Lamborghini Huracán LP 610-4 t
Uzairu badamasi

BARKA DA ZUWA SHAFI MAI ALBARKA

Alhamdulillah muna muku albishir insha Allah zamu dawo aiki gadan gadan!


Shafin farko

Haidar Ali
HUKUNCE- HUKUNCEN SHAN RUWA

Ali Khamenei4

T795: Shin bin Ahlussunna wajen shan ruwa yayin da mutum yake tare da su yana halatta? Kana mene ne ya wajaba kan mutum idan har ya ga cewa yin hakan ya fita daga cikin takiyya, kuma bai kasance dole ba?

A: Ba ya halatta ga mukallafi ya bi wani wajen shigan lokacin shan ruwa. Amma idan saboda takiyya ne to yana halalta a sha ruwan, sai dai akwai ramuwar wannan azumi. Ba ya halatta gare shi idan har yana da zabi ya sha ruwa har sai ya tabbatar da faduwar rana shi da kansa ko kuma ta hanya ta shari' a.
796: Idan ina azumi sai mahaifiya ta tilasta mini cin wani abu ko shan wani abu, shin azumina ya baci?

A: Ci ko sha yana bata azumi ko da kuwa bisa bukata ko tilascin wani mutum na daban ne.
797: Idan wani abu ya shige bakin mai azumi ba bisa radin kansa ba ko kuma ya nitsar masa da kansa cikin ruwa, shin azuminsa ya baci? Sannan kuma idan aka tilasta wa mutum bata azuminsa, misali wani yace masa idan ba ka karya azuminka ba zan cutar da kai ko kuma dukiyarka, to don guje wa wannan cutarwar sai ya ci abinci, shin azuminsa ya inganta?

A: Azumin mai azumi ba ya baci idan wani abu ya shige bakinsa ba bisa nufinsa ba ko kuma aka shigar da kansa cikin ruwa ba bisa radin kansa ba. To sai dai idan shi da kansa ne ya karya azumin nasa saboda barazana ko tilascin wani to azumi ya baci.
798: Idan mutum ya jahilci hukuncin rashin halaccin shan ruwa kafin karkatan rana zuwa yamma (zawali) idan har bai isa ga "Haddil tarakhus" (Wato wajen da ake ganinsa a matsayin karshen gari), sai ya sha ruwa kafin isa ga haddin tarakhus don ganin cewa shi matafiyi ne, to mene ne hukuncin wannan mutum, shin ramuwa ce ta hau kansa, ko kuma akwai wani hukumcin?

: Hukuncinsa kamar hukuncin shan ruwa da gangan ne.
799: Yayin da nake fama da mura majina ta kan taru min a baki, to maimakon in zubar da ita sai na hadiye, to shin azumina ya inganta ko kuma? Kana kuma a wasu ranaku na watan Ramalana na kasance a gidan wani dangimmu ne, to a dalilin mura da kuma kunya sai na gaza yin wankan wajibi sai dai taimama, ba na yin wanka har sai kusan sallar azahar, kuma na ci gaba da yin hakan har na tsawon lokaci to shin azumina sun inganta a wadannan ranaku ko kuma?

A: Babu abin da ya taba maka azuminka daga wannan hadiye majina da ka yi, ko da yake lhtiyati shi ne ka rama azumin idan har hakan ya kasance bayan majinan ta isa sararin bakinka, to amma barin wankan janabar da ka yi kafin alfijir ya fito, da kuma yin taimama a maimakonsa, idan har uzurin naka uzuri ne da shari' a ta yarda da shi, ko kuma taimamar taka ta kasance ne a karshen lokaci saboda karancin lokaci, to azuminka ya inganta, in kuwa ba haka ba ne to azuminka a wadannan ranaku sun baci.
800: Ni ina aiki ne a masana'antar (tono) karfe kuma yanayin aikinmu ya sanya a duk lokacin da na fara aiki da kayayyakin aikin wajen kura ta kan shiga min baki, haka yanayin aikin namu yake tsawon shekara. To a nan mene ne hukumcin da ya hau kaina?

A: Hadiye kura (wucewarta makogwaro) ta kan bata azumi don haka wajibi ne a nesance ta. To sai dai shigar kura baki da hanci kawai ba tare da ta wuce makogwaro ba, ba ta bata azumi.



.
Copyright © 2018~2022.
( Uzairu Badamasi Sufi )
Harkarmusulunci@yahoo.com
All rights reserved

Bamu Da Alhakin Tallar Da Ake Sawa Akan Wannan Website Din