pacman, rainbows, and roller s
Uzairu badamasi

BARKA DA ZUWA SHAFI MAI ALBARKA

Alhamdulillah muna muku albishir insha Allah zamu dawo aiki gadan gadan!


Shafin farko

Haidar Ali
KAFFARAR AZUMI DA KUMA GWARGWADONTA

Ali Khamenei4

T801: Shin bayar da kudi gwargwadon mudu na abinci ga fakiri don ya sayi abincin da kansa (yayin kaffara) yana wadatarwa?

A: Idan har yana da nitsuwa kan cewa wannan fakirin zai wakilce shi ya sayi abincin da wannan kudi daga bisani ya mallaki abincin a matsayin kaffara, to babu wata matsala ga hakan.
803: Macen da saboda ciki da kuma kusatowar lokacin haihuwarta ba za ta iya daukan azumi ba amma ta san cewa wajibi ne ta rama azumin bayan haihuwarta kuma kafin shigowar watan Ramalana na gaba. To amma da gangan ko kuma ba da gangan ba sai ba ta yi azumin ba, to shin kaffaran wannan shekarar ne kawai ya hau kanta ko kuma har na shekarun da ta yi ba ta rama azumin ba?

A: Kaffaran jinkirta rama azumin watan Ramalana na shekara guda ne ko da kuwa shekarun sun yi yawa. Kaffarar kuwa ita ce ciyar da mudu guda na abinci ga kowace rana. Ana yin hakan ne kuwa idan har mutum ya jinkirta rama azumi har wani azumin ya zo da gangan ba tare da wani uzuri na shari'a ba. Amma idan har akwai wani uzuri na shari'a da zai hana rama azumin to babu kaffarar a kan mutum.
804: Macen da aka dauke mata azumi saboda rashin lafiya, kuma ba ta samu daman rama azumin ba har watan azumi na gaba ya iso, to a irin wannan hali shin kaffarar yana kanta ne ko kuma yana kan mijinta?

A: Idan har dalilin shan ruwan azumin nata ya samo asali ne saboda rashin lafiya sannan jinkirin ramuwar ma saboda ci gaban rashin lafiyan ne, to a irin wannan hali wajibi ne ta ba da mudu guda na abinci a madadin kowace rana, kuma hakan bai hau kan mijinta ba.
805: Mutum ne yake da ramakon azumi na kwanaki goma, to sai a rana ta ashirin na watan sha'aban ya fara azumi, to shin a irin wannan hali zai iya karya azumin da gangan kafin "zawali" ko kuma bayansa? Kuma idan ya karya, to shin mene ne gwargwadon kaffararsa idan da ya karya azumin kafin zawali ne ko kuma bayansa?

: A irin wannan hali ba ya halatta ya karya azumin da gangan, to amma idan ya karya da gangan, idan kafin "zawali" ne to babu kaffara a gare shi, idan kuwa bayan "zawali" ne, to kaffara ta hau kansa, wato ciyar da miskinai goma, idan kuwa hakan ya gagara, to sai ya yi azumin kwanaki uku.
806: Mace ce ta kasance tana da ciki cikin watan Ramalana na shekaru biyu a jere sannan kuma ba ta da karfin yin azumi cikin wadannan ranaku, to sai dai a halin yanzu tana iya yin azumin, mene ne hukumcinta? Shin kaffara biyu sun kama ta ko kuma kawai ramuwa ta wadatar?

A: Idan har saboda wani uzuri na shari'a ne ba ta dauki azumin watan Ramalanan ba to ramuwa ce kawai ta wajaba a kanta. Idan kuwa rashin daukan azumin da ba ta yi ba ya samo asali ne bisa tsoron da take da shi cewa azumin zai iya cutar da dan nata, to bayan ramuwa wajibi ne ta ba da mudu guda na abinci a madadin kowace rana. Idan kuwa ta jinkirta ramuwar har sai bayan wani watan Ramalanan na wata shekarar ba tare da wani uzuri na shari'a ba, to wata ciyarwar ta daban ma ta hau kanta, wato wajibi ne ta ba da mudu guda ga wani fakiri a madadin kowace rana.
807: Shin kiyaye bibiye tsakanin ramuwa da kaffara yayin kaffarar azumi wajibi ne?

A: Hakan ba wajibi ba ne.



.
Copyright © 2018~2022.
( Uzairu Badamasi Sufi )
Harkarmusulunci@yahoo.com
All rights reserved

Bamu Da Alhakin Tallar Da Ake Sawa Akan Wannan Website Din