haramun ne, idan har ya kai ga fitan maniyyi to wankan janaba ta hau kan mutum. Idan kuwa har hakan ya faru ne a cikin ranar watan Ramalana to hukumcinsa hukumci ne na karya azumi da haramun. Idan kuwa kuma aka yi salla da azumi da janaban ba tare da wanka ko taimama ba, to salla da azumin ba su yi ba wajibi ne a rama su.
789: Shin istimna'in mace ga mijinta ana kirga shi cikin istimna'i na haramun ne?

A: Hakan ba ya daga cikin istimna'i na haramun.
790: Shin yana halalta ga mutumin da likita yake son diban maniyyinsa don gwaji sannan kuma babu wata hanya da za a sami maniyyin sai ta hanyar istimna'i, yayi istimna'in?

A: Matukar dai maganin ya ta'allaka ne da hakan, to babu matsala.
791: Wasu asibitoci sukan bukaci mutum yayi istimna'i don su debi maniyyinsa su gwada ko yana iya haihuwa ko kuma a'a. Shin wannan istimna'in ya halalta?

A: Istimna'i dai ba ya halalta ko da kuwa don gano karfin mutum wajen haihuwa ne, sai dai idan har hakan ya zama wajibi.
791: Mene ne hukumcin tunani da nufin janyo sha'awa a wadannan yanayi biyu:
a) Tunanin matan mutum.
b) Tunanin wata mace ta daban.

A: A yanayi na farko matukar dai babu wani haramun din da ya biyo bayansa kamar fitan maniyyi to babu matsala. Amma a yanayi na biyu ihtiyati shi ne a nesance shi.
793: Mutum ne mai azumi cikin watan Ramalana sai ya kalli wani abu mai ta da sha'awa har ta kai ma yayi janaba. Shin hakan ya bata masa azumi?

A: Idan har kallon nasa da nufin fitar da maniyyi ne ko kuma ya san cewa matukar ya kalli wannan abu to zai zubar da maniyyin (zai yi janaba) ko kuma haka al'adarsa take, to sai da gangan ya kalli wannan abu kuma yayi janaba. To hukumcinsa hukumci ne na mutumin da ya yi janaba da gangan. Wato wajibi ne ya rama azumin ya kuma yi kaffara.
794: Mutum ne mai azumi sai ya yi abubuwan da suke karya azumi ba sau da yawa a rana guda, to mene ne hukumcinsa?

A: Kaffara guda ce kawai ta hau kansa. Koda yake bisa ihtiyati na wajibi idan har wannan abin da ya aikata yana da alaka da jima'i ne ko kuma istimna'i ya ba da kaffara gwargwadon adadin da ya aikata din.



.
Copyright © 2018~2022.
( Uzairu Badamasi Sufi )
Harkarmusulunci@yahoo.com
All rights reserved

Bamu Da Alhakin Tallar Da Ake Sawa Akan Wannan Website Din