Polaroid
Uzairu badamasi

BARKA DA ZUWA SHAFI MAI ALBARKA

Alhamdulillah muna muku albishir insha Allah zamu dawo aiki gadan gadan!


Shafin farko

Haidar Ali

Kyawawan Halaye

Ali Khamenei2

Manzon Allah (s.a.w.a) ya
ce:-
ﺧﻴﺎﺭﻛﻢ ﺃﺣﺎﺳﻨﻜﻢ ﺃﺧﻼﻗًﺎ
ﺍﻟﺬﻳﻦ َ ﻳﺄﻟﻔﻮﻥ ﻭﻳُﺆﻟﻔﻮﻥ
"Zababbun cikinku su ne
wadanda suka fi ku
kyawawan dabi'u,
wadannan da suke da sakin
fuska, don haka mutane ke
neman kulla abokanta da
su".
(Tuhaful-Uqul shafi na 45).
*****
Mafi alherin cikinku shi ne
mutumin da alakarsa da
sauran mutane take da
kyau sama da ta sauran
mutane. Yana da sakakkiyar
fuska ta yadda jama'a za su
so kusantarsa.
Wannan hadisi ba yana
nufin za a fifita wani
mutum don kawai yana da
sakin fuska da iya cudanya
da mutane amma baya kula
da ayyukan ibadu da suke
wajibi a kan mutumin da
yake gudanar da ayyukan
ibadunsa na addini amma
baya da sakakkiyar fuska
ba. Abin da ake nufi shi ne
muminin da yake gudanar
da ayyukan ibadunsa yadda
ya kamata sannan ga
kyawawan dabi'u shi ne za
a fifita shi a kan muminin
da ba ya da kyawawan
dabi'u.



.
Copyright © 2018~2022.
( Uzairu Badamasi Sufi )
Harkarmusulunci@yahoo.com
All rights reserved

Bamu Da Alhakin Tallar Da Ake Sawa Akan Wannan Website Din